AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   169 / 213

504K to 507K   out of 636.6K words

jajirce akan zuri'arsa kodan su san ƴan uwansa sunada daraja a duniyarsa. Arziƙin da ALLAH yay masa bashi ke nufin ya banbanta da su ba ko ya fisu.
       ALLAH sarki Baban Sageer mutum ne mai sauƙin kai. Sai kawai shi ya gaida Hajiya Basariyya, ya kuma jajanta mata. Hakama iyalinsa duk suka gaisheta. Gaba ɗayansu ta amsa musu ne a ciki. Abin ya sosama Sageer zuciya sosai, dan haka da farko yay kamar bazai gaida Hajiya Basariyya ba sai da mamansa ta hararesa. Aiko cikin dakewa da tsumewa yace mata ina yini daga zaunen da yake. Daddy yay ɗan murmushi, dan shi abinda Sageer ɗin yayi wlhy birgeshi yayi, koba komai ya nuna mata iyayensa masu daraja ne a garesa ai.
      Daga gaisuwar Sageer ɗin kuma sai kowa yay banza da ita aka cigaba da hira cikin nishaɗi harda Hajiya Yaya da Ammie. Sai kuma hakan ya zafeta, fuuu ta tashi ta fice batare data cema kowa komai ba. Suma ɗin babu wanda yabi takanta. Har lokacin sallah yayi mazan suka tafi massallaci matan sukayi anan. Koda suka dawo zaman cin abinci sukayi, ganin kowa yana nan banda yaran Hajiya Basariyya Daddy yace aje a kira masa su har Huznah”.
      Babu jimawa kuwa sai gasu har Huznah ɗin. Yanda suka shigo zai baka tabbacin gudowa sukayi uwarsu bata sani ba. Haka ɗinne kuwa, dan Hajiya Basariyya na bedroom suna tattaunawa da Maman Yaseerah ta waya akan al'amarin Huznah ɗin. Da yake tana shiga ta koro Huznah falo sai itama ta samu tabi ƴan uwanta. Tunda suka shigo idanun kowa akan Huznah ne. Musamman Sageer, dan kallo ɗaya zakai mata kasan tayi kuka. Ji yay duk abin ya damesa, ga kunyar iyaye dole ya dake. Gaban Daddy Huznah ta fara zuwa ta durƙusa tana gaisheshi. Maimakon amsawa sai yay shiru kawai yana kallon ta. Hajiya Yaya data fahimci ransa a ɓace yake sai tai magana.
        “Kinga Huznah tashi daga dirƙuson nan kinji, zauna da ƙyau wannan durƙuson baida amfani a gareki”.
      Kan Huznah a ƙasa tace to, sai kuma ta zame ta zauna sosai ta sake gaida Daddyn. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya amsa mata. Tare da tambayarta lafiyarta. Kanta har yanzu dai a ƙasa tana wasa da yatsunta tace, “Alhamdullah”.
         “Yanzu Huznah daban aika ai kiranku ba bazaki zo ki gaishe ni ba balle sauran iyayenki ko? Maimakon ki ƙara hankali kinyi aure sai ma ki ƙara neman lalacewa. Ni nasan wannan ba tarbiyyar Sageer bace ba, dan ke da shi duk tarbiyyarmu ce”.
      “Kayi haƙuri Daddy. Nayi kuskure”. Huznah tai maganar hawaye na rige-rigen zubo mata. Shiru Daddy yayi tsahon sakanni. Sai kuma ya ɗan furzar da iska kawai ya ce, “Tashi kije ki gaida iyayenki. ALLAH yay muku albarka”.
        “Amin Daddy nagode”.
Ta faɗa tana miƙewa. Gaban Hajiya Yaya da Ammie taje duk ta gaishesu. Suma sauran ƙannenta suka gaida iyayen Sageer. Daga Ammie har Hajiya Yaya sun amsawa Huznah da kulawa sosai, suka sanya mata albarka, tare da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya. Ita dai kanta a ƙasa, damuwar mahaifiyarsu ce ke ci mata zuciya. A mamakin kowa sauran ƴan uwanta na ɗakin Hajiya Yaya duk sai suka nuna murnar ganinta, har manyan na tsokanarta. Suma su Waleed suka gaisheta. Sanyi sosai Huznah taji a ranta, zuciyarta cike da mamakin canjawar abubuwa da yawa na gidan. (Shin kodai ƙaddarar data faru ce ta sanya su komawa haka? Gafa yanda Hajiya Yaya ta canja kamar ba ita ba) abinda take ayyanawa a zuciyarta kenan...
         Sun fara cin abinci cike da raha babu jimawa sai ga Hajiya Basariyya ta faɗo musu rai a ɓace. Da wata irin tsawa ta shiga kiran sunayen yaranta. Kafin ta ɗora da faɗin, “Dan ubanku da iznin wa kuka zo nan?”.
       “Da izinin ubansu”.
   Daddy ya bata amsa kai tsaye. Kafin ma ta sake wata magana ya nuna mata ƙofa. “Ko ki fita anan, ko yanzu nan na baki mamaki irin wanda baki taɓa zato da tsammani ba”.
    Matuƙar ɓaci ran Hajiya Basariyya yayi, sai dai yanda Daddyn yayi da ganin yana neman kunyatata gaban kishiyoyi da ƙanensa da facaloli yasata juyawa ta fita tana ji a ranta yau duk sai taci uban yaranta. Koda ta koma sashenta kai-kawo ta dingayi kafin takai zaune cikin kujera tana faman girgiza ƙafa da kallon ƙofa. Sai dai shiru kake ji babu alamar yaran zasu dawo ma....

