Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   66 / 74

195K to 198K   out of 221K words

rabata da ɗan ta batare da sanin taba yarda wane irin yana yi zata kasance shin zatayi farin cikine ko kuma baƙin ciki takasa tantance halin da take ciki babama dai saida ya zubda ƙwalla ahaka dai aka cigaba da rarrashin su da basu baki har sukayi haƙuri suka fawwalawa Allah suka karɓi ɗan su shima duk juriyar sa saida yayi kuka idan ya tuna irin zalinci da yasa akayiwa mahaifinsa shikam duk da arashin sanine yana jin bazai taɓa yafewa kansa ba akan wannan laifin da ya aikata da kansa yasa aka ringa azabatar da mahaifinsa harda ƙanwar sa ma da suka fito ciki ɗaya da ita yasa ancutar dasu cikin kukan da bai taɓa yiba tunda yake ya tsugunna har ƙasa ya bawa baba haƙuri tare da neman yafiyar sa saida ya ɗauki loƙaci mai yawa yana basu haƙuri har saida baba ya dakatar dashi tare da cewa ya yafe masa suniya da lahira yasan ai arashin sani yayi hakan shi kansa da ace yasani bazai taɓa aikata hakan ba dan haka yadain ganin kansa amai laifi,

maama ce ta fara magana tare da ƙara basu haƙuri abisa cutar dasu ɗin da akayi aka rabasu da ɗan su da kuma abun da akayiwa baba suma suka nemi da su faɗi hukuncin da suke so ayiwa su fulani, ana tambayar su sukace su babu wani abu da zasuce ayi mata taje ita da Allah Allah ya saka musu,


papa ya ɗora da cewa inason duk abun da kuke so kufaɗa tare da yi musu alƙawarin kulawar su ta dawo hannun su sannan kuma shi sarki Salahudden zaici gaba da zama agidan dan ya riga da yazama ɗan gida baza ataɓa korar sa ba saidai kawai yaga ma tashi daga matsayin sarki zai koma daidai da kowa part ɗin sama yana nan amatsayin nasa ba yaje yaci gaba da zama acan,

fafur Salahudden yabasu haƙuri yace shi bazai iya zama anan ba subarshi kawai ya koma wajen iyayen sa suci gaba da zama tare, da ƙyar aka bashi baki akace yayi haƙuri ya zauna domin zaicigaba da zama amatsayin ɗa agidan idan yace zaitafi kamar ya watsa musu ƙasa a idone, nan ma dai ƙin Amincewa yayi saida maama ta saka baki amaganar sannan tace tana roƙon papa da tana so suma su dawo nan da zama sai aware musu part ɗin su sai yaringa ganin su kullum idan hakan yayi masa saidai ina suma su baba ƙin amincewa sukayi saidai sun saka baki akan sun yarda shi yaci gaba da zama anan ɗin in yaso yaringa zuwa can inda suke,

da ƙyar dai akasamu ya amince shima saboda iyayen sa, saboda yanaso yafara yi musu biyayya tunda har suka nuna suna son ya zauna ɗin zaizauna kawai saboda su ammafa kusan kullum yana tare dasu acan bacci ne kawai zai ringa shigowa dashi gidan abun da yabarwa zuciyar sa kenan,

ataƙaice👌........ daga nan aka gama duk wani abu da za'ayi mai magana yayi magana su fulani kuma aka fita dasu amma saida ƙyar dan meer bai barta hakannan ba saida yasan yanda zaiyi yayi mata wani dukan gwaggo ma ta ƙara da nata ba ita kaɗai bana har hajiya Sarah itama saida ta samu nata kason na dukan sannan aka kwace su da ƙyar aka fita dasu daga fadar,

nan dai guri ya kacame da surutu kowa na fitar da abun dake bakin sa ga ɗan uwansa,

can na hango su saleem da shettiman da bossay da kuma sam suma suna tattaunawa akan yanda wannan abun yakasance tare da jajantawa saleem bisa abun da akayiwa mahaifinsa da taya sa murnar samun yaya,

