Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   29 / 74

84K to 87K   out of 221K words

kamar ba gaskiya ba wai yau shine guri ɗaya da mace kuma ta kwanta masa akan jikin sa harda taɓasa amma yakasa ɗaukar mataki lalle wannan yarinyar ba ƙaramar sa'ace da ita ba data nemi dagula masa lissafi loƙaci guda,
dafe kansa yayi kawai tare da ƙanƙame idon sa sannan ya budesu duk aloƙaci guda sannan yakai hannun sa kan nata hannun da niyar ya dauke shi daga kansa sai kawai yaga tajanye hannun tare da ɗora kanta akan hannun ta kuma still de agurin ta ƙara kwanciya tana wani mitsin mitsin da bakai alamar de bacci yaƙara yi mata daɗi tashi ba yanzu ba kenan,

Oh my God yafaɗa a fili tare da kaima ta dukan da bai shirya ba dan ya fahimci inyaci gaba da biye mata za a iya samun matsala kuma shine aruwa
shiyasa ya ɗalamata duka a dantsen ta na hannu,.
azabure ta tashi zaune ba shiri tana warwaro manyan idanun ta waje kamar zasu faɗo tare da dafa gurin da yadake ta dan taji zafi sosai cikin motar ta shiga bi da kallo tare da juyawa wajen window tanakallon waje ganin duhu yasata juyowa da sauri ta kalle sa tace naga dare yayi me nufinka tun ɗazu ina cikin motar nan tungari da haske fa muka taho amma yanzu inga dare yayi ya akai hakan ta faru dan Allah me kayimin meyasa nakai tsawon wannan loƙacin kagafa dare yayi wayyo Allah na Abbana na shiga uku na dan Allah ka faɗa mun abun da ka bani nasha da yasa na fita hayyacina har nakai tsawon wannan loƙacin dan Allah ka gaya min?
  duk surutun da take masa bai tankama ta ba kuma baya jin zai iya  tanka mata ɗin ahalin yanzu  saboda halin da ya kuma tsintar kansa bayan ta tashima daga kan sa yafi jin abun akan yanzu akan ɗazu,

magana fa nake maka kayi min banza ka gayamin abun da kayi min acikin motar nan tafaɗa tare da ɗan daga murya,

yanzuma banza yayi mata sai kawai ma ya kifa kansa akan staring din motar yana damke ido shi kadai yasan yanda yake ji sauƙin sama ɗaya batasan abun dake faruwa ba yasan da shikenan rainasa zatayi amma tunda batasan aika aikan da tayi masa shikenan gwara yayi mata banza dan hakan sai yafiye masa,

magana taƙara yi masa yagaya mata meyasa takai wannan loƙacin acikin motarsa amma nan ma bashiru ba amsa,
haka taci gaba dayi masa bala'i tana ɗaga murya saboda shirun da yayi mata ba ƙaramin hassalata yake ba,

  jin ta damesa ta isheshi ta takura masa yasashi ɗan ɗagowa batare da ya kalleta ya kalli gefe sannan yace fitar min amota  yafaɗa alamun rai aɓace,
    bazan fita ba sai ka gaya min abun daya faru dani yaza ayi ina maka magana kayi min banza kagaya min abun da kayi min,

   "Jijjiga kai kawai yakeyi kiris yake jira dan tagama kaishi ƙarshe kawaide yana ɗan ɗaga mata ƙafane saboda yasan shine bashi da gaskiya kuma bama yaso ta fahimci halin da yake ciki tafara zargin wani abun shiyasa amma badan hakaba da tuni ya fita ya buɗe mata ƙofa ya jefata waje,

