dan haka kiyaye kar nasake jin wata kalma marar daɗi ta fito daga gare ki kuma kidena kukan nan ina ƙara gaya miki kinji abun da nace ko,
cikin sanyin jiki tace to kayi haƙuri bazan ƙaraba,
"tom shikenan komai ya wuce sai anjima,
zai kashe wayar kenan yaji yace gobe da ƙarfe nawa zaka kawo shi?
ina ruwan ki bade nace zan kawoshi da safe ba sai kijira kigani ko sai kinsani abun da banga dama ba mtswa yaja tsaki tare da kashe wayar,
ɗif taji ya kashe wayar zare wayar tayi daga kunnen ta tare da hararar wayar kamar ita tayi mata laifin aranta tace masifaffe kai ba agama magana ta arziƙi dakai yanzu yagama yimaka magana cikin sanyin murya kugama lafiya amma sai ka ƙara jinsa yayi sama kamar me almutsutse ta faɗa tana turo baki sannan ta ƙara kiran sa amma sai taji wayar ma akashe tsaki taja daman tanaso yagaya mata loƙacin saboda bataso matar gidan taga loƙacin da za akawosa dan batasan awane irin yanayi za akawo sa ba tunda duk taga jini ajikin sa ɗazu kuma duk yabi yajigata bataso sauran mutanen gidan susan halin da yake ciki, amma tunda yakashe wayar ta ƙara gwada kiran nashi gobe da safe kafin yataho sai tagaya masa inda zai kaisa,
tashi tayi daga kan gadon ta cire hijab ɗin da tun ɗazu takasa cire wa sai yanzu bayan ta cire ta hau cire kayan jikin ta ta ɗaura zani sannan ta shiga banɗaki dan gabatar da wankan ba jimawa ta fito tare da canza kaya sannan ta shinfida sallaya tafara jero sallolin da ake binta,
yana kashe wayar yasakata a airplane mode,saboda yasan zata iya kirannasa shikuma yagaji da wayar shiyasa yayi hakan duk da yana tausayin nata amma ta wani ɓangaren na zuciyar sa hakannan yakejin haushin abun da takeyi masa kuma ya biye mata,
ɗora kansa yayi akan staring din motar tundaga farkon haɗuwar su da loƙacin da tatafito har tazo inda yake kalaman da yayi mata ne yashiga dawo masa da loƙacin da harta shiga mota har zuwa can da abubuwan da suka faru acan da baccin da tayi masa akan cinya da abun da tayi masa harde zuwa rabuwar su da kuma wayar dasukayi yanzu babu abun da bai tunaba kansa ne ya ƙulle ya rasa wane kalar tunani zaiyi da irin wannan sabon halin da ya aro yakeyi dan yasan ba halin sa bane,
yana mata magana cikin sanyin murya harda rarrashinta da bata haƙuri da naiman yafiyar ta shi shi da kansa kamar ba Sameer ba yau wata na niyar canza masa tunani dole yadakatar da wannan tafiyar tasu zaima sakata a blacklist sannan ya goge number ta gaba ɗaya mahaifinta kuma yafasa kaishi da kansa zai sallame sa kawai ai ba ƙaramin yaro bane da har sai ankaishi agida shima idan akarabu dashi zai iya zuwa da kansa, shikenan ya rabu dasu bazai ƙara shiga harkar suba yarinyar kuma bazai ƙara ganin taba itama bazata ƙara ganin saba daga yau
yau suka haɗu kuma yau zasu rabu duk dade acikin mata tayi masa abun da ba macen da ta taɓa yi masa makamamcin irin abubuwan da tayi masa ayau kuma ya rabu da ita,
atake agun yagama yanke sharar duk yanda zaiyi tare da yin blocking din ta sannan ya goge number kamar yanda yace zaiyi, saida ya kawar da komai da tunanin ta aransa da duk abun da ya wakana atsakanin su,
sannan ya tayar da motar ya cigaba da tafiya yamaida akalar tunanin sa kan yanda zasu shirya tafiyar tasu gobe yana tunani yana tuƙin sa ahankali kamar ba abun dake damunsa bai isa gida ba sai wajen ƙarfe tara da wani abun ya ƙarasa,
