AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   206 / 213

615K to 618K   out of 636.6K words

hararta sai ga AA ya shigo da Ahmad sarkin kuka kenan. Oum ce ta amshesa cike da so da ƙauna tana faɗin, “Oh oh oga rigima kenan, kai dai kaf halin tsohonka Fawzan na kuka ka iya shi. Kodai yunwa yake ji?”. Tai maganar tana kallon AA dake kallon Maanal, duk yau basu ga juna ba, dan da sassafe ya fita sai yanzu yake dawowa gidan yayi meeting a fadar shugaban ƙasa da wasu mutanensa.
        A hankali cikin nutsuwa da maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Maybe Oum, dan Abah yace tun ɗazun suke a wajensa. Amma shi wannan boss ɗin ko ba yunwa ma akwai rigima ai.”
            Oum tace, “Sai fa boss ɗin, Baby zauna ki bashi abincinsa.”.
     Baki Maanal ta turo, sai dai yanda AA ya tsareta da idanu sai ta kasa cewa komai ta zauna Oum na saka mata shi a jiki. Zama AA yay a hannun kujerar da ta zauna yana kallon su, sai ga Ameerah ta shigo. Gaishe shi tayi, ya amsa da kulawa yana faɗin, “Ameerah samo min tea a kitchen ɗin nan naku”. Da to ta amsa tana juyawa, Maanal ta ɗago tana kallonsa tana yamutsa fuska saboda Ahmad dake shan abinci, bata san randa zata saba da feeding ɗin nan ba ita kam. A sanyaye ta ce, “Bakaci abinci ba?”.
      Shima yana wani kallonta a narke ya ce, “Baki bani ba Besty, yanzu baƙya tani sai yaranki ai a gidan nan”.
     “Kai Besty ban san sharri, amma Didi fa tace an shirya maka abinci a sama”.
            Hannu ya kai yana gyara hular Ahmad dake zamewa, sai kuma ya ɗan kalleta da faɗin, “Ai ban shigo nan ɗin bane sai yanzu. Bari kawai nasha tea ɗin, saina haura na ɗan watsa ruwa naga idan zan iya ci. Zanje muje asibiti da su Babu ma”.
      Tana ƙoƙarin yin magana da kai hannu fuskarsa ta cire zare daya ke akan gashin sajensa Ameerah ta dawo da tea ɗin. Amsa yay yana faɗin, “Thamks” a maƙoshi, ta jinjina masa kai da kallon Maanal. “Madam a kawo tea ɗin kema?”.
     Zatai magana AA ya ce, “Barta wannan zai ishemu kaɗan zan sha”.
   Kai kawai Ameerah ta jinjina ta wuce, sai ya kai kofin bakin Maanal. Yana sha yana bata cike da kulawa su CFO sukai sallama. Bashi da alamar tashi sai ma damar shigowa ya basu, Maanal ta gyara Ahmad dan bata son a gani mata jiki. Turus CFO da ƙawayenta suka tsaya suna kallonsu. Sai kuma ta ƙaƙaro murmushi da faɗin, “Ashema kana gida Sir”.
     AA da zuwan nasu ya bashi mamaki tunda yasan jiya tazo wajen walima a dake ya amsa yana kai kofin tea a bakin Maanal, itama ta sha abinta dan zuwa yanzu ta fahimci take-taken matar sarai akan mijinta. Zama sukayi ƙawayen nata suma fa AA ya tafi dasu, hakama Maanal ɗin so cute da ita kamar ba ita ta haihu ba. Ji wata soyayya mai narke jiki tea ɗin ma sai miji ya bata tabɗin.
      Sun gaisa AA ya amsa sau ɗaya ya basar, sai Maanal ce ma ta ɗan sake musu, sai kuma gasu Najma sun kawo musu ruwa da lemo da nama. Barka sukayi da ALLAH ya raya, CFO tai musu bayanin ƙawayenta ne sunzo ta nan street ɗin shine tace suzo su musu barka. Godiya Maanal tayi, dai-dai AA na miƙewa da jan hancin Maanal kaɗan yace, “Kin shanye min tea”.
      Murmushi tayi tana kallonsa a narke ta ce, “Kaine fa ka bani”. Gefen fuskarta ya sumbata ya amshi Ahmad daya gama yama koma barci yana faɗin, “Yana iya dake. My Kiddo zamuje ka taya Abiee wanka tunda Ommy tace jego take”. Ya wani kashema Maanal ido ɗaya yay wucewarsa. Murmushi kawai tayi da girgiza kai. Su CFO suka rakashi da kallo kamar mayu.
    Duk da CFO na aiki a Maawad babu wani sabo bayan na gaisuwa tsakaninta da Maanal. Yanzu ma sai ta kasa sakewa da su. Suko sun wani baje juna hira da cin kayan da aka kawo musu. Kusan mintuna arba'in sai ga AA ya fito tsaff da shi yayi wanka sai uban ƙamshi yake yi, inda Maanal take yazo ya miƙa mata lins na hannu, babu musu ta amsa ta saka masa. Ya wani duƙo ta saka masa hula tamkar sun manta da su CFO. Fuskarsa ya bata ta masa kiss shima yay mata sannan yace, “Ki kula min da kanki da twin's sai na dawo”.
       Kai ta jinjina masa tana murmushi tace, “ALLAH ya tsare min kai da tsarewarsa, ya baka kariya da ƙarfin ikonsa.”
     “Amin my everything”.
Ya faɗa yana sake kissing lips nata sannan ya wuce. Ai zuciyar CFO sai taji tana harmutsawa. Bai ko kallesu ba ya wuce ciki-ciki yana faɗin, “Thanks”.
     Hawaye sosai suka cika zuciyar CFO, Dan kwallin data saka dai da'alama yabi iska. Tunda ko haɗa ido basuyi dashi ba. Kuma malamin daya bata ya tabbatar mata in dai basu haɗa ido da AA a yau ba gaskiya bazata taɓa samunsa ba har abada. Ganin tana share hawaye ƙawayenta suka lallaɓata sukai ma Maanal sallama suka tafi, dan suma dai sun san sai haƙuri kuma ƙawarsu ta rasa.....

