Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   47 / 74

138K to 141K   out of 221K words

sai yaji kamar ma anriga da andaura da su dukan da yaji irin nasihar da take masa,

cikin sanyi jiki yace Ammi baki san abun dake faruwa ba ko,

kamo hannu sa tayi suka zauna akan gado saboda taga tsantsar damuwar a fuskar shi da kuma idon sa tasan yana cikin wani halin,

dan shafo fuskar shi tayj tana kallon sa tace gaya min me yake faruwa,

kamar zaiyi kuka yace Ammi sun sace tafa tun jiya muke nemanta bamuganta ba yanzu bansan halin da take ciki va taba raye ko tana mace bansani ba Ammi sun raba ni da ita Ammi bazan juri rashin taba wallahi ina sonta Ammi yana fada sai ga hawaye yafara saukowa,

cike da tausayawa tafara share masa hawayen sa tana cewa yayi shiru saboda ita batama kawo wacce yake nufi ba duk atunanin ta budurwar da yace yana so ita aka sace saida tagama goge masa hawayen sannan tace a wace unguwar take kuma garin ya akai aka saceta ina iyayen ta,

  kasake yayi yana kallon ta jin abun da tace tana nufin ma bata gane wacce yake magana ba,

"zuciyar sace takara karaya wata kwallar na kara taruwa acikin idon sa yace Ammi bakisan wacce nake nufi ba ko?

tace "eh mana" ai baka taba nuna min koda hoton tane bare ka kawota mungaisa,

Ammi Ameesha fa nake nufi,

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu me kake sanar dani abu haka ba dadin ji ya akai haka garin yaya kukayi sakaci har aka dauketa,

Ammi wallahi bamu bane daman ranar da natafi naje gidan sai akace antafi office da ita sai na bisi can daga can kuma muka tafi gidan su dayan wannan wanda akace agidan sarki yake bayan munje muka barta agidan muka tafi..........nanade ya kwashe duk abun da yafaru yabata labari,

Sosai itama ta tsorata da wannan labarin tayi mamaki,

nashiga uku ni Ameena yanzu in ba aganta ba taya zaku tari wannan baiwar Allahn ku gaya mata Allah sarki ashe batayi karya ba jikin ta yagaya mata gaskiya da har ina ganin rashin hakurin ta ashe ta fini gaskiya Allah sarki dadda amma bazanso taji wannan labarin ba kuma nasan muddin baku nemota ba ko ba dade ko bajima sai tasani bazata iya jure rashin taba nasan zata shiga mawuyacin hali inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un  gaskiya wannan abun baiyi min dadi ba bantaba kawo hakan zata faru ba yanzu ita dadda tana can gidan,

"Eh Ammi tana cen yanzude ansa yara suna ta hira dan adebe mata kewa karta tuna da ita dan tace sai ankaita har wajen sarki ta sanar dashi mun dauke mata jika da kyar de ta hakura ta zauna yanzude bansan halin da take ciki ba tana cen ko ta hakuran ko kuma de me yafaru oho sai na koma zanjiyo sode muke zuwa gobe idan munkoma gurin munsamo wata shedar to idan kuma bamu samu ahaka zamu daure kawai mu gaya mata halin da ake ciki tunda ko mun boye yanzu dole tasani nan gaba kuma abun dai yafi mata rashin dadi zata iya cewama bata yarda ba karya muke,

Ammi "tace aikwade ba abun da bazata fada ba bakaga yanda mukayi da itaba dazu da jiya itama labarin abun da yafaru da abun da dadda tace tabasa labari.........,


