Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   52 / 74

153K to 156K   out of 221K words

maganar dan ta tabbatar wa da kanta zargin takeyi akansa,

maama zanso ki nunamin wannan gwaggon da kike magana akai saboda maganar ki zata iya zama gaskiya ni bansan inda dangina suke ba nadai san na taso da mahaifin na sannan da matar sa da ƙannena wanɗanda muke uba ɗaya dasu mahaifiya ta kuma banma taso da itaba bansan taba ancemin tun ina yaro ta rasu,

sukuma ƴan gidan mu tunda natafi neman aiki ina kasuwanci naɗau loƙaci me tsawo banzo gida loƙacin kuma da nadawo gidan natar dashi arufe dana tambaya ake cemin ai sundaɗe da tashi kuma ba'asan inda suka koma haka nai ta nemansu bansamu inda suke har na haƙura na koma naci gaba da rayuwata ni kaɗai bayan nayi kuɗi ma naƙara bada cigiyar su lungu da saƙo harda gidan jaridu da tv amma ba asamu inda suke ko kwanaki ma anƙara cigita min su haryanzu shiru bansan inda suke ba maganar da nake miki dai yanzu mutane biyun nan da kika gani su kaɗaine dangin na daga ɗana sai matata banda kowa bayan su, ya ƙarasa maganar cike da kalar shiga damuwa,

gaba ɗaya ƴan falon babu wanda bai tausayawa rayuwar sa a duniyar nan kowa kagani da kalar tasa damuwar shidai yanzu idan kagan sa bazakace yana cikin damuwa ba sai ka rantse da Allah bashi da wata matsala arayuwar gani zakai duk abun da yake nema yasamu ashe haka Allah yake tsarin sa baya haɗawa mutum duka gashi da uwar kuɗi amma kuɗin basu isa sun siya masa abun da yarasa ba, idan yabaka wani abun sai ya hanaka wani abun haka Allah yake tsarinsa,

maama ce tace Allah sarki "zan haɗaku kwa kaganta dangin ka kuma kar kaƙara cewa baka dasu ba mutum biyu bane suka rage maka mutane ba adadi ne kaiɗin ɗan dangine cikakke ma kuwa uwa da uba,

babu yanda za ayi ace mahaifin da ya tsugunna ya haifema ya yafi yabarka ina tabbatar maka da duk binciken da kake musu suna jinka kawai basu da ra'ayin kane akusa dasu saboda basu suka haifeka ba shiyasa basu damu dakai ba,

mahaifiyar ka kuma tana raye ba mutuwa tayi ba amma dan in tabbatar maka da hakan in ba damuwa ina so ka aske wannan gemun da yacika maka fuska ya canza maka kamanni gaba ɗaya idan ka sake akwai wani baƙin tabo agefen ƙasan haɓarka idan nagansa to tunanin danake ya tabbata idan kuma bangani ba to bahaka bane duk da nagani a hoton da kuka ajiye afalon ku loƙacin babu gemu amma ina son ingani azahiri in tabbatar da ba camera bace zahiri ne,

da sauri Abu ya tashi tsaye yana kallon ta da hannun ya nuna ta yakasa magana da ƙyar ya iya haɗo kalaman bakin sa yace maama wane irin tunani kike akaina karkice tunanin danakeyi zai zama gaskiya taya kika san da tabo a fuska ta kuma meyasa kike tunanin waɗan cen mutanen ba iyaye na bane taya duk hakan tafaru,

Saboda nice  mahaifiyar ka labarin da nabaku cewar anfitar min ɗa daga ɗakina ansace shi na nemeshi na rasa to wannan yaron bakowa bane face kai!!

