kedai bakida imani tunda nake bantaɓa jin irin wannan ɗanyaen aikin ba ke naki watakon yafi na kowa nidaman tun farko banyarda dake ba saboda daman zubinki zubin munafukai duk wanda yaga ƙwayar idonki yasan ƙungurumar munafukace da kanta kamar ƙullin maganin bokaye,
har gabanta taje tare da ɗago kanta da hannu ta fara duddun gure nata kai tana cewa "Allah ya toni asirin ki yau wai mema akejira ba ayiwa yara tsira taba tunda ga hujja an samu kuma me yarage ai naso inzo inga an sauya mata kamanni amma sai inzo inganta ras da ita babu wani tabo to ni wallahi bari infara yi mata dan idan naganta haka zaune lafiya ƙalau raina bazai min daɗi ba amma idan naga ana magana tana cikin wani halin sai nafi jin daɗi tana gama faɗar haka ta ɗaga wani ɗan katako da tazo dashi daman saboda dukan ta ta taho dashi ƙwala mata tayi akai zata ƙara sauke mata wani papa yayi saurin riƙeta yace haba gwaggo kiɗan dakata mana afara yin magana dan Allah ki rabu da ita ki samu waje ki zauna yanzu ba wannan loƙacin bane,
kasan Allah bazan rabuda ita hakannan ba sai na tsiyayer mata da ido,
daƙyar papa yajata amma duk da haka saida ta ƙara ziro katakon ta gefen sa ta bugawa fulani akafaɗa sannan tabar wajen,
Allah sarki fulani tana zaune ta sunkuyar da kai takasa ɗaga ido ta kalle kowa ranta duk yabi ya dagule ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse ciki saboda jin kunya da taƙaicin abun da ake mata gashi kuma batasan ma me zai faru ba wane irin hukunci za a yanke mata ba,
zama gwaggo tayi amma duk da haka bakinta yaƙi yin shiru da ƙyar aka samu tayi shiru sai kuma ta koma hararar ta tana girgiza kai sai karkarwa take jikin ta tsima yake kawai so take taga jikin fulani jaga jaga da jini an kunkunbura mata wani gurin sannan hankalin ta zai kwanta amma yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta,
suna cikin haka saiga su Azeema sun shigo ita da mana da saleem, bakin su ɗauke da sallama suka shiga,
amsa musu akayi tunda suka shigo kallo yadawo kansu kowa su yake kallo yamaida hankalin sa gare su musamman ma ma mama da kana ganin ta kaga sarki Salahudden kuma suna kama da saleem ma sosai,
dan haka tun kan ace komai ma kowa ya tabbatar da cewa lalle waɗannan jinin sane sune ƴan uwansa ba ƴan cikin masarauta ba,
itadai mama batasan komai ba game da maganar saboda ba asanar da itaba kawai Azeema haka tace mata suzo ana nemansu masarautar saboda angano ta kuma gata ga baba komai lafiya babu wani abu da yasame ta dan ta kwantar musu da hankali har suzo shiyasa tayi musu haka,
amma ganin kowa yana ta kallon su sai yasa duk suka tsargu dan haka ababakin ƙofar suka samu waje zasu zauna,
gwaggo ta miƙe zunbur tace ina ku ina zama anan ai taron nakune ku matso daga gaba gaba kuji abun da wannan tsinanniyar da tagama kwashe kayan ta daga gaban ma'aiki ta tsula wannan gagarumin zunubin ko kunyar Allah bataji ba ta raba ɗa da mahaifiyar sa tazo ta koya masa mugayen ɗabi'un irin nata,
