ya tashi yana niyar fita, yazata baba zai dakatar dashi amma yaga har yakai bakin ƙofa baba baice komai ba,
sai kawai yadawo yashi ga yin murmushi tare da tsugunna wa agaban babba yafara roƙon sa akan dan Allah ya taimaka suje tare baba kuma yaƙi amincewa de da haka baiyi ƙasa agwiwa ba yaci gaba da lallaɓa baba da haka har yasamu yayi nasara baba yace zaije ammade shi bazaije can ɓangaren wajen Fulani ba saidai yasan duk yanda zaiyi idan yarinyar ta fito sai su haɗu amma shide bazaije can ba wannan matar ta gansa tasaka aci mutuncin sa shiyasa duk wani abu idan zaiyi yake taka tsantsan baya yarda su haɗa hanya da ita indai ba dole ba wani abun ya haɗasu ba shima bada son ransa ba shiyasa yanzuma yace bazai je can ba saidai ita yarinyar idan tafito sai su haɗu,
Sosai hamza yayi murna da hakan ma yace ni baba ai indai zakayi mata magana to koma tayayane zakaganta yanzude bari in shirya sai mufita tare inyaso sai ka tsaya daga ɗan baya ni kuma zanje har inda take in taho da ita ko agaban wa take,
Allah ya shirye ka nidai na matsu inji abun da yasa ka raina matar nan baka jin tsoron ta kwata kwata abun naka har mamaki yake ban wallahi gashi kullum abun naka gaba yake ba ya raguwa baka shakkar ta ko kaɗan,
"Hhhhh baba kenan kabari very soon zakaji komai ka kwantar da hankalin ka so nake ta kaini ƙarshe inci mutun cinta agaba kowa wallahi nifa ahakan ma ni nake haƙuri da abun da take min nake daga mata ƙafa amma akwai ranar da zan danneta tagane bata da wayo,
"to Allah ya kyauta ni ai yanzu kafi ƙafina Hamza saidai kawai inci gaba da yi maka addu'a Allah ya shiryeka sannan kuma inci gaba da zuba ido inga ƙarshen wannan cika bakin naka,
"Wallahi baba ba cika baki bane amma de shikenan kawai abar kaza cikin gashinta abar wannan maganar bari inji insake wanka saboda gudun raini kaima kuma baba sai canza kaya dan baza muje dakai ahaka ba,
Kade san idan aka ganni da wasu kayan ba kayan aiki ba kuma ina yawo akwai matsala dan haka kabarni inke ahaka ni bana ƙarya kaide da kake da ƴancin canzawa sai kai ta canzawa amma nidai kabarni haka sai nafi jin daɗin fitar ma inkuma baka yarda shikenan sai inyi kwanciyata ince adawo lafiya,
"A'a baza ayi haka bama shikenan muje ahaka ɗin nidai kam sai na canza yana gama faɗar haka yashige cikin bandakin,
bai jima ba ya fito jakar kayan sa ya ɗauko yazaro wani yadi fari tass me laushi daga gani ma me tsadane ya ɗauko ya saka aka dauko hula itama aka saka yafito dos dashi kamar sabon ango,
Shidai baba yana zaune ya zubawa sarautar Allah ido duk inda yayi sai yabisa da kallo har yagama shirya wa yaɗauko turare ya feshe jikin sa dashi take ɗakin ya kauraye da ƙamshi,
saida yagama shirya wa tsaf sannan ya kalli baba "yace baba ya kaganni zan burgeta idan taganni,
"Ah ba dole ba irin wannan kyau haka a ina kasamu kayan nan nidai tunda muke bantaɓa ganinsa ba,
wata ƙayatacciyar dariya hamza yasake sannan yace lalle baba kana wasa dani iya haɗuwata da ita nasa aka ɗin ko min su baka gansuba sababbi ai yanzu nafara ɗinkuna agidan nan tunda na haɗu da ita kuma ai magana ta ƙare yanzude duk ba wannan ba baba kar kwalliya ta 5a fara samun mushkila taso mutafi,