tsit falon ya ɗauka jin furucin ta shikam Abu mutuwar tsaye yayi yayi ƙeƙam agurin kamar gunki,

batabi takansa ba ganin yanayin da yake ciki kuma bata jira wani daga cikin su yayi magana ba saboda tafiso sai taje ƙarshen maganar ta kafin ta bawa kowa damar yin magana,

cigaba tayi da cewa   "kaiɗin ɗana ne dan cikin nane tunda nafarka acan gidan naku natashi naganka nagane hakan amma ban tabbatar ba saboda gemun da ya rufe maka fuska kuma ina tunanin kode gizau kake min amma da naga hoton ka wanda baka da gemun sai hakan ya tabbatar min da kamannin ka da mahaifin ka aduk inda naga jinina sai ganesa koda ba wani jini muka haɗaba sosai amma ina ganewa abun da yasa aloƙacin ma banyi maka magana ba saboda nafi so sai mun dawo nan sannan kakaini har wajen iyayen ka sai intambaye su shin su suka haifeka nasan zasu iya faɗar gaskiya sai kuma gashi bamuje ko ina bama nagane hakan ta labarin da bakayar yanzu,

tofa kowa yayi saranda afalon yaudai so ake akashe su da al'ajabi daga wannan labarin sai wancen labarin,

babu wanda maganarta bata dake saba suma kenan bare kuma wanda akayi domin sa jinsa yayi wani iri kansane yafara sara masa da wani irin ciwo kamar zai tsage dan wannan lamarin da yadawo kansa nema yake yagagaresa ɗaukan sa taya za ace wannan matar itace mahaifiyar sa kai wannan ba gaskiya bane shifa mahaifiyar sa ta rasu,

saura ƙiris ya faɗi Ummy tayi saurin riƙo shi ta rungume sai kawai tasaki kuka,

cikin kukan take cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Alahamdullillh kawai abun da take iya nanatawa kenan tama kasa magana saida ta daɗe ahaka sannan ta sakesa tace kaje kaje gurin mahaifiyar ka kaje  ka rungume ta karungumeta kaji ɗumin mahaifiyar ka da kadaɗe baka jiba  kaje"

kai ya shiga girgiza mata alamar bazaije ba dan shi ganin abun yake bambarakawai wani iri kamar almara haka yakeji yakasa yarda da maganar ta,

ummy taci gaba da cewa wannan itace mahaifiyar ka ni naji ajikina hakan gaskiya ne gaya maka ne kawai banyi ba amma ni tunda kabani labarin dangin ka nima nayi tunanin anya kuwa su suka haifeka iyayen da suka haifeka bazasu taɓa guduwa su barka ba wallahi waɗan can ba iyayen ka bane maama itace mahaifiyar ka ta asali kaje gare ta,

ahankali yashiga takawa zuwa gaban maama, yana zuwa kuma sai ya tsaya yana kallon ta,

hawayen da suka tararwa maamane tasa hannun ta share su tare da miƙewa tsaye ga hawaye na sauko mata ita kaɗai tasan halin da ta tsinci kanta ahaka ta daure ta sakar masa murmushi tare da ware masa hannun ta tanaso yayi hugging,

ƙinyi mata yayi saida ummy ta ƙara yi masa magana sannan ahankali ya buɗa hannun sa yaje ya rungume ta itama ta ɗora hannun ta akan bayansa, wani abu sukaji gaba ɗayan su yana shiga zuciyoyin su yana ratsa su kaunar uwa da ɗa na ratsasu,

baisan loƙacin da hawaye suka shiga gangaro masa kan kumatun sa sosai yashiga zubda hawaye shi kansa baisan name yake ba sun daɗe ahaka rungume da juna,

su Ammi babu wanda bai zubar musu da ƙwala ba sun matuƙar basu tausayi  uwa da ɗanta amma anrabata dashi tun yana jariri amma sai bayan shekar masu yawa zasu haɗu wannan wacce irin rayuwa ce me zasuji aransu wane irin farin ciki zasu tsinci kansu aciki,

da ƙyar suka iya raba jikin su maama ta share masa hawayen sa tana kallon sa tace saida najika ajikina na ƙara tabbatar wa da ɗana ne da gaske,

naga har yanzu baka yarda dani ba amatsayin mahaifiya ba kana kokonto ko to zan cire maka kokonton idan kaga mahaifin ka domin kamannin ka sak dashi Kadena wasi wasi akaina bana faɗar abun da banda tabbaci akansa  sai nasamu hujja sosai kuma jikina yagaya min sannan nake faɗar magana bana faɗan abun da nasan ba gaskiya bane dan haka ka yarda dani amatsayin uwa agare ka,

da sauri yaƙara rungemeta batare da ya sake taba yafara magana cikin hawaye yace "nima haka saida naji ɗuminki nafara yarda ɗumin mahaifiya daban yake tunda nake bantaɓa tsintar kaina cikin irin wannan yanayin ba,

