Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   46 / 74

135K to 138K   out of 221K words

tashi tsaye daga kwance da yake yana faman washe baki shima yabi sam inda yaga yana niyar tafiya acewar sa tunda yaji kukan mace kuma yaji ya cire wayar daga hans free yana niyar barin wajen yace to sai yabishi yaji abun da zaice,

shide bossay bai tashiba yana gurin yana musu dariya ganin yanda suke abunsu sai abun ya burgesa watakon shi shettima yaƙi faɗa masa komai game da yarinyar da suka shige ɗaki amma yanaso shi yaji abun da sameer zaice shikuma sameer shima bayaso kowa yaji wayar da zaiyi kowade kansa yasani,  

yanda suke abun nasu sai suka tuno mishi da Ameeshan shi yasan da ba aɗauke taɓa da tuni shima yanzu yana tare da ita jikin sane yayi sanyi 😢 cikin sanyin murya yace Allah ya bayyana minke aduk inda kike Allah ya kareki da kariyarsa aduk halin dakika tsinci kanki Allah yabaki ikon haƙuri da juriya bakiji ba baki gani ba tun kina ƙarama antakurawa rayuwar ki Allah yakawo miki ƙarshen wannan abun,
Allah sarki baby meesha na ina sonki sosai Allah ya nuna min ranar da zan kasance dake ranar da zan wayi gari inganmu ɗaki ɗaya inganki amatsayin mata agereni ranar sai nafi komai farin ciki zan baki kulawa daga nan har ƙarshen rayuwa ta in sha Allah tsakanina dake mutuwace kawai zata rabamu, ji yayi hawaye na niyar taho masa da sauri yayi rufe idon sa yana karanto addu'ar neman sassauci game da abun da yake atare da ita, kwantar da kansa yayi ajikin kujerar tare da ɗora hannu akan ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa idan yana tuna yanda yake sonta sai yaji zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fito waje haka yake ji aransa.....,

sam tunkan yakarasa wajen kofar yaji tafiya abayansa juyawa yayi sai yaga shettima wani mugun kallo ya wurga masa me ciki da abubuwa da yawa,

dan juyar da kansa yayi yana magana kasa kasa yace Allah kwa sai naji ko wacece dan munafurci shine baza kayi wayar agaban muba zaka wani tafi daki to wallahi kafata kafarka sainaji duk abun da zakace,

girgiza kai sam yayi kawai batare da yayi masa magana ba ya wuce yana shiga dakin yayi sauri yarufe ya murda key yabarsa awaje ,

shettima buga kofar yashiga jin da gaskede ya kulle yayi tsayawa yayi awajen yana kara kunne ko zaijiyo muryar sa amma ba abun da yake jiyowa,

sam yana shiga dakin ya koma kan gado ya zauna yayi shiru yana cigaba da sauraron kukan nata baice mata komai ba harsaida ta dan tsagaita da kukan sannan tace hell cikin muryar kuka,

kasa amsa mata yayi saida takara magana sannan yace wa mai magana banda wannan number kuma ankira anata kuka wacece?

cikin kukan tace nice,

"ke wa?

"sumayya" tabashi amsa tana shirin fashewa da wani kuka yayi saurin da katar da ita yace ya akai?

"tace tunjiya nake kiran wayarka bata shiga yauma haka kuma kace ajiya zaka dawo min da mahaifina amma bangan shiba dan Allah ka taimaka kadawo min dashi shikadai ne gata na aduniyar nan kar ka cutar min dashi tana gama maganar ta fashe da wani kukan kuka biyu ne ya hadar mata ga na rashin mahaifimta ga kuma matar da tayi mata duka da safe dan bata tashi da wuri tayi aiki ba,

