Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Duk da tako wane ɓangare kowa akwai abinda ya damesa. Aranar dai Mamy da su Nuratu basu je aiki sashen Oum ba. Nuratu kuwa tasha uban bori akan sai taje har sashen Oum ta daki Maanal. Da ƙyar Mamy da Saheeba suka lankwasata bayan an kira Hajiya Turai a waya itama ta sake yin nata. Sai da Oum taje har sashen Mamy ta bata haƙuri da lallashinta sannan tace ita fa ba wannan bane ya ɓata mata rai bata jin daɗi ne. Ita dai Oum ta sake bata haƙuri ta taho. Sai kuma hakan ya damu Mamy ɗin, dan da ciwo kaga kanata hauka akan mutum shi ko'a jikinsa, (kamar dai yanda Maaanal tace AJIYA A DUHU kenan😂) washe gari suka fito akaje tafsir tare aka kumayi girki tare. A ɓangaren Fawzan shima dai ransa danƙare yake da al'amarin Mamy dan abin sai ya zame masa biyu. Wanda tai masa, da wanda ya faru akan marin Nuratu da AA yayi. Shi ko babban Yaya iya na marin Nuratun ne kawai ya bashi mamakin. Sai kuma ya ɗauka kawai Mamyn ta fusata ne saboda Nuratu na jininta. A ɓangaren Mamy kam abin da ya tsaya mata a zuciya Abah ne. Dan daga wannan nasiha bai sake cemata komai ba, hatta borin kin zuwa aiki da tayi na kwana ɗaya da ƙin zuwa shan ruwa sashen Oum ko'a fuska bai nuna mata ba balle ya tanka. Sai hakan ya girgizata ya kuma tsaya mata a zuciya taketa hasashe-hasashe ta kasa gane komai. Gefe ga tsanar Maanal da maganganun data gayama su Saheeba yana ƙara yima Mamy ciwo bama su Saheeba ɗin kawai ba. Sun kuma rasa ta yanda zasu rama duk da sun ɗauki alwashi kala da iri Saheeban da Nuratu. Na ƙarshe AA, matuƙar ciwo abinda ya farun yay masa. Dan haka ma a jiya ya shirya tafiya Lagos ya bar musu gidan. Dan baya buƙatar yin wata magana da Mamy in ba hakaba ALLAH sai zuciya ta kwashe shi yama Nuratu dukan mutuwa ya kuma koreta a gidan duk da Oum ta masa faɗa da nasiha sosai a washe gari. Itama Maanal karanta jotter ɗin da RK ya bata ya sakata kuka sosai jikinta kuma yayi sanyi matuƙa, dan haka ta ɗauka ɗammarar gyara abubuwa da yawan gaske...
Kwanakin azumi sun cigaba da tirzawa, wasu na ibada wasu zukatansu cike da burikan sharri. A randa aka shiga goman ƙarshe AA ya dawo gidan, zuwa dare kuma ya sake barin gidan acewarsa ya shiga ittikafi. Bai yarda wata keɓantacciyar gaisuwa ta shiga tsakaninsa da Maanal ba itama kuma bata nuna ta damu ba a zahiri duk da hakan ya mata ba daɗi, dan yanzu so take su daidaita sosai. Ita kanta Oum bataji daɗin yanda AA yayi ba amma batace komai ba. Shi kuma a ganinsa hakan da yay zaifi alkairi dan a cikin wani irin matsananciyar buƙata yake shiyasa ya zaɓi duk hanyoyin hana keɓancewarsa da Maanal sam.
A ɓangaren Abah da Uncle RK da su babban yaya kam suna ibada suna kuma shirya biki batare da sanin kowa ba. Yayinda suma dai ta ɓangaren Mamy bikin suke shiryawa acewarsu babu ɗaga ƙafa sati ɗaya da salla. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, azumi nata bankwana su Maanal nata ƙara dagewa a yin ibada. Duk da ita ma a farkon goman tai period, ALLAH dai ya taimaketa kwanansa uku ya tafi ta cigaba da azuminta. Tun azumi na goma sha biyar tela yazo ya gwada ƴan hutun su Oum bisa umarnin AA. Batare da kowa yaga kayan da za'a ɗinka ɗin ba kuma. Yau da azumi ke ashirin da bakwai ana saka ran salla nan da kwana biyu ko uku sai ga ɗinkuna sun iso kowa da sunansa. Zokaga murna da tsalle wajen yaran. Abinda ya ƙona ran Mamy babu Nuratu a ɗinki, duk da taga babu Maanal itama hakan bai dameta ba. Tako ƙara ƙullatar AA sosai a ranta, gashi dama ta fassara barin gidansa da wai yana haushi da ita ne. Bata san bawan ALLAH abinda ya damesa daban ba. A ranar shima Yaya Fawzan ya kwashe su da dare yin shopping na takalma da sauran tarkace. Harda Maanal da Oum akaje, nan ma baƙin ciki kamar zai kar Mamy. Duk da dai ta danne bata nuna ba a fili, harda kuma su Saheeba da Nuratu da Nibras. Kowa kuma ya zaɓo ra'ayinsa, Oum kuma ta zaɓo nata dana Mamy data ƙi binsu wai ita kawaici sai na Aba. Fawzan ya ɗauka musu shi da Baban yaya da AA dan Uncle RK ya fece Kano yace kansa bazai murfi ba ranar salla sabon amarcin shi da Nuwaira 🤣. Shi kuma babban yaya washe gari ya lodo uban cefane da kaji gyarru sai uban jan nama. Tuni sun hutar da Abah yin komai a gidan nan. Dan shi kansa bai san yaushe ne last da ya sai wani abu na abinci ko sutura ba koda ma kansa a gidan. Hatta da ƴan uwansa duk salla sai su babban yaya sun aika musu da kaji da cefane na abincin salla. Wannan sallar ma hakan ce ta faru, tuni nasu sun wuce Kano. Batare da sanin kowa ba kuma AA ya tura Kaduna da uban kaya ma Daddy kamar yanda suma su Babban yayan kanyi ga nasu surukan duk shekara...
