Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   11 / 74

30K to 33K   out of 221K words

meye abun damuwa aciki bayan muna tare inbaka ganta yanzu ba ai zaka ganta gobe ganin ta har sai kagaji ai tana rufe baki yace wlh hajiya bazan gaji da ganin taba nifa badan badan bama daki daya zamuna kwana idan natashi kuma mutafi aiki tare mu dawo tare baki hajiya tasaki tana kallon sa sannan tace nikuma sai abarni nikadai daman kwa bazan taba yarda ba nifa yarinyar nan koda komai ya daidaita zan roqesu subarta tace gaba da zama awajena har zuwa lokacin bikin ta shine kawai zai rabani da ita in sha Allah nasan bazasu hanani ba yace to Allah yasa ai hajiya ko tayi auren ma kuna tare ba inda zata tace dake shi mijin yace maka zai yarda yadawo nan da zama inama kataba jin inda a kai haka yace ai dolen sama ya zauna yana da inda yafi kusa dake ai ba inda zasu kuna tare dasu daga ita har mijin yana gama fada yace bari indan watsa ruwa inzo inci abinci baby sai yanzu ta dan fahimci zancen sa murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba itama ta wuce kitchen abincin masa ta hado masa bata kai dinning ba kawai sai ta ajiye masa akan center capet din dan daddare befiya cin abinci akan dinning ba yafiso ya zauna aqasa yayi balance yanda zaifi cinsa da yawa yaci ya qoshi saboda baya wasa da cikin sa akwai cin abinci bare kuma idan ya kwaso yunwa ba a magana sai yaci abincin kusan mutum biyu shikadai tana gama jere masa ta zauna awajen tana jiran fitowar sa......

Sam & Ammah

Saida yadan qara gyara zama tare da miqa duka hankalinsa gare ta sannan yace Ammah wata tambaya zan miki ko Allah zaisa kin sani tace ina jinka yace yanzu idan akace na kusan kusanka wa ake nufi kenan saida ta dan numfasa sannan tayi murmushi tace yanzu wannan har wata tambayace kaima ai zaka iya bawa kanka amsa yace Ammah da nasani ai bazan tambayeki ba tace to idan akace na kusan kusanka kamar ace mahaifiyar ai kaga itace ta kusa dakai to ba ita sai ace hasanarta ko kuma mahaifanta kaga su sune nakusan ta ita kuma itace ta kusanka kagane dan jimm yayi yace eh nagane to amma idan akace kuma zaku hada alaqar jin fa kinga kamar ba mahaifiya ake nufi ba tunda ita daman already jininku daya ba wata alaka da zaka hada da ita tace eh hakane tode wannan tambayar taka bandan fahimcekaba kaimin bayani dalla dalla dan har kaqara rikitani gyara zama yayi ya fuskance ta da kyau sannan yace yanzu alal musali ace bansan kiba ke kuma kin sani sai kikazo wajena fuskarki a rufe amma da ace kin bude zan iya sanin ki tunda nasanki abaya saidai rufe fuskar da kikayi yasa bangane kiba sai kawai kika zomin da wata bukatar ki wacce kike tunanin bazan iya ba amma sai kikace zaki bani kudi makude atake alokacin kika turamin kudade nikuma tsoro yasa nace miki na amince sai kike cewa idan banyi ba kinsanni farin sani kinsa gidan mu idan na kuskure tofa duka family na sai sunshiga wani hali hakan yasa nace na amince amma kifara gaya min ko wacece ke sai kicewa ai nima nasanki kece ta kusan kusana wanda zamu hada alakar jin nan da 'yan wani watanni kuma kika gargadeni akan kar inzafafa tunanj wajen gano ko wace saboda shima zaizame min matsala gwara kawai inyi aikin da kikasani idan ina son kwanciyar hankali sai nazo zancire miki abun da kika rufe fuskar sanadin hakan danyi kuma bangama ganin kiba kuma banqara sanin inda kaina yake ba sai agadon asbiti to kinji yanda abun yake kin gane yanzu tace eh na fahimceka sosai amma wanna amsar taka kabari ba yau ba sai nayi nazari sosai dan marairaicewa yayi yace plss Ammah ki gayamin yanzu kawai abune emergency nasan zaki iya mekika fahimta acikin wannan maganar bakajin hausane abun da na fahimta dinne ai nace kabari idan nayi nazari zan gaya maka shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace kafin ma ingaya maka kaiwaye yayi maka wannan tambayar ko a ina kaji labari dan shafa kansa yayi tare da dan cizan lower lip dinshi sannan yace Ammah wannan ba abun da yashafeki bane kawai amsa ake nema daga gareki idan komai ya tafi yanda akeso zakiji komai ta danji haushin maganrsa amma sai ta danne bata bari bacin ran yafito ba tace masa ok kawai sannan ta miqe tsaye tace sai kaji daga garene shima da sauri ya miqe tare da qarasawa gare ta yace dan Ammah na daga nan zuwa gobe ki taimaka kigama nazarin kigaya min kai kawai ta daga masa alamar to daga nan ta nufi dakinta shi kuma ya fita daga falon tare da nufar sashen Fulani inda zai kwanta saboda yaga dare yayi atunanin sa kowa ya kwanta shiyasa ma be tsaya wani yin nocking ba kawai yatura qofa yashiga kai tsaye hajiya sarah inason ganinki agidana tun lokacin da kika tafi ka barni cikin duhu haryanzu nakasa fahimtar inda maganar ki ta dosa tun alokacin nake taqara trying number ki amma bata shiga me yafaru ne abun da yaji fulani nacewa kenan itama jin kamar motsin mutum yasa ta dagowa daga kan kujerar da take idanunta suka sauka akansa bata jira amsar da za abata ba kawai ta datsi wayar tare da miqewa gabanta na dan dukan uku uku tana tunanin Allah yasade baiji abun da take cewa ba wata zuciyar tace to meyema idan yaji ai ba gane abun da take cewa zaiyiba tuna hakan yasata sakin murmushi tare da qarasowa kusa dashi tace tunyaushe kashigo daman kai naked jira shiyasa na zauna anan tunda naga alamar kwana biyun nan baka son zuwa inda naked be tanka Mata ba saima wani kallo me cike da ma'anoni da ya wtmatsamata da yasa saida takawar da idonta daga garesa bece mata komai ba ya raba ta gefenta ya wuce sashen sa yabarta agun atsaye tana takaicin kallon da yayi mata da kuma kin kulatan da yayi kamar wacce aka dasa agun haka ta tsaya tana tunani kala kala saida ta dau wajen minti uku agun batare da tayi wani kwakwaran motsi ba sannan ta girgiza kai tayi gaba tare da cewa dani kake zancen zan saita maka zama acikin gidan nan baka san halina bane labari na kake ji

