da jan motar yayi gaba yana cikin tafiya ya hango su can wajen titi atsaye,
agabansu yayi parking din motar tare da yi musu horn atare suka juyo gaba ɗayan su ganin shine yasa shettima saurin bude gaban motar ya shiga tunka yagama shiga yake tambayar ta ina?
shigowar sa idon sa ya sauka akan ta hakanne yabashi damar samun amsarsa batare da sam yabasa amsa ba,
bossay ma bude bayan motar yayi ya shiga inda take, bayan ya rufe sameer yaja motar batare da ya kula kowaba ko kallon inda sukema baiyi ba saima ƙara hade rai da yayi shi adole bazai kulasu kar su samu damar yin wata magana shiyasa ya ɓata fuska gudun raini, saidai abanza dan hakan da yayi bai isa ya hanasu tambayar saba,bossay ne yafara yi masa magana dacewa gaskiya aikin ka na kyau kace har ka ƙwmus ta kenan yafada yana kallon fuskarta da dan fara'a a fuskarsa yaƙara dacewa wannan ai tsaf zaka iya kidnaping mutane batare da bata lokaci dan naga alamar zaka iya fiya da hakama koma waye zaka iya kwamishewa,
da sauri yajuyo ya kalle sa sannan ya mayar da hankalin sa ga tuƙin sa da har zai tanka masa saikuma ko me yatuna sai yayi shiru kawai yacigaba driving din sa,
jin yayi shiru yasa shettima cegaba da cewa kai da angaya maka shidin nawasane ai tunda yaje dolene ta mutu akansa musamman ma da yayi mata kalaman sa nasan baiwani sha wuya ba wajen shawo kanta amma de abun tambayar anan shine dadewar me kukakyi tundazu kabarmu muna jira wallahi ƙafata har tafara ciwo saboda tsayuwar da kabarmu muna yi,
dan gayamana abun da kace mata ta yarda ta shigo motar da wane kalami kayi alwala kadan bamu musha(murmushi yayi tuna inda yasan kalmar dan bamu musha)
wani irin harara ya aika masa da ita can ƙasaƙasa da murya yace me ya hanaku zuwa kugani daga nan yayi shiru yasan idan ya biye musu ransane zaita ɓaci dan ba barinsa zasuba agaba zasu sashi suyi ta tsokanar sa saboda yaga alamar sungama rainasa,
cigaba yayi da tuƙin sa tare da ƙarawa motar gudu,
yana jinsu sunata tsokanar sa suna dariya amma yaƙi ya kulasu duk abubsu dole suka hakura sukayi shiru da magana saboda sukai kiɗan su suke rawar su,
unguwar da suka kaisa nan suka nufa adan ƙanƙanan lokaci suka ƙarasa gidan da suka ajiye sa yanzuma bossay ne ya fito yaje ya bude musu gate din sukuma suka shiga ciki bayan yagama yin parking duk suka fito,
sameer ne ya bude bayan motar inda take kwance har yanzu bata farfaɗo ba ɗagowa yayi sai kawai suka hada ido da shettima dariya shettima yayi masa dan yagane abun da yake shirin yi,
dan ƙaramin tsaki sameer yaja tare da kawai da idonsa daga kansa amma yayi tsaye yakasa taɓuka komai kuma bayaso wani yadauke ta acikin su shikuma bayaso ya dauketa suyi tunanin wani abun shiyasa yakasa tabata,
ahaka bossay da yagama rufe gate yaƙaraso wajen yasamesu,
shima tsayawa yayi ya kalli wannan ya kalli wancen ganin duk sunyi carko carko kamar nonuwan maza,
shettima ne yadanyi gyaran murya sannan ya kalli bossay yayi masa alama da ido akan sutafi, gaba sukayi suka barsa awajen,
binsu yayi da kallo yama rasa me zaiyi har suka shiga cikin gidan bai motsaba daga inda yake ba,
ganin tsayiwar baza takai shiba ya tsugunna ya shiga cikin motar yana ta wani taɓe fuska da yatsinata sai yasaka hannu zai taɓata sai kuma yafasa yajanye hannun sa yayi hakan wajen sau biyar amma yakasa tabata daga ƙarshema sai kawai ya fito daga cikin motar yana ƙara binta da kallo,
ajiyar zuciya yasauke tare da furzar da iska me huci daga bakin sa tare da cije lip dinsa na ƙasa yana dan jijjaga kai,
