Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Dan koma an kaita can ɗin ba zama take yi ba, sai dai taita jibgar ƴaƴan jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta faɗa ta kama ta haye tana kiransa AA).
Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3 abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya ƙaru. Duk da tana a cikin waɗanda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai taɓa Maanal a duniyar nan Ajwaad baya ƙaunarsa. Hatta Ammie idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan sa'an Amaal ne yana girmeta kaɗan sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a dake san. Idan abu aka bama ɗaya ɗaya bazai taɓa cinsa ba sai ɗaya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu iri ɗaya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a ɗakko kala guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ƙananun kayanta irinsu pant, hula, vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana ɗaukar abun nasu wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matuƙar kulawa da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki....
Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha biyar. Suna a ajin ƙarshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar ƴan uwansa tuni ya tserema Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a ƙasa. Zuwa yanzu shaƙuwarsu ta sake wuce inda ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu wasu abubuwan da yawa ana ƙoƙarin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar da alaƙarsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu...
__________________★
Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara zasuyi ya sashi duƙawa. Dariya ta saki da siririyar muryarta kafin ta ɗane bayan nasa. Lunch box ɗinta da school bag ɗin dake ajiye ya tattara ya ɗiba sannan ya miƙe. Dariyarta tasa Ammie dake kitchen leƙowa. Takaici ya sata tsayawa kawai tana kallonsu, sai da ya kai ƙofa yana ƙoƙarin fita ta dakatar da shi.
“Yanzu Ajwaad bazaka hutama ranka ba dai?. Ka sauketa ta taka da ƙafarta, dan ubanta ba tun jiya ta taka ƙafar ba”.
Cikin yanayinsa na sanyin murya ya ce, “Ayya Ammie ALLAH ƙafan bai sakin mataba har yanzu. Bari muje su yaya Fadeel na jiranmu a mota”. Kafin ma ta sake cewa wani abu harya fice. Kai kawai Ammie ta girgiza tana komawarta, dan babu abinda suke buƙata yaran nan sai addu'a. Idan ta tuna mutuwa zata iya ɗaukar wani a ciki tabar wani har tausayi suke bata. Idan kaga Ajwaad na farin ciki ko surutu to tare yake da Maanal. Dan duk rashin son maganarsa sai da ta sakashi ringa yi, idan ma baiyi ba addabarsa take har sai ya tanka zata barsa. Kokuma taje ta takalo masa faɗan da dole ya tafi ramo mata......✍️.
😀😂🤣Eh lalle su Maanal an tsula tsiya a nahiyar arewacin Najeriya 😆🏃
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖5️⃣6️⃣
______________
........Tuni su Fawzan har sun shiga mota. Da sauri driver ya amshi kayan hannunsa, shi kuma ya ƙarasa gaba ya buɗe ya sakata dan nan ne wajen zamanta dama. Sai da ya gyara mata skirt ɗin ta sannan ya rufe ya zagaya kusa da ƴan uwansa ya zauna. Cikin tsokana da dariya Fawzan ya ce, “Oh oh Lilly bestyn Auta (Dan haka suke kiranta). Auta bestyn Lilly. Idan yaran nan kuka girma munada kallo a anguwar nan wlhy. ALLAH yasa dai kar ku haɗiye juna ko ku ƙone mu saboda eh......” ya ƙare maganar cikin shaƙiyanci. Banza Ajwaad ya masa, sai ma ƙoƙarin fiddo books ɗin Maanal yake yana dubawa. Yayinda Fadeel da suke kira (Babban yaya) yay ƴar dariya, hakama driver. Tsagal Maanal ta ce, “Yaya F minene eh...? Kuma sai mu cinye kammu kamar mayu”.
Dariya Fawzan ɗin ya sake kwashewa da shi. Tare da faɗin, “Lilly ba yanzu zaki san eh.. ba. Sai nan gaba. Ke dai ALLAH yabar tare”.
Cikin rashin damuwa tace, “Amin”. Sai kuma tai kneeling a kan kujerar ta saitin Ajwaad da yay kamar baya a motar tana lekensa. Cike da shagwaɓa ta ce, “Besty!”.
Ɗagowa yay kawai ya kalleta batare daya amsa ba. Wuyansa ta nuna masa tare da faɗin, “Baka sa tie ɗinka ba fa”.
