ku kinfi rainani wallahi to wallahi saidai uwarki ta baku gu kusha isakar dan duk sai kun mutu kunbarni sai naga gawar kowa acikinku har ubanna ki daman shi naga harma yafini tsufa da wuri zai mutu wannan wallahi bai gaji jiki irin nawaba duk wanda ya biyo ni bazai mutu da wuri ba amma duk da haka sai ya rigani mutuwa,
ohh gwaggo ai namanta ashefa ke za abawa gadin duniyar ma gaba ɗaya kece me gadin ta sai kowa na duniya ya mutu ya barki ko hajiya gwaggo,
aniyarki ta biki komade menene sai kun mutu kun barni ko banyi gadin duniya ba ammade kiris zai rage bankaiba dan ina mutuwa ba daɗewa za ayi tashin duniya kowama ya mutu a huta,
dariya momma tayi ganin gwaggo zata fara sakin layi yasatayi saurin cewa bari inkawo miki wani abun idan kinci maci gaba daga inda muka tsaya Hajiya gwaggo me ranƙafe Allah ya nuna min ranar mutuwarki ranar har ƙaramin shagali zamu haɗa tana tafaɗa tayi saurin barin wajen amma duk da haka saida gwaggo ta jefe ta da filo tana ƙara sirfa mata wata masifar harda su zagi itade momma dariya kawai take har ta ƙarasa kitchen daman sun saba indai suka haɗu sun ringayi kenan har sai sun rabu kuma daman duk cikin jikokin ta sunfi wasan jika da kaka shiyasa yanzuma da suka gama zaman fadar da harta tafi sai kuma ta fasa tace sai tazo wajen ta.......
ba jimawa momma ta fito da try cike da kayan marmari data yanyanko mata sai sai juce da kuma snaks duk ta haɗo mata ta ajiye mata agaban ta sannan ta kalle ta tace to acici dame za afara gashinan kicinye idan ma bai ishekeba sai aƙaro wani tafaɗi maganar tana tashi ta koma gefen kujerar ta ta zauna tana kallon ta,
gwaggo kam sai faman washe baki take saikace bata taɓa ciba ko kuma bata saba ciba haka take intaga abinci itade tana son abinci koma meye kawai taga bakin ta na tauna,
meat fie ta fara ɗauka takai baki saidai tauna ɗaya tayi masa ta dawo dashi saboda yaji da taji,
"Amma kede akwai muguwa wallahi kinsan bana son yaji ko kaɗan amma shine kika kawo min shi danki cutar dani ko to ke da Allah ga abunki nan ni nama fasa ci gaba ɗaya sai ki kwashe kayanki hankalin ki ya kwanta naƙi ci daman haka kike so tafaɗi maganar harda hararar ta tana kawar da kai gefe,
"momma saura kiris dariya ta kwace mata ganin yanda tayi saurin kaiwa baki kuma tayi saurin dawo dashi kunshe dariyar ta tayi gudun karta ƙara harzuƙa gwaggo tayi saurin saukowa ƙasa tace haba gwaggo ta kinsan de ai bazan taɓa baki abun da zan cutar dake ba kiyi haƙuri kici wani abun wallahi bansan da yajiba aciki bani nayi ba kuma banci ba ga fruit nan kisha bari insamo miki wani abun marar yaji wallahi bansan da yaji ba Allah da gaske nake, "dalla malama rufe min baki kina sane ai kikawo min bazan taɓa yarda bakisane ba ni bari ma kiga tafiyata basai na ƙara dawowa wajen ki ba bare kicutar dani sokike daman kiga bayana ai to saidai ni inga bayanki duk baƙin cikin ki, tafaɗa harda dungure mata kai sannan ta miƙe tsaye,
da sauri momma ta miƙe itama tace dan Allah gwaggo na kiyi haƙuri kici wani abu inma baza kici komai ba kizauna muyi hira kinga kindaɗe daman bakizo ba kuma nasan inkika tafi zamu daɗe bamu ƙara haɗuwa ba,
"ni bazan zauna ba idan kinason ganina kibiyo ni inda nake amma bazaki ƙara ganin ƙafata anan gurin ba, ke karma kizo inda nake na hutar dake daga yau bani bake munkunce mutun cin dake tsakanin mu mun raba gari dake tunda ke muguwa ce,
"haba gwaggo tunda muke dake haka ta taɓa faruwa banda yau yauɗin ma kuskure akasamu dan Allah kizauna,
da ƙyar tasamu ta lallaɓata ta haƙura ta zauna itama ɗin daman ba tafiya zatayi ba tsokanar ta take kawai,
zama tayi taci gaba da shan fruit tana sha tana lumshe ido saida ta kusa rabi sannan tadakata tare da kallon momma tace ke wai ina wannan marar mutuncin ɗan naki da baya ganin kowa da gashi naji ance yadawo amma bantaɓa ganin saba,
"ai ya daɗe dawowa ma gwaggo dan yamafi wata ɗaya baizo ya gaidake ba?