shiru yayi na dan dakiku sannan ya bude baki zaiyi magana yajiyo ta wayar kamar anamata magana zagi yaji ana kutuntuma mata cikin kuka ta shiga bawa matar hakuri bata gama bada hakurin ba yaji tass ankwashe ta da mari runtse idonsa yayi kamar shi aka mara haka yaji marin acikin ransa kasa magana yayi yana cigaba da sauraron fadan da waccen matar  take mata ta kara marinta duk yanajiyo sai kuna can yaji yadena ji sai ihunta da yake ji kasa kasa kashe wayar yayi saboda wani irin abu da yaringa ji yana taso masa daga kasan zuciyar sa yana tunani to wace wannan me dukan nata anya kuwa mahaifiyar tace tunawa yayi tana cemishi shikadai ne gatan ta to anya kwa ba mahaifiyar ta tarasa ba waccen kuma take cutar da ita  tsaye yatashi yafara zagaya dakin yana tunani yanajjn ransa namasa ba dadi,

saida yabada kamar minti goma sannan ya dauki wayar sa yakira number da ta kirashi ga mamakin sa sai yajita akashe kara gwadawa yayi amma ana cewa switch up saida yakira wajen sau goma bata shiga ba sai kawai ya mayar da wayar aljihu ya dauki key din motar da zai fita da ita yasa shi shima a aljihu saboda bayaso su bossay sugani suce zasu bishi ko su tambaye sa ina zashi shiyasa yasaka komai a aljihu tare da shga bandaki dan ya wanke fuskar sa kar suga alamun damuwa agareshi suyi tunanin wani abun..

"Shettima dake tsaye har yanzu yanaso yajiyo abun da sam keyi amma bai ji komai ba kawai yajuya tare da yin kwafa ya juya ya koma falon bahaka yaso ba yaso yaji kodawa yake wayar amma yayi masa haka hmm zai zaka fito ne kasame shi yayi maganar yana zama akan kujera,

jin maganar shettima yasa bossay ya bude idon sa dakana gani kasan akwai dam uwa atattare dashi,

  "bossay yakalli shettima yace ya naga kadawo har angama wayar ne,

"hmmm rabu da dan iskan ya rufe dakin munafuki sai yafito kaga yanayiwa mutane zare zaren ido da hade rai shi adole kar ace wani abun kuma wallahi sai mun fada hakan ma ai ba tsira yayi ba yagama yafito ya sameni anan,

dan murmushi bossay yayi yace to yanzu sai kaga laifin sa naga kai nakama yafi nasa yanzu fa kazo ka shige daki da yarinyar mutane baka gayawa kowa ba kukaje kuka dade adaki kuka fito kuma kaki fadar komai shine yanzu kai kake so kaji tasa hirar da zaiyi,

"kai manta da wannan ni ai ba budurwa ta bace shikam nasan budurwa ce kasan ma ni wacce nake zargi?

bossay yace "a'a

shettima harda gyara zama yana kallon bossay da kyau sannan yace wallahi ina tunanin wannan yarinyar ce da mukaje gidan su wacce muka kama mahaifin ta,

bossay yayi dariya yace ai babu watakil ma amaganar ka itace idan ba itaba wace macence zata kirasa tunda kace bashida budurwa baya kula mata kuma nima naga alamun hakan kaga kwa waccen daga haduwa da ita mukaga sauyi saidai muyi musu fatan alkhairi,

Gaskiya de kam hmmm wai nake shiga yayi sauri ya kulle ni abun harma mamaki yaban wai sam ne yau dakansa yake daga wayar mace tare da barin wajen tunda muke dashi ko  baitaba boyemin wani abu ba ko kuma yakasa yin abu gabana komeye agabana yake bayajin kunya bayajin tsoro amma yau gashi Allah yanunamin karshen abun gasky wannan wabun dole inyi mamakin sa,

ah kadan ma kagani bade mace ce ba zata sauya sa fiye da yanda kake tunani kaima bagashi nan ta canza ka  ba kaki gaya masa shiyasa shima yayi maka haka, yana gama fadar haka ya dan matso da fuskarsa wajen shettima sannan yayi kasa kasa da murya yace yauwa yanzu bayanan ni gaya min abun da yafaru dan fa har ihunta najiyo tana cewa wayyo mama na kuma daga jin ihun ni nasan na menene dan haka dan gaya min bazan fadawa kowa ba wallahi,