shide baba yau yana ganin abun mamaki da farko in akace masa Hamza zai iya yin irin waɗannan abubuwan bazai yarda sai gashi yanzu nema yake yafi ƙarfin tunanin sa,
Miƙewa yayi yana riƙe baki ganin irin takun da hamza yake yana dariya suka fito daga ɗakin atare suka nufi hanyar can cikin masarauta saboda tsakanin su da ɓangaren masu gida da tazara dan haka dole sai baba yaƙara gaba sosai kafin yasamu inda zai tsaya ya jirasu,
________Azeema
tana zaune gaban Fulani tana yi mata tausa zuwa yanzu tasaba da gidan amma akullum cikin kyalla ido take ko zata ga mahaifin ta amma shiru bata taɓa haɗuwa dashi ba dan hartafara fidda rai da ganin sa kuma yanzu ba koda yaushe take samun loƙacin kantaba ko da yaushe suna tare da fulani tana yi mata bauta wataran ma idan papa baya ɗakin kusan kwanan zaune take wajen yi mata bauta itace ɗauko wannan ɗauko wancen share nan goge nan duk wani aiki ya dawo gurin ta girkine kawai ba abarta tayi ba saboda ba ayarda da ita ba sosai baza a iya bata girki ba saboda tsaro,
idan tagama wannan wahalar kuma loƙacin da takeso ta keɓe tayi waya da yaya saleem sai ɗayar me aikin da suke kwana ɗaki ɗaya sai ta hanata tun abun baya damunta har ta fara shiga damuwa ta fara tunanin ma kamar da gayya ake mata haka ba aso aganta ita kaɗai shiyasa gaba ɗaya yanzu ta canza gata nan sai ahankali goma da ashirinne suka haɗar mata ga rashin ganin mahaifin ta ga kewar su mama da take ita da saleem tana son kiran sa amma babu dama hakan ya gagara ga kuma masoyin ta datake ta son gani kuma shima basu ƙara haɗuwa ba zuwa yanzu tasan ba aljani bane saboda Fulani ma ta taɓa sakata take ta gyara part ɗin sa batare da ya sani ba amma kuma da taje ta gagga hotunan sa da hakan yaƙara tabbatar mata ba aljani bane kuma ɗan gidanne amma haɗuwar su tayi wuya, ji take kamar ta bar gidan amma ba dama dole taci gaba da zaman gidan,
tana zaune awajen sukaji an turo ƙofa batare da anyi nocking ba fulani ce ta fara dagowa dan ganin me shigowa dan atunanin ma ko mutumin natane da yasaba shigowa kai tsaye amma sai taga akasin haka zuba masa ido tayi tundaga sama har ƙasa tana mamakin abun da ya shigo dashi kai tsaye batare da ambasa iznin shigowa ba ga kuma kalar shigar da take jikin sa to me yake nufi da hakan, shiru de tayi bata tanka masa ba tana jiran taga iya gudun ruwan sa,
Azeema kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta daga gare sa itama de tayi mamakin ganin sa cikin irin wannan shigar bayan kuma tasan shima bawane agidan wata zuciyar ce ta shiga ce mata kikasani ko ba abun dakike tunani bane wataƙil ba ɗan aiki bane tunda har yayi irin wannan shigar gashi kuma ya shigo kansa tsaye batare da ko sallama ba kuma bataji Fulani tace mata komai ba dan haka tayi saurin kawar da tunanin sa taci gaba da abun da takeyi,