koda hakan bai kasance gaskiya ba ni bayarda na ɗaukeki amatsayin mahaifiya nayarda dake na na karɓeki hannu bibbiyu duk wani abu da ɗa zaiyiwa mahaifiyar sa nima zan miki bare ma kuma nima naji ajikina ke ɗin uwace agareni ni nasan soyayyar da muke yi miki muduka ba abanza ba rashin sani ashe keɗin uwace gare ni sosai Abu yashiga yin maganganu da har saida maama ta dakatar dashi sannan ta raba jikin ta da nasa,

Suna rabuwa  ya ɗaga hannun sa  sama yafara godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana wannan ranace da bazai taɓa mantawa da itaba arayuwar sa baima san da wanne irin kalamai zaiyi amfani ba wajen nuna farin cikin sa ga mahaliccin sa,

sai loƙacin ƴan falon suka shiga tofa albarkacin bakinsu suna ƙara taya su murna,

Maama sosai ta tsinci kanta cikin farin ciki mara misaltuwa wai yau gata ga ɗan ta ga kuma jikokin ta har guda biyu koda iya wannan aka barta tagama samun duk abun da take nema arayuwa ko a iya hakane taci galaba akansu su da sukayi ƙulla ƙula suka tarwatsasu sai gashi Allah ya haɗasu duk loƙaci ɗaya me yakai wanann abun farin ciki saura ɗayan kuma shima tana fatan Allah ya haɗata da shi nan kusa in sha Allahu bai mutuba yanda taga sauran shima sai tagansa kafin tabar duniya,

afili tayi ce Allah yabayya na min kai Sameer Allah yakare min kai aduk inda kake,

"duka falon suka amsa mata da  "Ameen'"

komawa kowa yayi ya zauna duk wanda ka kalli fuskar sa kasan yana cikin farin ciki ayau ɗin nan,

bossay saboda zumuɗi miƙewa yayi yace bari yaje ya taho da su sameer su taho tare,

Ammi tace "gaskiya dai yakamata suyi sauri suzo suji wannan abun farin cikin zanso inga dadda inga yazatayi idan taji wannan labarin,

"gaskiya dai nima zanso ganin ta cewar ummy,

maama ce tace "a'a rabu dasu suzo atsanake ba sauri muke ba muna nan daku har dare ba inda zamu,

kawaidai je waje ka kiramin wancen yaron me zuciyar kutare yazo yaji,

dariya suka ɗanyi sannan bossay badan yaso hanasan da tayi ba yace mata to sannan ya fita zuwa wajen Meer yana fita suka ci karo dashi abakin ƙofa yana shirin yi masa magana kawai ga watsa masa harara yabi ta gefen sa ya shiga falon da kallo bossay yabishi har yagama shigewa cikin falon, sannan yabisa abaya,

akusan tare suka shiga ciki yana shiga rai aɓace bai kalli kowaba yace ummy zan koma gida idan zaku tafi kutashi mutafi inkuma kuna nan inyi tafiyata danni banga amfanin zuwan nan ba,

wakake da suna ne wai me naji kuna cemasa maama tayi maganar tana kallon su ummy ɗan murmushi ummy tayi tace Meer muke cemasa amma cikakken sunan shi Sameer,

maama tace ashe suna me daraja gare kice samari na tara ƴaƴa da jika suna iri ɗaya duka ƴaƴana sunansu sameer baban sa ma Sameer aka raɗa masa da ya ɓata ne naƙara haifar ɗayan aka ƙara saka masa sameer mahaifin khadeeja kenan amma shi naji ba acanza masa sunan ba tunda loƙacin yana ɗanyin magana shiyasa bai manta sunan sa ba gaskiya naji daɗin hakan,

kallon Meer tayi tace gto gaskiya kaidai ba  ɗauko halayen masu sunan kaba saboda duk bahaka suke ba duk acikin mu ka tsallake kowa ka tsallake mahaifiyar ka da mahaifin ka ka tsallake kakannin ka na farko ka tafi kaje ka ɗauko halin kakar ka tabiyu,

tunda tafara magana yake kallon ta yana yatsina fuska shi akan meyasa zata ringa haɗasa da wata can bare agefe har zai buɗi baki yamayar mata da amsa,