fulon dake gefe shettima ya dauka yajefa masa yace to muna fuki dan iska ashe kunnuwan ku yana kaina to bazakaji ba yara basa jin irin wannan maganar kabari duk sanda ka girma zan fada maka abun da yafaru,

rike filon bossay yayi yana dariya yace au nine ma yaron naka kasande da nayi auren wuri da tuni na ajiye yara kusan biyar yanzu amma zaka cemin yaro nade san ba abun da zaka nuna min da bandashi,

suna cikin haka saiga sameer nan yafito daga dakin fuskar sa adaure yazo zaiyi hanyar waje shettima yayi saurin dakatar dashi da cewa alaramma ina zuwa haka ba sanarwa kuma meye na daure fuskar dama kasaketa kafi kyan gani dan mude kasan ba tsoron ka zamuji ba, gwanda ma kadena wannann abun duk abun mutum yanzu munsan kowaye shi da kuma abun da yake aikatawa adena yimana wata fusfusga ana cin magani,

juyowa sameer yayi tare da cilla masa dakuwa yace fuck u wallahi kafita daga idona naga alamar yan kwanakin nan raini yafara shiga tsakanin mu ko to wallahi kabini ahankali kasanni sarai banda mutunci kar kabari inkulla takun saka dakai bazakaji ta dadi ba dan haka kafita aharkata sai mu zauna lafiya,

"inna ƙi mai zai faru ko zan dakune inzaka iya dukana kuma bismillah ga jiki ga tsoka ga kuma fata kadaki inda yayi maka saurayi mijin yan mata,

hmmm zakayi bayani ne ni yanzu bani da lokacin ka ina da abunyj agabana  zan fita amma ba dadewa zanyi ba,

cike da tsokana shettima yakara cewa ah daman ina kato dani ina za aban lokaci daman lokacinka ai banawa bane nata ne dan haka aje abata lokacin ta nima dakwai inda zanje abani nawa lokacin,

bossay yace banda wanda aka baka dazu sai ankara baka wani yanzu yakamata kabarta ta huta ai ko na mamajo kazamane bamu sani ba,

dariya suka saka gaba dayan su dan har sam saida yadan dara yana girgiza kai yace ni kunga tafiyata sai nadawo yajuya zai fita bossay yayi saurin cewa uhm naceba dan Allah idan hanya ce muje kasauke ni agida daman nima yanzu nake tunanin inje indawo ka ajiye ni inyaso sai indawo idan kadawo sai kayi min waya,

sameer yace to muje amma fa bazan kaika har gida ko kuma muje sai driver yakai ka kawai ma basai ka wahalar dani ba,

bossay ya nike tsaye yace to hakan ma yayi nagode muje,

shettima ma tashi yayi yace to nikuma fa waye zai maidani gida ko ni bamu da gida da duk kuke so kutafi ku barni anan,

hararar sa sameer yayj sannan yace bamu sani ba bazamu tafi dakai ba wallahi kayi zaman ka anan sai ka kirata ku dora daga inda kuka tsaya yan iska kawai,,

dariya shettima yayi yace wai dan Allah ku mai kuke tunani munyi da yarinyar nan nifa babu abun da nayi mata wallahi kuma dena tunanin wani abun yafaru babu abun da yafaru kawaidai wata yar magana mukayi da ita,

"Sameer yace kaide  kasani can ta matse muku kai da ita sai kafadawa wanda baisan halin ka muje kai in kuma zaka tsaya kaci gaba da jin karyar da yane zubowa to sai kataho yana kaiwa nan yafita daga  falon da sauri bossay yabi bayan shima shettima yabi su yana dan murmushi dan shi mamakin su yake su duk atunanin wani abun sukayi da suka shiga dakin...,

akusan tare suka karaso falon fulani suna fitowa Azeema ma na fitowa daga kitchen tana ganin su ta koma ciki da sauri ta rufe kofar tana sauke numfashi,

sam ne yaja tsaki yace munafuka sai yanzu zakiji kunyar lokacin da kika zo kika wuce mu kika shige har uwar daki bakiji kunyaba sai yanzu,

to ina ruwanka da ita shishshigi to tayi din me ruwan wani aciki,

"Babu " sam yabasa amsa yaci gaba da tafiyar sa,

har suka karaso wajen motar babu wanda ya kara yiwa kowa magana saida sukazo gurin drivern sameer ya karaso wajen sai sameer yagaya masa yakai bossay gida ya kalli shettima yace kai kuma ga motar kanan daman baka dauka ba sai ka tafi gidan ku da ita,