bayan ya shiga ba zarce ko ina ba sai part ɗin fulani inda nasa part ɗinsa yake baibi takan su shettima duk da daf da shigowar sa yaga kiran shettima yasan basu tafi ba amma ayamzude baida loƙacin su hutu kawai yake buƙata a halin yanzu,
momma ce ta sauko daga step din upstairs, maida hankalinsu sukayi gareta kafin tafi magana ma ta rigasu da cewa yanzu na hango shigowar sa ta window ya tafi part ɗinsa yabarku da jira,
cike da ƙosawar gajiya da zaman gurin shettima yace momma rabu dashi wulaƙanci yakeji dashi yasanu sarai jiransa muke kuma sai kiran sa nake baiɗaga ba shine ya shigo gidan ya tafi yayi wucewar sa bari muje mu same sa dan ina so in wuce gida da wuri gashi har goma ta kusa,
wannan yaron wallahi wulaƙancin sa dayawa yake kuɗin ma da kuke tare ashe bai tsallake kuba kowa sai ya nuna masa halin sa Allah ya shirye sa ya rage wannan mugun halin nasa,
dan murmushi shettima yayi yana miƙewa tsaye sannan yace haba momma inda sabo ai munsaba wataƙil yagaji ne shiyasa kikaga yayi mana haka amma masana ko ba muje ba ma zai mememu saboda wani aiki da muke bari kawai muje,
tace to Allah ya kyauta dan mutum kuma yagaji sai ya sauke gajiyar tasa akan kowama nidai wannan halin nasa ba ƙaunar sa nake ba,
momma sai haƙuri wataran zaidaina dayayi aure ne zai rage wasu abubuwan,
Mamman tace to ahaka taya zai samu matar auren duk wacce aka haɗasama da ita wallahi an cuceta dan wuya zata sha ba matar da zata ita zama dashi da wannan halin nasa,
shida matan ma ba kulawa yake ba yace ai nan duk ba matar da zai iya aura duk faɗan da nake masa ba saurara ta yake ba saidai ma yafaɗi abun da yayi niya yaƙara gaba yabarni agun,
cikin dariya shettima yace kar ki damu momma sirikar is coming very soon keda ki zuba ido kawai ki sha kallo,
har cikin ranta kuwa taki daɗin abun da yace sannan tace banason wasa da gaske kake yana da budurwa?
a'a momma baza aji mutuwar sarki abakina ba kibari idan tayi tsami kyaji da kanki kinsa ance waƙa abakin me ita tafi daɗi,
aikam cike da farin ciki da annashuwa tace to Allah ya nuna min wannan ranar idan da gaske kake danni nasan wannan abune me wahala bazan yarda ba har sai lokacin da ya tabbata,
to shikenan momma zaki yarda ne bari de muje kawai muna ƙara ɓata loƙaci to shikenan sai kundawo ku tuso min ƙyeyarsa yazo yaci abinci kafin ku wuce,
"yace to momma ai zama mubiyo mu ɗauki Ameesha idan zamu tafi,
dan taɓe baki tayi tace ai bangaya muku bama ai yarinyar nan tazama ƴar gida yanzu hakama basa cikin nan bakuji ba hayaniyar suba sunshiga cikin gida wataƙil ma suna sashen su Maman Ammar (yar uwar ta wacce aka haifesu tare me suna karima),
kubarta tunda ba makaranta tayi week end anan agayawa mahaifiyar ta kun ara mana ita dan haka kuje abun ku dan tasamu ƙawaye baka ga yanda ta sake acikin suba,
duk shiru sukayi babu wanda ya iya tanka mata,
naji kunyi shiru ko baza kubarta bane ta katse musu shirun nasu
da sauri bossay yace a'a shikenan ba matsala Allah yakaimu,
shide shettima ba haka yaso ba gaba ɗayan suma ba haka suka so ba amma ba yanda suka iya baza su iya cemata a'a ba suna ganin girmanta baikamata tazo musu da wata buƙata ba su hanata bata cancanci haka agare suba dole su amince ko suna so ko basa so,
