masaniya akan abun da yafaru jiya ko? daga cikin mutanen wasu suka shiga jinjina kai alamar eh...
cigaba tayi da cewa jiya wajen yamma ansamu wani babba alamari da ya firgitar da al'umma ajiyan nayi tunanin gabaɗaya duniyar ce ko ince garin nema, saidaga baya kuma nakejin labarin wai iya cikin masarautar ne abun yafaru,
a gaskiya lamarin yayi matuƙar furgita ni yasakani aruɗu kuma yaban mamaki kai ba abunma da baibanba saboda al'amari wanda nide iya tasowa ta arayuwata bantaɓaji ba kuma bantaɓa gani ba abu kamar almara kamar a mafarki, shiyasa na taraku anan dan jin ta bakunan ko da wanda yake da masaniya da abun da yafaru domin wannan ba abun zama bane dole atashi tsaye dan magance gaba karmuje nan gaba muna ciki muji munkifa ankashe mu loƙacin mu beyi ba yakamata asan abunyi,
maganar ta saida tabasu dariya jin yanda ta tsorata kamar ba sarauniya fulani ba yau itace da tsoro ƙarara afuskarta kuma har wai su kifa ko wazai kifar dasu, dan haka saida wasu suka ɗan dara,
itama ɗan dan murmushi tayi tace kuna dariya Allah gaskiya nake faɗa wannan ba abun wasa bane maƙiya kuma meye bazasu iyaba muna zaman zaman mu sai kuga anyi abun da zai halakar da mu gaba ɗaya tunda suka fara da haka danni de wannan abun cewa zanyi turo mana akayi da ranar Allah amma gida yayi duhu ga ƙara yaseen wannan ƙarar turo mana akayi sufa maƙiya da mahassada ba abun da bazasu iyayiba, dan haka dole mutashi tsaye dan kare martabar masarautar mu da tsirar da rayukan mu,
"a'a wannan fa ba wani ture kar kuyiwa wani ƙazafi aradun Allah kuka shuka abunku kuma zaku girba ai ni ajikina wannan ƙarar wallahi domin wanna abun da yafaru ƙullallan makirci ne kawai na asiri shine ya warware saida kuma nima bazan muku ƙazafi ba akan kune saboda daman sarauta ta gaji haka mebi andaɗe da binne shi sai ajiyan Allah yayi kuncewar sa domin sarauta ce daɗaɗɗiya baza ace ga wanda yayi ba amma dole wannan abun karyewar wani asirin ne daman shi asiri ai haka yake akwai wanda in ya tashi karyewa har jijjiga guri yake ginin wani gurin ma zai iya faɗowa wannan ai yazo da sauƙi,
a zamanin mu meye ba magani, irin waɗan nan abubuwan ai tsohon abune awajen na wallahi bayau fara ji ba kuma nasan bayau zan gama jiba saboda wannan haline na mutane ga duk wani wanda ke zaune acikin masarauta sai yayi saidai wani yafi na wani muma da ba muyiba ai da ba mukai wannan loƙacin ba araye, in asirce asircen nanne ba wani ɓoye ɓoye kuma duk munyi saidai namu na hankali mukayi bare kuma ku da kullum kai ƙara buɗewa yake duniya ta zama abun da ta zama,
kuma kuma nasan kunyi kallon ku kawai nake ina kawar da kai duk wani mitsin mutum saidai inbeye agaban ido na ba amma yar nake kallon ku shiyasa ma zakuga bana shigowa saboda inna ce zan dawo nan to wallahi ruwa ma sai ya gagari wasu sha ajirayi ranar ƙin dillaci kuma ajuri zuwa rafi watarana tullun zai fashe ne........