Abu ya dakatar dashi sannan tace Meer kasan wacece wannan kasan wa ka daɗe kana taimakawa kwance a asibitin kasan meyasa kaji kana sonta kake bata kulawa fiye da kowa kake yawan shiga damuwa idan antaɓata ko wani abun yasameta kake rikicewa kasan wacece ita,

cike da rashin fahimta Meer yake kallon sa sannan ya girgiza kai batare da yace komai ba yana cigaba da kallon mahaifin nasa,

miƙewa tsaye Abu yayi sannan yakama hannun me yakaishi har gaban maama yace wannan da kake ganin ta azaune itaɗin mahaifiya tace uwace agareni kai kuma kakar kace duk abun da kayi mata na taimako kakar ka ka taimaka,

zaro ido yayi yana maimaita maganganun Abu ɗin na ƙarshe sai maimaita wa yake kamar me koyon karatu,

Abu taya hakan zata faru meyasa tun acan duk bamu saniba sai yanzu anya kuwa hakan me yiyuwa ne gaskiya wannan maganar ba gaskiya bace wai bama ka taɓa cemun mahaifiyar ka ta rasu kuma taya za ayi wannan ta zama uwa agare ka,

ummy ce ta tashi tana ɗan murmushi daman tasan ko kowa ya yarda bazai yarda ba saboda shi amurɗe yake ba a iya tanƙwara shi ta daɗin rai sai anyi masa da gaske yake fahimtar wani abun,

kamasa tayi ta zaunar dashi tace "nutsu kaban hankalin ka nan gaba ɗaya kamar yanda tace hakan kwa yayi a tsanake tafara bashi labarin duk yanda akayi sosai tayi masa bayani tun baya ganewa har yafara ganewa,

sosai kwa shima lamarin yayi shocking ɗin sa da ƙyar ta iya yarda da hakan dan ba ƙara min mamaki yayi ba,

ana gamawa ya miƙe tsaye yace "dole su gane basu da wayo ko su waye ashe daman harda mahaifina acikin wannan zalincin nasu tabb akwa sunjawa kansu masifar da tafi ƙarfin su ko suwaye sai sun ɗanɗani kuɗar su domin sai na gana musu azaba me matuƙar wuya kafin inkasu lahira, dukan su sai sun ziyarci lahira da hannuna zan raba kowa da ransa tunda basu kashe ba to ni zan kashesu, (tofa daman lamarin ba dangin iya bare na baba ya zafafa akai zai ɗau mataki ina kuma ga shi aka taɓo faɗan nasune bana wajeba ai sa inda ƙarfi kuma yaƙare)

aloƙacin da yake waɗannan maganganun duk wanda yakalle sa sai ya tsorata dan sosai ya canza halittar sa yajuye ta ta koma ta mugaye marassa imani hannun sa kuwa sai faman karkarwa yake idonsa yayi ja jijiyo yin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu dasu daman shi haka yake bai iya fushi ba daman mutum kullum fushi da harhaɗe rai batare da anyi masa komai ba ina kuma ga antaɓo sa taɓowa ma me muni irin wannan ai duk wanda yafara shiga hannun ya shiga uku wataƙil saidai uwar sa ta haifi wani idan kuma ta daina haihuwa ta ɗakko agidan marayu ko tagama rayuwar ta ahaka,

dadyn su bossay baisan loƙacin da jikin sa yafara rawa ba babu wanda ya lura dashi ya tashi daga gurin yana niyar barin falon,

caraf idon Meer yafaɗa akansa yana ɗaga ƙada zai fara taka benen babu wanda ya ankara sai ganin Meer akayi yayi tsalle ya dire agaban dady da hannu ɗaya yajawo sa yadawo dashi gurin cikin wata iriyar murya me amo da karsashi irin ta jaruman maza yace maama kifaɗan abun da wannan mutumin yayi ninasan baida gaskiya gashi yanzu ya tashi zai gudu daga gurin amma kinƙi kifaɗi abun da yayi ko to wallahi idan baki faɗa ba hukunci na zai fara aiki akansa,

gaba ɗayan su miƙewa sukayi Ammi kam har tafara hawaye, bossay cike da tashin hankali yayi kan dady zai ƙwace sa Meer ya turasa gefe saura kaɗan ya bige da jikin ƙarfen kujera Allah ya karesa,

gaba ɗayan su babu wanda ransa bai ɓaci ba Abu ya daka masa tsawa yace kai wai kafara haukane yaza ayi kazo gidan mutum kuma karinga tuhumar sa gaban iyalen sa kai idan akayiwa naka iyayen zakaji daɗi meyasa baka tunanin kafin ka yanke abu,

