Sarki Sameer 2 Wasa Farin Girki By Yaya Azeema

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   61 / 74

180K to 183K   out of 221K words

ya riƙe hannun ta yafarajanta tana ta kuka tana cewa ta saketa tana kiran aunty Rasheeda sai turjewa take tana jan hannun ta amma ko gizau ɗin alamun zai saketa baiyi ba har suka fice daga gurin bata daina kukan ba tana juyawa baya tana waiwayon gurin,

saida sukaje wajen motar sannan ya sake ta ummy ce tayi saurin fitowa daga motar ta kama hannun ta tana kallon meer tace me yafaru da ita badai dukanta kayi ba daga shiga kiranka sai yarinya ta fito da kuka me kayi mata shiru yayi yana huci tare da kawar da kansa gefe baida biyar bata amsa kenan,

maida dubanta tayi ga Ameesha sannan tace ƴata me yafaru me yayi miki itama kasa bata amsa tayi saboda kukan da take,

ganin duk basu da niyara bada amsa tasa ummy ta shigar da ita motar tace sai kazo mutafi kazo ka shanya mutane mun kai wajen 30 minutes muna zaune muna jiran ka saboda ka raina mutane kuma kafito anayi maka magana ka saka yarinya kuka kuma kayi shiru kaƙi magana ta ƙarasa maganar cike da ta ƙaicin abun da yayi sannan ta shiga itama,

maama dake jinsu tayi shiru abayan mota ta ɗanyi murmushi sannan tace banda abunki tunda kika gansu haka ai ba lfy sai kibari muƙara sa sannan kowa yafara saukowa sai muji me yafaru ko kiyi masa uzuri muƙara sa,

kallon ta Ummy tayi tace Allah maama yaron ne ya iya abun haushi kafito da yarinya tana kuka kuma anyi masa magana yamaida mutane ƴan iska wallahi bana son wannan halayyar tasa da kullum gaba take mutum kullum sai baƙar zuciya da baƙin hali,

Murmushi dai maama ta ƙara yimata batace mata komai ba,

Abu ma da ransa ya ɓaci ya ɗan ɗaga murya yace ba magana ake maka bane in kuma baza katafi ba bani key ɗin ni sai inyi driving ɗin tunda kai ba a isa dakai ba idan kaga dama ka dawwama anan gurin atsaye har ranar da zaka mutu dan iskanci da wulaƙanci daga cewa bari ka shiga ka fito shine ka shiga kayi zaman ka ai da kasani baka fito ba kai zamanka acan shima dai faɗa ya rufe sa da shi, ashe duk wannan tsawon loƙacin da ya ɗauka aciki yana lugudar su Rasheeda suna nan suna jiran sa,

duk da faɗan da abu yayi masa amma ba aloƙacin ya shiga ba saida ya ƙara ɓata loƙaci yana tunanin su Rasheeda ji yake kamar ya koma ya cigaba da dukan su har sai yaga sundaina motsawa sannan ya rabu dasu dan gani yake su suka ƙara sakawa akayi masa faɗa yanzu abundai biyu ne ya haɗar masa ga ɓata masa ran da sukayi ga kuma faɗan Abu da ummy cike da ɓacin rai sai huci yake fitar wa kamar dafaffan abinci da ƙarfi yaja murfin motar kamar zai ɓallesa haka yajawo sa ya buɗe sannan ya shiga fuskar nan tasa tamau babu ɗigon annuri akanta idon sa har ƙanƙancewa suke saboda tsabar baƙin cikin da yake cin zuciyar sa gashi sai ta farfasa take,

yana tayar da motar yaja wani mugun reavers aguje ya kwashi motar kamar zai tashi sama haka gafara janta tunkan ya hau kan titin ma,

maama na ganin haka tayi saurin cewa ɗan gwaggo ina da magana ɗan tsayar da motar minti ɗaya baiji abun da tace ba yana shirin hawa titi abu yadaka masa tsawa tare da cewa ba magana ake maka ba wallahi idan baka shiga hankalin ka ba sai nayi maganin ka agunnan,

burkin ma da ƙarfi yataka sa duk saida sukayi gaba suka dawo Allah ma ya tsare babu wanda ya bugu,