wata tsuhuwace da tafi kowa tsufantaka agurin take faman wannan zuba surutun itaɗin uwa ce ga sarki me murabus(papa) mahaifiyar suce wacce suke kira da gwaggo ita ba a ɓangaren take zaune ba tana cen ɓangaren autan ta Ibrahim dan ɓangaren suma sai ka fita daga masarautar tunda mijin ta *sarki Sameer* ya rasu bayan ɗan ta ya hau mulki ita kuma tace ta gama zaman cikin masarautar ita da zaman ta aciki saidai ta kawo ziyara ko kuma idan wani zama yakama akirata ayi shine suka koma wajen masarautar ita da autanta da kuma matarsa da ƴaƴan sa saidai duk da haka shi autan nata Ibrahim yana da part ɗin sa acikin masarautar dan haka ƴanƴan sa ma sunfi zama acikin tunda suka girma kuma suka koma ciki ga ɗaya yarage daga ita sai shi sai matar sa amma awajen ma ɓarin ta daban ita da me aikin ta shiyasa ma batafiye shigowa masarautar ba sosai a iya can take rayuwar ta kuma ba komai dake faruwa aciki take sani ba ba ta tambaya kuma ba a gaya mata saboda tana da zafi mafaɗaciyaci tana da faɗa sosai ga zuciyar bala'i dan zan iya cewa ma duk wani wanda ya fito daga tsotstsonta tofa sai yagado wannan zuciyar kama ga ƴan ƴanra ga jikoki harma tattaɓa kunen ta watakon irin su sam da suke tattaɓa kunne awajen ta....(ashe su sam ba abanza ba wannan zuciyar) duk da ta tsufa idan ka taɓota ka shiga uku dan duk min tsufan ta zata iya cewa zata dake ka dan ta wani wajen bata da mutunci ta wani wajen kuma akwai haƙuri ga abun dariya da barkwanci idan taso amma idan bataso abuba sai kace tafi kowa rashin fara'a da wulaƙan ta abu ita ba mutum ba kowa da komai ma yi mishi take dan ita har abinci ma wataran faɗa take dashi bare kuma ɗan adam ga bata ɗaukar wurgi da raini ko loƙacin baya da ƙuruciyar ta yanzu zakai mata abu duk girmanka tace ka rainata akwai son girma,
duk iskan cin fulani tana shakkar gwaggo idan tana gurin to bata yin abun dataga dama tane denawa saboda bataƙi taci mutun cin ta ba ko agaban waye idan tayi ba daidai ba shiyasa basa son ma abun da zaishigo da ita cikin duk sanda tazo sai tayi musu abun da zaisa su ƙara jin tsanar ta kuma suna ganin kamar da gayya wataran take musu abu dan tasan babu yanda za ayi da ita,
musamman fulani jitake kamar ta shaƙeta idan ta ganta..
itama kuma gwaggon bata giya shiga harkarta ba shiyasa ma halin su baizo ɗaya sunfi mutun ci da Ammah dake ita Ammah babu ruwan ta da ita koda tayi mata wani abun da bataji daɗin sa ba bata taɓa nuna mata saboda ta ɗauke ta kamar uwa tana yimata biyayya sau da ƙafa shiyasa itama gwaggo bata fiye yi mata wasu abubuwan ba take ɗaga mata ƙafa saboda taga bata da matsala daman ɗayar ce me shegen tsiwa tun tana ciki ta fahimci hakan shiyasa ma koda ta fita indai ta shigo tofa saitayi abun da zata musguna mata dan wataran ko ganin tama batason yi.........gashi kuma ba yanda zatayi da ita itace uwar sarki......,
fulani sunkuyar da kai tayi duk sai tajita wani iri aranta kuwa ta zagi gwaggo yafi cikin carbi sai taji dama bata haɗa zaman ba koma waya gayyato ta itade batace akirata ba kawai sai ganin ta tayi aciki tasan hakan zata iya faruwa amma bata taɓa tunani zai kai haka muni ba yaza ayi taso gaban mutane ta ringa cewa suna asiri to uban wa zasu asir ce lalle sai ta koyawa wannan matar zama abun nata yayi yawa dole ta saita ta dan ta kaita ƙarshe duk da tana uwar mijin ta hakan bazai hanata ta koya mata hankali ba dole yasan abunyi akanta bazai yiyu tana abu ita kuma tana warware mata ba tana sama da kowa tafi ƙarfin kowa acikin masarautar amma ita zata zo tana gaya mata abun da taga dama dole ta gane kuren ta nan kusa basai anje ko ina ba..........✍️
more comment more typing, no comment no update.
