mummunar faɗuwa da har saida ta dafe gefen zuciyar ta sannan tashiga karanto sunayen Allah saida taɗanji daidai sannan tafara takawa ahankali zuwa wajen hoton tare da kafe shi da ido bata ko ƙiftawa,. tana daf da ƙaraswa gurin taji takun mutum alamar ana daukowa daga bene tsayawa tayi tare da ɗan juyowa dan ganin wanda yake saukowa, ido biyu sukayi da ummy da take sanye cikin abaya pitch collar da miyafin ta Kalar ta,
tunda taga maama ta shiga sakin murmushi harta ƙarasa saukowa takowa tayi har inda take tana ƙara faɗaɗa murmushin ta sannan ta gaida ita , bayan sungama gaisawa, ma'ana tace yauwa tunɗazu nake jiran fitowar ku danni na riga da nagama shiryawa tafiya kawai nake sonyi kigayawa me gidan naki,
sosai abun yabawa ummy ba yanzu duk bayanin du sukayi mata jiya bata yarda ba ashe ya shiga ta hagu ya fita da dama, ajiye duk wani mamakin ta tayi agefe sannan ta sakar mata murmushi tace to shikenan maama bari zan kirasa ai yama tashi shima amma bari kifara karyawa sai inkirashi ɗin tana gama maganar ta kamo hannun ta suka koma kan kujera ta zaunar da ita,
maama kam binta kawai take bata ƙara cewa komai ba,
bayan ta zauna ta kwalawa me aikin su kira tasanar da ita cewar ta haɗo mata breakfast bata dau loƙaci ba taje ta haɗo ta kawo, zatayi saving ɗinta ummy tayi saurin dakatar da ita dacewa taje kawai,
da kanta ta sauko tayi saving ɗin maam ƙarɓa tayi tare dayi mata godiya sannan tafara ci yaude tace da ɗan yawa ba laifi bayan ta tagama, aka kwashe kayan, sannan ta maida hankalinta ga ummy tace to nagama ci sai kije ki sanar dashi dan bana so ƙarfe goma tayi min acikin garinnan,
ba yanda Ummy ta iya dole ta tashi taje ta sanar dashi duk yanda atakaicedai duk yanda sukaso su shawo kan abun ta haƙura sai gobe ƙin yarda tayi daga ƙarshe ma tace zata tafi da kanta sai da suka ga haka sannan suka ce mata sun yarda zasutafin ba shiri suka hau harhaɗa kayan da zasu tafi dashi duk da bawani kayan shirgi suka ɗauka ba iya abun da yazamar musu dole ne suka ɗauka loƙacin da suka gama shirya wa suka fito loƙacin ƙarfe shabiyu saura,
jirgi suka so suhau amma babu dama saboda basuyi boocki ɗin ticket ba tun wuri, dan haka dole suka tarkata inasu inasu suka shiga mota har driver yazo zai jasu amma abu ya dakatar dashi yace meer yajasu saboda basu san ranar dawowar suba bazai yiyu su tafi dashi can ba gwara yake gida idan sun dawo sai yadawo,
godiya yayi musu yaƙara gaba abunsa,
shikuma meer badan ransa yasoba zaiyi tuƙin nan ba wallahi dan shifa arayuwata sa bayason aikin wahala duk abun dazaisa yaji yagaji baya yayi bare kuma tuƙi da basaba yi yayiba ace kuma tundaga nan har zuwa wani garin duk dade bai taɓa zuwaba amma yasan dole yayi nisa,
yanata cika yana batsewa ya shiga ya tayar da motar aransa yana rayawa dabadan wannan matar ba wallahi ba abun da zaisaka shi yin tuƙin amma anci darajar wannan matar,
kan titi suka hau sai kuma yace wacce hanyar zanbi yafaɗa batare da ya kalli inda Abu yake ba dake gefen sa azaune,
da hannu Abu ya nuna masa inda zaibi da gudu kuwa yaja motar kamar zasu tashi sama haka yake jan motar saida Abu yayi masa magana akan ya rage gudun da yake amma kamar ma zigashi yayi haka yake tafiya,
sunzo wajen danja inda aka tsayar da motoci tsayawa yayi badan yasoba yana ta faman jijjiga kai kamar yaci gaba da tafiya haka yakeji jikin sa ha tsuma yake, ana basu hannu kuwa yaƙara jan motar aguje tare da buge motar gaban sa batare da ya bi takan buge motar dayayi ba kuma sarai yaji ya gani amma yaƙara gaba ko waiwayar su baiyi ba,
motar da suka buga suma da gudu me jan motar yaja motar tare da bin bayansu, kusan yar tsere suka fara su meer nagaba motar da suka bige na bayansu shima yana zuba nasa gudun dan ganin sun cimma su meer,
Saida ya ƙure wuta sosai sannan yakamosu wuce su yayi tare da shan gaban motar su meer,.