      A nan kuwa babu wanda ya sake magana kowa ya maida hankalinsa ne ma a cin abinci. Sai dai banda Huznah da damuwa tai mata yawa. Kasa haƙuri Sageer yayi, dan hankalinsa duk yana akanta. Cikin sanyin murya ya ce, “Baƙya son abincin ne?”.
      Kasancewar bai ambaci suna ba kowa sai ya ɗago musamman yaran, sai dai ganin hankalinsa akan Huznah yake sai suma duk suka juya suna kallonta. Itama a karo na farko ta ɗan ɗago ta kallesa. Sai kuma ya girgiza masa kai muryarta na rawa ta ce, “A'a ina so”.
        “To kici”.
   Ya sake faɗa da kulawa.
Kanta ta jinjina masa. Daddy da sauran iyayen da sukai kamar basu san mi akeyi ba kowa sai ɗan murmushi yake yi. Itama Huznah sai taji sanyi a cikin ranta. Karo na farko taji wani abu mai nauyi a ƙasan zuciyarta game da Sageer.
       Ana gama cin abinci ƴan Kano sukai haramar wucewa. Jin cewar anan zasu bar Huznah Daddy yace a'a. Sageer ya ɗauka matarsa su tafi. Amma sai Baban Sageer ya ce, “A'a baza ai hakaba Yaya. Kayi haƙuri bawai zanyi jayayya da kai bane ba. Yana da ƙyau a barta tai kwana biyu a gida ta gana da ƴan uwanta. Ai tayi ƙoƙari sosai. Bayan salla idan ALLAH ya kaimu sai yazo ya ɗauketa su tafi.”
     Ammie tasan halin Daddy sarai da dagiya, haka ma Hajiya Yaya sai suma suka haɗa baki suna lallashin Daddy ɗin. Dole ba dan yaso ba ya haƙura yay shiru. Shi ko man Sageer nata addu'a a ransa ALLAH yasa kada Daddy ya yarda. Sai dai addu'ar tasa bataci ba. Miƙewa yay ya fita tsakar gida, ya aiko Hameed da suka fita tare yay masa kiran Huznah ɗin. Batayi ko musu ba ta tashi ta fita. Tunda ta fito yake kallonta, harta iso inda yake tsaye a barandar sashen Yazeed. Sanin kowa yana ciki tana isowa gabansa kawai ya jawota ya rungume cikin jikinsa. Ya saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, yayinda Huznah ke mutsu-mutsun kwace kanta duk da tana tsoronsa. Kamar ba Man Sageer ba cikin sanyin murya kamar ɗazun ya ce, “Please mana Sweetheart. Baƙya jin tausayina ne? Kin san fa zanyi kewarki sosai.”
       Yanda yake mata maganar da halin nauyin zuciya da take a ciki yasata jin zata iya haƙure masan. Sunfi mintuna biyu kafin ya saketa. Baya ta ɗan ja kaɗan daga kusa da shi. Yana binta da kallo shi kam. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Mike damunki ne? Nasan dai ba haka muka baro gida ba dake. Kuma har muka shigo cikin gidan nan ma ba haka yanayinki yake ba. Ga fuskarki da sayin mari....”
