Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Huznahr amma ta shige sashen uwarta bata nema kowa ba?”.
Cikin sauri Ammie ta ce, “A mata uziri tayi kewar gida kaiko Daddynsu. Watanni kusan biyar ai ba wasa ba”.
Shiru kawai Daddy yayi, dan yasan Ammien ta faɗi hakanne kawai dan hanashi yin faɗa.....
★A ɓangaren Hajiya Basariyya kam tasan baƙi zasu zo kam ƙwarai, amma Daddy bai gaya mata daga ina ba, dan sai da safe ma taje gaisheshi ya sanar mata. Jin ƴan uwansa ne yasa bata ɗauki abun da muhimmanci ba. Dama takanta take ta ɗauki damuwar duniya ta ɗorama kanta akan wannan al'amari. Har dubu ɗari biyar yayanta ya bata amma basu birgeta ba. Yo wanda ya rasa miliyoyi mi zai yi da wata dubu ɗari biyar, ita dukiyarta kawai take son a dawo mata da ita. Idan ba hakaba wlhy ta gama shirinta tsaf kotu zata shiga da Yazeed. Babu abinda ya dameta da wani halin da yake ciki, dan ita bata yarda wai sakashi akai ba, kawai dai ya tattare musu dukiya dan tasan ta uwarsa ma zai dawo da ita. Idan ba da gayya akai ba taya zai ƙi taɓa na Asiya. Kai itafa duk ma uwar ubanda za'ayi sai dai a yi sai ta kai Yazeed kotu in har nan da sati biyu dukiyarta bata dawo ba, koda sakinta ne sai dai Daddy yayi. Miye amfanin zama ciki talauci, yo talauci mana, yanzu shi Yazeed ɗin yana zagayewa ya saida kaddaririn Daddyn ba shike nan komai ya ƙare ba, tunda Daddyn ya tabbatar musu ya zuba kaso tara na kuɗin account ɗinsa a sayen wani tsohon Company da zai gyara ya sayar kamar yanda yakeyi a zuwansa abujar nan. Kwata-kwata yace kuɗin dake tare da shi zasu taka kara sun karya ba, hatta abinci yace a fara lallaɓawa a gidan. Aiko wannan alamomin talauci na tunkaro su ne ai a bayyane.
Dan haka koda ta koma sashen ta sabgar gabanta ta cigaba dayi. Sai da mai aiki ta gama haɗa breakfast ne ta fito a bedroom. Sun zauna kenan zasuyi breakfast ɗin ne Huznah ta shigo tamkar wadda aka jeho. Da farko duk tsai sukai suna kallonta kamar basu santa ba. Sai kuma autarsu ta ce, “Aunty Huznah da gaske kece?”.
Faɗar hakan ya sasu miƙewa gaba ɗaya sukai kanta. Hajiya Basariyya datai sumar zaune saboda ganin cikin jikin Huznah ƙuru-ƙuru a cikin idannunta. Babu abinda zuciyarta ke mata sai luguden daka. Tabbas magana ta girma, Huznahr ta, ɗiya mafi soyiwa a zuciyarta ce ɗauke da cikin jinin Sani, jinin talauci da fatara. Sageeru dai da yazo ya raɓu dasu anan tamkar boyi-boyi.....
Tunaninta yay zurfi har bata farga ba Huznah ta iso ta rungumeta tana sakin kuka. Sai lokacin ne take dawowa a hayyacinta. Komai batace ba tai shiru kawai tana sauraren Huznah ɗin. Tsohon mintuna biyu ta tureta daga jikinta, cikin ɓacin rai ta ce, “Biyoni!!”. Ta nufi hanyar bedroom ɗinta. Ba Huznah kawai ba hatta sauran yaran shiru sukai suna bin Ummin tasu da kallon mamaki. To mike faruwa? A zatonsu ai sai tafisu ma murnar ganin Aunty Huznah ɗin. Huznah da hankalinta yafi nasu tashi bayan Hajiya Basariyya tabi cikin sassarfa. Tana shigowa ɗakin ta iso gabanta zata tambayeta mike faruwa kawai taji saukar zazzafan mari fuskarta. Kafin Huznah ta gama dawowa a hayyacinta Hajiya Basariyya ta sake sauke mata wani marin ta gefen haggu. Huznah ta fashe da kukan azaba tana durƙushewa.