wani wawan burki meer yaja da saida yasa su ummy sakin salati gaba ɗayansu dan sun saddaƙar ma ya buga musu motar,
meer na jan burki ya ɓalle morfin motar tare da fitowa azafafe Abu na kiranshi kar yafita ya tsaya amma ina baisaurare sa yafita,
shima wancen ɗin azafafen ya fito daga tasu motar zuciyar sa na tafasa ,
gaba ɗayan su suna fitowa kowanne su gadan gadan sukayi kan juna batare da kowa ya tankawa kowa ba saboda daman kowa yasan laifin da yayi,
da sauri su ummy da abu suka fito daga motar suka nufi bayan meer zasu riƙeshi dan gudun abun da suka ga yana shirin yi............✍️✍️✍️✍️✍️
Tofa wata sabuwa🤔 masu karatu me kuke tunanin zai faru anan gurin????
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
[6/19, 7:23 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️59&60
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"da sauri su ummy da abu suka fito daga motar suka nufi bayan meer zasu riƙeshi dan gudun abun da suka ga yana shirin yi............✍️
saidai ina tunkafin suƙarasa garesa har sunkaiwa juna shaƙa atare meer ne yafara kaiwa ɗayan duka abaki atake bakin ya fashe shima cikin zafin nama da taƙaicin naushin da yayi masa shima yaɗaugo da nasa hannun yakai masa naushi amma sai kafin yakai ga fuskar meer, meer yayi azamar cafke hannusa kuma yana cafkewa ya murɗe hannu,
jin zafi da yayi yasakashi dauko duka ƙarfinsa da jarumtarsa shima ya murɗewa meer hannu duk da bawani sosai ya murɗa masa ba saboda ƙarfin su ba ɗaya bane duk da kowa yanaji da nasa ƙarfin amma zubin hallitarsu ma ba ɗaya ba meer yafishi ƙirar maza amurɗe yake,
duk ƙoƙarin Abu da su ummy da sukeyi wajen ganin sun rabasu amma hakan ya gagara, dan caƙumewa sukayi da faɗa kowa zuciyarsa akusa take kamar zata fito waje su shettima na suma suka fara ƙoƙarin rabasu amma sunkasa sai dukan jikin su suke kamar suna filin daga haka suke dukan junansu daga ƙarshede meer yayi kukan kura ya tattaro duka ƙarfin sa ya cukwikuye sam ya ɗaga sa sama ya nunawa Allah yana shirin direshi ƙasa (oh 🤔ashede gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta yau sam ya anhaɗu da wanda ya fishi zafin rai) maama da su ummy gaɗayan su babu wanda baije gurin ba sukayi saurin ririƙe hannun sa suna haɗasa da Allah akan ya daukesa cikin ɓacin tai Abu yace wlh idan baka saukesa ba sai ranka yayi mummunar ɓaci dan sai na nuna maka fushin dabaka taɓa gani ba tunɗazu muna maka magana amma kaƙi sauraron kowa saboda raini to dan ubanka kar ka fasa kaci gaba kaga yanda zanyi dakai agurin nan yaƙarasa maganar yana sakin hannu sa da yariƙe shi saboda shima fa zuciyar tazo kusa kiris yake jira shima yafara kai dukan saboda yanda kukaga meer shima haka yake dan meer gada yayi daga garesa saidai bambancin su shi Abu yanzu da ya manyanta ya rage sosai baya sai kakaishi ƙarshe nan zaka ga ɓacin ransa saboda wata irin zuciya garesu me abu kaɗan zasu maida shi yazama babba musamman meer bashida haƙuri kwata kwata baima sanshi ba,
