AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   99 / 213

294K to 297K   out of 636.6K words

Sai jacket da itama ta kasance brawn color a hannunsa ya saƙale batare daya saka ba. Sosai fuskarsa data sha gyara gashin sajensa ya kwanta luff-luff ke'a ɗaure, kamar ko yaushe idanunsa manne da sirrin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata shi. Tafiya yake ɗai-ɗai a kuma nutse cike da ƙasaita yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa takalmansa masu matuƙar ƙyawu sau ciki na bada ƙarar sauti kaɗan-kaɗan.
       Sosai Nuratu ta shagaltu da kallonsa, ji take kamar ta haɗiyesa ta huta. Dan daya ɗan gittata zuwa gaban Mamy mayataccen ƙamshinsa ya daki hancinta jitai illahirin jikinta na rawa. AA da bai san ma tana yi ba dan shi ko lura da ita baiyi ba a wajen ya ɗan zubama Mamy ido kafin ya risinar cike da girmamawa ya furta, “Zamu wuce Mamy”.
        Ƙin yarda Mamyn tai ta kallesa, kasancewar su Oum a wajen kuma yasa tai masa addu'a cike da nuna rashin kulawa kamar yanda take musu. Muryarsa a sauƙaƙe ya furta, “Thanks you” a hankali. Sai kuma ya matsa gaban Abah. Murmushi Abah yay masa, tare da ɗaura hannunsa a kafaɗarsa. Sai kuma ya matsar da bakinsa kusa da kunnen AA ɗin ƙasa-ƙasa ya furta, “A rufan asiri a dawo min da yarinyata lafiya Oum's boy, kaga dai gudun rigimar uwar taka yasa na baka salin-alin”.
        Idanu AA ya lumshe tare da sakin guntun murmushi kansa a duƙe. Batare da ya yarda ya kalla Aban ba ya gyaɗa masa kai, muryarsa a sanyaye yace, “In sha ALLAHU Abah zan cika alƙawari”.
    “ALLAH yay muku albarka”.
Abah ya faɗa yana murmushi da ɗan bubbuga kafaɗar tasa. Gaban Oum AA ya ƙarasa..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣7️⃣