"ai basai kamin gorin gida ba  amma de ba inda zani da motata ataka zamu tafi tare muje mu dawo ni ba gidan da zani raka ka zanyi duk inda zaka,

"baka da hankali naga alamar wannan yarinya tafara saka abun da ba daidai ba tunda kafito ka ishi mutane da surutu ka damemu daga kace wannan sai kace wancen to wallahi ba inda zani dakai malam kawuce ka shiga motar ka katafi gidan ku inkuma baza ka tafi ba ka koma ciki kajira indawo kazabi wanda yayi maka daman nasan so kake mutafi ka koma gurin ta to ga damanan munbaka ka koma ciki dan Allah nasan abunne yake cinka kake neman zaucewa akan mutane to mu bamu da maganin abun kaje tayi maka magani,

kafin shettima yace wani abu sam yayi sauri ya  bude motar sa yashiga yana shiga kuma yasata a louck yana masa murmushi sannan ya zuge bakin glass din motar yana daga masa hannu tare da tayar da motar yaja yabarsa agun atsaye kamar gunki dan yau sameer yagama gaya masa maganar da baitaba ji yayi irin taba yabasa mamaki,

bossay ma saida yayi masa dariya sannan yace sai anjima ade bi ahankali kar awuce da abun kunya azo ana dana sani kar ka cuci yarinyar mutane de kabarta kuma kade ji ba dadewa zamuyi ba dan haka kayi ka koma dan nasan amatse kake dan ana kallon idon ka za agane ba lafiya kake va nidai inkara baka shawara kar awcu gona da iri ayi komai baya baya,

da sauri shettima yayi kansa zai kaimasa nausi yayi saurin matsawa tare da shigewa mota shima yana masa dariyar mugunta yacewa driver yasaka motar a louck sannan ya tayar haka kuwa driver yayi shima yana yar dariyar sa kasa kasa dan yagane hirar da suke yi yasan me suke nufi tayar da motar yayi yaja suma suka tafi bossay harda lokowa ta windo yana kara tsokanar sa,

shettima kamar ya nutse agun haka yake ji wai har bossay ma yasamu damar yi masa irin wanna zancen aikwa zasuyi bayani wallahi duk sai yarama abun da sukayi masa daya bayan daya sai yarama sai sunyi danasanin wannan abun da sukayi masa yau shi zasu gayawa magana irin wannan kuma sugudu yama fasa tafiya gida zai koma yajirasu su dawo takan sameer zai fara sai ya kunce mai zani agaban kowa da kowa bade yana da videon sa ba yana daukar mace to wallahi ha momma sai ya nunamata yaga karshen rashin mutuncin irin nasa shikuma bossay zai duba yaga ta inda zai rama dan shi nasa magan ganun ma sunfi na sameer zafi zai sanine shima sai yagane bashi da wayo in yasakasu gaba sai yasa duk sun tsani kansu dan bazai raga musu zai hada da karya da gaskiya da abun da yafaru da abun da bai faruba ma duk sai ya hada yagayawa mutane da sukeyi.....,,