Kansa ya maida ya cigaba da gyara mata abinda batai dai-dai ba a assignment ɗin da aka basu da tayi, dan jiya fushin faɗan da yayo mata bai tsaya ya koya mata ba sai Amaal ce ta mata. Kafin a hankali ya ce, “Zan saka sai mun sauka”.
“Ohhh”.
Ta faɗa tana cigaba da kallonsa. Duk abinda taga zai gyara mata sai tayi tambaya. Shi kuma ya bata amsa. Har ya kammala ya maida books ɗin shima ya maida hankali a kanta. Gaba ɗaya ta addabesu da surutu. Baka jin muryar kowa sai tata. Sai ko dariyar driver da Fawzan masu tayata dan shima Babban Yaya halinsa kusan irin na Ajwaad ne. Baida yawan magana. A haka dai har suka iso makarantar dan akwai ɗan nisa. Kasancewar a tsohuwar anguwarsu makarantar take. Ƙyawunta da son da suke mata yasa iyayen basu canja musu ita ba. Kullum driver zai kawosu ya dawo ya ɗaukesu.
Yanzun ma dai shine ya goyata, Fawzan ya taya shi da ɗaukar bags ɗin su da lunch box ɗin abinci data kasance ɗaya. Sai da ya rakasu har aji da kayan sannan ya wuce sashensu na yan secondary inda baban yaya Fadeel ya nufa. Ajwaad kam na sauke Maanal a mazauninsu dan kujerarsu ɗaya ta jawo bag ɗinsa. Zip ɗin baya ta buɗe ta ciro gogaggen tie dan uniform ɗin nasu kamar suit suke. Sai dai na mata skirt ne na maza wando. Zama yay a kujera tana daga saman desk ya miƙo mata wuyansa. Tsaf ta ɗaura masa dan tuni ta iya. Idan ka gansu dolene su birgeka kamar ba ƙananan yara ba. Ta gama ta gyara masa rigar da faɗin, “Wai Besty mi akai maka kake ta fushi. Inma dan ƙafatace ba nace maka na daina jin zafin ba. Tun jiya fa ka daina dariya why?”.
Shiru yay baice mata komai ba. Hakan yasa takai hannu saman sumarsa daya gyara ta shiga harmutsata. Hannunta yay ƙoƙarin riƙewa amma taƙi ta bari. Dole sai da yay dariyar da take so sannan ta barshi. Cikin dariya ya ce, “Besty wannan wane kalar kuturun wulaƙanci ne”.
Itama cikin dariyar ta amsa masa da, “Kamafi ƙyau a haka ALLAH”.
Rankwashi ya kai mata, ta kauce. Yay ƴar ƙwafa da faɗin, “Zan rama ALLAH ya kaimu Friday”.
“Mi zakayi?”.
Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓare lollipop daga cikin ledanshi.
“Meyi baya faɗa ai”.
Ya bata amsa yana fige alawar ya saka a baki. Hararsa tayi, shima ya rama. Sai kuma suka ƙyalƙyale da dariya. Saida sukayi mai isarsu sannan ta zare alawar daga bakinsa ta sha. Sake maida masa tayi a bakin. Haka sukaita yi har suka shanye kafin malami ya shigo musu su nutsu kamar basu ba.
Kowa yasan a ajin basa taɓuwa. Maanal rashin kunya da tsokanar masifa, gashi itace ƴar ƙaramar ajin dan duk sun girmeta tunda rigimarta ce ya kawota cikinsu ba shekarunta ba. Ka taɓata ka haɗu da AA. Yanada zuciya ga ƙarfi, dan in har ka taɓa Maanal ka taɓoma kanka kuwa. Gashi da shegen naci akan faɗa dan baya barin saita kwana. Surutun Maanal yasa kullum sai an sakata a cikin ƴan surutu na ajin. Idan kayi surutu naira ashirin, in sha ALLAHU kafin a tashi sai ta tara ɗari biyu. Idan ance ta bayar taƙi biya, idan shugaban ajin ya biye mata suyi faɗa AA ya kamashi ya daka. Dole class master ɗin su ya maida shugabancin ajin akan Maanal ɗin, aiko tunda ta samu damar nan take tsula tsiyarta. Ta cikama ƴan aji kunne da surutu su suyi ta maka sunanka. Azo biyan kuɗi kaƙi biya Ajwaad yay maganinka. Hakan yasa ake tsoronsu, ta gefen ƙoƙari kuwa sune masu zuwa na ɗaya dana biyu, basu taɓa tsallake wannan positions ɗin ba. Ada kafin Maanal tazo ajin AA ke ɗaukar na farko, wata yarinya na ɗaukar na biyu. Amma tunda Maanal tazo shikenan fa matdayin yarinyar ya rushe. Kullum sune dai su biyun nan, babu ƙoƙarin da wasu basuyi ba ganin an turesu amma abin ya gagara.