"kinturo sa ne ai bakice yazo ba duk wani hali da yakeyi ai ku kuke ɗaure masa gindi shiyasa yake ƙara raina kowa ni asuwa zaije inda nake harma ya gaida ni yaron da wataran zaka haɗu dashi ahanya amma yanuna baisan dakai aduniyar bama bare yasan kana gurin ai wannan yaron wallahi kaf zuri'ata bame baƙin hali irin nasa ga shegen taurin kai bansan inda ya ɗauko wannan mugun halin ba dannidai bahaka nakeba kuma ƴaƴana ma bahaka suke ba kuma Sa'adatu ma bahaka take ba bare ince ki ita yagado,
cikin sanyin murya momma tace wallahi gwaggo ba wanda yake ɗaure masa gindi kullum cikin faɗa nake masa amma kullum abun nasa gaba yake saidai mucigaba da yi masa addu'a itakaɗai ce zata gyara sa,
taɓe baki gwaggo tayi cikin ko inkula da yanayin da momma tayi magana saima ciga da cewa tayi kedai wallahi baki yi sa'ar ƴaƴa ba hargwangwan da ɗayar ma akan wannan ja'irar yarinya me kama da tsutsotsi kullum cikin mutsul mutsul take sai fitina kamar beranniya batason zama guri ɗaya ni harna tsani ma tazo inda nake ganaci kuma ina koranta tana ƙara danno kai kace kuma zaka daketa tasa kajiwa kanka ciwo abanza shiyasa bana kulata idan tazo nake mata banza tagama abunta ta tafi dan wallahi tafi ƙarfin.......
"bata ƙarasa maganar ba taji faɗowar mutum akanta...
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nashiga uku zata karya ni wallahi zata karyani abun da gwaggo take ta faman faɗa kenan tana ture Amra dake kanta ɗane ɗane akanta tana mata dariya,
"ɗaga ni dan jakar ubanki kedai wannan bazaki ga annabi ba iya cin zalina dakike zai hanaki ganin annabi muguwa kawai nadan ƙashin nawa me ƙwari bane ai da tuni kindaɗe da ɓaɓɓllani kin karairaya min ƙafafu bazaki ɗagani ba sai nacimiki uwa agunnan wallahi kifita daga idona inrufe tana maganar tana tureta daga kanta amma taƙi tashi sai faman dariya take mata tana cewa "Allah bazan sauka ba nayi missing ɗinki dayawa fa yau wajen kwana uku kenan banga wannan ya gwalgwalalliyar fuskar taki ba me kama da ruɓaɓɓan tumatur wallahi matar nan ki tusfa da yawa bari muji da sauran ki ko kuma kinzama laida tana faɗar haka tasauka daga kanta duk a tunanin gwaggo ɗaga tan datayi tarabu da ita kenan dan harda murna ganin ta ɗagatan saidai kuma bazato ba tsammani taji an yago mata fatar fuskar ta wajen kumatu ai ba shiri gwaggo tasaki ƙara tana riƙe gurin tama cewa shikenan yau tarabani da fuskata ku dubamin babu komai anan gurin tafaɗa tana nuna musu inda takejin zafin Allah sarki tsohuwa ta rikice abun tausayi abun dariya,
ita kwa Amra dariya take harda riƙe ciki tanayi tana nunata da yatsa sannan tace wai daman kinajin zafi har yanzu fatar nan daman bata mutu ba ai ni nazata fa bazakiji zafi ba ayyya gwaggon mu me ran roba yi haƙuri bansan da zafi ba wai nan haƙuri take bata amma tana maganar tana dariya data gama maganar ma ta ƙara kwashewa da wata dariyar muguntar,