papa ne yaƙara dakatar da ita tare da bata haƙuri kuma ya roƙeta dan Allah tayi shiru kar ta ƙara cewa komai tayi shiru da bakin ta, da ƙyar dai ta koma ta zauna ammafa bakin nan bazai taɓa yin shiruba taci gaba da kwashewa fulani albarka da zagi da ba'a da cin mutuncin babu wanda batayi mata ko tayi shiru na ƴan mintina zata cigaba daga inda ta tsaya,
sudai su mama kansu ya ɗaure sun kasa gane inda maganar gwaggo ta dosa tsabar mamaki ma baisa sun kalli baba ba basu san ma inda yake ba kawaidai sun matsa gaba kaɗan sun zauna suna jiran ƙarin bayani game da wannan maganganun da matar nan take yi musu da basu gane kai da gindin sa ba,
saida Ammah ma taƙara bawa gwaggo haƙuri akan tayi shiru su fara magana sannan suka samu tayi shiru,
shiru gurin ya ɗauka bakajin motsin komai sai ƙarar Ac dake tashi acikin fadar kowa yayi shiru yaji ta bakin sarki me murabus (papa) saboda ayanzu dai kusan shine sarki shine mai faɗa aji kowa hukuncin sa yake jira,
gyara zama papa yayi tare da bin kowa da ido ɗaya bayan ɗaya kafin yayi gyaran murya zai fara magana Sam ya miƙe tsaye zunbur sannan ya ƙarasa gaban papa ya tsugunna sai yace kaka na nakaina dan Allah ina buƙatar wata alfarma agurin nan kafin afara magana inaso aɗan bani 10 minutes ko 15 wasu zasu ƙaraso nan ina ganin idan dasu maganar sai tafi tafiya yana da ƙyau ayi agaban su dan Allah ayi min wannan alfarmar,
duk da halin da papa yake ciki hakan bai hanasa yin murmushi ba sannan ya dafa kan sam yace "SU WAYE SU?
Sam yaɗan shafa ƙyeyarsa sannan yace "gaskiya bazan iya faɗar ko SU WAYE SU ba shiyasa nace amin alfarma saboda nafi son kawai ku gansu suna hanya yanzu zasu ƙaraso,
wani murmushin papa yaƙara saki sannan yace to babana baka da matsala anyi maka wannan alfarmar ko cewa kayi aɗaga wanann taron sai an ɗaga saboda darajar me sunan ka duk abun da ka nema za ayi maka shi dan haka muna jiran ƙarasuwar su,
sosai sam yaji daɗi daman tun zuwan sa yake ta duba wayar sa yana jiran yaji kiransu amma baiji ba gashi kuma yaga ana niyar afara shiyasa ya daure ya nemi alfarma awajen papa yasan daman za ayi masa dan haka yana gurin bai tashiba ya ƙara ciro wayar sa ya danna Number bossay yana ɗagawa yace wai har yanzu baku ƙaraso ba bansan me akace masa ba daga can kawai sai yace "ok kuyi sauri to dan Allah ku kaɗai ake jira daga nan kuma ya kashe wayar sannan ya kalli papa yace sun kusa zuwa, kai kawai papa ya ɗaga masa,
gwaggo tace "kai kuma su uban wa kaje ka jajibo mana ince dai masu kama mutane kakirawo masu ladaftar da mutum su koyawa waccen figargiyar hankali dan nasan halinka kaima bada ganan ba akwai iya mugunta duk dade haushin ka nakeji saboda baka da mutunci bakasan shiba kuma akaina rashin mutuncin ka yake ƙarewa saboda ka rainani fiya da kowa agidannan to wallahi bari masu dukan mutanen suzo saina shuna musu kai sun maka duka kaima daga nan sai kadain rainani,
hararar ta sam yayi sannan yace "ke matsala ta dake wallahi wataran baki san daidai ba sai ana wata maganar sai kisako wata maganar da ban ai ke Yakamata ma su zane idan sunzo saboda bakinki bashida saiti gigin tsufa yayi miki yawa shiyasa bana zuwa wajen ki dan nasan daf kike da mutuwa kar nazo ki shafa min dan nasan duk wanda yake raɓar ki da yawa kina mutuwa zai mutu ni kuma banshirya mutuwa yanzu ba yanzu ma nazo duniya ke kuma nasan ayanzu ma zaki iya mutuwa domi mutuwa ta ratayu awuyan ki da ita kike yawo duk inda kikaje tana tare dake shiyasa nake gudun haɗa hanya dake,