ahankali ya shiga takawa ko takalmin ƙafar sa bai cire ba yake takawa zuwa inda suke yana zuwa gaban su batare da ya kalli inda fulani take ba yace minti biyar ina son magana dake in ba damuwa mu ɗan je waje ko ɗagowa batayi ba bare yasa ran amsawar ta duk da tasan da ita yake amma sai ta nuna batama san yanayi ba,
fulani kam mamaki yagama kashe ta a zaune tana tunanin yaushe yaron nan ya riƙa irin haka yaushe rashin mutun cin nasa yakai haka abun har yakai yashigo mata guri batare da izinin taba kuma har cikin falon ta da takalmi kuma yazo yana magana da wata daban agaban ta lalle wannan yaron yagama riƙa yaukam yakaita ƙarshe sai ta nuna masa asalin kalarta abun nasa yayi yawa batasn meyasa ya rainataba haka amma yau zata sauke masa duk wani hauka da yake damun kansa duk abun da yake masa yawo akansa zata saita masa shi dan sai ya fuskanci mugun hukunci sai yayi nadamar sanin ta arayuwar sa sai tasa ya tsani kansa,
"magana nake dan Allah kizo ba daɗewa zakiyi ba zaku zaku gaisa ne da mahaifina shi yazo har inda kike idan zai ne ma min auren ki amma yace yana son ganin ki yanzu ɗan Allah ki taimaka kar ki watsamin ƙasa a ido kizo muje,
da mamakin jin furucin sa ta ɗago ta kalle sa jin ya ambaci mahaifin sa to me wannan mutumin yake nufi da ita bata gama tunanin ba taji fulani ta kwace ƙafar ta daga hannun ta hakan yasa ta katse tunanin ta ta maida duban ta ga Fulani,
cikin ɓacin rai fulani ta ɗaga hannu zata kifa masa mari amma sai akai rashin sa'a ya cafke hannun ta tare da nunata da yatsa yace kar ki kuskura hannun ki ya taɓa min fuska ba gurin ki nazo ba dan haka kar kishiga hurumin da ba naki ba ki tsaya amatsayin ki idan kuma bahaka ba hmmm yafaɗa yana girgiza kan sa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa irin ba mutun cin nan,
"tsugunna yayi gaban Azeema tare da kai ƙafafun sa ƙasa ya shiga roƙon ta da yi mata magiya kawar da kanta tayi gefe daga ƙarshe ma sai kawai ta miƙe tsaye zata bar wajen yayi saurin kamo hannun ta aikam tana juyowa ta sauke masa tafikan hannun ta afuskar sa tare da nuna shi da yatsa murya kamar zatayi kuka tace dan Allah ka rabu dani ka rufamin asiri nace bana sonka ko anaso dole ne so ko sokake sai kajawo min wata masifar ina zaman zamana bandaɗe da zuwa gidan nan ba amma kabi ka uzzirawa rayuwata tunda nazo kake takura min dan Allah karabu dani haka,
safe gurin da ta mare shi yayi tare da shafar wajen saidai yana shafi gurin sai yayiwa hannun sa kiss tare da sakin murmushi sannan yace daman idan budurwa ta mareka to marin soyayya ne dan haka ni banji zafi ba kuma duk abun da kike faɗa baidame ni ba dan haka kar ki zata wai zandena abun da nake zanci gaba daga nan har loƙacin da zaki fara sona nidai yanzu buƙata ta ɗayace kizo muje inkuma sai na ɗaukeki ne to zan iya ba abune me wuya ba agurina,
Kai karamin marar kunya ɗan iska uban wa kake nunawa fistara anan gurin kai ɗan gidan uban waye da uban me kake taƙama uban wa ya tsaya maka da kake gadara dashi ɗan matsiyata matalauci tsintacce kai har kana da damanr da zakaringayin abun daka ga dama anan to wallahi kaci ƙarya ka kwana da yunwa yau sai naga uban wanda ya tsaya maka adoron duniyar nan sai na wulaƙanta ka sai masa ka kwashi kashin ka a ahannu,