    "so yake kawai  tafita yana buƙatar zama shikaɗai amma sai ɓata masa loƙaci takeyi ganin hakan yasashi miƙa hannu  batare da ya kalleta ba ya buɗe mata ƙofa yace fita kuma bai matsa daga jikin motar ba dan hannun sa har hana gogan ƙirjin ta ɗan baya tayi tana mannewa jikin kujera numfashin ta har daukewa yakeyi  saboda kusancin da sukayi Allah Allah take ya matsa amma yaƙi matsawa jin yaƙi matsawa yasa ta bude idon ta da ta rufesu, tana budewa suka haɗa ido da ita harara ya wurga mata tare da yayimata kallon up and down ganin yanda duk ta bi ta takure ajikin kujerar wai duk dan kar ya taɓata, tsaki yaja cikin ƙasa ƙasa da murya yace ai ke kin iya taɓa wani tare da matsawa daga gurin yakoma kan kujerar sa,

sarai taji abun da yace amma takasa fahimtar inda maganar tasa ta dosa,
itama tsakin taja kamar yanda yayi mata tace zamu kwana anan kenan dan ba inda zani sai naji abun da kayi min wayasani ma ko wani abun ka shaƙamin ka kaini wani wajen daban Allah kaɗai yasan adadin cutarwar da kayi min ayau saidai ince Allah yasakamin Kuma wallahi Allah ya issss.....

bum taji ya doke mata baki, rau rau tayi da ido hawaye har sun taru a idon ta, ' dafe bakin tayi da hannu dan baƙaramin zafi taji ba aranta taci gaba da jera masa Allah ya isa mugu azzalumi ba kalar zagin da batayi masa ba amma acikin ranta,

muryar sace ta katse mata abun da takeyi,
zaki fita ko sai nayi maganin ki yayi maganar a ɗan fusace dan yagaji da abun da take masa,
itama afusacen cike da taƙaicin dukar mata baki da yayi tace " sai naji inda ka kaini tsawon wannan loƙacin

kamo kwalar hijabin ta yayi tare da jawota daf da fuskarsa har suna iya jin numfashin junan su zuba mata rikitattun idanun su da har yanzu basu gama dawowa daidai ba,
kasa jura tayi kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke idon ganin irin kallon da yake mata yasa taki loƙaci ɗaya tsoro ya dirar mata taji ma takasa faɗa masa abun da tayi niyya,
look at me taji yace mata amma sai ta kasa ɗagowa ta kalle sa,
"kinaso kiji abun danayi miki right?
sai yanzu ta ɗago ta kallesa ido cikin ido sannan tace "eh"
wani gida nakaiki nayi miki ciki..!


pls kuyi haƙuri zaku ga kwana biyu banayi dayawa wani sa'in ma banayi gaba ɗaya wallahi biki mukeyi wannan satin nayi busy dayawa sai ahankali,



                 
                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
           
[6/14, 8:40 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️55&56

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

      
"kinaso kiji abun danayi miki right?
  sai yanzu ta ɗago ta kallesa ido cikin ido sannan tace "eh"
   "wani gida nakaiki nayi miki ciki..!!

  zaro ido tayi tare da ware su akan sa bata taɓa tunanin jin hakan daga gare sa  ba ita duk atunanin ta zai nuna wata rashin gaskiya daga tambayar datayi masa bata taɓa kawo hakan ba sai taji dama bata tambaye sa ba da tasan zai iya gaya mata wannan maganar,  " tazata irin zaiyi mata wani kwana kwana yanda zatasamu damar yi masa abun da taga dama amma saitaji akasin haka shi ko kunyar faɗan cikin beye ba duk da tasan ma bahakan bane ashe sarai tasan bacci tayi amma take masa wannan tambayar daman ance tabarmar kunya da hauka ake naɗeta dan kar yakawo mata wani zancen akan ta kwanta masa ajiki shiyasa tayi masa haka ashe daidai da ita yake,