gwaggo da sauri ta miƙe tsaye tare da riƙe tace "kajimu da ɗan banzan yaro niɗin ce nake yawo da mutuwa to wallahi saidai idan munubiya da Abdallah ne suke yawo da ita dan jakar ubanka kai bakada zance saina mutuwa to duk baƙin cikin ka dani dai nan gani nan bari ɗumaman uwar mayya ba wanda ya isa yakashe ni loƙacina baiyi ba ni nasan duk sai naga gawawwakin ku kafin in mutu duk sai kun tafi kunbarni ɗan baƙin ciki wai ni ubanka me ka tsaya yi aƙasar nan baka koma ba can gurin ya hudawan ba masu baƙin hali irin ka nifa wallahi bana ƙaunar ganin ka agidan nan yanzu ma bansan kana ciki ba da banzo ba,
"to zo ki ɗauken kifitar dani mana idan kina da ƙarfi ko ke kifita daman kin ishemu kin cika mu da surutu bakin ki ko gajiya bayayi sai magana da masifa kamar wacce ta ƙone akai,
Hannu ta ɗaga zata makesa yayi saurin tashi daga gurin yana tashi kuma wayar sa tayi kara da sauri yazaro wayar tare da ɗagawa yace kun iso, "ok" bari inzo,
fita yayi daga cikin fadar cikin sauri,
yana fita yagan su abakin gurin hannun ya miƙawa su bossay suka gaisa sannan yagaida sauran sannan yayi gaba suka shiga binsa abaya sallama yayi yafara shiga sai su shettima da hajiyar sa sai bossay da Ammi da dadda suma atare suka shiga kowa dai kallon su yake da mamaki,
bayan sun shiga sai ummy riƙe da hannu Ameesha suka shigo bayan su kuma gimbiya SABREENA da ɗan ta daga baya kuma oga fata fata MEER na take musu baya fuskar nan ya ƙara haɗeta tamau gashi ya wani naɗe hannun riga kamar me shirin yin dambe jira yake kawai yaje ance casss ...... yabada warrrrrr💃💃💃💃💃💃💃
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️ 94
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
'bayan sun shiga sai ummy riƙe da hannu Ameesha suka shigo bayan su kuma gimbiya SABREENA da ɗan ta daga baya kuma oga fata fata MEER na take musu baya fuskar nan ya ƙara haɗeta tamau gashi ya wani naɗe hannun riga kamar me shirin yin dambe jira yake kawai yaji ance casss ...... yabada warrrrrr........
:Akusan tare gaba ɗaya ilahirin fadar waɗanda suka san sabreena suka miƙe tsaye suna kallon cike da mamaki da al'ajabi da ya kusan kashe su da rayuwakan su,
kowa yakasa magana saida ƙyar bakunan wasu ya buɗu ahankali suka fara furta gimbiya sabreena gimbiya sabreena dan sun kasa tantance abun da idanun su sukagane musu suna ganin abun kamar mafarki,
wasu kuma da baya da baya suka fara ja saboda tsabar mamaki da rikiɗewar da sukayi abun yazo musu bazato ba tsammani wasu kuma sun tsorata da ganin ta suna ganin kamar ba itabace fatalwar tace,
Ammah ma da ƙarfi tace Sabreena kuma kai wannan ba ita bace sabreena da ta daɗe da mutuwa shekarar ta nawa da mutuwa wallahi wannan sai dai inajin aljanune suke son buɗe mana ido da ita amma ni nasan ba itabace tafaɗa tana kallon sabreena kuma tana girgiza kai tare da yin baya da baya kamar zata faɗi idanunta duk sun firfito waje saboda tsabar mamaki da al'ajabi da suka gama kasheta da ranta,