cike da masifa Abu ya sauko zai sauke masa maama tayi saurin dakatar dashi tace yi shiru kar kace komai banni dashi badan Abu yaso ba ya rabu dashi amma shima zuciyar tasa akusa take yakaisa ƙarshe,

shiru motar ta ɗauka kowa yayi shiru dan Ameesha dake kuka dataga abun yafi ƙarfin tayi saurin yin shiru,

maama duk wannan halayyar tasu da suke babu abun da yabata haushi hakan ma da sukeyi ita daɗi yake mata tayi musu hakane dan aɗan samu loƙaci kowa zuciyar sa ta ɗan lafa,

bayan kamar minti goma duk suna jiran suji ta bakin amma tayi shiru,

saidaga bisani ta kalli ummy tace "kin iya tuƙi ko?

ummy ta kalle ta sannan tace "eh,

Maama tace "zakiya mayar damu gida,

ummy ta girgiza kai tace gaskiya maama ba lalle ba saboda bansan kan hanya ba ga kuma dare yayi ki barshi yakaimu kawai sai yatafi ahankali bari inyi masa magana,

maama tace "a'a rabu dashi ai ko kinyi masa bazai taɓa yin yanda akeso ba adai wannan halin da yake ciki kuma idan yayi tuƙin nan komai ma zai iya faruwa dan haka kiyi haƙuri kiyi sai in ringa nuna maki inda zaki bi,

ummy tace to maama tafaɗa tana niyar buɗe motar Abu yace "maama kawai dan ransa ya ɓaci kuma sai aringa rabuwa dashi waye ba ayi masa laifi kuma ka gansa nml idan rai yaɓaci hankali ai ba ya gushewa idan shi mahaukaci ne yayi tuƙin da zai kashemu kowama sai huta tunda shikaɗai Allah yayiwa zuciya,

maama tayi murmushi sosai sannan tace bashi kaɗai bane hardakai kaima ai kana da ita shiyasa bance kayi driving ɗin ba saboda kaima ranka yanzu aɓace yake koda ka karɓa kai kanka bazaka iya yin driving ɗin cikin hayyacin kaba shiyasa nace ita tayi dan haka nagama yankewa kar wanda yaƙara magana, babana ɗan albarka dawo kusa dani kagaya min damuwar ka kaji tafaɗa tare da dafa kafaɗar meer,

ganin ko motsawa baiyiba yasa ta fito daga cikin motar ta zagayo wajen sa sannan ta buɗe masa ƙofar ta kamo hannun sa bai musa mataba ya fito daga ciki basu shiga tace to fito kishiga fitowa ummy tayi ta koma driver seat sannan maama tace Ameesha ta shige ciki matsawa tayi sai ta fara saka meer aciki sannan itama ta shiga yazamana shine a tsakiyar maama da Ameesha,

tayar da motar ummy tayi tafara tuƙawa ahankali har suka hau kan titi suka fara tafiya cike da nutsuwa takeyi ba gudu kuma baiyi slow da yawa ba, Abu ne dake gaba yafara kwatan ta mata inda zatabi...,

maama ce ta jawo meer ta kwantar da kansa akan kafaɗar ta tace ɗan albarka waye ya taɓa min kai nasan wannan fushin naka ba abanza ba da kwai ƙwaƙƙwaran dalili ko har yanzu zuciyar bata fara sanyi ba,

shiru yayi baice da ita komai,

ganin hakan yasa ta ɗago da kansa tana kallon fuskar sa idon sa har yanzu yana nan ajansa bai raguba hakan da tagani kuma ya tabbatar mata da bazata taɓa samun amsa yanzu ba daga gare sa dan haka sai kawai tace kwanta anan ta nuna masa kan cinyar ta ko kunya baiji ba ƙato dashi ya kwantawa ƴar tsohuwa akan cinya,