        ****************************

______*meeshmeer*______

cizo da ta dasa masa ahannu baisan loƙacin da yayi sauri ya sakar mata bakinba kuma yana saki ta ƙara fasa ƙara da saida ta karaɗe duk banɗakin hannu yasa ya toshe kunnuwansa jin tana niyar fasa masa dodon kunne,

tsawa ya daka mata ke wace irin marar hankali ce baki da hankali kinaso ki kashe min dodon kunne ne ko me kike nufi me nayi miki zakisani agaba nida kika cije ni bance komai ba sai ke zakiyiwa mutane ƙara akunne,

sauri tayi ta ta tsugunna tana karkare jikin ta tanayin kuka ƙasa ƙasa jikin ta sai faman ɓari yake,

ba magana nake miki ba? "cikin kuka tace dan Allah kayi haƙuri nidai kafita bazan ƙaraba dan Allah kafita,

shiru yayi yana binta da wani irin mugun kallo yarasa ma wane irin hukunci zaiyi mata nayi masa wannan ƙarar acikin kunne gashi kuma ta cije shi ji yake kamar ya rufeta da mugun duka da zaisa tadena numfashi haka yayi tsaye akanta shi baifitaba kuma shi bai daina kallon ta ba kuma baita ɓata ba,..... itama kuma bata tashi ba daga gurin tana nan yanda take sai hawaye dake zubo mata kamar famfo.....

ummy dake ɗaki ma saida tajiyo ƙarar duka gidan ma saida yaɗauki ƙarar da tayi maama da bacci tajiyo ƙarar kamar amafarki ahankali ta shiga buɗe idon ta tana salati ta tashi zaune tare da dafe kanta tana tunanin ƙarar wacece haka ta tasheta daga baccin da take me daɗi tana mafarki tashi tayi ta wuce bandaki dan tayi wanka tafiya taji meke faruwa ko ba lafiya ba,


ummy dake ƙoƙarin dauko mata kaya jin ƙarar yasata tabar ɗaukowa ta fito da sauri ta fara taka benen dan ita atunanin ta ko faɗiwar ta ƙara yi,

tana zuwa taji ƙofar ɗakin arufe da ƙarfi ta bubbuga tana kiran sunanshi,

yakai hannunsa kenan zai damƙo gashin kanta yaji bugun ƙofar ko ba afaɗa ba yasan ummy ce dan haka da sauri ya janye hannun sa tare da fita daga banɗakin ya nufo wajen ƙofar yana ja ta buɗu ashe daman ƙofar ba akulle take ba kallon sa tayi tace me yake faruwa najiyo ihunta ko wani abun kayi mata?

kai ya girgiza mata yace ni kuma ummy me zan mata ba abun da nayi mata nima ina nan azaune najiyo ƙararta shine naje bakin ƙofar nake tambayar ta me yasameta tace faɗuwa tayi amma yanzude ta tashi tama ce ta kusa gama wankan,

"ayya Allah sarki wallahi nima saida nayi tunanin hakan nace ko faɗuwa tayi ashede hakanne daman nasan da ƙyar zata iya yin tafiya ƙafar nan fa naga alamar wataƙil sai mun kaita asibiti dan kamar ƙara kunbura tayi,

Meer yace eh nima haka nake tunani bari mugama sai muje adubata ko tasamu gocewar ƙashi,

ummy tace to shikenan yanzu bari in maida itama can ɗakin kawai ta shirya idan muka karya sai mutafi gaba ɗaya yanzu je ka taso maama ta shirya muci abinci bari ni intaimakawa wannan yarinyar infito da ita,

badan yaso ba ya amsa mata sannan ya fice daga ɗakin ransa babu daɗi na rashin hukunta tan da baiyi ba amma ba komai zasu haɗu agaba dan haka ya sauka ƙasa ya nufi ɗakin maama nocking yayi ta bashi izinin shigowa yana shiga yama tarar har ta shirya gaida ita yayi sannan yasanar da ita aiken ummy tace ai tama gama suje kawai dan haka atare suka fito dashi inda yaga an jajjere abinci wajen dinning nan yajata sukaje suka zauna yace sujira anan yanzu zasu fito,

kai yaro nikuwa intambaye ka ɗazu ina bacci naji kamar ƙarar yaro bande saniba macece ko namiji ko ba anan gidan bane,

yatsina fuska yayi yace eh anan gidan ne munyi baƙuwa ne ɗazu shine ta faɗi aƙasa shiyasa kikaji tayi wannan ƙarar suna tare da ummy yanzu zasu fito,

maama tace baƙuwa kuma daga ina daga zuwan mu sai baƙuwa ko daman kuna da ƴan uwa anan ne,