Cikin hakki da nunata da yatsa Hajiya Basariyya tace, “Huznah ni zaki wulaƙanta. Ni zaki tozarta ki bari wannan ɗan matsiyatan yaron ya ɗirka miki ciki harki ɗakko ƙafa kizo min da shi cikin gida. Ni Basariyya zaki kawoma cikin Sageer ɗan Sani maƙiyina. Ina nan ina faɗi tashin ganin na cetoki a talaucin can ashe kin ɗaukeni shasha wadda batasan mi take yi ba....”
Kuka sosai Huznah keyi tana girgiza mata kai. Ta ce, “Ummi wlhy ban tozarta ki ba, ban wulaƙantaki ba fin ƙarfina akayi....”
“Fin ƙarfi? Zaki ce min ne tun zuwa ɗaya da yay miki baki sake bashi kanki ba ne? In ce na farko kince fyaɗe yay miki? Wanda ya biyo baya har wannan shegen cikin ya zauna shima duk fyaɗen ne? Nace shima fyaɗen ne!!!!??”.
Yanda tai maganar a matuƙar tsawace sai da jikin Huznah ya fara rawa. Ta zube a ƙasa sosai daga durƙuson da take ta manne a jikin gado...
“Kiyi haƙuri Ummi, dan ALLAH kiyi haƙuri na tuba. Wlhy yafi ƙarfina ne, idan bamma yarda dashi ta arziƙi ba ƙarfin yake samun. Nabi duk hanyar data dace dan nayi magana dake amma wlhy ban samu ba ki tambayi Maman su Yaseerah ma. Hatta cikin nan nabi hanyoyi da yawa danna sanar miki tunda akace ina da shi amma narasa hanyar samunki, ga shi ya kwace min waya...”
“Tunda ya maidake jaka ba dole ya kwace miki waya ba yayta kuma tumurmusa. Shike nan na barki da shi kije ki ƙarata. Maza tashi ki koma inda kika fito dan bazaki zauna min a gida ba. Bazan rayu muhalli ɗaya da jinin Sani ba har abadan”.
Kuka Huznah take yi cikin tsananin tashin hankali. Ta rarrafa ta riƙe ƙafafun Hajiya Basariyya taba kuka da roƙonta. Hankaɗe mata hannuwa tayi ta fito tabar mata ɗakin. Huznah ta sake fashewa da kuka hankalinta na sake ƙololuwar tashi. Hajiya Basariyya na fitowa daga ɗakin rai a ɓace Amrah ke shigowa sashen. Koda ta gaisheta bata amsa ba, ita dai ta isar da saƙon cewar Daddy yace tazo. Daga haka ta juya ta fita tana mamakin ganin su Madeena duk sun nutsu ran Ummi kuma a ɓace matuƙa...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣7️⃣
______________
..........Rai a ɓace Mamy ta fita a mota ta shiga cikin gidan Hajiya Turai. Hajiya Turai na zaune a dining zatai kari mai aikinta tsaye tana zuba mata abinci Mamyn ta faɗo musu babu ko sallama. Kallon tsaff Hajiya Turai tai mata daga nesa, sai kuma ta miƙe tana wani shegen murmushi irin na ƴan bariki...
“Hajiya Kamila ce a gidan namu. Lale marhabun amaryar Darma, shalelensa uwar ƴaƴansa”. Ada idan Hajiya Turai tai mata irin wannan kirarin jin kanta take matuƙa a sama. Amma yau ko murmushin ma bata iya tayi ba. Zama kawai tai itama Hajiya Turai ta zauna. “Hajiya Kamila lafiya kuwa? Sai naga ranki kamar a ɓace?”.
“Ba dole raina ya zama a ɓace ba Hajiya Turai. Harni Saheeba da Nuratu ke shirin wulaƙantawa? Sun manta da nice silar shigarsu gidan”.
“Subahanallahi miya faru kuma?”.