Ameesha bata san loƙacin da bakin ta ya suɓice ba tace kai  babba ne fa tana faɗa kuma tayi sauri tasa hannu ta toshe bakin ta,

dariya maama tayi tana kallon ta tace to ina ruwanki da girman sa bama son sa ido, tana gama faɗa mata haka tasa hannu tana shafa masa kai tana cewa idan bai kwanta ba waye zai kwanta kinga ke kina da daddar ki ni kuma ga nawa shalelen nafi ji dashi akan kowa duk wanda ya taɓasa ma sai inda ƙarfina ya ƙare,

ummy dake tuƙi tace wallahi maama wannan dakike gani ba ayi masa gwanin ta idan ya tashi rashin mutun cinsa har ke zai haɗa kar ƙiƙara lalata sa yaci gaba da abun da yake ya lafiyar kura bare ta ƴaƴan ta,

Maama tace au ashe ƴan baƙin cikin da yawa to kwa ƙwalelan ku cinya ce ya kwanta saidai ɗan baƙin ciki ya mutu,

Ameesha tayi dariya tace tabb wallahi abun ma ko kyan gani ma babu dan Allah maama kice ya tashi,

duk abun da suke yana jin su bai tankawa kowa ba saida yaji abun da Ameesha tace sannan ya girgiza kai tare da ɗaga ƙafafuwan sa gaba ɗaya biyun ya saukesu akan cinyar ta itama tare da matseta da jikin kujera yanda zaiyi blance ya miƙar da ƙafarsa,

Wayyo maama kinyi masa magana wallahi da nauyi ƙafata zata karye daman kuma zafi take mun tayi maganar cike da shagwaɓa kamar zatayi kuka,

dariya sosai maama tayi mata tace "haka yake so yaji sa daman idan yabar ƙafar sa aƙasa bazaiji daɗin kwanciyar ba amma kinga idan yayi haka sai yafi jin daidai,

miƙa hannu tayi ta ƙara gyara masa ƙafafun ya miƙar dasu da kyau sannan taci gaba da shafa masa gashin kansa tana ɗan bubbuga wa tace maza kayi yanda kake so a inda kake so kaji daɗi babban jikana, tayi maganar tana satan kallon Ameesha dan taji me zatace tana ɗan murmusawa,

hawaye Ameesha tafara zubarawa tace wallahi da nasan hakane da ban biyo kiba kinsa haka zaki min kika rabani da dadda ta,

to ko asaukeki koma maama tace da ita,

goge hawayen tayi tana haɗe rai tana turo baki tace "nidai wallahi kice masa ya ɗaga ni ƙafara zafi zata karye,

maama tace baki da baki bagaki gashi ba ke kigaya masa mana,

turo baki ta ƙara yi tace "ni ba ruwana dashi bazan ƙara yi masa magana ba mugu ne ba abun da ya iya sai cin zalin mutane yanzu mafa wasu mata yakama aciki ya ringa dukan su yanzu hakama suna can akwance wataƙil ma wasu sun mutu kuma daga cikin su harda Aunty na nasan babu abun da sukayi mishi saboda mugunta da fin ƙarfi nima dannaje na bashi haƙuri shine yakama ya haɗa dani daga cewa yayi haƙuri yazo ummy na kiransa ya dawo kaina taƙarasa maganar tare da wurga masa harara ta ƙasan ido harda murguɗa masa baki hda ɗan tsaki ƙasa ƙasa yanda tasan bazaiji ba,

maama tace au abun naki kuma yanzu harda sharri to nidai ko jikina duka kunnuwa ne bazan yarda ba,

ummy ce tayi saurin cewa inna lillahi hayatee daman baka daina dukan mata ba wlh maama da gaske ne haka kwanaki yayiwa wata yarinya wai kawai dan ta shiga office ɗin sa shine bakiga irin dukan da yayi mata harda su cire mata kaya saboda tsabar iya shege irin nasa da rashin haƙuri,

maama tace kofa me zakuce saidai kuce amma bazan goyi bayan kuba duk abun da yayi yayi daidai wallahi sai kace mahaukaci hakan nan zai gansu ahanya yakama duka sai kace taɓaɓɓe duk halin sa nasan bazai taɓa yin haka duk yanda akayi su suka jawowa kansu suka shiga harkar sa bana raba ɗayan biyu ma ko irin ƴan iskan matannanne suka gwada masa halinsu shikuma ya koya musu hankali gwanda da yayi maganin su wallahi,