      Karo na farko ta ɗago ta kallesa, ganin yanda ya tsareta da idanu sosai sai ta sake ɓata fuska ta ɗauke nata. Kansa kawai ya ɗan girgiza, dan tun ɗazun ya gama ji a ransa Mahaifiyarta ce ta mareta, ba kuma ya son yimata shishshigi akan mahaifiyar tata, wani gefen kuma baya son yin ko maganar Basariyya ma a gabanta dan wlhy zai iya danna mata zagi. Ya tsani matar ƙwarai-ƙwarai da gaske. Waya ya ciro a aljihunsa ya miƙa mata. “Ga wayarki, na canja miki layi, hakan na nufin bana buƙatar sake ganin number kowane namiji a ciki. Ga amanar cikina nan na baki Huznah, dan ALLAH, dan girman ALLAH duk tsanani kada ki bari a cutar min da shi. Ke dai kin san irin wahalar da kika sha kafin cikin nan ya zauna, na tabbata kuma ko baƙya sona kina son ganin gudan jininki kema a duniya. Huznah idan har kika bari wani ya baki shawarar salwantar da cikin nan ki sani tamkar kunyi kisan kai ne.....”
       A birkice ta ɗago tana kallon sa. Ya jinjina mata kansa. “Tabbas abinda na faɗa haka yake, dan duk abinda ke a cikinki zuwa yanzu an gama busa masa rai Huznah. Dan haka salwantar da shi na nufin kisan kai ne, kuma wlhy, wlhy na rantse miki da UBANGIJI NA bazan yafe ba, ba kuma zanyi ALLAH ya isa bane kawai, zan kaiki kowacce irin kotu domin haƙin ɗana ko ƴata. Shiyyasa ina mai sake baki shawara, ina kuma roƙonki da duk wani abinda kikaga yafi ƙarfinki ki sanar dani a waya. Na baki dama kiyi sati biyu in sha ALLAHU zan zo da kaina na ɗauke ki bayan salla da kwana huɗu. Zan saka miki kuɗi a account ɗin ki, bana son ki ɗaurama kowa lalurarki koda ta son cin wani abu ne da za'a a fita a sayo a waje na kwaɗayi. Ki kuma dinga ƙoƙarin barin wayarki a buɗe zan dinga kiranki akai-akai in sha ALLAHU.”
       Hawayen dake zubo mata ta share. Sai shima ya matsa ya sake rungumeta, sannan yasa handky ya share mata hawayenta tas ya sumbaci kumatunta da lips ɗinta. Lokacin da suka dawo inda su Daddy suke har su babansa sun shiga mota. Shima sallama yay ma su Ammie da su Daddyn ya shiga motar suka wuce idanunsa akan Huznah da itama ta kafeshi da kallo irin wanda bata taɓa masa ba a gidansa. Sai kallon ya tsaya masa a rai sosai har suka kama hanyar Kano yana zane a cikin idanunsa da zuciyarsa...........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*