"a'a bamu da kowa"

ammade yanzu kiyi shiru kawai kibari idan ummy tafito tagaya miki ko wacece ita danni bazan iya doguwar magana ba ina baki labari.....

da mamaki ta kalle sa amma batace masa komai ba kawai tayi shiru kamar yanda ya nuna yana da bukatar hakan dan haka bata ƙara ko kallon inda yake ba bare tayi masa magana dan itama fa akwai miskilan ci dan yama fi yawa a halaye ta dan magana bata dameta ba.......

ummy nashiga taga Ameesha tsugunne tana faman kuka da sauri taje tana yi mata sannu sannan ta miƙar da ita da ta tai maka mata ta ƙarasa wankan tana ta faman jijjin kunya shaka har suka ƙarasa ta kamota suka fito jikin ta ɗaure da towel suna tafiya tana yi mata sannu har suka fito daga ɗakin suka fara saukowa kan benen dake yana yin falon mutum idan ya sauko daga sama bazaiga na kan dinning ba haka shima nakan dinning ɗin bazaiga me saukowa ba dan haka har suka sauko suka shige basu gansu ba,

ɗayan ɗakin da yake extra ta kaita ta zaunar sannan taje ta lalubo mata wata ƴar doguwar riga da ita ta ɗage mata kuma tayi mata kaɗan daman sannan ta kawo mata tabata ta saka amma duk da haka ta yi mata yawa yawo take aciki bata daura ɗan kwali ba tabar gashin ta dake daure babu komai afuskar ta amma tayi kyau dan ma fuskar tata ta ɗan kun bura saboda kukan da tasha,

kamo hannun ta ummy tayi tana ɗan ɗingisawa ta taka ƙafar da kyar da kuma taimakon ummy suka fito daga ɗakin dinning ɗin ta nufa da ita acewar ta idan ta zaunar da ita sai taje ta taso sauran kowa yafito suci abinci sai kuma taga harma sun rigata zuwa,

da ɗan fara'arta ta ƙarasa gurin tana gaida maama, maama ta amsa mata gaisuwar idon ta yana kan Ameesha da kanta ke ƙasa batare da ta ɗago ba kawai tace ina kwana,

maimakon maama ta amsa mata gaisuwar sai kawai tace a ina kuka samo yarinya naji ɗanki yace wai baƙuwa kukayi amma inbari inkin fito in tambaye ki ko wacece,

jin abun da tace yasa Ameesha ɗagowa dan ganin mai maganar caraf idon su ya haɗe da na juna,

maama ba ƙaramin tsorata tayi ba da ganinta ji tayi ƙirjinta ya wani irin bugawa sakamakon kamanni da tagani a fuskar yarinyar,

da ƙyar ta iya haɗo kalmomin bakin tace ya sunanki?

kallon ta Ameesha ta ƙarayi sannan tace Ameesha,

"A'a na gaskiya kuma full name zaki gaya min,

dan numfasawa Ameesha tayi sannan tace Khadijah Sameer ya.........

ai bata ƙarasa faɗar sunan ba maama tayi zunbur ta miƙe cikin ɗaga murya tace Sameer Sameer Sameer de...... sai ambaton sunan sameer take takasa wata maganar,

gaba ɗayansu suka shiga binta da kallon mamaki.......✍️✍️


Please more comment


                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/6, 11:35 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 82

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️




     " maama ce ta fara takawa ahankali har ta karasa gaban Ameesha taba zuwa takara kurawa fuskarta ido tade tabbatar da kamannin de datagani da gaske ne,