cike da borin kunya ta sunkuyar da kanta tare da ƙoƙarin kwace kanta daga riƙon da yayi mata daman ya riga da ya buɗe motar tun ɗazu dan haka bata yarda taƙara haɗa ido dashi ba tayi saurin juyawa zata fita ya riƙo hijabin ta tsayawa tayi cak batare da ta juyo ba,
murya na rawa tace ni kasakeni dan Allah banason kallar iskancin nan dakakeyi min duk kazo ka addabi rayuwata ni wallahi nayi danasnin sanin ka ayau din nan yau baƙar ranace agareni ranar da bazan taɓa mantawa ba ka cuceni ka cutar min da mahaifi kaje kai da Allah, Allah ya fika mugu kawai mayaudari tana faɗa tayi saurin kwace hijabi ɗin ta tare da fita daga motar sai da tafita sannan ta juyo tace ɗan iska kawai badai cikin ka ajikina ba saidai kaje kayi da waɗanda kasaba mutum banda latsa ƴaƴan mutane ba abun da ya iya mtssww taja tsaki ganin ya yunƙura kamar zai fito yasa ta kwasa aguje sai kace ƙaramar yarinya haka ta kama gudu,

' tsayawa yayi ta cikin motar yana kallon ta baisan loƙacin da yasaki wani ƙayataccen murmushi ba gudun nata ba ƙaramin burge sa yayi ba ga tsoro ga rashin kunya,
ya zuba mata ido saboda haryanzu ba abuɗe mata ƙofa ba sai faman bugawa take da ƙarfi ta ayi tana juyowa dan ganin kartaje yafito yakama ta,
yana sane dan yaga yazatayi sai kawai ya buɗe motar ya fito,
duk da darene amma hasken kwan na ƙofar gidan su bai hanasa ganin yanda tazaro idanu ba kamar zatayi kuka tana ɗan manmannewa ajikin gateɗin kamar zata shige ciki kuma bata bar kwankwasa ƙofar datakeyi ba amma har yanzu ba a buɗe ba,

ahankali yashiga takawa zuwa inda take acikin ransa dariya ce take cinsa amma a zahiri sai ya wani haɗe rai kamar me shirin zuwa dambe,

jitakeyi kamar ta nutse dan batason yakamata wani bugun ta ƙara kaiwa ƙofar da ƙarfin tsiya,
yana daf da ita yakusa zuwa inda take dan har ta saddaƙar ma yakamata kawai taji an buɗe ƙofar da sauri kaamr wacce aka hankaɗa ciki haka tayi saurin faɗawa gidan har tana ture me gadin da ya buɗe mata ƙofar, "tana shiga ta turo ƙofar da ƙarfi,
ganin ta shige yasashi yin ƙwafa tare da juyawa aransa yace Allah ya taimakeki yarinya da kinga yanda ake iskanci, yana cikin tafiya yajiyo muryar tanacewa wooooo aide baka kamani ba inka isa ka dawo wooooo woooo juyowa yayi ahankali yana binta da kallo tunda ga up har down ganin ta yayi ta zuro kai tana leƙensa suna haɗa ido tayi masa gwalo tana hararar sa jinjina kai kawai yayi ya juya yatafi yana mamakin irin shirmen da takeyi da yaganta doguwar yayi tunanin wata babbace ashe girmanne ya riga hankalin zuwa yarintace kawai take ɗawainiya da ita dole yayi mata uzurin wasu abubuwan da take masa,

yana ta tunanin shirmenta har ya ƙarasa wajen motar ya buɗe ya shiga har yanzu bata bar bakin ƙofar ba tana tsaye tana kallon sa har ya shiga mota ba ɓata loƙaci yayiwa motar key sannan yaja batare da ya ƙara kallon inda takeba yayi gaba abun sa,