_________★

       AA da kansa yaje har masaukin ƴan Giro ya ɗauki su Babu yakai asibiti. Sailu da Babu gwaje-gwaje akai musu da sake bada magunguna. Gwaggo ce akai ma sabon gwaji. Babu wani kai-kawo result ya nuna ta ɗauka itama. Duk da ta jima da sallamawa sai da tai kuka sosai, sai Ammie data samesu a asibitin ce ke lallashinta. RK dai ya zauna ya sake basu shawarwari da sauransu. Aka ɗan saka musu drip su duka sannan suka shiga office ɗin RK dan yace zasuyi magana.
      Result ɗin Mamy ya ciro ya bashi na gwajin HIV. Bayan ya duba zuciyarsa na wani kalar rawa ya ɗago yana kallon RK. Da ɗan rawar lips ya ce, “Uncle HIV fa?”.
     “Nima irin wannan yanayin na shiga da Dr Hamaad ya kawo min result. Haka na sake mata sabon gwaji amma still dai abu guda ya bamu. Na ma rasa inda zan kamo lamarin Ajwaad. Amma babu wanda ya sani gaskiya har ita, dama ina son ku dawo ne suma Yaya da Aunty muyi musu gwajin ko zamu samo bakin zaren”.
     Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un AA ke maimaitawa kawai hannunsa dafe da kansa. RK ya taso cike da kulawa ya ta zauna a kujerar dake facing wadda yake zaune. Ya ce, “Ajwaad calm down, itafa rayuwa gaba ɗayanta jarabawa ce. Yanda mukai haƙuri dana baya yanzu ma haka zamuyi kaji.”
      AA ya ɗan murmusa kaɗan, idanunsa da suka kaɗe ya ɗan zubama RK. Sai kuma ya furzar da iska kaɗan. “Rafeeq bana fatan ace Oum da Abah suna da wannan ciwon suma. Rashinsa kuma zai sakani a wasiwasi mai girma na ina Mamy ta samoshi”.
        “Bana tunanin ta mummunar hanya, dan zan gaya maka gaskiya na jima ina bibiyar Aunty Kamila ban taɓa samunta da makamancin abinda zai iya sawa ta samu ba. Kayi haƙuri ɓoye maka abubuwa da nayi.......”
    Gaba ɗaya ya zayyane masa komai daya sani tun ɗan zamansu a Paris, har su suka dawo Nigeria suka barsu acan. Bai gama fahimtar komai ba sai bayan kawo Maanal Mawaad Company, a lokacin daya kaita gidansu ya gane komai na alaƙarsu. Tun a lokacin ya shirya barin rayuwarta, ya fara koyama kansa haƙuri da ita, duk da zuciyarta taƙi amsa saboda da gaske sonta yake har takai ya sallama gaba ɗaya ranar da tazo gidan Shahidah da motarsa. Sai kuma randa ya sameta a asibiti yaji maganganu su a ɗakin jiyyarta. Yaja numfashi da cigaba da faɗin, “Nata tunanin ta yanda zan gyara komai auren ya koma kanka amma ban san yaya zan yi ba, kuma bana son gaya ma kowa tunda Yaya ya gargaɗeni. Kawai randa naje Kano dan musu maganar kai kuɗi na samu Aunty Kamila taje tayi magana da Abbu da Baba Sardauna, sai kawai nai amfani da damar na zauna da Mah-mah”........✍️206