Ada saboda kalar fatarsu tazo ɗaya kowa ɗauka yake Maanal ƙanwar su AA ce ta jini. Duk da babu ta inda suke kamanni na halitta sai dai fatansu yana kama sosai. Sai da tafiya tai tafiya kowa ya fahimci yanda alaƙar take. Duk da su ɗin yara ne da yawan mutane kai tsaye suke fassara alaƙar zuwa wani abu daban. Duk da su dai yaran babu wani abu makamancin hakan a tattare da furucinsu na baki, mawuyacine ma ace su sun san minene wata soyayya, amma hatta iyayensu na ganin zuwa nan gaba Wannan shaƙuwar zata iya rikiɗewa ta koma hakan....
(To bari muga ko hakan zata kasance😀🏃.)
★★★
Kamar kullum ƙarfe uku dai-dai aka tashe su. Suna ƴan farko-farkon fitowa. Dan sun san driver ɗin su baya wasa. Ƙarfe biyu da rabi yake isowa. Uku a gate take masa. Ilai kuwa sun samesa inda yakan jirasu kullum. Dan su Fadeel ma har sun rigasu fitowa. Cike da tsokana Fawzan dake kallonsu ya ce, “A'a ƴar gurguwar Besty an warke ne?”.
Ƙafar tata ta kalla sai kuma ta kalla Bestyn nata. Harararta yay itako ta ƙyalƙyale da dariya tare da matsawa kusa da Fawzan. Nuni ta masa daya duƙo dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba. Haka suke dogaye dan iyayensu ma duk dogayene. Shiyasa ko shi AA ɗin dake 15 years ya shallaketa sosai. A cikin kunne ta gwargwaɗama Fawzan, “Dama fa dan ya goyani ne Yaya F. Dan yanzu idan nace yamin goyo sai yace wai na girma. Kaga yanzu ai na samo dabara”.
Mi Fawzan zaiyi ba dariya ba. Harda kwanciya jikin mota. Yayinda Maanal ta shige mota da sauri itama tana tata. Tsaf AA ya fahimci abinda ta faɗa dan yana kallon motsin bakinta. Dan haka baice komai ba ya saka bags ɗin su da lunch box ɗin cikin booth kawai shima ya buɗe motar ya shiga. Dai-dai nan Yaya Fadeel ya iso shi da abokinsa. Ta saitin da Maanal take abokin nasa ya ɗan leƙa yana tsokanarta dan mutuniyarsa ce. Kafin ya mika mata chocolate da in dai suka haɗu sai ya bata. Cike da ɗoki ta masa godiya tare da bye-bye. Ta buɗe chocolate ɗin ta, kamar yanda suka sabama juna duk abinda ɗaya ya samu sai ya raba da ɗaya ta raba biyu ta juya ta miƙama Ajwaad rabi duk da tasan ba lallai yasha wannan ba. Ilai kuwa maimakon ya amsa harararta yayi ma. Ta taɓe baki kamar zatai kuka da faɗin, “Wai miyasa baka son amsar abun hannun Ya Abdull ne Besty?”.
Banza ya mata bai tanka ba. Maimakon hakan ma sai ya ciro headphone ɗin daya saka a kunnesa. Dariya Fawzan yay da faɗin, “Kishi mana Alaji. Kinga Lilly bani nasha tunda shi na mazan ya motsa”.
Bata wani fahimci mi Fawzan ɗin ke nufi ba ta miƙa masa duka chocolate ɗin ta juya itama a dole tayi fushi. Shiko ya ce, “Uhhm gaba takaini, ban nasha faɗan masoya hutu”.
Harararsa Babban Yaya yayi. Cikin ɗan zaro ido ya ce, “Babban Yaya mi kuma na maka kai kuma?”.
“Kai bakinka bashi da linzami ko?”.
Cewar Fadeel ɗin.
“To ayi haƙuri babban yaya na daina”.
Shiru motar tayi babu wanda ya sake magana har suka iso gida....