cike da takaicin wulakancin da yayi mata naqin kulatan dayayi ta nufi dakin ta da tunanin abun da zatayi masa acikin ranta,
shikam anasa bangaren bema san tanayi ba dan dagaske bai fahimce me take cewa ba saboda tsakanin su da yar tazara shiyasa kawaide yaji tana magana amma baya tantance abun da take fada abun da yabashi haushi da har yagane duk yanda akai abun da take fada bana alkhairi bane dana alkhairi ne ai bazatayi saurin katse kiran ba daga ganin sa dalilin da yasa yaqi kulata kenan yayi wucewar sa daman yanzu ba wani dasawa suke ba tunda yagane take taken ta ya fit a harkarta gaba daya,
yana qarasawa dakin sa ya hau cire kayan jikin sa ya fada bathroom be dau lokaci ba yafito jikin sa daure da towel sai guda daya kuma da ya nannade gashin kansa dashi guri yasamu ya zauna gaban dressing mirror sannan ya kunce towel din kansa ya qara goggogewa sannan ya dauki lotion ya shafe jikinsa tareda turaruka nide tsaye nayi ina kallon ikon Allah sai kace amarya zata gurin me gida anaso aburge shi haka shima yake tafaman shafe shafe da murtsike murtsike yadau wannan ya shafa ya ajiye yadau wancan harda shafa wani abu akan lips din shi da nidai yau nafara ganin sa a hannun sa tunda akahaifeni aduniya ban taba gani ba saida yagama tsaf sannan ya mike yaje gaban slyzing drawer bayan ya bude ta yadauko wasu kaya marasa nauyi yasaka sannan yaje yadauko fresh milk a fridge din dak in ya dan sha kadan sannan ya mayar sannan ya haye kan tamfatsetsen gadon sa tare da jan lausassan blanket dinshi ya rufe duka jikin shi dashi amma banda fuska lumshe kyawawan idanunsa yayi ko addu'ar bacci beyiba yayi kwanciyar sa some times daman bata dameshiba abunde dana lura dashi kamar yana da dan qarancin yawan ibada ahaka yayi kwanciyar cikin qanqanan lokaci bacci yayi awan gaba dashi asuba tagari,