"momma ce tayi mata magana tace meyasa zakiyiwa gwaggo haka dan Allah kinga yanzu kinjawo mana bala'i tunda kika sa ta zubar da hawaye itama momma dariyar take son yi amma ta dake saboda kar gwaggo ta haɗa da ita idan ta dawo hayyacin ta,
Allah ya isa tsakanina dake wallahi bazan barki ba sainasa an zane minke sai an farfasa miki jiki ni zakiyi wa wannan rashin mutuncin cire min fata to kwa wallahi bakiyi a abanza ba wannan karon sai rama duk muguntar dakike min sai narama ta yauɗin nan bari wancen marar mutuncin yadawo tunda shi kike tsoro daman zan sakashi ya karairaya min ƙasusuwan ki Allah wadarai da halinki gwaggo ji take kamar ta shaƙota amma tana tsoron abun da yarinyar zata iya aikata mata idan ta taɓata shiyasa ta rabu da ita kwai saboda tana tunanin yarinyar nan ba ita kaɗai bace tana tare da mutan ɓoye shiyasa ko tayi niyar yi mata wani abun take kasawa,
Woooo wooo waya ce kikawo har loƙacina da kin mutu ai da tuni kin huta amma kinƙi mutuwa nifa nagaji da ganin ki ma shiyasa nakeso na ƙarasa ki yaseen da sauri gwaggo ta miƙe tsaye tace bari ni kafin ki ƙarasani ni inƙarasaki dan jakar ubanki shegiyar yarin kai dan kinga ina rabuwa dake ko to wallahi ba ƙarfina kika fi ba,
da sauri Amra tabar wajen tana mata dariya ta haye sama gurin su Ameesha kamar yanda tace ita zata fara shiryawa hakan kwa tayi ita tafara shiryawa shiyasa ta sauko dan nunawa momma shirin nata dace ita zata farayi sai kuma tayi karo da gwaggo shiyasa ta tsaya neman magana bata faɗi abun da yakawo ta ba,
[6/22, 10:59 PM] Rashh: komawa gwaggo tayi kan kujera tazauna tana faman sauke numfashi tana zabgawa Amra Allah ya isa da zagi kala kala itade momma hakuri kawai take bata tana yi mata sannu dake farace kwa gurin da Amra taja mata har yayi ja,
ruwa momma ta dauko mata sanyi tabata atake kwa ta karba ta shanyi shi tas tana sauke ajiyar zuciya tayi lamo ajikin kujera sai faman wuqi wuqi da ido take ido ya raina fata......
[6/22, 10:59 PM] Rashh: da gudu Amra ta fada dakin nasu tana dariya tana shiga ta qulle qofar da muqulli Hamra tace ke meyafaru harda sawa qofa maqulli wa kika tsokano,
"cikin dariya tace gwaggo ce ta biyoni wai dannaja mata kumatu kinga yanda tayi harda kuka wai taji zafi hhhhh taqara sakin dariya,
"Allah ya shirye ki wallahi kin takurawa wannan matar kina shiga haqqin ta da yawa dan wulaqanci yau abun naki harda sakata zubar da hawaye gaskiya baki kyauta ba daman mungama muje kuma idan muka fita sai munyi miki calin calin da sister Ameesha munkaimata ke ta rama abun da kikayi mata ko kuma murama mata ko ya kikace sister tayi maganar tana kallon Ameesha data gama shiryawa itama dan dariya tayi sannan tace gaskiya de haka yakamata muyi mata kakar kuce ko?
a'a wallahi babar kakan muce fa shine dan taga ta tsufa dayawa take mata abun dataga dama ta rainata da yawa,
"a'a bangane ba kamar ya babar kakan ku nufin ki bama kakar kuba kakar maman ku kenan ko?