______________


........Gaban Oum AA ya ƙarasa, Maanal na gefenta sanye cikin Abaya red color datai mata matuƙar ƙyau, tai rolling kanta da mayafin, sai mitsitsiyar handbag a hannunta. Suna haɗa ido ta kauda nata, shima nashin ya maida akan Oum, cike da kulawa ya rungumeta, “Oumna zan yi missing ɗinki”.
         Ya faɗa cikin maƙoshi. Murmushi Oum tayi, tare da ɗan bubbuga bayansa. Sai kuma ta ɗagoshi cike da kulawa fiskarta da murmushi ta shafa fuskarsa. “Nima haka Auta, amma karka damu kamar yau ne ai zaku dawo. Ga Baby na nan zata kula min da kai”. Tai maganar tana juyawa ta kamo hannun Maanal. A cikin nashi ta sanya, a tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya kuwa. Sai dai a zahiri kowa a dake yake, dan Maanal ma kanta a aƙasa yake, shine ma dai ke kallonta ƙasa-ƙasa. Addu'a sosai Oum tai musu, tare da damƙa ma junansu amanar kansu. Daga haka tace suje lokaci na ƙurewa. Gashi jirginsu 5:20 zai tashi.
       Sai yanzu ne Saheeba ta buɗe baki da ƙyar tai musu addu'ar dawowa lafiya, hakan ne ya zaburar da Nuratu, itama ta ce, “Ya AA ALLAH ya tsare”.
     Hannu kawai ya ɗaga musu, tare da kai ɗayan hannunsa ya amshi trolling ɗinsu da Maanal ta kama zata ja. Ɗan ɗagowa tai ta kallesa, suna haɗa ido ta janye tare da sakar masa akwatin. Shima bai ce komai ba ya turashi yay gaba, ita ko Maanal sai da ta sake rungume Oum sannan ta wuce idannunta cike da hawaye. Ji take kamar zasuyi tafiya ne mai jimawa.
       Da sauri AS ya zaburo ya amshi akwatin hannun AA ɗin domin sakawa a booth dake buɗe. Shi ko jikin motar ya nufa ya tsaya har Maanal ta iso, ganinsa tsaye ya sata fahimtar ita yake jira ta shiga. Dan haka ta nufi shigar, hannu yasa ya tare mata saman kai dan karta buge, sai kuma akai rashin sa'a abayarta ta nema taɗeta. Riƙota yay da hannunsa ɗaya bayanta ya jinginu da jikinsa. Muryarsa a ƙasan maƙoshi can ƙasa sosai ya ce, “Are you okay?”.
    Kanta ta jinjina masa tana ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta matsa daga jikinsa ganin su Oum duk suna kallonsu har tana iya hango yanda fuskar Mamy, Nuratu da Saheeba ta canja, shiga tayi sai dai tana ɗan yamutsa fuska dan ƙafarta na ɗan mata zafi. Lurar da AA yayi saboda idonsa a kanta yake ya sashi kaiwa tsugunne irin na yanayin maza ya ɗaga Abayar kaɗan ya kamo ƙafar dake a cikin ƙyaƙyƙyawan baƙin takalmi fes-fes da ita. Takalmin ya zare ya ajiye, batare da damuwa ba ya ɗaura ƙafar a saman jikinsa. Ji Maanal tai kamar tayi kuka dan nauyin Abah da Oum. Amma yaya zatai tunda tasan ba fasawa zai yi ba. Duk da haka sai da tai magana a sanyaye ta ce, “Bafa da yawa bane”.
     Bai kulata ba, sai ƙoƙarin ɗan jajjan ƙafar kawai yake yi, sai da yay kusan na minti biyu sannan ya maida mata takalmin ya gyara mata ƙafar a cikin motar tare da rigarta ya miƙe. Da kansa ya rufe mata murfin sannan ya juya ya kalla su Oum dake kallonsu cike da jin daɗi, sai dai banda su Mamy. Dan ji tai wani irin ƙududu ya riƙe mata zuciya katamaumau. Nuratu kam ƙwalla ne suka cika mata ido ma. Hannu ya sake ɗaga ma iyayen nasa sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da AS ya buɗe masa ya shiga ya zauna. Suma su AS sukai sallama da su Oum ɗin suka shiga motar ta fice.