“Miye ma bai faru ba. Ko kin san tunda yarinyar nan Saheeba ta koma sashenta har yanzu bata sake taka inda nake ba daga ita har Nuratu. Nasan uwarsu ce ta kitsa musu wani abu saboda na hukunta Saheeba zatai ɓarin baki a gaban Fadeel. Ta kumayi maganar auren Nuratu da Ajwaad nace mata ta dakata akai lokacin da suka ambata. Shike nan fa laifi na. Yanzu zan fito shine a kan idona Nuratu da Saheeba suka nufi sashen Fateema har jaɗa ido nayi da Saheeba amma ta ɗauke kai kamar bata ganni ba.”
“Ke kikaja tai miki hakan ai, dan ke kika ɓarar da girmanki a idanunta!”.
A tare Hajiya Turai da Mamy suka juya suna kallon Nana dake fitowa daga bedroom. Kafin wani cikinsu yace komai ta cigaba da faɗin, “Kuma da kike cewa kece silar kaisu gidan kema kin san wannan gangan ne, ALLAH dai ya kaisu dan babu yanda kika iya. Aunty lokaci yayi da zaki san mun gaji da zama a ƙarƙashin mulkin mallakar ki ni da ƴaƴana. Saheeba dai ta riga ta zame miki ƙadangaren bakin tulu. Yanda kika haihu a gidan Darma itama ta haifa gama na uku nan zai zo. Kinga kenan dai-dai da dai-dai kuke kenan. Idan kince ke kika saka Fadeel ya auri Saheeba kema ai Fateema ce tasa kika auri Aliyu. Duk da wannan hallacin nata kuma kika zaɓi bijire mata da kwashe shekaru a buri da ƙudirin ƙuntata mata. Dan Saheeba ta bijire miki a yanzu ai bai kamata kiji zafi ba harda kwaso ƙafafu kizo kawo ƙararya wajen ƙanwar mahaifinta”.
Ba ƙaramin daka zuciyar Mamy keyi ba da kalaman Nana, kallonta kawai take yi al'ajabin duniya na neman halakata. Har sai da takai aya sannan ta iya faɗin, “Nana!”.
“Yes sunana ne Aunty Kamila.”
Idanu kawai Mamy ta ƙureta da su tana kallo. Sai kuma ta saki wani shegen murmushi mai ciwo tare da faɗin, “Hummm Nana ke nan lallai kina wasa da al'amarina. Amma zaki sha mamaki a wannan gaɓar. Zan tabbatar miki da rijiya ba wajen wasan makaho bane”.
“Hahaha Kamila kenan, nake wasa da al'amarin ki ko kike wasa da nawa. Karki manta ke da sirrinki duka a tafin hannuna kuka. Dan haka a maimakon tunanin bani mamaki ki sani nice zan baki nawa mamakin dan ke ai tuni kika kai ƙarshen bani naki mamakin. Kinga kuwa kece zan nunama bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ba. A tunaninki kin samu nannar banza da ƴaƴanta, ki cigaba da bautar damu kina ɗorasu a tafarkin tsiya ke kina kwance kina barci hankali kwance su suna yima kansu fenti da ruwan kashi mai wari ko. To bara kiji ke warin kashin da kika sakasu sukai wanka da shi zai fara addaba. Dan wlhy a shirye nake tsaff na ɗagaki sama na nunama kaf family ɗin Darma wacece ke. Kinga kuwa kece zaki a tutar babu, garama tawa ko gidan ta baro ƴaƴanta sun san itace uwarsu kuma a hannunta suka tashi. Keko fa? Idan zaki haɗa taron duniya da kayan cikinta ƴaƴan da kike hargowa da tada jijiyar wuya ke da su sai dai gani sai hange. Sunanki ƴar dakon ɗaukar ciki da naƙuda kawai a wajens.......”
“Tassss!!!”.
Kake jin saukar mari a fuskar Nana, ai Mamy bata gama sauke hannunta ba itama Maman Saheeba ta ɗauke tata fuskar da marin. Sai lokacin Hajiya Turai ta tashi ta shiga tsakkiya. Mamy da idannunta suka kaɗe jazur ta ce, “Nana ni kika mara?”.