"Eh"
" tab amma har yanzu tana raye amma ta tsufa da yawa?
"Eh mana tsohuwa ce amma inkika ganta bazakice takai haka ba tana da kyaun jiki ne kawai,
"gaskiya de nikam zanso inganta wallahi kalli fa ko momma ta kusan tsufa bare kuma kakan ku shima nasan tsoho ne amma ita kuma ace tana raye Allah me iko amma ta kusan kaiwa shekara dari biyu ko?
dariya suka yi gaba dayan su suka ce mata wallahi bata kaiba amma de basu san shekarar ta nawaba,
" to dan Allah idan munje ku gwada tambayar ta muji,
Hamra tace "saidai Amra ta tambayar miki itace daidai da ita ni yanzu dake ta rainani sai ta hauni da masifa saboda masifaffiyace amma tana shakkar Amra, Amra saitayi mata abu ta rabu da ita amma ni inayi mata zata hauni da masifa dan taga ni bana yimata abun da Amra take mata, ko gigin tsufane yake rudata wanda yake mata rashin mutunci bashi takewa ba wanda kuma yake mata biyayya akanshi take saukewa,
"Hhhh" ita kuma haka take to wallahi tsufane dan Allah kuzo muje karta tafi ina so inganta ke kuma Amra idan munje kiqara tsokano mana ita nifa wallahi inason inga tsoho na masifa ko yace zaiyi gudu ko duka abun na ban dariya wallahi,
" lalala kice kema irin Amran ce to wallahi nidai ba ruwana ke da ita duk da kina baquwa ba ruwanta sauke miki zatayi dan ba mutunci ne da itaba,
"Eh na yarda aide nasan bata fini gudu ba danni zan iya satama muyita yar guje guje a falon nan nasan zata gaji dan kanta,
"yauwa yar gari ashe halin mu daya dan Allah zo muje mu dan wahalar da ita kafin mu wuce nasan yaya ammar yana can yana jiran mu kar yayi fushi yafasa zuwa,
"Hamra tace ai ko awa nawa zamuyi bazai fasa ba tunda daman badan mu zaiyi ba ga dan wacce zaiyi kinga kwa dole ya jiramu dan fitar nan tashi ce saboda kansa zaiyi ta ke kinga wani kallo da ya ringa yi miki gaba daya fa yagama tafiya,
sister gaya mana siriin dan naga loqaci guda ya kware miki cewar Amra tana dan daga mata gira daya,
"ni dan Allah kubar wannan maganar ba wani danni kawaide zaikaiku ne dan ra ayin kansa badan niba kuma ni ba abun danakeyi kai nifa inama da wanda nakeso karma kuyi tunanin wani abun,
"muma ai bamuce komai ba muje de kawai ai wannan ne haduwar farko loqacin da za azo ana cewa wallahi nayi missing dinshi na dade bangansa ba yen yen yen nande gaba wallahi kar azo ana mana yar murya akan yayan mu ehe cewa Amra,
" Allah ya kiyaye ma ranar kwa bazata taba zuwa ba kunga ni dan Allah a ajiye zancen nan idan kuma bahakaba wallahi zan iya fasa zuwa,
tab da kwa kinga yaya ammar har cikin dakin nan dannasan tsaf zaishigo ya fita dake dan ba kunyar kowa zaji ba acikin gidan nan har gwarama da ace ya sam yana nan to shine ma watakil bazai shigo ba amma kinga yanzu tsaf zai shigo ya fita dake,
"hmmm kanku ake ji ni mutafi dan Allah banason wannan surutun naku in kuma bazaku fita ba incire kayana in kwanta daman baccin be isheni ba,
"mu mun isa mufasa fita yanda na tamawa fitar nan ai bazanso wani abun da zaisa afasa ba, cewar Amra kenan,
ke kika sanide kuma de kunsan inna fasa ba fita ko,
Hhhh munsani mana auntyn mu muje kawai atare suka fito suna ta kara tattaunawa har suka fito falon, momma kadai suka gani acikin falon da sauri Amra tace momma ina gwaggo tayi tamayar tana dariya tina abun da yafaru dazu,