*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣1️⃣


______________



..........Maanal na zaune a falonta waya take da Didin ta Amaal da Shahidah ta video call a laptop. Bayan sun gama gaisawa cike da tsokana Amaal tace, “Kai Auta cikin nan fa ya miki ƙyau. Kinga wani fresh da kika ƙara. Wlhy skin ɗinki kamar wata ƴar Ethiopia.”
       Ta riga tasan halin Amaal idan ba faɗa sukai ba bata jin daɗi, dan haka tace, “Duk tsokanar ki yau dai bazan kulaki ba Didi. Cikin lafiya ana zaune ƙalau”.
           “Tab tsokana kuma. To miye abin tsokana anan. Bayan komai a bayyane yake kowa ma ya sani.”
     Cikin ɗan faɗuwar gaba Maanal ta ce, “Kai Didi dan ALLAH ki bari. Ni banda komai ALL......”
     “Karma ki rantse hajjaju. Wai kina nufin baki san da cikin bane ba? Bayan kowa ya gama sani kice ke baki sani ba kar ki rainama kanki wayo”.
    Fuskar Maanal na nuna ruɗani sosai ta kalla Shahidah dake murmushi. “Didi kinganta ko. Kice mata ta bari bana so. Kawai daga aure sai ciki sai kace wata mayya”.
      Wata shegiyar dariya ta suɓucema Amaal har da hawaye, Shahidah kanta dariyar ke son zuwa mata tana danneta da tsiya-tsiya. Ta ce, “Auta manta da ita, kin san dai halinta ai. Amma gaskiya ta faɗa miki kina da ciki. Ke kanki baki jin canji a jikinki, ko ciye-ciyen da kikeyi ai ya kamata kiyi tunanin hakan.”
     Ba ƙaramin waro idanu waje Maanal tayi ba, ta kalli cikinta ta kalli Yayun mata. Sai idanunta sukai rau-rau da hawaye. Haba kwana uku ke nan abin duniya ya isheta saboda rashin ganin period ɗinta. Sai ciwon da take ji mararta na mata har ma take tunanin zuwa asibiti a kan hakan. Sai kuma yau ta tashi dai alhmdllh shiyyasa ma ta manta da batun asibitin. Hawayen da suka zubo mata ne ya saka Shahidah faɗin, “To miye kuma abin kuka. Wannan ai abin farin ciki ne Maanal. Yau kece ɗauke da ciki, cikin ma na Ajwaad. Bake ba mu kammu a cikin farin ciki muke. Kullum hirarmu kenan da Ammie. ALLAH dai ya saukeki lafiya. Itama Amal ɗin dake miki dariyar ai cikin ne da ita”.
       Sai kawai dariya ta suɓucema Maanal itama, ta ce, “Oh Didi Amal keda kikace kin daina haihuwa? Yaya kuma akai haka?”.
     Harrarta Amaal tayi, tace, “Yanda akai ke da Ajwaad haka nima akayi anan”.
       Maanal tai mata gwalo tace, “Oho dai”.
    Kai kawai Shahidah ta gurgiza tana murmushi. Sai kuma ta katsesu da faɗin, “Badai wata matsala ko? Duk da nasan in har kema irin salon cikinmu kika ɗakko a yanzu baki da wata matsalar laulayi kam, sai nan gaba. Dan koni cikin Barrah inaga sai da ya kai wata biyu ma nasan da shi.”
          Haka kawai sai Maanal taji kunya ma, hannu tasa ta rufe fuska da faɗin, “Didi dan ALLAH abar maganar kawai.”
       Ƴar dariya Shahidah tayi, Amaal ta ce, “Almuna fun-fun, yanzu ne kuma kika fara jin kunyar mu, bayan nasan kina nan kina ji a ranki kamar ki tashi kita rawa dan farin ciki. Ɗan Besty fa a cikin ki. Inyeee lallai Besty baifa zo da wasa ba. Da yake abin na Besty da Besty ne zuwan farko kawai sai akai ehee”.
      Karan farko da Maanal taji bazata iya maidawa Amal tsokana ba, sai ma tasa hannu ta kife fuskar laptop. Harga ALLAH kunya ce taji ta kamata matuƙa. Cikinta ta kalla, tare da ɗaura hannunta a samansa ta wani lumshe idanunta. Sai ga hawaye na gangarowa a saman fuskarta. Muryarta na rawar kuka ta ce, “Ya ALLAH Alhamdullah, ashe dama zanga wannan ranar a rayuwata, ni Maanal ce ɗauke da ciki na ɗan mutum, kuma cikin ma na Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Besty na dai ba wani ba, kai jama'a......”