sallama sukayi mata sannan suka tafi shettima ne yayi bossay jagora har suka ƙarasa part ɗin mama fulani suna shiga ba kowa afalon direct suka nufi dakin sa afalo sukayi sallama amma ba amsa dan haka kai tsaye shettima yatura kofar suka shiga ciki,
nan made bayanan dan haka suka ƙara nufar ɗakin sa,
"akan sallaya suka gansa yana sallah zama sukayi sukajira har ya idar sannan suka fara yi masa magana suna tsokanar sa yanzu ka kyauta mana dan Allah awa nawa mukayi muna jiranka ko soyayya ce tayi daɗi ka manta damu, banza yayi dasu ya tashi daga kai yadauke sallayar sannan yasaka kayan bacci yagama duk yana jinsu amma yaƙi tanka musu har yaƙarasa duk abun da zaiyi ya haye gado tare da jan abun rufa,
kutumar ubanan shettima yace tare da miƙewa tsaye ya doshi inda yake kwance yana zuwa ya yaye abun rufar tasa..............✍️✍️✍️
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
[6/15, 11:22 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️57&58
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"kutumar ubanan shettima yace tare da miƙewa tsaye ya doshi inda yake kwance yana zuwa ya yaye abun rufar tasa..............✍️
wallahi sai ka tashi saboda tsabar rashin mutun ci tun dazu muna jiranka amma kazo kayi kwanciyar ka kana shirin yin bacci saboda ka maida mu ƴan isaka,
tashi zaune yayi tare da dafe kansa batare da yakalle saba yace dan Allah karabu dani da abun da yake damuna kar ka ƙara min wani ciwon kan,
"au haka ma zakace mune ciwon kan Kenan?
to ai naga bakuzo da niyar jin komai ba shiyasa nayi muku haka idan kun gama sai kutafi inyaso gobe mayi magana yaƙarasa maganar tare da komawa ya kwanta,
shettima yace to shikenan badama mutum yaga abu bazai faɗa ba mufa duk abun da muka gani sai munfaɗa ko me zai faru saidai yafaru ah to idan kuma mutum bayaso afaɗa sai ya dena yin abun gaɗan danma kaci sa'a bangayawa momma ba,
Ina jin tsotone kaje kafaɗawa duk wanda zaka gayawa kuma kufitar min daga ɗaki gobe da safe ƙarfe takwas zamu bar garin nan zuwa Abuja kar wanda ya ɓata mana loƙaci mu haɗu a hospital,
in kunfita kurufe min ƙofa yana kaiwa nan yaƙara jan blanket ɗin saya rufe har kansa,
tseye shettima yayi batare da ya motsaba Saida yagama tsayiwar SA Dan kansa sannan ya matsa daga gurin sa inda bossay yake ya kalla yaga har yafara gyangyaɗin bacci tashin sa yayi yace mutafi kawai sai gobe,
"dan murza idonsa yayi tare da yin miƙa da hamma duk aloƙaci ɗaya sannan ya gyara tsayuwar sa yace me yace maka dan shi tun shigowar su ya fara gyangyadi dan duk ba jin zancen su yake ba,
kasan shi de me hali baya fasa halin SA yau mutanen ne suka motsa yaƙi cewa komai kawide yace mutafi wai gobe ƙarfe takwas mi haɗu a hospital zamu tafi abuja,
"abuja Kuma? bossay yatambaya,
"Eh haka yace"
me zamuyi acan? "nima bansani ba muje kawai muna ƙara yin dare Allah yakaimu gobe maji duk ma abun dake wakana tunda bega damar sanar damu ba sai mu hakura,
ok to shikenan mu wuce, tare suka jera suka nufi ƙofar waje har sun kusa fita dan har sun saka ƙafar su awaje shettima yayi saurin dakatawa tare da juyowa yace ai bamu karɓi key ɗin ba yana faɗar haka ya koma da baya tare da ɗan ɗaga murya tun kafin ya ƙarasa wajen sam ɗin yace where is the key?