........“Ban ɓoyema Mah-mah komai akan abinda na sani ba, itama hankalinta ya tashi ta tabbatar min bazata taɓa yarda a aurama Maanal wani idan ba kai ba. Dan haka ta samu Abbu suka kirani muka tattauna sosai a daren muka samu baba Sardauna. Shima yayi mamakin jin cewar anga su Maanal amma baku gaya masa ba, amma sai yay muku uziri tunda ga yanda abin yazo. A wannan zaman muka tsara komai da maganar ɓoye maka saboda kada aunty Kamila ta biyo ta wani wajen ta hanaka auren tunda ba'asan ainahin abinda ya faru a wancan karon ba. Amma yanda ta nuna a zuwan datai Kanon tafi damuwa da a aura maka Nuratu sai duk muka sha jinin jikinmu da ita. Shine dalilin rufe komai sai da aka ɗaura aurenku kowa ya sani harda ku da su Yaya ma. Hatta riƙe Maanal da Yaya yayi ya hanata tarewa harda gudunmawar Baba a ciki, dan shi yace ayi hakan saboda aja zancen bikinka da Nuratu sam baya son haɗinku tarbiyyar yarinyar batai masa ba. Baya son kuma ya nunama Aunty Kamila ta biyo ta wani hanyar ta tursasaka aurenta matsayinta na uwa. So a taƙaice magana ta ALLAH ban taɓa kamata da wani abu mara ƙyau ba. Sai dai yanzu zamuyi wannan gwajin yanzu, daga nan sai mu tafi mataki na gaba dan dole sai munga results ɗin da zamu samu a kansu suma”.
      Kai kawai AA ya iya jin jina masa. RK ya shiga masa nasiha da kwantar masa da hankali. Dan yasan halinsa sarai....

     Koda ya koma gida bai gayama kowa komai ba, yama samu ƴan Giro sunzo musu sallama dan asubanci zasuyi. Dama dasu Gwaggo ya wuce gidan. An haɗa musu shatara ta arziƙi ma kayan suna harda turamen zani da dubu ashirin-ashirin aka saka musu. Babban Yaya da Yaya Fawzan ne kuma suka bada kuɗaɗen. Oum zannuwa. Sai kayan suna na musamman, nama kam ƙaton botiki aka cika musu harma wanda basu zo ba suma da kayan sunansu. Itama Maanal da su Amaal kuɗaɗe da abubuwa suka haɗa musu sosai. Sun yima Babu ɗinkuna suka saka masa kudi masu yawa a account. Sai dare sosai suka wuce masaukinsu bayan anyi sallama. Washe gari sunayin sallar asuba suka wuce Haƙila harda kukanta, dan shi Sule yana nan an barshi za'a kaishi Rehab a fara treating ɗinsa akan batun shaye-shaye, AA nason ya gyara rayuwar yaron da ikon ALLAH a maidashi makaranta tunda kwata-kwata fa yanzu yake 15years da wasu watanni....