Washe gari

Yana tashi bayan yayi sallar asuba ya koma ya kwanta be tashiba sai wajen qarfe 11:am sannan ya farka shima saida shettima ya tasheshi awaya sannan ya tashi yana tashi ya shiga yayo wanka yazo yaqara kwalkwale jikin sa kamar yanda yasaba sannan yasaka kaya tare da qara feshe jikinsa da turaruka yafito sai faman zuba qamshi yake idan yazo waje kafinma ya qaraso gurin turaran sa zai rigashi zuwa saboda ba kadan yake sawa ba gasu kuma masu tsada da dadin qamshi fitowa yayi cikin takunsa na isa da qasaita da mulki da izza duk wanda yayi karo dashi yaga yanda yake takunsa kai kasan bada ganan ba shidin na dabanne koman sa na dabanne ya sha bambam da sauran samari(nide nace da sauran tuzuraide )yana qarasowa falon fulani yasame ta ita da papa azaune akan kujera qarasawa yayi ya gaida su gaba dayansu fuskarsa ba yabo ba fallasa duk dade ba wani sakinta yayi sosai ba amma de da sauki akan yanda yakeyi da ita koda yaushe cikin sakin fuska duk suma suka amsa masa har papa na tsokanar sa da matsoraci dan zuwa yanzu ya sauko daga haushin nashi da yake ji fulani ce tace haba de yaron nawa ne matsoraci kana ganin mutum dirare ga kwanji kace masa matsoraci wannan ai sai ya iya yaqi da mutane sama da dari uku ma batare da yagaji ba papa yace a ina din to kwa kallon kitse kikewa nama wannan ba abun da yaya iya jiya mace fa yaringa tsoro abun mamaki wai harda guduwa qato dashi abun ma abun haushi hade rai yayi ciki ciki yace papa ai wannan ba mutum bace aljanace nikam bana son ko ahanya inyi gamo da ita bare kuma har inje inda take Allah ya kiyaye bada ni ba wlh da ace cewa akayi ga wani nan yazo zai cutar daku to anan zaka gane ina da tsoro ko bani da shi amma bawai kahadani da aljana ba kuma kace bazan tsorata ba wannan ai wajibine kaima nasan kawai basarwa kake amma naga tsoro a idon ka kawai na yi maka shirune dukan wasa papa ya kawo masa shi kuma ya guje yace daga fadar gaskiya Allah ko na rantse bazata cini ba papa kaima ka tsorata dakiya de kawai kafimu papa yana dan murmusawa irin na manya yace yaron kai wai yaushe zaka koyi riqe magana duk maganar da tazo bakin ka baka tsoron fadar ta yace ai saboda ba wanda naked jin tsoro kaf fadin duniyar nan shiyasa bana shakkar kowa caraf fulani tace har uwarka da ubanka kenan marar kunya ko kunyar fadar hakama bakaji ba agaban mu ko bani da daraja agunka ai shi uban ubankane ka daraja shi tunda ni daman tunda nagama cin kashi da fitsarin ka na dauke ka tamkar da awajena amma da wuyanka ya isa yanka ka balaga shikenan nazama marar amfani awajen ka sai kawayi garima kafi qarfin kazo inda nake ka gaida ni saidai in munhadu ahanya hayar ma wataran bana samun damar gaisuwar saidai kayi min kallon banza ka wuce to ko uwarka bata isa tayi min abun da kake min ba kuma zanyi maganin ka jiyama Allah ne ya taimake ka amma da sai na kwashe fuskar ka da maruka marar mutun ci kawai wanda besan darajar nagaba dashi ba ni wallahi ka isheni zama kayi ka tattara inaka inaka kabarmana gida bama son ganinka ka ishemu tana rufe baki yace basai kizo ki fitar dani ba tunda agidan zakariyya nake zaune kutumar uban nan nikake kirawa sunan mahaifi ni ni sameer tafada cike da hayagaga kamar zata rufe shi da duka saboda yakira sunan mahaifinta,
lalle sameer yanzu abun har yakai ga haka to kwa zaka gane kuren ka sai na koya maka hankali wallahi ina daga maka qafa amma ba ka gani to wallahi zamu saka qafar wando daya dakai,
Saida yabita da kallon sama da qasa tare da kawar da idon sa gefe yana sake hade rai sannan yace musaka rabima kuma dakike nakira sunan mahaifinki kinji nazageshi ko nafadi wata mummunar magana akansa sunan sa kawai nakira zakariyya kuma daman dan afada aka rada masa da ba aso aringa fada da kawai sai asaka masa sunan da kike kiransa dashi kinga muma sai muringa fada amma tunda akasaka masa zakariyya dole muma mace zakariyya kema kuma yanzu kikace min sameer sameer kuma sunan baban papa ne kema kenan sai yace zaiyi fada saboda kin fadin sunan babansa ko uba yafi ubane,
kana tayo gadan gadan zata rufe shi da duka papa dake zaune yana kallon su daman in sunayi baya saka musu baki saboda fulani ta hanasa amma da yaga abun nasu yana neman wuce gona da iri yasashi saurin tare fulani yace haba da girmanki dan Allah karki biye masa tundade kinsan halin sa muma hakuri muke dashi wani kallo ta watsa masa da yasashi matsawa daga tare tan da yayi yaja gefe tare da jan bakinsa yayi shiru aransa ya ayyana wlh ko yaron nan zaiyi mata dukan tsiya baze dakatar dashiba tunda ita ta bukaci hakan miqewa sam yayi tsaye tare da kafeta da ido yana jiran yaji me zatayi masa da kwa tagayawa aya zakinta idan ta kuskura hannuta yataba shi ganin yanda ya hade rai kamar kumurci yasa ta dan dakata daga niyar abun da tazo tayi masa sai kawai ta nuna sa da yatsa tace kai ka saurare ni nan bawajen wasan rijiya bane inkana cin qasa to ka kiyayi ta shuri saboda bata da dadi baka san ko wacece ba ko dan Allah fa to ke wace gashide naganki agabana kuma kamar kowa nake ganin ki nade san sunanki maryam zakariyya yar gidan talakawa sannan kuma me fuska biyu wacce bata abu dan Allah saidan cikon wani burin nata da sawa azabatar da mutane daga ke har wancan jankin dan naki kallon ku nake ke zancewa in kina cin qasa to kikiyayi ta shuri kici gaba da abun da kukeyi kar nake kallon ku kuma kibini ahankali dan daf nake da tona miki asiri acikin masarautar nan dan gakkin da ka raina shi yake tsokane maka ido kina ganin kin raineni kamar kin haifeni amma kuma baki isa kimin wata barazana dazaisa inji tsoron ki dan atafin hannuna kike kada kiga ba anan nake zaune ba amma duk wani takun ki ba wanda ba agayamin ina son in fara tanadar kwakwarar huja ahannu na kafin zaman masarauta ya gagare ki dan namiki alkawarin sai anyi miki korar wulakan ci a masarautar nan dai nasakinyi regretting din abun da kika aikata dan haka muzuba dani dake shige kafasa sai ki canza taku ni kuma zan gano kiyi koqarin hanani binciken danakeyi inzaki nasara yaqarasa fada tare da watsa mata wani banzan kallo me cike da gargadi sannan be tsaya sauraron ta ba ya wuce abunsa ko inda papa yake kallaba yafita daga falon ransa abace kana ganinsa kasan ba lafiya ba yana fita yanufi part din momma dinsa......