shiru baibasa amsa ba, har yana Shirin ƙara tambayar sa yaji yace yana jikin motar mana me zanyi dashi anan ko anacin muƙulli ne duk kunbi kunta kurawa rayuwata wallahi,
tsaki shettima yaja batare da ya kulasa ba ya juya suka fita,
suna fita suka shiga motar tare da barin masarautar saida yafara kai bossay gida sannan shima ya wuce gida,
bayan yaje gida tunkan ya buɗe ƙogar hajiyar sa ta rigasa buɗewa tare da cewa ina take naganka kai kaɗai tunɗazu kasa nakasa tsaye nakasa zaune ina jiranku,
Oh hajiya to meye na damuwa kinsande bazan bari wani abun yasame ta ba yafaɗa yana jan hannunta suka koma cikin falon,
"to inba abun davyasame ta inganta mana yanzu kuma me katsata yi yanzu fa shaɗaya saura,
zuba mata ido yayi saida yabari takai aya sannan yace hajiya yau nafara kai shaɗaya awaje naga har sha biyu ina kaiwa amma baki taɓata tamyata ba sai yau naga alamar wannan yarinyar inbanyi wasa ba kwacen uwa tunda anfi damuwa da ita akaina,
ɗan murmushi hajiya tayi masa tare da lakace masa hanci sannan tace naji koma me zakace kace ayanzu de nafi ji da ita akan ka dan haka gaya min inda ka kaimin yarinya kafin muhau sama dakai yanzun nan,
"siyar da ita nayi fa yanzu haka ma kuɗin suna cikin boot masu yawa zo muje ma kigansu kuma ki shirya gobe zamu bar ƙasar nan dan mungama kuɗi yaƙarasa maganar cike da basarwa kamar da gaske yake,
ahh ashe bani kaɗai nake wannan hasashen ba tun farkon ganina da yarinyar nasan zatayi tsada idan akasiyar da ita mungama kuɗi daman shirya yanda za ayi nake ta faman yi nakasa yanda zan ɓullowa abun sai gashi kai harka gama min da ita gaskiya kayi namijin ƙoƙari yakamata injinjinawa jarimin ɗana to yanzu ya akeciki wacce ƙasar Ka shirya mana zamu koma dan harna ƙosa ma gari ya waye inganni aƙasar waje, ya kaganni acan tafaɗa tana wani ɗage masa gira tare da kallon kanta tundaga sama har ƙasa tana ɗan karkaɗa kai,
tunda tafara maganar yake faman tiƙar dariya harda dafe ciki jin yanda ta bashi amsa daidai dashi saida yayi me isarsa sannan ya dakata yace hajiya kinfi ƙarfina ai, to ƴarki tana gidan su sam momma tace abarta tayi weekend tare da su Amra,
itama dariyar tayi sannan tace to ai shikenan Allah yakaimu, daga nan de suka ɗan taɓa hira har yasanar da ita tafiyar dazasuyi gobe, daga nan sukayi sallama kowa ya nufi ɗakinsa,
*Washe gari*
kamar yanda yagaya musu hakan sukayi gaba ɗayan su babu Wanda ya wuce loƙacin da yabasu amma duk da haka yariga su zuwa a can suka sameshi ,
bayan sun shiga ciki sun haɗu sun gaisa fuska ba fus ba asss suka gaisa dasu sannan yasanar dasu duk yanda sukayi da mahaifin sumy har zuwa inda zasu da kwatancen da yabasu bai rage musuba bayan ya gama yi musu bayanin,