Azeema ma suna tare da Ameesha suna taya juna murna,

Hajiya dadda ma har tasaki jikin ta itama akan farko da gaba ɗaya tayi shiru kamar babu ita agun saboda jikin ta ba ƙaramin sanyi yayi ba da jin labarin nan da taga yafi ƙarfin kanta, sannan ta shiga taya jikarta murna da bayyanar ahalin ta har ƙwalla ta zubar na farin ciki da kuma ta tuna da mijin ta Malama da ƴarta da tamutu da Sameer da ta ɗaukesa tamkar ɗan cikin ta saitaji jikin ta yakuma yin sanyi,

su ummy ma baki har kunne idan ta kalle ta taga wai yau itace cikin dangin mijin ta abun yana mata daɗi Musamman idan ta tuna zataje ƙasarta ta ta nunawa mahaifin ta dangin mijin ta kamar yanda yayi fushi da ita yace har sai ta kawo su to yanzu loƙaci yayi zasu shirya da mahaifin ta loƙacin da zata ringa nufar gidan su koda yaushe batare da taji farga bar haɗuwa da mahaifin ta ba gaskiya yau ta tsinci kanta cikin farin cikin da ta daɗe batayi irin saba,

su Hajiyar shettiman ma da su Ammi kowa yayi mamaki yanda komai yakasance haka da kuma taya su farin cikin haɗuwa da junan su.....,

hakadai kowa yayi abun da yakeso agun anataya juna farin ciki wasu kuma baƙin ciki kowadai da kalar yanda ya fahimci maganganun wasu kuma hukuncin da akayiwa su fulani baiyi musu ba sam wasu kuma basuji daɗi ba masoyan ta kenan,

Allah sarki bawan Allah hamza da babu wanda yake bi ta kansa yana zaune guri guda ya haɗa kai da gwiwa yana faman zubar da hawaye batare da kowa ya lura dashi ba shi kaɗai yasan halin da yake ciki na damuwa yayi da nasanin kasancewar sa ɗaya daga cikin masu iyaye masu halin mahaifiyar sa baitaɓa sanin haka mahaifiyar sa take ba anya ma kuwa ita ta haifeshi ahikaɗai sai tunanen tunanen yake bashi da wanda zai rarrashe shi sai yaji ya tsani kansa dama duniyar gaba ɗaya ji yake inama ya mutu agun ya hutawa ransa......,


sam ne yafara lura dashi dan haka yayi saurin yi masa magana tare da sanar da papa shi dan ganin anmanta dashi, anan shima dai aka bashi haƙuri tare da jansa jiki da kwantar masa da hankali duk da mahaifiyar sace ta aikata hakan amma saboda halinsa na gari yasa babu wanda ya nuna masa hantara ko kuma nuna jin haushinsa akan abun da mahaifiyar sa tayi hasalima haka akace laifin wani ai ba ya shafar wani dan baka ya kwantar da hankalin sa daga yanzu shima yadawo ɗan gida ya zaɓi inda yake so ya zauna dan badan ta sanadin saba da baza ataɓa sanin sirrin dake ɓoye ba, haka sukai tayi masa basu rabu dashi ba har saida sukaga yaɗan saki jiki dasu kaɗan duk dade sunsan taci na ciki bazai taɓa mantawa ba amma dai yaɗan sake ba kamar ɗazu ba........,

daga nan kuma suna cikin fadar papa ya bada umarnin aje agyarawa gimbiya sabreena ɓangaren ta saboda tunda ta mutu babu wanda akasaka aciki an ƙulle sa kawai amma wasu loƙutan akan shiga aduba sa sannan a gyarashi tsaf kamar da wanda yake kwana aciki,