ɗan gidan gwaggo ƴan iska ne ko tayi maganar tana leƙan fuskar sa kai ya ɗaga mata alamar "eh,

yauwa nidai nasani da dalili to wallahi ina bayan ka kamar doro kacigaba da yanda kakeyi duk ƴar iskar da ta kawo ma wurgi kaci uban ta ka koya mata hankali kai ko alama ma kagani ka saita mata tunanin ta daga kanka bazasu ƙara ba,

Tabb gaskiya maama baza kuringa zama guri ɗaya ba duk yanda zanyi inga baku zauna guri ɗaya ba zanyi tundadai ke zigashi zaki ringa yi ba ƙya ganin laifin sa idan yaga haka ai cigaba dayi zaiyi maimakon ki hanasa amma sai kifara taya ɓera ɓari to wallahi da sake,

maama tace "aikwa dai ba yanda zakiyi nidashi mutu karaba ke nan gabama ɗaki ɗaya zamu ringa kwana kuma duk inda zashi tare zamuje duk wanda yayi mana ba daidai ba kuma mu haɗu mucimar uwa zanma ƙara gayyato mana gwaggo tafiyar sai tafi daɗi, duk wanda yashiga sabgar mu sai ya gane bashi da wayo ko ɗan gidan gwaggo yanzu ma saida ta leƙa fuskar sa kuma tasamu haɗin kansa yanzu harda buɗar baki yace "eh,

tace "yauwa ɗan gari na gidan gwaggo bani biyar inbaka goma ta miƙa masa hannu su tafa baisan me take nufi da hakan ba amma ganin ta miƙo hannu sa yagane nufin ta dan haka sai kawai ya ɗago hannun sa suka tafa hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba daman haka take so yafara sakin jikin sa shiyasa take yin haka tana goyen bayansa dan ta jawo hankalin sa zuciyar sa tayi sanyi kuma taga alama tasan zuciyar sa yanzu tafara dawowa normal,

itadai Ameesha shiru tayi saboda haushi da taƙaicin su gaba ɗayan su haushi suka bata dataga bata ita suke ba suna ta surutun sa ta ɗan saci kallon tare da hararar sa ta janye idon ta tana kallon ƙafar sa tana ayyana abun da zatai masa ta rama kafin asauka gashi har anshigo layin gidan sun kusan ƙarasawa,

sarai yaganta loƙacin da ta harare sa rabuwa yayi da ita kawai dan tara ta yake duk abun da tayi masa,

tana cikin kalla tana wani abu ya faɗo mata rai karkaɗa kai tayi harda cije baki da ta ɗaga kai taga har sunzo me gadi ya buɗe musu gate sun shiga sai kawai ta tsugunna kamar zata ɗauko abu aƙasa sai kawai ta saisaita daidai wajen ya tsan sa tasaka abaki ta gasa masa cizo awajen, bazato ba tsammani yaji azaba baisan loƙacin da yasaki wani ɗan ƙaramin ihu ba da sauri ya janye ƙafar tare da miƙewa zaune ya riƙe ƙafar yana kalla,

fashewa da dariya Ameesha tayi sosai ta shiga yin dariya harda riƙe ciki bata taɓa tunani zaiji zafin cizon ba wai sai gashi harda ihu idan ta kalle sa taga yanda yake zaro ido yana kallon ƙafar sai ta sake fashewa da dariya,

Maama dai da take goyen bayan sa saida tasaka masa dariya tunda komai agaban idon ta akayi komai taga abun da Ameesha tayi masa dan haka itama saida ta dara sosai,

ummy tana gama daidaita parking ɗin jin dariyar su tayi yawa ta juya tana tambayar dariyar ne akeyi duk sun kasa bata amsa sai dariya suke,

wani abune yaso masa wuya ya tokare masa a wuya na taƙaici ga tayi masa laifi kuma tazo tana masa dariya hannu ya ɗaga zai maketa maama ta riƙe hannun sa da sauri tana so tayi masa magana amma dariya ta hanata,