     Sannu a hankali Maanal ta lumshe idanunta da hawaye suka ciko. Jin suna neman zubo mata ta buɗesu tare da kai yatsarta ta ɗauke su tana kallon waje. Sarai AA na hankalce da ita, dan haka ya kai tattausan hannunsa ya kamo nata dake ajiye a kan cinyarta, saman tashi ƙafar ya dawo dashi yana mai harɗe yatsunsu waje guda. Ta gefen ido ta ɗan dubesa, ganin ba ita yake kallo ba ta shagala sosai a kallon nashi, dan harga ALLAH idan tace bai yi mata ƙyau ba ma tayi ƙarya. Ta shagala sosai a bazata ya waiwayo suka haɗa ido, cike da borin kunya ta kauda nata gefe tana ɓata fuska. Shi dai baice mata komai ba, kuma bai daina kallon nata ba har sai da wayarsa ta motsa alamar shigowar kira. Ɗauka yay ya duba, babban yaya ne. Dan haka ya ɗaga tare da kai yatsansa ya gyara zaman bluetooth ɗin kunnesa baƙi, cikin yanayinsa na rashin son ɗaga sauti yay sallama... Tsabar yanda yake magana can ƙasa su kansu su AS dake a gaba ba jinsa suke ba. Ita kanta Maanal dan kawai ta nutsu ne ta maida hankali a kansa duk da ba kallonsa take ba. A haka suka iso airport dan gudu sosai sukayi.
     Bai motsa domin fita ba, ita kuma ya riƙe hannunta bai bata damar ta fitan ba. Magana suke da AS. Ita Maanal ma tayi zaton bada shi za'a ba. Sunja kusan mintuna biyu a haka sannan aka buɗe musu. Juyawa yay ya ɗan kalleta, kafin ya saki yatsun hannunta dake sarƙale da nashi a hankali sannan ya yunƙura ya fita yanzu ma jacket ɗinsa da bai saka ba har yanzu a hannu. Itama ɗin fitar tayi, dai-dai driver na rufe side ɗin data fito ɗin AA ke isowa wajenta. Yayinda AS daya fiddo akwatinsu da wani da bata san na waye ba ya tura su yay gaba. Shi kuma da yake binta da wani kallon ƙasa-ƙasa hannunsa ya miƙa mata. Hannun ta zubama ido, sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ita ɗin dai yake kallo idanunsa na komawa ƙanana. Yau dai ta fahimci kurumtar ce ta motsa ta miskilanci, dan haka ta ɗaura hannun nata a hankali saman nashi, shiko ya haɗesu da ƙyau sannan suka fara takawa a tare.
      Dole duk wanda ya kallesu su burgesa, dan kallo guda zai tabbatar maka da su ɗin ma'aurata ne. Sun matuƙar dacewa da juna kuma, duk da ita ɗin ƴar ƙarama ce a gabansa, dan koda take da tsaho tsahon nata gaba ɗaya bai wuce kafaɗarsa ba. Arba da ma'aikatansu su Yaqub ya sakata jin nauyi da kasancewar a yanda suke. Shi ko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma amsa musu gaisuwar da suke masa yake ta hannyar jinjina kai. Itace ke amsawa cike da jin nauyin da su kuma suke fassarawa da jan ajinta. Dai-dai nan kuma aka fara shelar neman matafiyan da zasu tashi a jirginsu zuwa Qatar. Gaba yay riƙe da hannun nata su AS da su Yaqub da yaƙi yarda ya kalla ko inda Maanal take biye da su. Sai da sukai ƴan abubuwan da suka kamata kafin wucewa inda jirginsu yake. A haka yana riƙen da ita suka shiga, su sun wuce vip ne.