dan da nan kwa akaje aka rufar masa da masu gyara aka gyarashi tsaf aɗan ƙanƙanan loƙaci komai yazama ready me shigar sa kawai yake jira,


su mamma da babama sukayi sallama da su suka tafi saida banda Azeema, Azeema tunda suka haɗu da Ameesha suka manne cike da kewar junan su hakan yasa su baba suka barta Salahudden ma zai bisu aka dakatar dashi akan yabari komai yaɗan fara daidaita kafin yayi shiri na musamman dashi da iyalen sa harma da su papa duk sai suje tare aƙara fahimtar juna,

basu daɗe ba suka wuce gida tare da ƙyautar kuɗaɗe masu yawa da papa yasa aka basu, tare da bada mota da fadawa suyi musu rakiya har gida,

daganan kuma zama yaƙare akan sai an ƙara yin zama nagaba an tattauna akan yanda za aɓullowa al'amari wajen zaƙulu mugayen, sannan akace gimbiya ta koma part ɗin ta tare da su dadda da Ameesha, Abu kuma shima aka gyara masa wani part ɗin inda zasu zauna kafin asan abunyi dan ba nan yakamata ya zauna ba dole abashi waje ƙawatacce amatsayin sa na ɗan sarki guda kuma ana tunanin zai zama sarki tunda yanzu kan kujerar babu kowa amma dai kafin ya hau sai anfara daidaita komai domin yanzu ba wannanne akan gaba ba,

sannan anjinjinawa su bossay kan namijin ƙoƙarin da sukayi wajen taimakawa su Ameesha sananna akace ayau suje su ɗauko mutanen da suka kama su dawo dasu cikin masarautar sai aci gaba da tuhumar su anan,

su Hajiya ma da Ammi tun agurin sukayi sallama dasu suka tafi gida saidai fa duk wannan abun da akayi babu wanda yace mahaifin bossay shi ya buge ta da motar sun rufe abu kuma daman maama ce ta gargaɗesu akan hakan tunkan ayi zaman dan haka har akayi aka tashi babu wanda yasan da wannan maganar har suka tafi,

dagan nan kuma papa da su maama suka fito atare dan nufar part ɗin ta suna fitowa aka fara sakin saraiwa ana hurata ga kuma ganguna da wasu suke bubbugawa na murnar dawowar gimbiya sabreena saboda gaba ɗaya ilahirin Masarautar babu wanda baiji labarin da wowar ta ba kuma an fahimtar dasu cewar daman ba mutuwa tayi ba shiyasa suka haɗa wannan abun da su nuna farin cikinsu akan hakan suna waje amma babu labarin da bai riskesu ba daman na saukar sarki agaban su akayi basa buƙatar ƙarin bayani, kiɗa suke sosai wasu kuma ma rawa tsofaffin bayin da suka santa mata suma suka dawo ta bayanta suka fara take mata baya tare da kwararo mata kirari nan da nan maama tafara jin kanta asama tunawa da baya da tayi daman tafiyar ta ta daɗe da canzawa ta koma gimbiyoyin ita da papa ne agaba sai Meer da ta riƙo hannun sa badan yanaso ba kawai yake binta, sai su Abu da ummy da dadda baya su Ameesha kuma suna tsakiyar su ita da Azeema da ta riƙo hannun ta, harda gwaggo ma itama tana cikin tawagar su bata bari anbarta abaya ba,

ahaka suka ringa tafiya anayi musu kiɗe kiɗe tare da kirari har aka rakasu part ɗin sannan suka dakata masu kiɗan matan kuma Saida suka rakasu har ciki sannan aka sallame su tare da yi musu godiya,