fulani kam saida ƴan kusa da ita suka dafeta sannan ta iya tsayawa da ƙafafun ta dan magana ma ta gagare ta sai wani uban gumi da yake tsatstsafo mata ta kowacce gaba dake jikin ta loƙaci ɗaya yagama wanke mata jiki idon kyam akan maama takasa janyewa ga jikin dake faman karkarwar sanyi atake dai wani irin mugun zazzaɓi ya kawo mata ziyara loƙaci ɗaya tare da ciwon kai hannu biyu tasaka ta riƙe kan danjin sa take kamar zai rabe gida biyu yabar jikin ta,
papa ne yafara takowa zuwa inda suke jikin sa na karkarwa kamar zai faɗi ya ɗaga hannu sa yana tafiya nuna ta dashi tafiya kawai yaka Bama yasanin inda yake saka ƙafar sa saidai idan yabiyo ta wajen mutane suyi gaggawar bashi hanya ya wuce bakin sa sai motsi yake yana yayi magana amma maganar taƙi fitowa ya kasa cewa komai,
yana daf da zuwa kusa da ita yaja burki ya tsaya sakamakon jin nauyin da ƙafarsa tayi masa,
da ƙyar ya iya buɗar bakin sa dake faman karkarwa kamar maijin sanyin sannan ya iya cewa maa..ta..tattt...taga...ri.... yayi maganar cikin in ina da rarraba ta kamar me koyon magana,
ganin sa kuma sai yasa take taji idon ta ya cika da ƙwalla taf ba shiri ta fara zubar da hawaye take taji zuciyar ta ta karaya batasan loƙacin da wani irin kuka ya taho mataba cikin kukan itama tace "mai martabanaaa....tana faɗa sai kawai ta fashe da wani kukan tare da ɗaga ƙafar ta da tayi mata wani irin nauyi ta manta ita wace kuma a ina take haka tayi taku da basu wuce uku ba taƙarasa gabansa tana zuwa daf da shi kawai ta faɗa jikin sa ta rungume sa tana ƙara sakin wani kukan kuka kawai take takasa magana kuma takasa sakin sa,
gwaggo dai da tayi suman wucin gadi tayi ba asaniba hakanne ya hanata magana dan tafi kowa tsorata da ganin ta matar da ta mutu me kuma ya dawo da ita indai ba fatalwar tabace ta dawo, dan haka tunanin fatalwar da tayi ne yasata tayi saurin komawa bayan kujerar ta takure waje ɗaya ta ɓuya saboda kar fatalwar ta ganta ta kamata,
runtsi idon sa papa yayi tare da ɗagota tabbasa jikin sa ya tabbatar masa da ita ɗince matar shice ta dawo gare sa zuciyar sa tagaya masa haka domin kuwa daman duk acikin matan sa yafi sonta itace wacce ya aura da soyayya kuma haryanzu son da yake mata bai raguba yana nan yanda yake duk da ya tsufa shidaman tun aloƙacin bai yarda ta mutuba dan kusan hauka yayi loƙacin da akace masa ta mutu kuma aka hanasa kallon gawarta saboda maganganun da yake aloƙacin yana cewa bata mutu ba shiyasa aka rirriƙeshi har aka gama komai akakaita ba tare da yaganta ba,
yana ɗagota ya kafe ta da ido yana mata kallon ƙirulla itama shi take masa sun tsaya batare da sun ƙara wani ƙwaƙƙwaran motsi ba kuma basu sake yin wata maganar ba,
ganin ana ta ɓata loƙaci kuma batare da amfahimci komai gaba kuma yanayin da suka tsinci kansu bisa ga dukkan alamuma sun manta da mutane agurin kowa yazuba musu ido wasu na jiran ƙarin bayani game da ita waɗanda basu santa ba kenan waɗanda ma suka santan suna jiran suji taya tadawo duniya bayan ta mutu hakanne yasa waziri (Alƙasim ƙanin papa kuma kakan sam) daman shima zuciyar sa adake take bai wani tsorata da ganin taba dan haka sai ya ƙarasa gabansu tare da kamo papa yace "yakamata ka arowa kanka nutsuwa yaya nanfa cike yake da yara da manya kamata yayi ayi abun da yadace a wayarwa da mutane kai dannaga harda masu ɓuya dan tsoron ganin ta amma sai ai gaggawar sanar dasu ainahin abun dake faruwa saboda kowa yana cikin duhu,