“An mareki Kamila, ke wacece da zaki mareni na ƙyaleki. Idan kin manta bari na tuna miki shekara ɗaya ce da watanni kika bani ko a haihuwar ma. Sannan abinda kika sha nima shi nasha. Balle kiyi tunanin kin fini zafin rai. Dan ni ba Fateema bace da kika raina. Wlhy goge miki hadda zanyi tsaff. Butulu kawai mai maida sharri da alkairi. BALBELA WAJENKI FARI CIKINKI BAƘI. Ai ke ko hakkin Fateema ma bazai bar zuciyarki farin ciki ba. Ta riƙeki da zuciya ɗaya, ta sadaukar miki da mijinta, baya sonki baya ƙaunarki amma ta tursasashi ya aureki, ta koya masa zama dake amma baki da abin hari da ƙiyayya sai ita. Sannan har kike tunanin wai nawa ƴaƴan zasu kwanta ki cigaba da taka mu. Ke awa kuma. Ai wlhy idan kikace zakiyi wannan wasan sai dai buzinki, dan bazan taɓa tuna ni dake jini ɗaya muke ba. Kaca-kaca zan miki na tafi na barki a kwance”.
Ba ƙaramin ragargaza zuciyar Mamy kalaman Nana keyi ba. Jikinta har rawa yake yi, idannunta kuwa wani bishi-bishi take neman fara gani da su. Eh ta jima da fahimtar ƙudirin Nana a kanta, amma batai tunanin sun kai wannan matsayar ba ko kaɗan. Ita Nana ke datsama magana irin haka. Lallai kuwa tayi sakaci, lissafinta kuma ya samu rauni anan. Da ƙyar ta iya ɗaga hannu ta nuna Maman Saheeba dake jijjiga jiki...
“Nana zan baki shawara ki shirya, dan haɗa game dani tamkar haɗa karo ne tsakanin triller da napep. Wlhy ni Kamila nayi alƙawarin sai na wulaƙanta rayuwarki ke da ƴaƴanki. Sai na hanaki barci mai daɗi da kwanciyar hankali. Sai kinyi nadamar kasancewarki jini na”.
“Ke ce zaki wulaƙanta Kamila, kuma kece zaki daina barci mai daɗi duk da nasan dama kin jima da daina yinsa, Nadama kuwa ai kin jima a cikinta tun daga randa kika yaudari kanki kikai ƙyautar ƴaƴanki akan yaudara da zamba cikin aminci. Yanzu nadama ɗaya ta rage miki, wadda itace zata kaiki ƙasa wanwar, shine sauran ƴaƴanki su san wacece ke. Dan Aliyu Darma kam na tabbatar idan ma bai sani ba abubuwa kaɗan ne suka rage masa. Kin dai ga yanda ya watsar dake kamar yanda yake watsar da tutun jikinsa a masai. Dan haka nima ina baki shawarar rufe bakinki ɓam idan ba haka ba ni ba dani zakiyi Game ɗin ba da zuri'ar Darma ne, dan sai sun nuna miki ke ɗin ƙaramar ƴar wasa ce. Kin dai san suwaye jinin Darma, dan al'amarin ɗanki Ajwaad da kika nunama baƙin halinki kawai ya isheki aya. Kuma kada kiyi tunin ni ko ƴaƴana wani zai rufa miki asiri, wlhy tsifar gashin kan mahaukaciya zamuyi miki. Idan kinji ƙarya kuma, bismillah mu fara wasan”.
Komai Mamy ta kasa cewa, sai jinjina kai take kamar mahaukaciya. Ta kalla Hajiya Turai datai wani irin da fuska ita a dole tana cikin damuwar abinda ke faruwa. Nan ma kan kawai ta kaɗa ta ɗauki bag ɗinta ta fice idanunta na sake birkice mata bishi-bishi. Ganin yanda take tafiya tana haɗa hanya Hajiya Turai ta biyota da sauri. Da ƙyar Mamy ta iya kai kanta jikin motarta, Hajiya Turai dake binta a baya ta riƙeta tana faɗin, “Dan ALLAH Hajiya Kamila ki kwantar da hankalinki, kin dai san halin Nana basai na faɗa miki komai ba. Ni dama ina tsoron zuwan irin wannan ranar ina tsoron nayi magana ne kawai tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa sai ALLAH, ciki ɗaya ba wasa ba.”