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[6/22, 11:09 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️63&64
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
"bayan gwaggo tagama magana nan yashiga tofa albarkacin bakinsa wasu suna goyon gwaggo akan maganar datayi gaskiya ce wasu kuma basu soba saboda jam'u da tayi nacewa suma duk suna yi suna ganin hakan baidace ba tace wasu suna asiri acikin masarauta kuma sude sunsan ba abun da sukeyi wannan kamar ƙazafi da cin fuska tayi musu agaban mutane..,,
wasude basuyi magana ba saboda sunsan gaskiya ne anayi amma basu da bakin magana ahakade zuciyoyin wasu babu daɗi taro yatashi batare da ansamu wata mafita game da faruwar wani abun da yafaru kowa yafita daga fadar rai ba daɗi.........
_____Ameesha
zaune take kan gadon su Amra ta zuba uban tagumi ta tafi duniyar tunani,
momma ce ta shigo ɗakin ganinta tayi tagumi yasata ta ƙarasa gabanta da sauri tare da riƙo hannu wanta tace me yafaru haka kika zabga uban tagumi me kike tunani firgit tayi tadawo daga tunanin nata cikin inda inda tace ba komai kawaide zama nayi natashi ne naga su Amra basa nan,
ɗan kallon ta momma tayi badan ta yarda ba tace ayya to yi haƙuri tashi inkaiki wajen su sunje wajen kakan sune sugaida shi nazata ma bazasu daɗe ba shiyasa nace suje da naga kina bacci amma yanzu kiyi haƙuri zo muje inkaiki kema sai ki gaida shi ko kai ta ɗaga mata tare da miƙewa tsaye sannan suka fita daga ɗakin atare tana riƙe da hannun ta,.
saidai ma suna zuwa falo basukai ga fita ba sai ga su Amran sun shigo da gudu Amra agaba hamra abayan ta ɗaya tana cewa Wallahi ni zankaita itama Amra nacewa bana rigaki zuwa ba kuma daman ai ni yace ba ke ba wallahi baki isaba su duk abun da suke ma basu lura da su momma ba saboda hankalin su ba awajen yake ba
saida momma ta dakatar dasu sannan suka lura dasu da sauri Amra taje ta riƙe Ameesha tace zo muje yi sauri,
momma ce ta kwace Ameeshan daga riƙon da Amra tayi mata tace ke wai lafiyar ku ƙalau ina zakuje kunshigowa mutane guri ko sallama babu,.