shettima yace to Allah yakaimu lafiya yadawo damu lafiya Allah yabamu nasara, ɗan dakatawa yayi sannan yace yauwa munji wannan bayanin amma baka yimana ɗayan bayanin ba Ka barmu cikin duhu har yanzu bamu kawo haske ba,
cike da rashin fahimta sam yake kallon sa har yagama maganar sannan yace wane bayanin kuma banfahimce ka ba,
ɗage masa gira ɗaya yayi yana dan sakin murmushi sai kuma ya kwantar da hannun wansa duka kamar za aɗora masa abu sannan yafara yawo dasu kamar yaɗau jariri yanayi yana kallon sa
shide Sam har yanzu bai gane me yake nufi ba,
ganin bai fahimta ba yasa sam cewa I'm so sorry pls stop carrying I hate it yaɗa cike da kwaikwayon irin muryar sa,
sai yanzu yagane abun da yake nufi duka yakaima sa adantsen hannun sa shettima yayi saurin gocewa yana dariya bossay ma dariyar yake masa,
memakon yaji haushin dariyar da suke masa, kawai baisan loƙacin da shima murmushi ya kwace masa ba,
Ahhhh ehh shikenan wlh ai bama sai kabamu amsaba mungane komai awannan murmushin cewar shettima,
bossay ya ɗora dacewa nidai tunda nake dashi bantaɓa ganin murmushi akan fuskar saba amma yau dalilin wata nagani kagafa har yanzu yakasa dainawa yaƙarasa maganar yana nuna sam,
ai nagani yau dole inkaiwa momma albishir daman ban tabbatar bane shiyasa bangaya Mata ba tun ɗazu amma yanzu zataji komai,
haɗe rai yayi kamar bashine ya gama yin murmushi ba, cike da dakewa yakalle su yana nunasu da yatsa yace wallahi bana son shirme da shiririta ku bakusan aikin da yake gaban kuba ko to koma me kuke tunanin da yarinyar nan ba hakabane babu wani abu da yashafi abun da kuke tunani dan haka kubar duk wani banzan tunani agefe mufuskan ci abun da yake gaban mu in kunga dama kufito mutafi in kuma zaku cigaba da zama sai kuyi tazama agun ni kunga tafiyata yana kaiwa nan yayi gaba yabarsu agun da baki sake, yana jiyo su suka cigaba da dariyar su da kuma surutun su basu fasaba bayaso suyi tunanin wani abun danshi bahaka bane agurin sa abun da basu sani ba akwai abun da yatuna da yasashi yin murmushi amma sunzo suna ta shirmen su akan wani tunanin daban,
yana zuwa wajen motar suma suka fito baya ya buɗe ya shiga sukuma suka shiga gaba shettima ne a mazaunin driver bosssy kuma agefen sa ahaka ya tayar da motar suka fice daga cikin asibitin. suka dauki hanyar Abuja.......
*ABUJA*
tunda maama(sabreena) ta idar da sallahr asuba bata koma ba tayi zaune bayan ta gama addu'o'in ta ta zauna abakin gadon tana jiran gari yayi haske taje tace musu zata tafi dan bacci ma da ƙyar tayi shi jiya so take kawai tagan ta agarin kano...
har gari yayi haske sosai amma bata ji motsin kowa ba datagade tagaji da zam kuma bataji ɗuriyar su yasata fitowa daga ɗakin ta dawo falo tsayawa tayi ta shiga ƙarewa gidan kallo daki daki take bin ki ina na falon da kallo ahaka har idonta ya faɗa kan wani tafkeken hoto da yake can wani lungu gabanta taji yayi wata iriyar