wata zuciyar ce tace masa wai meye hakan kake yi kashiga kawai kadauko kana ƙara ɓatawa kanka loƙaci wai sai kace kai bana miji ba wannan yarinyar zaka zauna kana wani jin shakkar tabata,
cike da dakewa yakoma cikin motar gadan gadan zai tabata sai kuma yafasa rintse idon sa yayi tare da dukan kansa yaƙara jan wani tsakin,
da ƙyar ya runtse idon sa ya daure ya cize yasa hannun sa akanta bayan ya dora hannun nasama akanta kasa ɗagota yayi sai da yaja lokaci sannan ya ciccibofa ya fito da ita tare da ɗorata akan kafaɗarsa yadafe ta da hannu daya dayan hannun kuma ya rufe ƙofar da ita sannan yafara tafiya da ita aransa yake ayyana bata da nauyi juyayi kamar ba abun da yadauka haka yakeji saboda rashin nauyin ta,
ahaka yana zancen zuci yaƙarasa bakin ƙofara sannan ya tura ya shiga ciki yana shiga yayi karo dasu abakin ƙofa ashe duk abun da yake suna leken sa suna masa dariya da suka ga yakusa shigowa ne yasa su matsawa daga jikin ƙofar,
tunda ya shigo suke binsa da kallo suna so yakalle su amma shikuma yaƙi yarda su hada ido ɗin,
ganin zai sauketa yasa shettima saurin cewa dan Allah dan tsaya inyi muku hoto wallahi kaga kyaun da kukayi banza yayi masa saidai kafin yakaita ga kwantarwar har shettima yadauke su a hoto loƙacin da yakai ga dan durƙusawa zai kwantar da ita yaƙara yimusu wani aƙallade saida yayi musu wajen guda biyar kafin ya ajiyeta,
bayan ya kwantar da ita yajuyo yana kallon sa wayar yazo zai kwace shettima yayi saurin janyewa tare da mayar da ita aljihu yana yimasa dariya,
hade rai ya kuma yi sannan yace wai ku dan Allah me yake damunku yanzu loƙacin wasane bakusan abun da ya dace ba da wanda baidace ba kunzo sai faman shirme kuke to wallahi last warning kufita daga idona be for I losing my temper wallahi bazakuji da dadi ba yafada yana nunasu da yatsa alamar gargaɗi,
"Shettima na yar dariya ciki ciki ya ƙame kamar soja yayi salute dinshi tare da cewa sorry sir bazamu ƙaraba,
ciki ciki yace mutum sai shegen son girman tsiya duk de hade ranka bazan gogeba wannan hoton sai yaje har gaban Ammah,
me kace cewar Sameer yana kallon sa ,
tabe baki Shettima yayi sannan yace mekwa nace ni ba magana nayi ba,
jijjiga kai yayi kawai yana girgiza kai sannan yayi gaba batare da yaqara tanka musu ba shiga dakin da suka ƙulle mahaifinta tura ƙoafar yayi da ƙarfi, yana shiga yaganshi a tsaye yana faman rarraba ido naushi yakai masa abakin sa atake bakin ya kuma fashewa, ya ɗago kenan zaiyi magana ya qara kai masa wani sosai ya shiga dukansa kamar an aikosa kuma yaƙi bari yayi magana shima kuma ko A baice masa ba sai duka kawai,
su Shettima ne suka shigo cikin dakin ganin yana niyar kaisa lahira,
yasa su saurin dakatar dashi suka shiga tsakanin su,
tsugunnawa yayi agurin tare da dafe kansa hakannan yaji yana mugun jin haushin shi da yagansa maganganun wancen mutumin ne suka shiga dawo masa cikin kwanyar kansa sosai yake jin zafi da ƙuna a zuciyar sa,
mahaifin sumy kam yana gefe a yashe yajigata kana ganin sa kasan ya daku ba ƙarya, dan numfashin sa har daukewa yake yi idon sama duk sunyi ciki ciki baya ganin su sosai yajigata ko motsi yakasa yi,
"sameer tashi yayi daga tsugunen da yake ya ƙarasa gaban shi tare da durƙusa gabansa yana kallon ɗago fuskar sa yayi da kyau yanda zaifi ganin sa cikin amon murya yace zaka fadi inda yake ko sai na karar da numfashin ka agurin nan waye shi kagaya min yafada cikin tsawa da daga murya kafada nace waye shi?