Fuuuu ta fice batare data kalla kowa a cikinsu ba ta shige gidansu. Shima motar ya buɗe batare da ya jira an shiga cikin gida ba kamar yanda aka saba ya shige da ƙafa. Oum na zaune a falo ya shigo. “Oum good afternoon ”. ya faɗa a taƙaice yana shigewa ɗakinsu, dan su duka su a ɗaki ɗaya suke amma kowa da gadonsa. Da kallo Oum ta bisa, sai kuma ta girgiza kai kawai dan tasan ɗayan biyu ne fushin Auta. Kodai wani ya taɓa Maanal, ko shi da ita sun samu saɓani. Shigowar su Yaya Fadeel ya katse tunaninta. Su duka ita suka nufa, cike da shawagwaɓa suka zauna a gefe da gefenta kowanne yasa kansa a kafaɗarta duk da sun fara zama samari, koma muce sun zama. Dan Fadeel yana shekarar ƙarshe ne a secondary, Fawzan na aji biyar. Fuskarta ɗauke da murmushi ta shafa kawunansu dake cike da suma. “Da alama yau sojin gidan nan sunyi laushi, dan fuskar baban Commondo ya nuna.”
Dariya Fawzan yay da faɗin, “Oum wancan Commondo ɗin naki ba gajiyace ta maisheshi haka ba. Saɓani ya samu da rabinsa, bakiga sun barmu da dakon kayansu ba”. Ya ƙare maganar yana nuna school bags ɗinsu da lunch box ɗaya da suke zuba abinci.
Cikin ƴar dariya Oum ta ce, “Ai zancen gizo baya wuce ƙoƙi. Tana ina ita to?”.
Yanzu kam Fadeel ne yay ɗan murmushi da bata amsa da, “Itama tayi gida. Wannan yaron naki da alama zaiyi kishin tsiya Oum. Shike nan shi babu wanda ya isa ya raɓu Maanal koda da wasa ne. Ki lura da ko mu dan baida yanda zaiyi ne kawai. ALLAH ki ringa masa addu'a ALLAH ya sassauta masa”.
Sosai Oum ta saki murmushi mai ƙayatarwa. Kafin ta miƙe tana faɗin, “Kuna sakama autana ido a gidan nan. Tunda baya so a raɓar masa half ɗinsa a bar masa kayarsa mana”.
Miƙewa sukai suna dariya suma. Kowa ya nufi ɗakinsa domin yin shirin islamiyya kuma....
★★
A ɓangaren Maanal itama dai haka ta shiga gida a kumbure. Su Shahidah dake dawowa tun ƙarfe biyu daga tasu makarantar suna tsakar gida suna wankin uniform. Da kallo suka bita dan ita ko kulasu batai ba. Koda ta shiga ciki ma bata nema inda Ammie take ba duk da tana jin motsinta a kitchen. Ɗakin Ammien ta shige dan ita nan ne wajen zamanta. Ɗakinsu kullum cikin faɗa take da su Shahidah da neman fitina da su, su sakata abu taƙiyi, su daketa Ajwaad ya rufesu da azabar masifa kamar Shahidah bata girmesa ba. Ganin haka yasa Ammie maidota ɗakinta ita sai aka zauna lafiya. Duk da a hakan ma idan neman maganar ta ya tashi takan shiga ɗakin nasu tayi ɓarnarta son ranta ta fito. Suyi magana tace ita sharri sukai mata mi zatai a ɗakin nasu da babu komai sai tarkace.
Gado ta faɗa ta sanya kuka, tafi mintuna goma har sai da Ammie tazo tana mata magana. Da farko ƙin tashi tayi ma sai da ta daka mata tsawa sannan ta tashi a firguce dan tana tsoron tsawa matuƙa. Cikin haushi Ammie ta ce, “Wane kalar shashanci ne kuma wannan zakizo kinama mutane kuka daga dawowa. ALLAH Manaal ki maida hankalinki a gidan nan. Ke kullum girma kike amma kina sake maida kanki wawuya. Baki da lafiya ne?”.
Kanta ta girgiza alamar a'a. Sai kuma ta sake matso hawayen da suka taru mata a manyan idanunta da kai kasan idan ALLAH ya kai ta zama budurwa ba ƙaramar ƙyaƙyƙyawar yarinya za'ai ba. Dan ko yanzu mutane da yawa kance za'aga ƴammata a wajen nan. Maanal irin yaran nan ne masu shiga rai lokaci guda. Balle gata da baki da rawar kai kuma. Uwa uba tsiwar tsiya...