dabaya da baya fulani tafara ja da baya saboda tsabar firgita da rikice da ya risketa alokaci guda ga wani uban gumi da yagama wanketa daman ance marar gaskiya ko aruwa gumi yakeyi saura kadan ta fadi qasa tayi saurin dafe kujera hannun ta duk karkarwa yake jitayi qafafunta sun mata nauyi sun kasa daukar ta da sauri ta lalibi kujera ta zauna hadi da dafe kanta da taji kamar yana juya mata papa dake tsaye yana mamakin yanayi da ta shiga danshi duk atunanin sa kawai sam yafada ne dan ya tura mata bakin ciki amma sai yaga kuma kamar ta shiga tashin hankali da jin maganganun nasa qarasa wa yayi agabanta zai ruqo hannun ta tayi saurin daga masa hannu tare da yimasa tsawa bace min daga gani banason maganar banzau bayan kana jinsa yagama cin mutun cina amma ka kasa yimasa komai papa murya narawa yace kiyi hakuri kada ranki yabaci nasan da wasa yake miki kuma ai ke kikace kar na...bata bari ya qarasaba ta qara doka masa wata ysawar kafita nace bana son ganin ka anan tafada tana huce tare da nuna masa qofar fita da yatsanta ko motsi beyi ba bare tasa ran zai fita bakaji ba nace kafita tafada qarfi da har saida falon ya amsa.......✍


Kwana biyu kunjini shiru bana danji dadi ne wlh ina fama da ciwon kai amma yanzu Alahamdulillah da sauqi,
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿19&20
Bismilah.......✍

        papa murya narawa yace kiyi hakuri kada ranki yabaci nasan da wasa yake miki kuma ai ke kikace kar na...bata bari ya qarasaba ta qara doka masa wata ysawar kafita nace bana son ganin ka anan tafada tana huce tare da nuna masa qofar fita da yatsanta ko motsi beyi ba bare tasa ran zai fita bakaji ba nace kafita tafada qarfi da har saida falon ya amsa......

Miqewa yayi jiki babu kwari sum sum sum kamar wani munafiki haka ya tashi ya fice daga falon da tunanin ganin wannan lamarin da yabasa mamaki  ganin yanada matar sata shiga tashin hankali abun da baitaba gani ba kenan yasan tsayayyiyar macece ita baka taba gani alamun tsoro atattare da ita kuma bata karaya awajen magana amma yau wandata raina tayi jika dashi ma yazo ya gaya mata maganar da har

11 / 74