"juyawa yayi gurin sabreena daman mutuniyar sace dake wayayyene ɗan boko kuma yanada ilimi addini shiyasa bai wani tada hankalin sa kamar kowa ba yasan hakan zata iya faruwa daman duk da yayi mamaki shima amma ba sosai ba kamar na sauran yana da saurin fahimta,
na damar sabreena ne tunda tana gidan kallon ta yay sannan yace "gimbiyar mu U are welcome barka da zuwa dafatan kin iso lafiya muna miki fatan alkairi da dawowar ki cikin mu akan gaba loƙacin da ake buƙatar ki lalle wannan babbar ranace tafarin ciki agaremu gabaki ɗayanmu,
da kansa yayi musu iso suka zauna sannan ya kalli ƴan cikin fadar da wasu sunfara maganganu ƙasaƙasa fadar na neman rikicewa da surutun wasu dan haka ya ɗan ɗaga murya yace "pls kowa yayi shiru sannan ku koma gurinku ku zauna sannan ya nuna wani keɓattacen guri aka nunawa su ummy da su dadda suka zauna suma,
yazamana kowa yana zaune amma banda shi kunsan me hali baya fasa halin sa yana tsaye inda yake bai motsaba daga inda yake yana kallon kowa dake ciki 1 by 1 yana nazartar su dan a iya yanzu ya riga da yagama selacting ɗin mutane da zai sawa ido dan duk wani wanda ya nuna alamar rashin gaskiya yagama ware sa gefe shiyasama ya tsaya saboda yafi ƙara ganin kowa da kyau yakuma bambance su da kamannin su,
shidai papa hankalinsa gaba ɗaya yana kan sabreena yakasa ɗauke idon sa akanta bare ma yaga sauran da suka shigo tare,
waziri da sai yanzu ya lura da rashin zaman Meer yace, kai yanaga ƙa tsaya anan ka ƙaraso kazauna mana,
wani irin kallo Meer ya watsa masa mai kama da harara harara gargaɗi gargaɗi gadai shine ta ƙamaimai dai bansan irin wannan kallon na Meer ba bangane masa ba, sannan ya janye kansa daga gurin sa yaci gaba da abun da yakeyi ya tsaya ƙyam akansu kamar wanda akaturo shi akace yabawa kowa kariya,
zaro idon waziri yayi tare da haɗiye yawu ya karkaɗa kai bai ƙara gigin ƙara yi masa magana ba amma aransa yana jinjina abun da yayi masa ba ƙaramin mamaki abun yabasa ba daga magana sai yayi masa kallon banza, yadai rabu dashi saboda ko ba afaɗaba bazai wuce ɗayan biyu ba yaron nan da jininsu yake kama tsayuwar da yayi kuma sai tayi masa kama da ta sarakai saboda tsayiwace ta girma wacce kana gani kasan ba raini da sarauta ajikin sa ma'anadai ɗan gidanne shima shi abunma burgesa yayi wani tunanine yafaɗo masa rai sai kawai yasaki murmushi tare da jinjina kai duk dadai baisan kowaye shiba amma dai ransa yabasa wani abu saurin kawar da maganar yaron yayi aransa sai ya mayar da hankalinsa ga ƴan gurin,
kowa da magana abakin sa amma yakasa saboda halin da suka tsinci kansu babu mai walwala ko sukuni acinkin su Ammah bakin ta ya ƙulle takasa magana amma dai ita har ranta iyaka gaskiyar ta bata yarda da cewa sabreena mutun ce ba amma dai tayi shiru taji ko zata yarda nan gaba amma fa ko ta yarda bazata ta taɓa bari