       Murmushi AA dake sakkowa daga sama yayi, sai kuma ya shiga takowa a nutse zuwa inda take. A gabanta ya zauna saman table ɗin bayan ya janye laptop ɗinta dake wajen, ya kai hannunsa shima ya ɗaura a saman nata. Da sauri ta buɗe idannunta tana kallonsa, suka zubama juna ido cike da wani irin rauni da soyayya. Cikin taushin muryar dake fita acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Nima kina so nayi kukan ne?”.
      A hankali tai ƙasa da idanunta, tare da duƙar da kanta, shima sai ya ciri tissue ya miƙa mata. Batayi musu ba ta amsa ta share hawayen, har lokacin hannayensu na'a saman cikin. Ta ɗan zubama hannayen ido, sai kuma a hankali ta ce, “Miyasa ka ɓoye min? Baka son muyi murna tare? Baka son nima nasan na zama uwa? Baka son nasan ina tare da gudan jinin Besty na, my half......”
          “Kiyi haƙuri ban ɓoye miki ba, nafi kowa son mu kasance da farin cikin wannan ni'imar da UBANGIJI yay mana a tare Besty, na ajiye wannan sirrine domin yi miki surprise shiyyasa. Sai dai wani ya min shigar sauri. Amma Besty ko ƴar kunya babu ɗan fari ne fa”.
     Murmushi ta saki a karo na farko, sai kuma tasa hannu ta rufe fuskar tata da ƙoƙarin miƙewa zata gudu. Dariya ya sanya tare da riƙeta. Tana zame-zame bai saketa ba ya koma inda ta tashi ya zauna yana ɗorata a saman cinyar sa. Son cire hannun nata yake taƙi yarda, sai ma ta kife kanta a ƙirjinsa kawai.
     “Shike nan na bari, na kuma yarda ana kunyar ɗan fari. Wai ya kaga Besty a labor room”.
         “Yanda akaga kowa mana. Ko ka zata ni raguwa ce”.
      “Ni shaida ne Besty na ba raguwa bace ba”. Ya faɗa a cikin kunnenta. Murmushi tayi itama tana ɗagowa, da wani sassanyan kallo ta kashe masa ido ɗaya. Tare da faɗin, “Ashe dai ka gane”.
     Murmushi ya sake saki, ya kamo fuskar tata cike da shauƙi da soyayya ya manne lips ɗinsa akan nata, idanunsu cikin na juna ya fara sumbatar ta, sai kuma ta lumshe natan a hankali dan bata iya jurar kallon cikin idanunsa sam. Suna da wani sirri na musamman mai ruguza nata dukkan kuzari a duk lokacin da ya tsareta da kallo da su. Sunyi matuƙar shagala a falon har sun kai wani matakin da basu farga sun kai ba, sai da ƙurar ta lafa ya tasata da tsokana da dariya, itako tana masa shagwaɓa da faɗin ya gama da ita, dan abin kunya a falo. Cak ya ɗauketa sukai bedroom yana dariya cike da ƙeta. Dan bawai bata jin jikin bane ba a hannunsa, ba kuma tana iya dauriyar bane ba har yanzu, kawai dai Babynsa na taimaka masa ne wajen samunta yanda ya kamata batare data farga ba, sai daga baya kuma ta dasa masa rigimar tata, shiko baya gajiya da lallashi.....

__________★

       A lokacin da nan Maanal da AA ke faranta rayukan junansu, a ɓangaren Saheeba abin duniya ne ya isheta. Yau kwanan amarya tara kenan a gidan, ta gama kwanakinta bakwai tun shekaran jiya. Haka ta zage tai gyara da tunanin mijinta zai dawo gare ta a ranar amma sai Babban Yaya ma ya tsiri tafiya Kano. Sai yau da Ameerah zata sake amsar girki duk da basu zauna sun tsaida kwana bibbiyun ba sai ga shi ya dawo da yamma. Kuma tana jin lokacin da yake kiran Ameerah ɗin ya sanar mata ai masa sakwara, dan suna a sashen Oum da yanzu ta dage da zuwa ita da Nuratu yay kiran. Da farko Ameerahn tayi kamar bazata tashi tai aikin ba sai kuma zuwa can bayan sun dawo sashen nasu taga ta shiga kitchen tana aikin. Tafasa zuciyarta taketa

169 / 213

Chapters