       Ganin hakan sai da yasa Maanal sauke ajiyar zuciya a ɓoye. Duk da ya jita bai nuna yaji ba, sai ma taimaka mata da yaya ta zauna a nata sit ɗin kafin shima ya zauna a nasa dake kusa da ita. Ta inda suken keɓantaccen waje ne madaidaici zaman mutum biyu tamkar wani falo ko ɗan ɗaki, zaka iya maida kujerun gado idan kaso. Ga television da kayan dai ƙawa yanda ya kamata. Tuni Maanal ta zama baƙauya, dan ita kam bata san akwai hakan a jirgi ba. Kai masu kuɗu na sha'aninsu. Bata tsinke da al'amarin ba sai da AA ya danna wani ɗan bottom ta gefen kujerar belt ya saka kansa da kansa a jikinsu. Dai-dai jirgin na tashi zuwa sama dole ta lalubo hannunsa a cikin nata. Kallonta yayi, sai kuma ya buɗe tafin nasa ya maida natan a ciki ya sargafe yatsunsu cikin na juna. Sosai ta sake ƙanƙame masa hannun har tana kafa masa ƙubunanta da ba wani tsahone da su ba dan bata wasa da yankewa a kan fatarsa. Aiko sai da ta fasa masa fata abinka da ba'asan wahala ba. Bata fargaba kuma sai da jirgin ya gama dai-daita ta buɗe idanun, hannun nasu ta ɗan kalla tana sauke ajiyar zuciya, har zata janye sai kuma tai saurin sake kallo. Sosai taji gabanta ya faɗi, babu shiri ta juyo da shi ganin yana ƙoƙarin juyarwa dan karta gani. A sanyaye cike da damuwa ta ce, “Ya ALLAH na ji maka ciwo”.
     Komai bai ce ba, ya dai ɗan kalli hannun ya kauda kansa. Yayinda ita kuma ta buɗe yatsun nata tana matso da hannun saitin bakinta ta shiga wura masa iska da baki kamar wanda ya kone. Ai ba ƙaramin ratsa jijiya da jinin AA hura hannun nan yay ba, a take ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Dole yay ƙoƙarin janyewa yana faɗin, “It's okay”.
         Kanta ta jinjina masa idannunta na cika da ƙwalla, sai kuma taja tissue ɗaya dake ajiye a kwalinsa ta shiga goge jinin daba wani zuba yake ba ya dai nuna alamar fita ne kawai. Dai-dai nan ma'aijaciyar jirgin ta shigo bayan tai ɗan knocking, tray ɗin hannunta mai ɗauke da coffee ta ajiye, sai kuma ta dubesu domin jin ko suna buƙatar wani abu ne. Cikin harshen turanci Maanal tace suna buƙatar First aid box.
         “No...”
    AA ya faɗa yana ƙoƙarin dakatar da ita, amma sai maanal ɗin tace taje ta kawo. Itama ganin jinin yasata fita, babu jimawa ta dawo da wata matashiya kamarta da first aid ket ɗin a hannu. Kai tsaye inda suke tayo, ta ajiye box ɗin tana ma AA sorry. Shi ko kallonsu ma baiyi ba. Maanal ɗin da duk ta rikice kawai yake kallo ƙasa-ƙasa. Mata ta kawo hannu zata kama hannunsa Maanal tai mata tsawa batare da ita kanta tasan mi tayin ba. Cike da masifa tace ta bata zata masa. Karo na farko AA yay wani ɗin killer smile na gefen baki ya lumshe idanunsa kawai. Sai dai yana kallon yanda take goge masa jinin a ɗofane tana kuma hurawa da baki wai kar yaji zafin spirit. Sai yaji kawai abin ya masa suger. Ƙoƙarin tsokanarta yay, dan haka ya ɗan ja hannun baya kamar wanda yaji zafin.
     Ai da sauri Maanal ta kallesa a raunane ta ce, “Da zafi ko, I'm sorry”. Yanda tayi kamar zatai kuka yasa shi ƙara girman idanun nasa a kanta yana kallonta ciki-ciki. Kansa ya girgiza mata ganin yanda ta zuba masa idanun dake tara ƙwalla. Kan nasa ya girgiza mata kaɗan, sai kuma ya juya nasa hannun nata ya koma sama, ya matso da shi tare da ɗan duƙowa ya sumbata. A hankali ta lumshe nata idanun tare da jan ajiyar zuciya.
      Su dai ma'aikatan jirgi sun shagala suna kallon ikon rabbu, wannan al'amari kamar a film, dama a baƙaƙenmu akwai masu irin wannan shagaltacciyar ƙaunar, dan wannan ta wuce soyayya sai tsantsar ƙauna mai zafin gaske da sam bata ɓoyuwa a idanun masoyan. Da ƙyar ɗaya tai ƙarfin halin miƙama Manaal plaster ɗin data yanko tare da ƴar audiga. Maanal ɗin ta amsa ta sanya masa sannan tasa plaster ɗin a sama. Tattarwa sukai suka wuce suna waigensu..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣8️⃣