     Suma su Amaal sun kammala komai daya dace zuwa azhar suka wuce gidan Shahidah. Maanal harda kukanta, dan kowa ya wuce ba'a barta da kowa ba sai yarinya ƙarama da zata dinga tayata da raino da ta saka aka taho mata da ita daga Giro. Sai Meeno data dawo nan gaba ɗaya tunda ta dage. Dama basu wuce ba sai da suka gyara mata ko'ina, dan haka komai neet Najma da Ameerah ma dake fama da kansu sun shigo sun ƙara gyara abinda ya dace, daga nan sukai zaman tayata hira data ɗauke mata hankali ta bata nutsuwa. Twin's ba wani zama suke a wajenta ba, sai idan suna kukan abinci ne ma ake kawo mata su. Suna sashen Oum da Abah wajen dangi.....

_________★

       Da dare matuƙar gajiyar da Maanal tayi yasa da wuri tai barci, dan yaran ma sai Oum ce data shigo da su tai musu shirin barci aka kwantar da su bayan sunsha madara sunyi nak. Oum tai musu addu'a ta koma sashen ta dan sunata hirarsu da ƴan uwa ne tunda suma gobe in sha ALLAHU zasu wuce. Gashi idan an haɗu sam ba'ason a rabu, shiyasa duk daren tafiyar sai kiga an kusan kwana ana hira, ko Kano sukaje hakace ke faruwa suma.
     Meeno da Nafisa suna sashen Najma tare da sa'oinsu dake can. AA bai shigo ba suna tare da ƴan uwa ana shan hira suma. Da wannan damar Nibras data gama yankema kanta shawara a yau bisa tunzurawar ƙawarta ta lallaɓo ta shigo sashen. Kwana biyun nan duk ta gama lura da yanda ake haɗama AA abinci, sai tayi amfani da hakan itama ta shiga neman fruits salad da taji yana faɗa a haɗa masa ɗazun. Wanda Najma ta haɗa masa kuma ta manta shaf bata kai ɗakinsa ba ta ajiye a kitchen na sama a fridge dan ita ko Ameerah ke bashi abinci tunda aka fara shagalin sunan nan ko Amaal, yau Amaal sun wuce, Ameerah bata jin daɗi tunda tai sallar magrib ma bata sake fitowa ba tana a bargo. Ita kuma Najma hirar dangi ta saka ta mantawa dan AA ɗin da kansa yace ta haɗa masa fruits salad ɗin ma kafin su wuce nasu sashen dan yaji Maanal na cewa da tayi isha'i zata kwanta yau ta gaji. Koda ta kammala sai takai fridge na sama ta ajiye masa, ta dafa tea shima a flaks ta ajiye ta wuce nata sashen. A kitchen ɗin ƙasa ta fara dubawa, ganin bata ganshi ba ta haura sama tana ta waige-waige da fatan kar wani ya shigo, amma duk da haka sai da ta leƙa bedroom ɗin Maanal taga tana barci sosai ita da yaran fitila ma a kashe sannan ta koma ƙaramin kitchen dake a saman nasu ta buɗe fridge sai ko gashi ta gani. Murmushi tayi sosai, ta fiddo bowl ɗin ta ajiye, ta ciro abinda ke cikin kimono ɗinta ta warware takardan sai ga ƙwaya ƙanana har biyu. Abu ga samu ta daka su tana murmushi sannan ta zuba ta motse. Tray ta ɗauka ta haɗa masa komai ta saka akai ta ɗauki tray ɗin ta wuce bedroom ɗinsa.
     Yau ne karo na farko data taɓa shigowa bedroom ɗin tun bayan aurensa da Maanal. Ɗakin ya haɗu dan komai an canja shi. Sai ƙamshi mai daɗi da taji ɗakin Maanal nayi ke tashi anan ɗin ma. Baki ta taɓe cike da kishi ta ajiye komai ta fita. Kawai sai taji ƙamshinsa kamar yana hawowa saman. Da sauri ta shige kitchen ta kashe fitilar..