yasan halin mahaifin nasa sarai tunda yaji yafara irin wannan batun to yasan zai iyayin komai akansa koda ba duka bane to zai iya musguna masa ta wani fannin shiyasa badan yaso ba kuma azuciyar sa bawai dan yana tsoron mahaifin nasa bane kawadai baisan me zai mishi bane bayaso yayi masa wani abun da zai ja masa raini agaban waɗan nan yaran,(kunji fa tsaurin ido wai su sam ɗinne yara tabb)
kuma duk abunsa ba yana ɗagawa mahaifinsa ƙafa ƙarewa ma baifiye shiga harkarsa ba saboda irin waɗannan abubuwan dan inbeyi baya baya dashi ba wataran za a iya samun matsala atsakani shikuma bayason hakan tafaru saboda yasan halin zuciyar ba daidai take da ta mutane ba,.
sauke sa yayi saida fa kuma yana saukesa ya hankaɗa sa gefe yafaɗi,
tofa mutumin bai daddara ba da sauri yasake miƙewa tare da narko masa wata ƙatuwar ashar da tunda nake ni bantaɓa ma jin irin ta ba ko a ina yasamo ta oho dande maimaita saɓo, saɓo ne da nafaɗa muku irin zagin nasa,
saidai abanza dan ko akwalar meer saboda baisan ma zagi bane haka su abu ma duk ba wanda yasan me yace saidai su shettima sungane kalar zagin nasa duk da halin da suke ciki hakan bai hana dariya fitowa ba dariya suka shigayi,
da sauri sam ya juya yakalle su da mamaki ƙarara a fuskar sa suna nufin su abunma dariya yabasu meyasa suna ganin halin da yake ciki amma su shiga yi masa dariya,
suna ganin ya juyo yana kallon su sukayi saurin haɗiye dariyar su ganin irin kallon da yake musu ya suka shiga sunnar da kai ƙasa suna wurwurga ido ba wanda ya ƙara iya haɗa ido dashi,
jinjina kai yayi tare da barin abun da zai musu acikin ransa yayi sannan ya juya ga meer da yake ta faman fitar da huci da iska me zafi daga bakin sa haɗi da jefawa sam kallo me ma 'anoni da yawa da kuma gargaɗi,
ganin irin kallon da yayi masa batare da ya karaya ba yaƙara yin kansa yana zaginsa yanace wallahi sai na kasheka bade ni kayiwa hakaba sai ka gane baka da wayo sai nasaka nadamar sanina arayuwarka wallahi sai na kasheka saidai uwarka ta haifi wa........tassss yaji andaukesa da mari bai ankara ba yaji an ƙara sauke masa bashi kaɗai ba gaba ɗayansu babu wanda beyi mamakin marin da maama tayi masa ba,
dafe fuskar yayi tare da saurin ɗagowa dan ganin wanda ya mare sa waro ido yayi da mamaki yake binta da kallo aransa yake ƙara mamakin meyasa wannan tsohuwar marinsa me yayi mata,
sauke hannusa yayi zuciyar sa na tafarfasa yace saboda son kai zaki mareni shi bakiga abun da yayi mana ba amma ba wanda yaga abun da yayi shine zaki mareni saboda ku kukakawo sonkai duniya ko kuma angaya muku shikaɗai ne ɗa me gata to muma ai bada gidan matsiyata muka fito ba da gatanmu badaga sama aka jefo muba kuma wallahi sai na iya sawa anɗaure duka dangin ku kubar ganin kuna da kuɗi kai kuma ka ɗauka ƙarfina kafi ko yafaɗa yana maida kallon sa ga meer to wallahi baka daki banza dan bazan taɓa barin kaba duk inda ka shiga sai na memoka sai nasa anƙulleku gaba ɗayan ku matsiyata kawai,