"shiru ba amsa jin yaƙi basa amsa yasa yaƙara daga hannun zai kai masa duka yaji an riƙi masa hannun,
bin hannsa yayi da kallo har zuwa kan nata hannun ahankali ya shiga bin hannun nata da kallo har yazo kan fuskarta hawaye yagani a fuskar ta, saurin kawar da kansa yayi tare da kwace hannun sa,yana maida shi kan mahaifin nata zai dake shi tayi saurin shiga gaban mahaifin nata ji kake tass akan fuskarta dafe kunci ta tayi tana wani sakin marayen kuka cikin kuka tace kadake ni kaci gaba da dukana mai mukayi maku nida mahaifina daman sato ni kayi shine zaka yaudarene maiyasa zakayi mana haka mai wane irin zunubi muka aikata maka da muka cancan ci wannan hukuncin daga gareka kallifa yanda ka maida mahaifina kuma hakan bai ishe kaba kake shirin ƙara masa wani,
kai wane irin marar imani ne baka da tausayi me ya aikata maka takarasa maganar cikin daga murya tana share hawayen da suke rige rigen zubowa,
cak ya tsaya yakasa motsawa saida tagama maganar tata sannan yasa hannun sa yajanyeta gefe taga taga tayi zata fadi yayi saurin tarato da hannu daya saida tagama daidaita sannan ya sake ta,
ƙara riƙo mahaifin nata yayi sannan yace idan kana son ranka da na ƴarka kafada min kai bama ita kadai ba har matar ka da mahaifiyar ka duk nasan inda suke dan haka kazaɓa rayukan ku ko wancen azzalumin da kake karewa,
ƙara matsowa tayi kusa dashi tace maizai fada maka? "banza yayi da ita baikalli inda take ba yaci gaba da tambayar sa amma yaƙi magana,
shake wuyan sa yayi da kyau yanda zaiji ƙanshin rahila,
cikin kuka ta riƙe hannun sa tana jansa amma ko gezau takasa juyawa tayi tana kallon su Shettima da sunyi tsaye suna kallon su sun kasa saka hannu kuma sun kasa cewa komai,
dan Allah kuzo kuriƙeshi kar yakashe min mahaifi wallahi idan yakasheshi duk sai na shigar daku ƙara tunda kuma baku da imani kuma ganin za ayi kisan kai amma babu wanda yayi yunkurin hanawa, komawa tayi kansa taci gaba da jan hannun sa tana dukan sa tana kai masa cizo amma yaƙi saki daga ƙarshe ma sai yasa dayan hannun sa ya riƙe mata duka hannuwa biyun,
da ƙarfi tace abbaaaa kafada musu abun da suke buƙata zasu kashe ka dan Allah kafada musu Abba kafada musu na roƙeka tafaɗa tana ƙara sakin wani kukan muryarta har tafara dashewa saboda tsabar kuka,
kukan da take ni ya dami sameer yasa shi sakin mahaifin nata,
yana sakinshi yafara tarin wahala harda amai ga jini da yagama bata masa fuska duk yayi gaja gaja dashi kuma yakasa magana duk da zuwa yanzu ya fara saduda musamman ma da yaga ƴarsa ahannun su,
zaka fada din ko incigaba? cewar Sameer,
cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace
yana ABUJA................✍️✍️
[6/4, 1:34 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖NEW TEAM💖
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️47&48
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace yana ABUJA....