dariya ya shiga yi mata saida yayi me isarsa sannan ya shiga nunata da hannu yace saidai mu kwashi kashin mu tare nikuma bari ingaya miki wani albashir da baki sani ba daga ranar da kikayi ƙoƙarin aikata wanj mugun abun akaina nikuma ranar za tona miki asiri kowa sai yasan ko ke wacace acikin gidan nan kinsan kuma daga loƙacin zaman ki anan ya ƙare ko angaya miki ba wanda yasan abun da kika shirya to idan kin manta intuna miki kibi ahankali tsohuwa ina tausayin ranar da asirin ki zai tonu kuma inbakiyi wasaba ni da kaina zan tonashi abu shekara da shekaru da ba wanda yasani awa ɗaya tak ta isa insaka kowa yasani dan haka kibini ahankali kar kiƙara shiga sabgata kiyi rayuwar ki inyi tawa sai mu zauna lafiya ina fatan kin gane yauwa abu na ƙarshe ina so kisaka wannan yarinyar mutafi tare zan fita ina jiranta awaje wannan umarnine ba taimako nake nema ba idan kunne yaji jiki ya tsira yana kaiwa nan yayi gaba,
wani mugun fitsari Fulani taji ya taho mata ga uban zufa datagama wanke ta loƙaci guda kwakwalwar ta tadena aiki ta rasa wane irin tunani zatayi kuma takasa furta koda da kalma ɗaya ce da lalibe tasamo kan kujera tayi saurin zama gudun karda ta faɗi har ta manta da gargaɗin sa na ƙarshe sai yanzu ya faɗo mata da sauri tayi wa Azeema nuni da ƙofa alamun taje batare da ta iya haɗa ido da itaba,
Azeema da itama kanta yagama ɗaurewa da wannan lamarin da bata taɓa zaton sa ba ko a mafarki sai gashi a zahiri yau fulani ce gaba wani yaro yagama gaya mata magana son ransa ya kuma tafi abunsa duk ƙarfin izzarta da mulki amma ta rabu dashi to wannan wane irin sirri ne da bata son kowa yasani to shi ya akaima yasani no wonder taga yana abun da yaga dama ashe akwai abun da yasani game da ita shiyasa yake abu kansa tsaye, wani tunani ne ya faɗo mata hakan yasa ta sakin kayataccen murmushi ko me ta tuna oho mata,
da sauri ta nufi hanyar fita saidai tundaga bakin ƙofa tahango yanda gari yayi baƙi alamun hadarine agarin sauri tayi ta ƙarasa fita wajen tana fita kwa tagansa abakin ƙofar kallon kallo suka shiga yima juna kafin daga bisani tayi saurin janye nata ido tare da sunkuyar da kai, yaf yaf yaf ruwa yafara saukowa suna dan gefe baya taɓasu da yagade kamar ruwa zai tsuge kuma yasan ma baba yatafi tunda ya dade agurin gashi kuma hadari ya haɗo yasan dole yanzu ya koma ɗaki baizai jira saba, dan haka kawai sai yace "kije ki koma ciki idan ruwa ya tsaya zan dawo yanzu baban nawa ya koma ɗaki saidai anjima zan ƙara kiranki,
to kawai tace sannan ta juya ta koma ciki,
shikuma cikin sauri zuciyarsa fal da farin ciki yasan ko banzade zai ringa samunta duk sanda yake so tunda gashi waccen matar ta korota dan yasan badan ita ba da bazata zoba amma yanzu shikenan yasamu mafaka kullum ita zaisa ta turota shi kuma zai dage har yajawo hankali ta gare sa murna kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha haka yake jin sa yana tafiya loƙaci zuwa loƙaci yana sakin murmushi ruwa na saukkowa kansa sai yaji hakan yaƙara sakashi cikin annushuwa.......