cikin haki Amra tace momma yaya Ammar ne fa yace muzo muɗauko duk wanda ya riga kaita zai masa babbar kyauta shiyasa kika ga muna gudu taƙarasa maganar tana ƙara jan hannun ta momma tace to me zaimata yana ina shiɗin meyasa shi bazaizo ba saidai akaita kuje kuce idan son ganin ta yake yazo inda take amma ba inda zata saura kaɗan Amra ta saki kuka jin abun da momma tace duk wannan gudun da tayi abanza kenan momma da wani zance wai yazo da kansa tade san halin ya Ammar ba zuwa zaiyi ba, cikin turo baki tace momma dan Allah kirabu damu mutafi yanzufa zamu dawo kuma idan yamin kyautar nan fa zan sanmiki Allah kisake ta mutafi shifa ganin ta yace mana kawai zaiyi saboda labarin ta da muka bashi shine yace muje mu ɗaukota,
"eh wallahi momma dan Allah kibarmu mukaita cewar Hamra,
momma riƙe baki tayi sannan tace to Allah ya kyuata gata nan tunda kunfi ƙarfina amma karkuɗaɗe kunji ni dariya Amra tayi tace bazamu daɗe ba momma mungode tana faɗa taja hannun Ameesha suka fita waje hamra na binsu abaya itade Ameesha binsu kawai take batare da tace musu ƙala ba,
ahaka suka fita daga part ɗin suka nufi part ɗin su Ammar suna ƙarasawa suka shiga ciki yana zaune afalon yanda suka barsa haka suka dawo suka sameshi yana jiran su,
da sallama suka ƙaraso falon ya amsa musu fuska asake idon sa akan Ameesha yana ƙara faɗaɗa murmushin sa dan yanda suka bashi labarin kyaunta sai yaga tama fi haka. masha Allah kawai yake faɗa acikin ransa har suka zo kusa dashi,
Amra "tace wallahi ni na kawota dan haka ni za aba kyauta badanni bama momma cewa tayi baza tazoba Hamra ta harare ta tace yaya wallahi ƙarya take nima nasaka baki Saida na saka bakima sannan momma ta Amince muka fito da ita,
shi duk surutun ma da suke masa hankalin sa ba akansu yake ba gaba ɗaya yatafi gurin Ameesha ita kwa ta sunkuyar da kai saima wani iri da take ji jin idonsa akanta na yawo saitaji soma take tabar wajen dan ta tsani kallo arayuwarta,
"saida Amra ta taɓasa sannan yadawo garesu yace me kuke cewa nan suka ƙara maimaita masa abun da suka ce yace to yanzu de duk kunci kyauta kunsan me za ayima?
"a'a suka haɗa baki wajen faɗa"
kushirya gaba ɗayan ku har ita sai mufita inkaiku duk inda kuke son zuwa muje shopping kowacce tazaɓi abun da take so,
atare suka tsalle harda rungume juna sukace yawwa yayan mu shiyasa muke sonka nan suka shiga lissafo inda suke son zuwa yace to kuje kushirya har suna shirin barin wajen yace to ni baƙuwar taku ko gaida ni batayi ba bamu gaisaba kuke shirin fita,
ɗan murmushin yaƙe Ameesha tayi cike da jin kunya tace ina kwana katashi lafiya?
"bana amsawa saida na roƙa zaki gaida ni,
to yi haƙuri ai naga kuna magana ne shiyasa nayi shiru inajiran idan kungama sai mu gaisa,
tunda tafara maganar yake bin bakin ta da kallo har saida tayi shiru sannan yace to shikenan na haƙura badan halinki ba, sunana Ammar duk danasan ma kinji abakin su Ni yayane awajen su inafatan kema zaki ɗaukeni amatsayin yaya ni kuma zan ɗaukeki amatsayin ƙanwa kamar su ina fatan hakan ba wata matsala,?