Abu wai meyasa kake min haka idan ina abu kadena dakatar dani ko ni bansan me nakeyi ba tunda muka shigo matar nan ta nuna sa kuma shima ya nuna rashin gaskiya taya kake tunanin zan rabu dashi ai wallahi duk wanda nakama a case ɗin nan sai na kamasa koda basa hannun aciki amma matuƙar yasan wani abun ko anyi agaban sa wallahi shima sai kamasa dan haka wannan mutumin ma ba ruwana da iyalen sa inkaga na rabu dashi to sai na gane gaskiya,

tasss yaji a akan fuskar sa Abu ya kwasheshi da mari rai aɓace yace kaci gaba ina magana kana magana muzuba nida kai muga ɗan halak kafasa kuma kasake shi inbaka son ranka ya ɓaci anan gurin,

maama ce ta miƙe tsaye tace karda kasake taɓashi kayi nafarko kayi na ƙarshe indai akan case ɗin nanne yayi duk abun da yaga ya dace yanda basu da zuciyar imani nima haka nakeso ya nuna musu rashin nasa imanin ya taka nasu so nake susan bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane nasan ku ƴaƴan na kun manyanta baza ku iyayin komai ba dan haka bani daɗin wannan yaron da yakasance jinina yakasan jika agareni dan haka inban haifi wanda zai rama min mugunta da mugun taba to nahaifi wanda ya haifi wanda zai ramamin dan haka nagoyi bayan sa ɗari bisa ɗari,

Ammi da bossay ta kalla da suka ƙame suna jin zigar da take yimasa,

tsayiwar ta ta gyara tana kallon su da kyau tace ina mai baku haƙuri abisa abun da yafaru koma ince zai faru tun ɗazu yaron nan yake min zancen sa amma saboda ku da kuma mutun ciku da taimakon da kuka bawa jikata makasa cewa komai amma yanzu dole kuji wannan yazama dole ɓoyewar ma bata da amfani domin ko ban faɗa ba wannan yaron ba rabuwa zaiyi dashi ba,

gabansu ne yafaɗi tsakanin bossay da Ammi kowa na tunanin jin me kuma ya aikata haka mai mune akan baiwar Allah nan Allah yasadai bada sa hannun saba acikin zalunci da akayiwa waɗannan mutanen idan hakan ta kasan ce ina zasu tsoma rayuwar su,

basu kaɗai ba su kansu su Abu baƙaramin mamaki sukayi ba da jin batun ta,

cigaba tayi da cewa "ba ƙarya zan masa ba kuma ba sharri ba ba ƙazafi ba shi kansa yasan abun da ya aikata min amma duk da haka bazan faɗi abun da yayi ba saboda ku amma ina so yafaɗa da kansa kuma hafaɗi wanda yasa shi da dalilin da yasa yayi min haka ɗin, babana sakar shi zaiyi bayani da kansa yaci darajar matar sa da ɗansa amma badan haka ba sai yafara ɗanɗana kalar irin azabar da yayi min kafin ma abarshi yayi bayanin amma yanzu saboda masu daraja irinsu za 'a ɗaga masa ƙafa, yayi bayani da kansa,

kallo fa yakoma kan dady kowa shi ya zubawa ido yana jiran yaji me zaice amma yaƙi magana saidai kuma kallo ɗaya zakai masa kagane tsantsar tashin hankalin da yake ciki kana ganin sa kasan baida gaskiya.........,


************************

_______*Dadda*

saida su Amra suka gaji da tsokanar tafa dan kansu sannan suka rabu da ita sai sunga tana niyar tashi zata fita sai suƙara hanata ahakadai sukai ta wahalar da ita itama ta wahalar dasu momma tafiya daga ɗakin dan taje takawo mata abinci aikam dadda naganin

52 / 74