****************************
cikin bacci taji wani irin sanyin na ratsata duƙunƙinewa waje ɗaya ta shiga yi tana karkarwar sanyi tun tanajin abun kamar amafarki har ta fara buɗe idon ta tsorone yakamata ganin dakin yayi duhu ga ruwan da yafara sauka da ƙarfi sosai hankalin ta yatashi tashi ga yin kuka ƙasa ƙasa datajide abun bana ƙare bane sai ta miƙe tsaye cikin laluɓe tafara tafiya hata isa gaban gadon ɗakin saboda zuwa loƙacin idonta ya washe tana ɗan iya ganin abubuwan ɗakin tunda ba dare bane hadarin da ya haɗo yasa ɗakin yin duhu,
tsayawa tayi tana kallon sa yanda ta nannaɗe jikin sa a bargo yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, rasa yanda zatayi tayi sanyi ne yake ratsata kuma bataso ta tasheshi daga bacci sai kawai ta zagaya ta ɗayan ɓangaren ta lallaɓa ta haye gadon kusa dashi sosai ta ƙara matsawa saboda tasamu ta rufa itama duk girman bargon ya kusa nannaɗe sa ajikin sa ɗan guri kaɗan yarage,
sauran gurin ta kamo ta ɗaga shi ahankali sannan ta kwanta tare da juya masa baya abun rufar ne baigama rufe ta ba sai ta ƙara matsawa kusa dashi sosai har bombom ɗin ta na ɗan gogar jikin sa saida ta tabbatar ko ina ya rufu sanann ta rufe kanta tare da sauke ajiyar zuciya jin ɗumi yafara ratsata ai tuni ta ƙara lulawa duniyar bacci...........✍️✍️✍️
tofa wanga ɗiyafa zata jawowa kanta bala'i ke wa ga aike ki bakinsan yagama korankiba daga ɗakin amma shine harda hawar masa kan gado abun harda su cikin bargo🤔🤔🤔
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[7/2, 8:56 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️77&78
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"ruwa ake sosai kamar da bakin kwarya,
yayin da bayin Allah biyun nan suke sharar baccin su hankali kwance tare da mannewa da juna batare da sanin su ba meer cikin bacci ya runggumo ta saboda duk atunanin sa filo ya rungume ita kuma batasan ma yana yiba baccin ta kawai take shara (daman kunsanta da bacci gashi kuma daman ta kwana batayi ba ga lafiyayyen gado da bargo ga kuma dumin jikin sa ina ai tuni ta manta aduniyar da take hankali kwance take baccin hani'an sunkai wajen awa daya suna bacci lakacin kuma ruwa yafara tsagaitawa,
ruwa na gama daukewa meer yafara juyi alamun zai tashi hannun sa yadago da niyar cire abun rufar daga kansa amma sai yaji hannun yayi masa nauyi alamun kamar andanne masa hannun ahankali ya shiga bude idon sa yana budewa kwa ya saukesu akanta da sauri yasake ta daga rikon da yayi mata saida hannu daya yasamu damar janyewa dayan kuma tana kai ta danne masa tsoro ne yakamasa lokaci guda jin mutum akusa dashi dan baigama ganin fuskar ko wacece ba kuma shi harga Allah yama manta da babun ta shiyasa bai kawota aransa,
tunani ya shiga yi waye akusa dashi rashin me basa amsa da ɗayan hannun ya ɗaga bargo ya buɗe su gaba ɗaya tsulum idonsa ya sauka akan fuskarta daman facing ɗin juna suke yi zaro dara daran idon sa yayi akan ta yana mamakin ganin ta kwance akusa dashi daman duk gargaɗin da yayi mata bataji ba bayan yace kar yatashi yaganta agidan ma gada ɗaya amma shine abunna ta har kan gadon sa kuma kusa dashi akan hannun sa wannan wacce irin yarinya ya haɗu da ita anya ba mayya bace ko aljana daga haɗuwa tabi ta nace masa ta maƙale masa yau ya ɗebowa kansa bala'i,
da ƙarfi yaja hannun sa da take