Sam, bossay, shettiman, harda hamza ma da suka jawo shi ta ƙarfin tsiya saboda tausayin sa suke yi atare suka fita sai suka wuce part ɗin fulani gaba ɗayan su dan su samu su huta kuma su tattauna,

su waziri ma da sarki Salahudden ahaka dai ɗaya bayan ɗaya dai ƴan cikin fadar suka ringa ficewa daga ciki Ammah ce ƙarshen fitowa daga ciki tana tafiya tana harhaɗa hanya saboda jirin da yake ɗawainiya da ita ganin yanda akayi watsi da ita anma manta da ita agun sunyi gaba sun barta hakan sai taji babu ɗaɗi aranta ga kanta da yake mata wani irin ciwo ahaka ta daddafa taƙarsa har part ɗin ta tashige ɗaki tare da faɗawa kan gado tana sauke numfashi,

su papa ma bayan sun shiga wata hirar suka ƙara ɗorawa kiran sallah ne kawai ya tashe su shima kuma suna idar wa suke kara dawowa su ɗora daga inda suka tsaya abinci kwa mai rai da lafiya akayo musu daga part ɗin momma sukaci suka ƙoshi basu suka dakata da hirar ba sai dare sannan aka raka su Abu inda aka gyara musu Ameesha da dadda kuma suma aka basu ɗaki ɗaya harda Azeema, sai kuma wani ɗakin dake ciki maama tace jikantane zai zauna meer ya zauna tare da ita bataso yayi nesa da ita su zauna part ɗaya gwaggo madai da ƙyar ta iya tafiya makwancin ta,

zuwa loƙacin kuma su sam har sunje sun dauko su baban sumy da wanda suka ɗauko a Abuja saida ba azauna dasu ba anbari sai zuwa gobe suma kuma su bossay duk gida suka tafi shi da shettiman yarage daga sam sai hamza da yakasa sakin jiki kwata kwata yanayi abu kamar marar lafiya......✍️✍️   
  
  
                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)
 
*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

              
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*
    
    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 97

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

     washe gari yanda aka kwanta da farin ciki haka suka tashi da farin ciki kowa ka tsinta acikin masarautar yana farin ciki da dawowar ahalin masarauta labaride ya karaɗe ko ina da ina har ƴan wajen gari ma sunji labarin abun dake faruwa shikenan yanzu za afara mulkin adalci, kowa yayi Allah wadaran da halin da  fulani ta tafka shekara da shekaru ana mulkin zalinci acikin masarautar yau gashi rana ɗaya Allah ya kawo ƙarshen abun,

suna zaune a part ɗin maama gaba ɗayan su bayan sun gama yin breakfast suka dawo falo suka zauna har gwaggo ma har tazo falon yacika maƙil da mutane wannan yazo yafita wannan yazo fita ana ta zuwa tayasu murna wasu kuma gulma ke kawosu suzo su ganne wa idon su abun mamaki,

basu suka daina karbar baƙi ba saidai aka kira sallar Azhar sannan aka dakatar da kowa bayan sunyi sallah sun dawo suka ƙara cin abinci rana sannan aka ƙara baje babin hira kafin daga bisani papa ya umarci su sam da suma duk ana falon tare dasu, yace "suje su ɗauko mishi mutanen da suka ɗauko jiya amma can cikin fada zasu kaisu zai zo ya samesu dan haka ba ɓata loƙaci sukaje suka kwaso su daga inda suka ajiyesu suka kaisu cikin fadar kamar yanda papa ya basu umarnin haka sukayi sannan suka dawo suka sanar dasu,

da papa da gimbiya sabreena da dasu gwaggo kusan dai su duka suka ƙara fita suka nufi fadar tare da fadawansu dake taka musu baya,

Ameesha kam tun asubar fari su Amra da sukaji labarin ƴar uwar su ce sukaje gurin ta suka ɗauko su ita da Azeema suka koma part ɗin momma sukaci gaba da shagalin su da taya juna murna,

su papa na ƙarasawa cikin fada kowa yasamu wajen ya zauna saidai fa har yanzu kan karagar mulki babu wanda yake zama akai so ake sai angama komai sannan a nutsu ayi babban shagali a ɗora sabon sarki, yanzu dai kusan papa ne akan gaba shi zai ringa juya komai kafin nan gaba saboda acikin su babu wanda yasan kan mulkin dole sai yana nuna musu komai ahankali,

bayan kowa ya zauna fadar ta ɗauki shiru aka umarci su baban Meer da su ma tso gaba su gabatar da kansu da kuma laifin da ake tuhumar su,