"ina iyayen ki suke ina kuma mahaifin naki, maama ke tambayar ta,

Ameesha shiru tayj takasa bata amsa itama tana kallon ta,

Ummy tace "maama wai meke faruwa kin santane naga kina mara kallon sani,

Juyo maama tayi tana kallon ta tace ko bansan taba amma wannan duk inda ta shiga ta fito tabbas jini nace wallahi yarinyar nan jinina ce ni naji hakan ajikina kallo daya naimata nagane hakan domin ga kamannin dana nan afuskar ta kamar su daya sak tana fitowa naga kamar shi sak,

duk mikewa sukayi suna kara duban su da mamaki dan har suna tunanin anyama kuwa ba ciwon tane ya tashi ba,

ummy ce ta karasa gabanta tare da riko hannun ta tace maama anya kuwa dagaske ne wannan fa yarinyar dazu suka hadu da babana yanzu kina ganin har zaki iya tuna kamannin sa bayan kindade rabon ki dashi inaganin de gaskiya kamace kawai ki manta da wannan maganar kawai kizo muci abinci sai kisha magani,

Kasake maama tayi tana kallon ta idanun ta har sun cicciko da hawaye ta bude baki da kyar tace me kike nufi da insha magani kina nufin ina haukane bansan me nake ba bani da tunani bansan kama ba nida dana taya kike tunanin zan iya manta kamannin sa har yanzu kamannin sa basu bar idona ba ina tuna lokacin da mukayi rayuwa dashi dan haka koma me zakuce kuce amma nidai nasan wannan yarinyar jini nace gashinan tace sunan baban ta sameer kuma nima dana sunan shi sameer,

wallahi ke jini nace kar ki dauki maganar su ina cikin hankalina nake wannan maganar kitaimaka maama duk tabi ta rude sai zuba surutu take tana hawaye tana jan Ameesha sutafi ita kawai akaita wajen danta, ita kuma Ameesha taki binta kuma taki cewa komai sai kuka da takeyi itama takasa magana,

Abu ne da yagama karantar su gaba dayan su yakaraso gabansu batare da yace da su komai ba ya riko hannun Ameesha itama maama ya riko hannun ta sannan yace ya kamata mu zauan sai anfi fahimtar juna yana fadar haka yajasu zuwa falo suma su ummy da meer binsu sukayi abaya,

Afalon kowa yazaunada kyar maama ta zauna shima tare da Ameesha kujera daya suka zauna tarirrike mata hannu dan jitake kamar zata gudu idan tasake ta,

Abu ne yafara magana sunan maama ya kira ta bata amsa masa ba kuma bata dago ba saboda hankalin ta gaba daya yana kan Ameesha sai kara kallon ta take,

maama yakamata kafin kifara yanke hukun ci kifara jin ko ita wacece ban karyata kiba nacewar jinin kice domin jini ba karya bane ko baki fada ba ga kamannin ku kuna kama ana kallon ku ansan jini daya ne saidai kuma banda tabbacin hakan saboda hakan tana iya faruwa kaga me kama dakai alhalin kuma baku hada dangi ba amma de yanzu muna so kifara bamu labarin ki inyaso sai itama muji nata labarin kinga tanan za agane idan kuna da alaka idan kuma labarin ku yasha bambam kinga baku da wata alaka sai mu dauka amatsayin kama ce kawai,

tana gama fada mata ta share hawayen ta tare da kara komawa wajen Ameesha da tayi tsaye agun kamar gunki tana jin maganar matar kamar amafarki,

taba zuwa gaban ta ta rungumeta tana kara sakin kuka kamkam takara yi mata ajikin ta kamar zata mayar da ita cikin jikin ta kaunar yarinyar nakara shigar ta,

sude ba wanda yakara magana agun duk sun zama yan kallo kamar sun samu tv,

har Abu ma da tun farkon faruwar abun yake tsaye daga bayan su yana kallon su,

saida ta dauki lokaci tana rungume da Ameesha sannan ta raba jikin ta da nata ta kamo hannun ta tace muje kikai ni wajen mahaifin ki inason ganin sa ni nasan jikina bazai bani karya ba ammade nafi so ingansa, tayi maganar tana niyar fara jan Ameesha wai su tafi,

ahankali Ameesha ta shiga girgiza mata kai sai hawaye kuma yafara saukowa zirrrr kamar ana turo sa,