Abu ne yafito kuma yana fitowa yayi wucewar sa bai tsaya wajen su ba dan har yanzu bai dawo daidai ba cike yake da haushin Meer,

ita kuma Ameesha gani hakan yasa tayi sauri ta buɗe motar ta fita saida ta fita ta ƙara kwashewa da dariya ta zagaya wajen ummy da ta fito daga ciki itama ta maƙale abayan ta,

ummy tace ke kikayi masa laifi kenan to matsa daga bayana ke dashi ummy wallahi rama abun da yayi nayi ɗora min ƙafa fa yayi kuma nace da zafi ya ɗaga min yaƙi nikuma da na gaji shine na cijeshi,

ummy tace kinyi daidai kam gwanda da kika rama amma da ba ruwa na idan bai haƙuraba zan riƙeki ya rama tunda shi ba cizon ki yayi ba,

kai ummy kema goyon bayan sa zakiyi kenan shikenan tafaɗa tana matsawa daga kusa da ita da sauri ummy ta riƙota tana dariya tace da wasa nake miki zo mutafi murigasa shiga,

suna juyawa zasu tafi maama da shi suka fito tare yana ta jan hannun sa tasake shi amma taƙi sakin sa saida suka fito har sun fara tafiya sai maama ta sakeshi dan taga me zaiyi tana sakin sa kwa da sauri yayi wajen su Ameesha,

daman Ameesha tana tafiya tana juyowa ganin ya taho wajen ta da sauri yasa taja hannun ta zata gudu ummy ta riƙeta ƙam tace zo gata na riƙema ita,

wayyo ummy dan Allah kisake ni wallahi dukana zaiyi mugune fa shi dan Allah kisake ni saura kiris ta fashe da kuka,

yana daf da ƙarasawa kusa dasu sai ummy tasake ta tare da shan gaban meer tana dariya itama,

Ameesha tunda taji ansake ta bata ƙara tsayiwar rabin second ba ta kwasa aguje tayi cikin gidan saida taje bakin ƙofar dakin sannna ta tsaya ta juyo tana kallon su tana dariya harda ɗaga masa hannu tace aidai baka kamani ba tana faɗa ta kuma shigewa ciki ɗakin da ummy ta kaita da safe nan ta shige tare da sakawa ɗakin key,

cike da ɓacin rai ya kalli ummy yace "ummy kinga fa abun da take min ta rainani ta maidani ma abokin wasan kenan ni sa'an tane da zata ringa min irin waɗannan abubuwan wallahi na kamata sai karya nata ƙafa har ni zata ciza saboda ita mayya ce to wallahi sai tasan wanda ta ciza yafaɗa yana bin ta gefen Ummu ya nufi cikin gidan shima,

da kallo suka bishi ita da maama da ƙarasowa ta gurin kenan,

ummy tace "maama wannan faɗan nakine sai kisan yanda zaki rabashi tunda daman ke kika haɗa abunki sai kiraba,

maama tace "zan kwa raba muje kedai kiga ai nasan bazata zauna a falo ba ayau dai ba yanda zaiyi da ita saidai kuma yabarwa gobe dan bazanma bari su haɗu ba,

ahaka suka ƙarasa cikin falon suka gama ba kowa aciki shi har ga hau sama ɗakunan ƙasa suka fara dubawa har suka gano inda take ciki maama tace to buɗe mune ta can ɗakin Ameesha tace Allah bazan buɗe ba sai gobe ina nan so kike in fito ku haɗu kuyi min duka ko to bazan fito ba duk yanda suka so ta buɗe ƙin buɗewa tayi dole suka rabu da ita ummy ta wuce ɗakin ta gurin Abu,

ita kuma maama Saida ta ƙara zuwa gurin meer ta lallaɓa sa har saida yayi sallah agaban ta yagama duk abun da zaiyi ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin itama ta tafi nata bayan tayi wanka tayi sallah da addu'o'i sannan ta kwanta itama,


***************************

*Rasheeda*

da taimakon securities ɗin wajen aka taimaka suka shiga motar su amma babu wanda zai iya jan motar acikin su wanine daga cikin su yajasu yakai su har gidan su Rasheeda,

bayan ya shigar dasu ciki da ƙyar duk suke iya takawa suka fito suka nufi cikin gidan suna shiga suka tadda su momy a falon suna zaune suna jiran dawowar su harda mom ɗin Rasheeda itama tana falon,

gaba ɗayan su miƙe sukayi tsaye mom tayi saurin kamo Rasheeda cike da tashin hankali ta shiga tambayar ta abun dake faruwa taga shatin duka ajikin ta

61 / 74