jinjina kai shettima yayi jin ƙarfin hali irin na sam wai matsiyata kuma zaisa a ƙullesu shi a iya kallo ɗaya ma kayiwa mutanen nan ai kasan ba ƙananun mutane bane acan de kano kayi gadara da gidan sarautar da kake ji dashi amma anan wayasan ko kai waye duk aransa yake wannan tunanin,
jin maganar tsohuwar yasashi dawowa daga tunanin da ya tafi,
wai ku wacce irin zuciya gareku da bakwa ganin mutane da mutunci to inbaka fasa ƙulle muɗin ba bakaci ka dan halak ba kunzo kuncikawa mutane kunnuwa da surutun banza to wallahi inƙara jin bakin ka anan gurin kaga yanda zanyi dakai marar kunya kai shi baka ga anmasa magana ba yayi shiru ya rabu da kai shine kai dan ba a isa dakaiba kaci gaba da abun da kake saboda baka da kunya agaban mu zaka kama yiwa mutane zagi ko bakaji kunyar saba amatsayin sa na wanda ya girmeka ai kaji kunyar iyayen sa amma kake kiran iyayen nasa kana zaga to wallahi ka ƙara magana sai nayi ƙasa ƙasa dakai anan gurin, buɗe bakin kuwa yayi zaiyi magana ta ɗaga hannu itama zata kai masa duka abaki ba shiri kuwa ya haɗiye maganar tasa ganin da gaske take, sai kawai ya shiga gungunin wannan tsohuwar ta cika faɗa wallahi koma inaruwan ta da shiga abun sa shi ɗayan bata yi masa amma ni tazo tana balbale ni da faɗa saikace wani ɗanta sa'arta ɗaya wallahi kawai dande tsohuwa ce amma da sai ya rama marin da tayi masa,
marar mutunci ai faɗa zakayi inji da kyau baka tsaya kana ƙunƙuni sai kafito fili kayi magana zan gane kai cikakken marar kunyar ne,
ummy ce ta matso kusa da ita tare da riƙo hannun ta tace haba maama ki rabu dashi dan Allah tunda yayi shiru kowa yayi haƙuri kizo mutafi kawai Allah ya kiyaye gaba,
kallon sam tayi tace ɗan kayi haƙuri abisa abun da yayi maka bawai muna goyon bayan sa bane yasa kaji tayi maka haka tayi makane bisa rashin kunyar da kayi agaban mu baikamata ka ringa zagin mutum agaban iyayen saba kasan nadan mu ba zaginnan da kayi masa ba rabuwa zaiyi dakaiba kana gani tunda yafito muke kiran sa akan yatsaya kada ya taɓaka amma bai saurare muba amma kuma kai ka maida laifin kanmu duk ƙoƙarin da mukayi baka gani ba kana ganifa mahaifinsa gashi can ya koma mota yayi fushi dashi kuma tunda ya hanasa bazai ƙara taɓaka ba amma kai kazo kama ta zage zage wanda hakan baidace ba amatsayin ka na ɗa musulmi kadena zagi ko nan gaba ka gyara halin ka bakasan wataran dawa zaka haɗuba arashin sani kuma kaje ka jawowa kanka danasani da jin kunya,
kirabu dashi yayi duk abun da yayi niya jan abun kunya Kum ai yariga da yaja shi,