Abuja a ina?
Shettima da yazo wajen ya tambaya,
"cikin mawuyacin halin yaƙara cewa nima bansani ba nade san kawai a abuja yake saidai kuje kunemo shi nikuma kusake ni in koma wajen iyalina,
"idan kaga munsakeka to yazo hannun mu cewar Sameer yana wani binsa da kallon tsana,
mahaifin sumy yace nifa bansan komai ba akan case ɗinku meyasa kuma zakace baza kusakeni ba bana gaya muku abun da kuke buƙata ba kuma me ƴata tayi muku bani nayi muku laifi ba meyasa zaku saka ta aciki yaƙarasa maganar cikin sanyin murya,
taya kake tunanin zan yarda dakai bakasan komai ba kuma kayi mana ƙarya saboda yabaka cin hanci shiyasa, daka gayamana gaskiya tun farko da tuni hakan bata faru ba amma kanuna son zuciyar ka saboda kudi kasan zunubin da ya aikata dakake goyon bayan sa kasan laifin yin hakan dakayi yanzu duk matsayin ka dakake taƙama dashi zan iya shigar dakai ƙara akan laifin da ka aikata na karbar cin hanci, koma ince aikin daka hau daman badan Allah ka karba dan karinga tauye haƙƙin mutane waysani ma ko baka san komai ba kawai ɗoraka akayi kawai niban banma sam suwaye suka ɗoraka awannan matsayin ba saboda baka san abun da Yakamata ba kana goyon bayan rashiya gaskiya,
to bari inganta maka inma bakasani ba duk matsayin sai na iya sawa anƙulleka wanda yakiraka yahada mu nasan kasan matasayin sa wanda sama yake da kai to ni kuma ɗane agaresa dan haka shigar dakai ƙara ba abune me wahala ba,
dan dakatawa yayi yana cigaba da kallon sa suna hada ido da shi yayi saurin kawar da nasa idon
juyawa yayi ya kalle ta ganin yanda take ta faman fusge fusge zata kwace hannun ta daga riƙon da yayi mata amma takasa shikuma yana jinta kuma yaƙi ya sake ta,
"harara ta watsa masa ga fuskarta duk ta jiƙe da hawaye,"cikin hawaye tace ni kasakeni mugu azzalumi marar imani koma me yayi muku Yakamata kayi masa irin wannan dukan so kake ka kashe shi saboda kawai yaƙi gaya maka abun da kake buƙata sai ka kamasa da irin wannan dukan jifa yanda ka mayar masa da fuska to wallah Allah ya isa Allah yasakamasa nima yaudarata dakayi banyafe ba in sha Allah yanda kayi masa kaima sai kasamu wanda zaiyi maka irin haka,
"kai ko girmansa ma baka gani kuma agabana saboda baka da kunya bekamata amatsayina na ƴa awajensa kakama dukan sa agabana kai yanzu zakaji dadi idan wani yazo yana dukan mahaifin ka agaban ka wane me zakaji acikin ranka wane irin mataki ne bazaka dauka,
amma ni saboda macece nasan ba abun dazan iya yi maka amma kaje kai da Allah zakaga sakayya wannan abun da ka aikata Allah bazai barkaba Allah ya........"ɗall taji abakin ta sameer ya dallar mata baki, nunata yayi da hannu yace ki iya bakin ki kisan da wanda kike magana inbahaka ba kuma zan saita miki shi bana daukan raini,
"taji zafin dallar tata da yayi da yasa ta sakin kuka cikin kuka tace bakasan raini amma ni ka raina min mahaifi harkake dukan sa shi bai girmeka ba kuma agaban yar sa da yayi auren wurimada tuni ya ajiye ɗa kamar ka amma kayi masa abun da kayi niyya akwai abun da yakai irin wannan raini,