saida taga shiga motarsa da tafiyar sa sannan ta koma ciki ta rufe ƙofar tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tagama tsorata ɗazu da ba abuɗe gidan ba tasan da bazai taɓa rabuwa da itaba da yakamata saitagane kurenta,
cikin gidan ta nufa har taje bakin ƙofa sai kuma wani tunani ya faɗo mata burki taja ta tsaya gaban ta na faɗuwa yanzu me zata gayawa wannan masifaffiyar matar idan ta tambayeta inda taje bataso ta gaya mata cewar wasu sun kama mahaifinta kuma batasan ƙaryar da zata haɗa mata ta yarda da itaba,
sosai ta shiga tunanin abunyi,
tana tsaye agun tana tunanin mafita taji ance to munafuka kini babbiya kinje kingama yawon biɗiɗin naki zaki tsaya kina ɓoye ɓoye saboda tsabar kawarewa da barikanci ko inda sabo ai nasaba da wannan munafurcin naki sai kinsan kinje ki aikato alfasha ɗinki saikizo kina rarrabewa awaje shi saurayin da yazo ya ɗaukeki loƙacin bakiji kunyar fita ba har Saida kikaje ki ka sauke abun da yake damunki idan bakiyi ba bakyajin daɗi to hankalin ki ya kwanta kinje kin aikato abun da kika saba sai ki wuce ciki kuma wallahi kin kusan barin gidan nan gwara ki tattara inainaki inaki kibarmin gida dan bazan cigaba da daukar wannan iskancin naki ba nan gaba ki lalata min ƴaƴa shigiya munafuka kin wuce ko sainayi ball dake anan gurin,

Sunkuyar da kanta tayi idon ta har yakawo kwalla kanta aƙasa tabi ta gefen matar datake tsaye abakin ƙofar tana zazzaga mata wannan masifar,
dundu ta buga mata abaya loƙacin da tazo daidai da ita sannan ta ɗora dacewa Allah wadaran da halinki kullum cikin hijabi harƙasa saboda tsabar kwarewa a karuwanci shiyasa kowa yake cewa ba ruwanki saboda basaja dakike musu da hijabi sumimi kasum basu san musa abaka fir'auna azuci bace ke,
itade bata kula taba tayi wucewar ta ɗaki ita kuma matar ta tsaya taci gaba da ɗaga murya tana zazzaga mata masifa da jifanta da baƙaƙen magan ganun da duk suka zo bakin ta taitayi ko gajiya ma batayi ba anƙi kulata amma takasa denawa,

sumy na shiga ɗaki ta faɗa kan gadonta ta kifa kai ajikin filo ta shiga raira kuka tana cikin kukan taji wayar ta ta shiga ringing kin ɗagowa tayi bare ta amsa wayar bayan kiran ya katse wani ya ƙara shigowa jin antakura taɗan tsagaita da kukan tare d jawo wayar batare da ta duba me kiran ba ta ɗaga wayar haɗi da karawa akunne tayi shiru tana jiran taji me magana,
kamar amafarki muryarsa ta daki dodon kunnen ta cire wayar tayi akunne ta tare da kallon number tabbas itace ta faɗa aranta mayarwa tayi kan kunnen ta,
"ko baki ji me nace ba ne"
memakon tabashi amsa kawai sai tafashe da kuka sosai takeyin kukan kamar ranta zai fita ita kanta bata san loƙacin da ta fara irin wannan kukan ba daga jin murya sa duk daman kukan take amma na yanzu yafi naɗazu batasan dalili ba kuma kodan shi yaja mata akayi mata faɗan saboda baisan shiba da yanzu tana nan hankalin ta akwance haushi biyu ne ya haɗar mata loƙaci guda dan haka kwa taci gaba da kukan ta ba ƙaƙƙautawa duk maganar da yake mata bata tsaya ta saurare sa ba,