yana wannan tunanin  har yakoma part din fulani yan shiga falon ya shiga rarraba ido ko zai ganta amma bai gantaba tunawa yayi da tashi ga kitchen dazu dan haka kansa tsaye bawata fargaba ya tura kofar kitchen din ya su biyu  ya gani aciki ita tana wanke wanke dayar kuma tana girki saida yagama karewa bayan ta kallo sannan yadan yi gyarab murya atare suka juyo suna kallon sa gaban Azeema ya shiga dukan uku uku shikenan yanzu ba damar guduwa yakata, dayar kuma tunda tasanshi kamar dan gida yake awajen kowa yanda za agirmama dan gidan shima haka suke girmama shi dan haka da sauri ta tsugunna ta gaidashi sanna ta shiga tambayar sa abun da yake bukata yace mata ba komai tana ta mamakin abun da yakawo sa kitchen din kuma yace babu abun da yake so to me yakawo shi har ta juya zata cigaba da aikin ta ya kira sunan ta tana amsawa yace mata in badamuwa kidan ban guri kifito waje,

da sauri tace babu komai ita duk tunanin ta bai bata gurin dayar yazo tayi tunanin idan ta fito zace Azeema ma tafito amma sai taga tana fita daga kitcshen din ya mayar da kofar ya rufe da mamaki tayi tayi tsaye abakin kofar tana tunanin to me zaiyiwa yarinyar aikwa bazata bari wannan labarin ya wuce uwar dakin taba da sauri ta juya ta nufi dakin fulani dan ta sanar da ita abun dake faruwa tazo ta ganewa idon ta da kanta gani da ido yafi abaka labari.......

Suna karasawa unguwar bossay  yace ya sauke sama akofar gida ya gode a kofar gida aka saukesa ya kwankwasa me gadi ya bude masa ya shiga ciki shikuma drivern ya juya yatafi,

da sallama ya shiga falon gidan nasu amma babu kowa afalon dakin Ammin sa yafara zuwa yana shiga kuwa ya tara da ita tayi wanka ta saka wani less me dan karan tsada da kyau taci uban dinki ga stone ta ko ina sai kyakyali take, tsayawa yayi yana kallon ta ko kiftawa bayayi har sada tagaji da kallon da yake mata tace kaiafiya ka kafe ni da ido haka tayi maganar tana danyi mishi hararar wasa murmushi yasaki yace Ammi ganin nai kindau wanka irin wannan kyau haka kamar baki ajiye irin mu ba kamar fa budurwa haka kika koma kinganki ku da kyau amma de wannan kwaliyar da walakin wai goro a miya kamar fa amarya haka kika koma kode angon ne zai dawo ba'asanr da muba muma munyi shiri,

murmushi tayi tace bana son iskanci yaushe nafara wasa daki mahaifin nakune ango to kamar akunne sa sai nagaya masa,

to Ammi tunda ga amarya anan kinga kwa wanda zaizo ai angone dan Allah Ammi dagaske yau zai dawo,

dagske kam yau zai dawo kagama iskancin ka zan sanar dashi daman da guntun haushin ka da yakeji kaga sai yaji dadin sauke maka,

lokaci guda mood din sa ya canza tunawa da sanadin abun da Abban sa zaiyi saboda shirye shiryen bikin sa da zayi wani irin haushi ne da ta kaici yazo masa wuya ya tsaya masa, "Ammi wai dan Allah bazaki saka baki ba abar maganar auren nan wallahi ina cikin tashin hankali  yanzu ko nutsuwar kirkima bani da ita kallon sa tayj cike da tausayawa dan nata ta kalle sa tace Aliyu babu yanda zanyi kasan halinsa tunada yayi magana babu wanda ya isa yasa afasa auren nan saidai kayi hakuri kabi umarnin mahaifin ka Allah yasa hakan shi yafi alkhairi kaci gaba da addu'a idan ba alkairi bane zaka ga sauyi kaga anfasa idan kuma da alkhairi acikin sa dole sai anyi shi babu wanda ya isa ya hana ka kwantar da hankalin ka nasan da wacce kake so amma hakan bazaisa kaki samun taba sai hadasu su biyun saidai kayj hakuri ka kwatanta adalci a tsakanin su kar ka zalunci kowacce daga cikin su nasan kana da hakuri amma ka kara akai ka saukewa kowacce hakkin ta tundade dukan su suna sonka  ina ganin hakan bazai baku matsala ba kade kaci gaba da addu'a itace kawai mafita,

sosai jikin sa yayi sanyi

46 / 74