Matsowa sukayi jikin su ba karkarwar tsoro duk sunyi zuru zuru da su ga wahalar zaman da sukayi su sukaɗai baci ba sha saboda sam yama manta dasu babun da ake basu,

baban summy ne yafara ɗagowa cikin mawuyacin halin da yake ciki yace yace wallahi wallahi bansan komai ba kuma banda masaniya akan komai iya abun danasani kuma nagaya musu, yana maganar yana ɗan tsatstsorata yana kallon gefen sa sakamakon ganin Meer akan sa yana zagaye sa yana mishi wani irin kallo hakanne yasashi dakatawa da maganar da yake cike da tsoro da fargaba,

Papa ne yatsareshi da ido yana nazarin maganarsa kafin daga bisani ya ɗan numfasa yace "katababar maganar da kafaɗa iyaka gaskiyar ka kenan....?

kai abban sumy ya ɗaga masa tare da cewa "eh"

jinjina kai papa yaƙara yi sannan yace "tom naji bayanin ka amma fa kasani idan bincike yayi bincike aka gano kasan wani abun bayan wannan to wallahi hukuncin ka sai yafi na kowa ka yarda? yace "eh"

bayan yagama nasa bayanin aka koma wajen ɗayan da yake ta faman rarraba ido kamar ankama ɓera arami,

papa yace muna sauraron ka kagaya mana inda ka mayar mana da ɗa kuma waye yake saka,

cike da fargaba ya ɗago yana kallon papa sanna yace wallahi wallahi wallahi nayi muku rantsuwa har uku na rantse da mahallici na ni kaina bansan wannan mutumin da kuke magana akai ba hasalima ban taɓa ganin sab........,

baikai karshen maganar ba meer dake gaban sa ya kwashe shi da wani irin gigitacen mari tare da kai masa naushi afuska Meer bai sake shiba yakuma jin wata uwar shaƙa daga gurin sam da ransa yagama ɓaci da jin rainin hankalin da yake neman yayi musu, dan haka shima ya tashi rai aɓace ya shaƙesa da ƙara masa wani naushin sannan cikin ɗaga murya sam yace "mu zaka rainawa hankali da wata banzar maganar ka ko ka mayar damu ƴan ƙwaya ne ka kiramu da kanka kayi mana wani gargaɗi da tsoratarwa kuma shine yanzu zaka zo mana da wata banzar magana how dare you ehhhh.....! ya ƙarasa maganar tare da buga masa wata iriyar gigitacciyar tsawa idon sa har ya canza kala saboda tsantsar ɓacin rab da yafara zuwan masa,

jin haka yasa meer yaƙara karɓar sa daga hannun sam suka fara pacing pacing da shi suna neman kasheshi da duka, sannan su Abu saukayi saurin dakatar dasu da ƙyar aka iya rabasu aka kwace sa daga hannun su,

ahakan ma saida papa yasa baki sannan suka dakata su ka koma gefe kowa jikin sa na tsuma duk wanda yagansu dole su furgita ka su baka tsoro ko basu ce da kai komai ba kallon yanayin su kaɗai zai sa ka shiga taitayin ka,

shikam da aka gama luguda yana yashe aƙasa sai faman sauke ajiyar zuciya yake akai akai dan yaji ƙanshin mutuwa,

maama ce tace masha Allah tun ba aje ko ina ba kenan kadai ji ajikin ka ko dan haka sai ka taso ka faɗa mana gaskiyar magana idan kuma kace kwana kwana ɗin zaka cigaba

66 / 74