itama momma tana dariyar tace bayan kingama wahalar da ita din zata zauna ai ta tafi kuma wallahi tace saita kai qararki wajen papa tunda me sunan baba be dawo ba,
"Momma yanzu haka tana cen wajen papa hamar ta tambaya,
"Eh tana cen amma de bansan a ina zata same shi ba ko yana part din mama fulani ko kuma yana part din Ammah saidai kuje ku duba,
Amra tayi dariya tace lalle ma matar nan angaya mata ina tsoron papa ne ai saidai ma yagoyi bayana papa ai nawane kuzo mutafi yau akwai wata dramar naga kuyi sauri tafada tanayin gaba,
momma tace fitar taku fa ba gwara kuje inda zaku ba da kutsaya kuna batawa kanku loqaci yazo yayi ta jiranku dan Allah ku haqura ku tafi kar ku bata masa loqaci,
[6/22, 10:59 PM] Rashh: "a'a momma wallahi sai munje ai ba dadewa zamuyi ba inji hamra tana jan hannun Ameesha suka bi bayan Amra da har takai ga fita waje,
Atare suka jera gwanin ban sha'awa suna tafiya abun su har suka karasa part din Ammah suka fara zuwa tundaga qofar shiga wata jakadiya ta sanar dasu cewa basa nan,
part din fulani suka nufa saida kashe nan ma suna shiga basuga kowa a falon ba dan haka sai hamra da Ameesha suka zauna afalon ita kuma Amra ta qarasa can cikin dakin fulani bayan tayi sallama an amsa mata ta shiga sai ta samu fulani ita kadai nan suka gaisa sama sama saboda har yanzu bata dawo daidai ba daga abun da gwaggo tayi dazu,
mama fulani dan Allah gwaggo fa bata shigo nan ba?
data shigo ai da kinganta da kika shigo ko,
oh ai nazata ko ta shigo ta fitane shiyasa na tambaya,
" to bata zoba,
Ok to sai anjima....
tana fadar haka ta juya ta fice daga dakin,
tana fita tace bata nan muje kawai idan mundawo sai muje har inda take mu same ta..
dukansu mikewa sukayi suka qara fita daga part din,
tundaga waje suka hango Ammar har ya fito cikin shirin shi tsaf yayi kyau kuwa abun sa daman kuma me kyau din ne sai kuma ya qara da wanka sai abun yayi gwanin sha'awa yayi kyau sosai,
da sauri suka qarasa inda yake suna yabon kyaun da yayi shikam sai faman sakin murmushi yake daman yana sane yayi wankan dan ya burge Ameesha sai kuma gashi ya burgeta din duk da batace komai ba amma yasan aranta ta yaba da kyaun nasa,
da kansa ya bude mata gaban mota yace ta shiga qin shiga tayi ta juya ta kalli su Amra suna hada ido suka dage mata gira daya tare da bude bayan motar suka shige sunyi mata dariya qasa qasa,
bayanda ta iya haka ta ta shiga batare da ta kalle saba,
tana shiga ya rufe shima ya zagaya ya shiga ba bata loqaci yatayar da motar yajata suka fita daga masarautar ransa fal da murna,
saida suka dau hanya sannan yajuyo yana kallon ta tare da yi mata magana yace awace unguwar kuke shiru tayi taba tunanin amsar da zata basa jin bata basa amsa ba yasa yaqara cewa wacce makarantar kike nan tabashi amsa da haka de yadin ga jefo mata tambayoyi wasu ta amsa wasu kuma tayi masa shiru so yake tasaki jiki dashi amma hakan ya gagara amma yabawa kansa daga nan zuwa gobe sai ta saba dashi,
wajen wani shaqatawa yakaisu yasa kowa ya zabi abun da yake so akawo masa saida yajira ta zabi nata sannan shima yace akawo masa irin sa,
bayan ankawo musu sunci sun sha kowa yaci itana kuma bata tsaya fulako ba tasaki jiki taci abun ta son