sam de shiru yayi sai kuma jikin shi yayi sanyi jin ƴar nasihar da ummy tayi masa sai yaji ma kunya ta kamasa, shide inzai iya tunawa ma a kaf rayuwar sa da yataso baitaɓa haɗuwa da mutanen da yaji shakkar su ba irin waɗannan mutanen musamman tsohuwar da yaji yakasa tanka mata duk irin abubuwan da take gaya masa wai harda su mari lalle sunci sa'ar wannan rana ga baɗayan su (nikam nace bawan Allah faɗi gaskiya kace de ka haɗu da wanda yafika karkaje ya ƙara naɗa maka na jaki shiyasa kake shakkar su nide anawa tunanin kenan)
maama muje dan Allah juyawa tayi suka tafi yakin su uku zuwa huɗu sai kuma ta tsaya tare da juyowa ta kalli sam a inda ta barsa ahaka ta gansa,
"ya sunanka ta tambaya gaba ɗayan su suka dago suna kallon ta da kai nake kabi ka tsare ni da ido tafaɗa tana itama tana kallon sa kamar yanda yake kallon sa,
saida yagama jan loƙaci kafin yace SAMEER dam taji gabanta ya faɗi da meer da ummy jin sunan da yafaɗa ya gaba ɗayansu saida suka juyo suka kalle sa jin sunan su iri ɗaya,
ummy ce ta dawo da baya tana ɗan murmushi tace ahh ashe ɗana ne sunanku iri ɗaya kuna faɗa takwara da ta kwara ne ashe,
"jin abun da tace yasa sam ɗaga idonsa yakalli meer caraf suka haɗa ido dashi wani kallo meer ya watsa masa tare da harara irin karka min maganar banza dan kaji ance sunan mu ɗaya shima sam hararar yamayar masa da ita tare da kawar da kansa gefe,
'meer kuma gaba ɗaya ma yabar gurin ya koma can wajen motar sa saidai baishiga ba saboda kallon da yaga Abu nayi masa yasa shima haɗe rai tare da kamewa waje guda ajikin motar yana jiran ƙarasowar su ummy dan yagama gajiya da tsayuwar gurinnan ji yake ma kamar yace yafasa zuwa kano ɗin wannan yaron yazo ya ɓata masa mood ɗin sa gaba ɗaya,
Abu ne ya fito daga motar ganin basu da niyar tahowa, har yayi gaba zai tafi sai kuma yatsaya batare da yajuyo ba yace follow me yana kaiwa nan yayi gaba meer dake tsaye yasan dashi yake beyi wata wata ba yabi bayansa kamar yanda yace duk da bayason komawa kusa dasu,
daidai loƙacin da suka ƙarasa daidai loƙacin sukaji maama na tambayar sa sunan sa dan haka sai suka dakata duk da sunji sunan da yace ɗazu amma yanayin da ta tambayi sunan sunsan harda na na mahaifin sa take nufi
"ur full name? maama taƙara tambayar sa,
"Sameer Abadallah Sameer (SAS)"
jinjina kai tayi tare da yin shiru na wasu ƴan daƙiƙu,
kafin daga bisani ta buɗi baki tace awane gari kake?
zaiyi magana kenan meer ya rigasa da cewa maama wai me zaki mishi sai faman tambayoyi kike masa dan Allah kizo mutafi ni nagaji da wannan surutan kuntsaya da yaro salon jawa kai raini yanzu wannan yaron har yakai matsayin da zaku ringa sa'insar baki dashi shi waye ɗan uban waye ni inbaza kutafi ba wallahi zan fasa zuwa saidai ku nemi wanda zaiyi driving ɗinku yaƙarasa maganar yana ɗan ja da baya saboda jin idon mahaifin sa dayayi akansa yasan sarai kallon sa