Sannan cikin kuka tace nibanda iyaye iyayena sun rasu,

cak sukayi gaba ɗayan su suna kallon ta amma duk da haka maama bata yarda ba,

tsayawa maama tayi agaban ta sannan  tace dan Allah yarinya karkice min bazaki ba kitaimaka kizo muje inga dana ke kadai ce zaki iya hadani dashi na matsu inganshi Kitaimaka min kefa jikata ce ni na haifi mahaifinki awannan cikin nawa tafada tana nunamata cikin ta, tace ni na raine shi inason sa ina kaunar sa amma aka rabani dashi,

sai yanzu ta dago ta kalle sa sannan tace kafin aji nawa ina so tafara bani nata tunda tace bata da iyaye to daga ina tafito ina danginta,

Abu yace "hakane to yarinya ya sunanki?

"Khadeeja ta bashi amsa murya can kasa kasa,

to malama khadeeja muna sauraron ki zaki iya bamu dan takaitaccen bayani game da rayuwar ki kibamu labarin ki tundade ai duk kinde ji abun da akace kuma matar nan tace ke jinin tace tana tunanin ke jikar tace dan haka sai ki bamu labari ko Allah zaisa tunanin ta yakasance gaskiya kicire mu daga kokon to gaba dayan mu dan nima kaina ina bukatar jin karin bayani saboda nima naga kamannin ku da ita shiyasa muke so ki warware mana wannan zargin da muke muna sauraron ki malama khadeeja,

shiru Ameesha tayi kamar bazatayi magana ba sai kuma ta gyara zama kalamar da ta fara fitowa daga bakin ta sai cewa tayi tunanin ku zai iya zama gaskiya kamar yanda nace muku iyayen na sun mutu to dagskede mahaifiyata ta rasu amma mahaifina bai rasu ba amma ni kaina bansan shiba bansan ya kamannin sa suke ba ban taba ganin saba,

ni na taso ahannun kakata ne mukadai na taso nagani daga ni sai ita tunda nafara mallakar hankalina nake tambayar ta ina iyaye na da kuma dangina sai taki gaya min dan munsha fada ma da ita saboda ina aiki awani gida to mutanen gidan innayi laifi suna dukana sannan su zageni akan ni wai yar shegiya ce tsintacciya zagide ba irin wanda basamin ni kuma innakoma sai insaka ta agaba ince sai tagaya min amma bata gaya min muna haka wataran wani saurayin yarinyar gidan muna mutunci dashi wani zuwa da yayi sai ya tarar sundakenin yatadda ni ina kuka anan yake tambayata nikuma na bashi labarin halin da nake ciki shine yace zai daukeni yamayar dani gidan su da farko kakata taki amincewa sai da kyar de ta amince zamu koma aranar da zamu koma kuma wasu mutane suka shigo gidan sukayi min duka har suka kusan kasheni suna cewa wai ai kakata ta basu abun dasuke bukata in bahakaba kuma zasu kashe ni nan tace musu zata basu amma duk da haka saida suka dakeni suka bugan wani abu su atunanin su ma na mutu,

daga nan bankara sanin halin da nake cikiba sai bayan wasu kwanaki danayi a asibiti......labarin de duk abun da yafafu da ita tundaga farko har karshe tabasu bata boye musu komai ba har labarin da dadda tabasu da barin ta gidan su bossay har kawo yanzu zuwanta gidan su sama da sacetan da akayi da gargadin da matar nan

47 / 74