Komai Mamy batace ma Hajiya Turai ba. Dan kanta wani irin sara mata yake na ciwo. Fahimtar hakan yasa Hajiya Turai kiran drivern ta tace yaja Mamyn a mota ya kaita gida. Ita kuma ta taimaka mata ta shiga baya tana faɗin, “Kiyi haƙuri in sha ALLAHU zanzo gidan anjima. Zanzo muyi magana mai muhimmanci”. Daga haka ta rufe mata ƙofar driver ya shiga shima yaja Mamy suka tafi. Wani shegen murmushi Hajiya Turai ta saki, tare da ɗan cije lips ɗinta, sai kuma ta juya ta kalla gidan nata, ganin Nana bata fito ba ta ciro waya a aljihun rigarta tai kiran layin Sille. Bugu biyu ya ɗaga, tai wata ƴar dariya da faɗin, “Ai yanzu mammanka ta fita kamar ma hawan jininta ya tashi. Tsiya suka tafka da Nana bata wasa ba”.
“Sille yay wata irin dariya da faɗin, “Ƴan wahala sai su cinye kansu. Ke ni bama wannan ba ina buƙatar kasancewa dake. Ki saitama wannan ƙanwar tata hanya dan anan zanyi weekend”.
Cike da farin ciki Hajiya Turai tace, “Karka wani damu Baby yanda kace haka za'ai”.
“Anjima zan kiraki, dan akwai aikin da zaki bita kimin”.
“Okay ba damuwa sai na jika, dama na faɗa mata zanje anjiman”.
Komai bai sake cemata ba ya yanke kiran..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣8️⃣
______________
............A office kam yau aiki sosai Maanal ta tarar a ƙasa. A haka ma tana rage wasu abubuwan a gida duk da hidimar biki da suka sha. Shi kansa AA yana da ayyuka sosai, ga batun case ɗin can na gidan Daddy. Dan yana isowa office ɗin ma bai fara ayyukansa ba sai da ya gana da wani baƙonsa da zai masa aikin bincike akan layukan su Yazeed ɗin. Kusan awa ɗaya suna tattaunawa kafin baƙon ya tafi ya ɗora da ayyuka. Sunje break sun dawo bai ko ga Maanal ba balle abinci sai gata ta shigo da wani file a hannu. Ƙamshin ta kawai ya sanar masa itace, ya ɗan ɗago yana kallonta, kafin ya maida idanunsa a computer ɗinsa. Inda yake ta ƙaraso, ta ajiye file ɗin kan tarin files da aka ajiye masa sannan ta zagaya ta bayan kujerarsa ta kwanto kanta a kafaɗarsa ta ce, “Good afternoon Besty”.
Murmushi ya saki mai sanyi, har yanzu hankalinsa a computer ɗin ya ce, “Ya aikin?”.
“Ba daɗi ba wahala”.
Ta faɗa cikin kunnensa. Sai kuma ta sumbaci wuyansa da faɗin, “Ya naka fa?”.
Kafin yay magana akai knocking ƙofar, ɗan tsayawa yay da aikin nasa ya kalla ƙofar kaɗan, itama Maanal sai ta gashi tsaye sosai tana gyara veil ɗinta datai rolling dan abaya ce a jiki ta. Izinin shigowa AA ya bada, AS ya shigo Sen... Bukar biye da shi. Fuska sosai AA ya haɗe yana kallon AS da duk ya daburce, cikin son kare kansa ya ce, “Wlhy Sir nayi iya ƙoƙarina ya fahimceni amma yaƙi. Na faɗa masa ma ba da kai ya kamata ya gana ba yace shi kai yake son gani”.
Yayinda AS kema AA bayani shi Sen... Bukar nacan yay sumar tsaye da ganin Maanal. Itako tai kicin-kicin da fuska hannunta akan kafaɗar AA tana daga tsayenta. Shima AA ɗin Sen... Bukar yake kallo zuciyarsa na wata irin