"ba komai nikuma sunana Ameesha
"nice to meet you"
"same here" ta bashi amsa
sosai ya shagala da kallon ta shide ganin ɗaya yayi mata amma duk tagama tafiya da imanin sa jiyake kamar ya tashi yayi ta tsalle ya rungume ta saboda yanda yake ji acikin ransa,
"yaya bari muje mu shirya
"Ok"
kawai ya iya basu amsa sukuma suka juya suka nufi hanyar fita
tunda suka fita yake zubawa bayan ta ido bai ɗauke ba saida suka fita daga falon yadena ganin su sannan ya miƙe shima yana ƙara sakin murmushi da saƙe saƙe fal zuciyar sa ya nufi nasa part ɗin dan shiryawa shima,
tunda suka fita suka fara tsokanar ta wai daga gani fa yayansu ya ƙyasa da ita itade saidai tayi musu murmushi batace musu komai ba har suka ƙarasa part ɗinsu suka shiga da murnar su suka sanarwa momma dake falo tana jiran shigowar su,
itama da murnar tace kaga ƴan gatan Ammar to sai kuyi sauri kar kuɓata masa loƙaci yace ya fasa musamman ke Amra me shegen nawar shiryawa sai kiyi sauri tace momma ai ni zan fara shiryawa ma duk saina rigasu shiryawa,
momma tace dade bansan halinki ba sai kice haka,
"Wallahi momma da gaske nake,
momma tace "to Allah yasa da gaskenne,
"tace "Ameen" tana dariya
Hamra tace "wallahi momma karma ta shirya taga inzamu jirata tana zama zamuyi tafiyar mu mubarta taji asalan sa,
"ku kun isa ku tafi kubarni ai wallahi indai banje ba to babu me zuwa aciki kinku gwarama ki gyara maganar ki yarinya,
"au nice yarinyar taki ni kike cewa yarinya momma kina jin abun datace ko,
*Momma tace "ku tsaya faɗa ku ɓata loƙacin ku anan ku daman ai ba a abun arziƙi da ku lafiya sai kunsa mutum yi da baki,
ƙwafa Hamra tayi tare da jen hannun Ameesha suka wuce tana gunguni ƙasa ƙasa,
Amra ma bata ƙara cewa komai ba tabi bayansu suka tafi ɗakin su.....
da kallo momma tabisu tana jinjina irin wannan halin nasu na faɗa da bazasu taɓa zama lafiya ba sai kaji kansu ko yaushe zasu girma su dena wannan halin nasu......
"Assalamu alaikum ina masu gidan nan ?
sallamar ce ta katsewa momma tunanin da take da sauri ta miƙe tsaye tana washe baki tace lale marhaban hajiya gwaggo yau kece awajen namu sannu da zuwa tafaɗa tana nuna mata waje, zama gwaggo tayi itama
fuskarta dauke da murmushi
bari inkawi miki abun motsa baki gwaggo dan nasanki da kwaɗayi bakin ki besan tsofa ba,
dariya gwaggo tayi tace naci ƙaniyar ki kinji mun yarinya nikike cewa ina kwaɗayi yo inama ruwanki da bakina daman baki na tsufa to saidai ko inna uwacen taki ne ya tsufa amma banawa ba dannawa yama fi naki kwari aradun Allah, ni yi saurima kisamo min abu me ɗan daɗi daɗi kinsan banason barin bakina hakan nan ba abu acikin sa nafiso kullum inganshi yana motsi,
dariya momma tayi sanann tace kingani ko ai kwaɗayin kenan idan so kike kiji bakinki kullum cikin motsi ai goro yakamara ki nema kamar yanda ko wane tsoho yake ciki idan ya tsufa amma ke saboda kwaɗayi kinƙi cin goro sai abu irin na matasan mutane irin mu kinci zamanin ki kinci na ƴaƴan ki ga na jikokin ki amma duk dahaka be ishe kiba sai kinci na tattaɓa kunnen ki gaskiya yakamata kibarmu haka kiɗan bamu guri musha iska ko masumu muci wani abun muma amma duk kinbi kin handime na kowa,
uwarki sa'adatu nace uwarki sa'adatu ko bakiji ba in ƙara maimaitawa uwarki sa'adatu tafaɗa tana cilla mata daƙuwa kinji mu da ja'irar yarinya uban me zanyi da goro ai ni haryanzu banyi tsufan da zanci goro ba ke koma nayi bazanci ba cin goro ai na marasa aikin yine abun da inkana cinsa kamar taba yake zamemaka idan bakaciba kashiga wani tashin hankalin gashi kuma daman lafiyar ka kake lalatawa shiyasa ma masu cin suke mutuwa da wuri basu san kashe kansu suke ba,
ke wallahi ma Allah ya isana idan kika ƙara cemin inci goro bansan me yasaba kaf cikin