"gefen titi yasamu yayi parkin jin yanda take kuka hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba hankali tashe da mamakin abun da yasata kuka haka ya shiga tambayar ta abun da yake damun ta amma kamar ma ya ƙara zigata yake,
wani kukan take bata ko tsagaitawa kuma bata kashe wayar ba,
shiru shima yayi kawai yana sauraron sautin kukan nata da yakejin sa kamar daga ƙasan zuciyar sa yake,
bai ƙara yin magana ba bai kuma kashe wayar ba itama kuma haka bata fasa kukan ba kuma bata kashe wayar ba haka sukai ta tsayuwa har tsawan wasu luƙutan,

jin bata da niyar daina kukan yasa shi cewa pls I'm so sorry indai ni nayi miki laifin dakike wannan kukan to kiyi haƙuri idan kuma mahaifin kine ki kwanrar da hankali namiki alƙawarin gobe kafin kitashi daga bacci zaki ganshi agida amma dan Allah kidena wannan kukan karkisakawa kanki wani ciwon kinji,
Allah sarki shi duk atunanin sa duk saboda shi take wannan kukan saboda shi kansa yasan baikyauta mata ba,

jigaba yayi da rarrashin ta har yasamu ta ɗan tsagaita kukan nata ta koma shashsheƙa,
jin yanda yake mata magana yasa taɗanji sanyi aranta yaude rana ɗaya tasamu wanda ya share mata hawayen ta aduk laƙacin da irin haka ya faru da ita saidai tayi kukan tagaji ba mece mata tayi shiru saidai tayi shiru dan kanta idan tagaji, amma yau gashi harda Allah ake haɗata akan tayi shiru, duk da ta kuntatawa rayuwar ta a iya yau da suka haɗu dashi amma sai taji bazata iya cigaba da kukan ba gwanda tayi shiru kodan abun da yayi mata na rarrashin ta da yayi tasan idan taci gaba batai masa adalciba duk da shine silar shigarta wannan halin amma ta gwammaci tayi tayi shiru saboda shi,

jin tayi shiru kuma batace masa komai ba yasa ya ɗan gyara zaman sa aka kujerar tare da jigina kansa da jikin kujerar ahankali yace "nine ko?"
baiyi tunanin zatayi magana ba amma sai yaji tace "a'a",
da sauri yatashi daga jikin kujerar yana buɗe idon sannan yace to me yafaru me yasakaki irin wannan kukan haka naga kuma lafiya kika shiga gida me yafaru uhm,

" babu komai yaji tabashi amsa"
"really? Shima yace mata
"eh tabashi amsa
ni ba taɓa ganin inda akayi kuka hakannan ba duk inda akayi kuka dole akwai dalili musamman ma irin wannan kukan dakikeyi kar ki ɓoue min gaya min abun da yasaki kuka haka,
Shiru tayi bata basa amsa ba saboda batason tagaya masa ainahin abun da yafaru da ita hartayi kuka,
cikin ƙasa ƙasa da murya tace kawai na tuna mahaifina ne dan Allah karka cutar min dashi ka taimaka kadawo min dashi goben kamar yanda kayi min alƙawari ɗazu ina kewarsa da yawa ina buƙatar sa akusa dani bani da kowa sai shi Please and please na roƙeka kar kucutar dashi ta ƙarasa maganar tana shirin fashewa da wani kukan,
shiiiiit taji yace ta cikin wayar sannan ya ɗora da cewa ya isa haka kar kisake yin kuka nibnayi miki alƙawari kuma zan cika miki shi da yardar Allah amma nima kimin wani alƙawar kar kisake kukan akan wannan maganar ki kwantar da hankaliki zan kawosa da kaina kamar yanda nagaya miki sannan kuma ki yafe min duk abun danayi miki tun farkon haɗuwata dake har zuwa yanzu karki ƙara dangantani da kalomomin da kike kirana dasu ni ba mugu bane kamar yanda kike tunani kuma ba ɗan iska bane bana kula kowa bana shiga harkar kowa duk wanda kikaga nayiwa wani abu to shi ya shiga harkata idan baka kulani ba ko inda kake ban kalla bare inshiga harkar da batawa ba

29 / 74