"Bana raina mutane ba raina na gaba dani ina girmama duk wanda ya girmeni koda da kwana ɗaya ne, amma kaide bazan taba girmama kaba har abada saboda wanda baisan darajar mahaifin ka shima bazaka taba ganin darajar sa ba har abada taƙarasa maganar tare da ɗan ɗaga masa murya tana ƙara jan hannun ta amma haryanzu yaƙi saki ya kafe ta da ido kawai,
dataga yaƙi sakinta saida ta faki idon sa, sai kawai tasaka haƙoran ta akan hannun sa ta gantsara masa cizo me zafi kamar zata cire masa fata kuma taƙi saki, "jin zafin ya ratsasa yasashi kwace hannun sa da sauri tare da kwashe ta da wani lafiyayyen mari cikin bacin rai yaƙara kwashe ta da wani marin,
"cikin daga murya ya nuna ta da hannun ta yace wai ke wace irin jahila ce kinsan dawa kike magana Ni sa'anki ne bakida kunya ko harni zaki ciza, cizo cizo yamaimaita kalmar dan baƙaramin mamaki ta bashi ba cigaba yayi da cewa ke mayya ce daman to wallahi aniyarki tabiki dan nafi ƙarfin ki,
"yanzu de bata kulasa ba tafaɗa kan mahaifinta tana fashewa da wani marayen kuka, har cikin ransa mahaifin ta yaji marin da aka yiwa ƴarsa mafi soyuwa agaresa daman saboda ita yafada musu amma badan haka ba ko me zasuyi masa bazai gaya musu ba kawai sunci darajar ƴarsane saboda bayaso ana dukansa agaban ta gashi kuma itama baisan me zasuyi mata ba idan bai gaya musu ba shiyasa kawai ya yanke shawarar gaya musu din shima kuma iya garin da yake yagaya musu baigaya musu unguwar da yake zaune ba kuma yasan har gidan da yake,
"rungume shi tayi sosai ajikin ta tana ta fama kuka harda sheshsheƙa idan kaga yanayin da suke ciki dole sunana tausayi,
"yarfe hannun sa yake tayi yana kallon gurin da ta ciza din har ya kumbura yayi kala ga zafin da yakeji duk dauriyar sa nema yake yakasa daurewa din,
su Shettima ne suka shiga yi masa sannu ganin yanda gurin cizon yayi jaaaa abunka da da fari kuma ajeboo,
cike da kausarsiyar murya me cike da abubuwa kala kala yace kufita da ita daga nan kafin inkasheta aɗau gawar ta anan yafada yana nuna musu ƙofa yaƙara cewa kufitar da ita nace,
"Bossay ne yafara zuwa inda take yafara kanta amma sai ta riƙe baban nata gam,
saida su kadage kafin suka rabata da jikin shi shima da ƙyar suka bambanreta suka nufi waje da ita tana kuka tana ɗaga murya tare da ƙara zage shi har suka fice daga dakin yana ganin fitar su ya rufe dakin sannan ya juyoasukwane yadawo kusa da mahaifin nata yadago sa tsaye da kansa sannan yace kanason ƴarka ta cigaba da rayuwa kanason matar ka kana son mahaifiyar ka kanason kaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar kowa?
daga masa kai yayi alamar eh"
sameer yace to idan duk kanason to yazama dole kabamu bayanansa da address din unguwar da yake da kuma gidan da yake zaune inbahaka ba kuma wlh duk saina aikata abun da duk kaji dan saina tarwatsa farin cikin ka na tarwatsa rayuwar ƴarka?
"cike da dakiya duk da yanajin dan tsoro azuciyar sa amma yadake sannan ya kwace jikin sa daga rikon da yayi masa sannan yace kayi musu duk abun da kaga dama Allah yana tare dasu baka ida kayi musu abun da Allah baiyi musuba Allah yana tare damu tunda na riga bahaya maka abun da kake buƙata bayan nan kuma bansan komai zan ƙara gaya maka ba dan haka duk abun da ka yankewa ranka kawai ka aikata Allah ne shaidata nibansan komai ba,
shiru yayi yana