     AA da barci ya ciwo idonsa ya baro hiran yana gama haurowa yaji ƙamshin turaren daba na Maanal ba, amma da yake gidan da mutane sai bai wani saka komai a ransa ba duk da ya ɗan ji mamaki tunda yasan Maanal bata bari a hawo mata sama, yana kuma jin daɗin wannan respect ɗin nata. Ɗakin da take ya fara shiga, ganin yanda suke barci ita da yaran yay murmushi kawai, a ransa yana raya kamar wadda tasha wani abu. Kissing na yaran yaje yayi itama haka,  sannan ya fito dan wanka kawai zai yi ya dawo nan tare da iyalinsa zai kwana babu ruwansa da wani batun jego can.
     Koda ya shiga ɗakinsa kaya ya cire ya wuce wanka, sai da ya fito ma yake lura da tray ɗin nan. Ajiyar zuciya ya sauke yana zama da bathrobe a jikinsa ya buɗe bowl na fruits salad ɗin. Kamar ma zai haƙura da shan sai kuma fruits ɗin suka birgesa, dan exactly yanda Maanal ke haɗa masa ne, ya tabbatar koba itace ta haɗa ba ita ta gayama su Najma yanda zasuyi. Ko kawowar ma ya zata itace ta kawo masa, har yana ƙananun magana wai yanzu bata gashi sai ta yara. Haka dai ya ɗauka ya fara sha, sai kuma yay masa daɗi ya kuma sake yarda ita ta haɗa dan abincin Oum da Maanal ko a wani gida aka bashi sai ya banbance. Yasha sosai sannan yay shirin barci, ya ɗan zauna yana taɓa aiki kaɗan tea na kusa da shi bai dai zuba ba yana son fruits ɗin ya sauka. Sai mi zai faru kawai cikinsa ya fara ƙullewa. Wani barci ya fara cin ƙarfinsa. Tunfa yana jin zai daure harya kashe laptop ɗin yakai kwance batare daya sha tea ɗin ba dama a gado yake zauna. Kamar wasa barci mai ƙarfi yay gaba da shi, ga wata irin sha'awa na damunsa har a cikin barcin, jikinsa kuma yay masa nauyin daya kasa tashi ya je ɗakin Maanal yaga ko zai iya rage zafi koda bai samu mai gaba ɗaya ba. Amma ina kamar an dannesa da dutsina tsabar halin daya tsinta kanshi. Zuwa can kuma barcin ya tafi da shi gaba ɗaya ya koma mafarki...

       Najma na kitchen abinta a kujeran work table tanata chart da ƙawarta dake ƙara tsara mata komai da yanda zata yi. Sai faman jin daɗi take da sakin murmushi. Gaba ɗaya ta kasa tunanin idan ta tashi mata fa ga gida cike da mutane. Abinda kawai take dubawa ai ta bugar da Maanal itama. Dan abu ta zuba mata a shayi da tasha da yamma batare da sanin kowa ba. Saboda shayin na musamman ne da Hajiya Shuwa ke dafa mata tana sha akai-akai ita kaɗai.
    Ganin lokaci yaja ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar bayan ta sake fiddo mayataccen turaren da ƙawar tata ta kawo mata ta mulke jikinta da shi yanda ya kamata. Ai sai taji kamar ana ingizata da remote. Eh tana son AA sosai, amma bata taɓa tsarama zuciyarta bin wata hanya dan ya kwanta da ita ba. Sai da ƙawarta nan tata ta fara kwaɗaita mata al'amarin. Da farko ma bata amsa ba dan tana jin tsoro, musamman data san wanene AA ɗin. Sai da ƙawar tata ta bata turaren nan ta shaƙa sai taji ta amince ɗari bisa ɗari.
      Cike da ƙwarin gwiwa na mallakar AA a yau ta tura ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. A kwai haske mara ƙarfi, hakan ya bata damar ganinsa kwance a gado yayi rufda ciki. Murmushi ta saki zuciyarta na ingizata, ta cire kimono ɗin jikinta ta yar, figigiyar rigar barcinta ta bayyana. Itama cirewa tai ta yar, ta koma haihuwar tsohuwarta sannan ta nufi gadon.........✍️

207


.........Cikin barci kawai AA yaji an kwanta masa a jiki. Dan bayansa ta

206 / 213

Chapters