______________


.......Matuƙar saka rayuwar Huznah gaba Sageer yayi a wannan tsakanin da buƙatunsa. Tabi kowacce irin hanya na bijirewa amma ya nuna mata namiji yake. Sai dai taci kukanta da zaginsa a zuciya dan tsoronsa ALLAH ya dasa mata. Ko fita yay da zarar taji motsin dawowarsa zuciyarta ke fara dukan uku-uku. Gashi yanzu ya hana kowa shigowa gidan dan kullesu yake ta ciki, mutum ya ƙaraci bugunsa dole ya haƙura. Wayarta ya amshe ya kashe tun ranar da sukai waya da Hajiya Basariyya. Girki kam tunda tayi sau ɗaya ta ƙwaɓa musu hauka ya koma yi da kansa. A rana ta uku yasata shiga kitchen ɗin ya fara koya mata. Dan ya tabbatar mata yana da mata bazai dinga zuwa gidansu cin abinci ko saye ba. Idan zata zage ta zage babu abinda za'a fasa. Tako tabbatar da babu abinda za'a fasa ɗin kuwa. Dan tako ina baya raga mata yanzu. Hatta da gyaran gidan tsaye yake mata akai sai tayi komai yanda yake so.
         Sau biyu tana satar wayarsa ta gwada kiran Hajiya Basariyya sai taji tata wayar a kashe itama. Ba ƙaramin tashi hankalinta yay ba da rashin jin uwar tata. Shiko sarai yana sane da ita, abinda bata sani ba yaji komai akan abinda ya faru da Hajiya Basariyyar a kwanakin nan Daddynsu na faɗa ma Babanshi saboda haƙurin daya bashi akan ya barsu su koma ɗakinsu suyi azumi. Shine yake sanar masa abinda Hajiya Basariyya ta aikata, da idonsa ya ganta shi da ƴaƴanta a wani ƙauye bin malamai, su kuma sunje cinikin gona ne a kusa da ƙauyen. Amma yay masa alƙawarin maida Hajiya Yaya idan tayi azumi koda goma ne a gidansu.
        Sosai Huznah tai ramar dole a wannan gaɓar, ga shi kota kulle ƙofar ɗakin ma yanzu a banza ama wofi zai buɗe da wani key ɗin ne. Gida kuma in zai fita ta baya yake kulleta. Tun tana masa girman kai harta fara tunanin saukewa ta bashi haƙuri kozai taimaka ya bincika mata Umminta, dan tana son sanin wane hali take. Kamar kullum yau ƙarfe biyar ya dawo kasuwa. Tana falo zaune idonta a tv sai dai bata fahimtar komai kallon kawai take yi. Shigowarsa ta sata zabura tana masa sannu da zuwa. Sosai ya zuba mata ido dan mamaki. Amma sai baice komai ba ya gyaɗa mata kai kawai. Kitchen tai saurin nufa, a wani mamakin nasa bata jimaba sai gata ta fito da ruwa ta ajiye gabansa. Badan ruwan leda bane ALLAH sai ya tsargu wani abun mutuwar ta zuba masa. Amma yasan bazai yiwu ba tunda fure water ne....
       “A kawo abinci?”.
Ta faɗa cikin katse masa tunani. Sai ya samu kansa da sakin murmushi. “Kina lafiya kuwa Huznah?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
Iska ya ɗan furzar, sai kuma ya gyaɗa kansa da miƙewa yana faɗin, “Okay bara na watsa ruwa to, kibar abincin sai nayi sallar magrib tukkunna.”
          Murya a ƙasa ta ce, “To”.
   Nan ma sai da ya sake kallonta kafin ya wuce ciki abinsa yana kwasar dariya a zuciyarsa.....

      Ni kaina dai abin ya bani dariyar Man Sageer 🤣😜

_________★

        Gaba ɗaya Oum kewar yaranta take ji, dan ma babban Yaya da Fawzan sun ɗauke mata kewarsu. Nibras ma da farko ta shigo, amma jin hirar da su Fawzan keyi akan tafiyar su AA ɗin saita miƙe tsam kamar ma wadda jikinta ke rawa. Sallama tai musu cikin danne kukan dake neman zuwa mata tace zataje ta kwanta ta gaji. Da kallo kawai Oum ta bita. Hakama babban Yaya da tuni shima ya fahimci take-takenta. Amma a mamakinsu shi Fawzan ɗin da suka ji tausayinsa ya kama su shi hankalinsa ma nakan waya abinsa sai zabga murmushi yake dan charting yake da Najma.
     Sai sukai tunanin ai bai fahimci matar tasa bane saboda sonta ya rufe idonsa. Sai dai abinda basu sani ba Fawzan ya riga kowa fara fahimtar matar tasa da inda haukanta ke ɗawainiya wajen kaita. Ya barta

99 / 213

Chapters