Tunfa a daren masu aiki suka iso, dan duk salla su Oum na ɗaukar masu tayasu aiki saboda abinci akeyi bana wasa ba kasancewar ana fita da wani wa bayin ALLAH, kuma a cikin azumin ma akwai inda ake dafa abinci a raba duk lokacin shan ruwa batare fa kowa yasan daga su bane. Bayan ɗanyan abinci da shi kansa AA ke rabawa duk shekara shi da sauran ƴan uwansa. Dan asusu garesu na tara kuɗaɗe domin hakan kawai sai shekara ake ciresu ai hidimar taimakon bayin ALLAH. Oum kuma kaɗai tasan suna yin hakan.
Masu aiki sun kama aiki, Oum ta kaɗa ƴammatanta saloon da kitso. Mutuniyar taku dai nata daru, Oum tace babu fashi sai an mata. Itako aka fara wanke ma kan sannan akai kitso bamai yawan ba. Dan Oum tace a mata kaɗan tunda za'ai na tariya kwanan nan. Haka ma ƙunshi a yatsu kawai akai mata ja shike nan. Ta koma gefe yana sauke ajiyar zuciya ga haushin AA dama na cimata rai. Suma sauran duk an musu harda Oum, basu dawo gida ba sai la'asar, babu ɓata lokaci suka shiga haɗa abincin buɗa baki...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣7️⃣
______________
.......Alhamdullah ƙarfe biyar akace anga wata a saudia, yara suka fara murna da fatan ALLAH yasa a Nigeria ma a gani. Hakan kuwa akai, kafin ma tara sanarwa ya iso kunnen kowa daga Sarkin Musulmi cewar anga wata muma a Nigeria gobe salla. Ai fa tuni gida ya yamutse da murna. Zuwa tara sai ga AA ya dawo gida. Tunda ya shigo Maanal kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, yanda ƙannensa suka gaishesa itama ta gaishesa ne ta basar. Shi dai kallonta kawai yake ta ƙasan ido, Oum tace mizai ci ya miƙe yana faɗin,
“Komai ma na samu amma mara nauyi, bara naje na watsa ruwa Besty ta kai min can dan zata amshi saƙonta daga can, idan kinzo ina sama”. Ya faɗa maganar ta ƙarshe idonsa akan Maanal
Cikin rashi damuwa Oum data san da saƙon tace to. Shima sai ya fice bayan ya ɗan kalla Maanal ɗin karaf kuwa yaga hararar da take masa. Da sauri ya janye idanun yay gaba yana cije lips. Umarni Oum ta bata nata tashi ta haɗa masa abincin. Badan taso hakan ba ta amsa da to tana miƙewa. Shi ko AA sashen Abah ya nufa, acan ya samu Mamy tare da shi, ƙin yarda yay su haɗa ko ido. Kansa a risine ya gaisheta bayan ya gaida Abah. Idon Abah ya sakata amsawa kamar babu komai a ranta, amma ta ciki na ciki. Bai wani jima ba yace ma Abah zai je ya watsa ruwa yayi aski yana jin gashi duk a jikinsa. Abah ya sanya masa albarka ya fito. Sai da ya kalla sashen Oum sannan ya wuce nashi sashen.
★ Koda Maanal ta nema Najma tai mata rakkiya ƙi tayi, tace, “Tab, sokike Yaya AA ya koroni da tsarabar mari.” badan Maanal taso ba haka ta tafi ita kaɗai. Garin yayi sanyi sosai yau saboda hadarin da aka haɗa sai ya zama iska ba'ai ruwan ba. Sanye take da hijjab har ƙasa royal blue dayay mata ƙyau sosai, sai ɗan basket ɗin data riƙe na abincinsa. Tana gab da shiga idonta ya sauka akan Nibras dake zaune a barandar sashensu ta upstairs ko ubanmi take a wajen oho. Ɗauke kai Maanal tayi abunta ta cigaba da tafiya, batai wani zaman yin knocking ba ta shiga da sallama. Babu kowa a falon ƙasan kuwa sai dai ko'ina a gyare tsaf, har yanzu kuma dai sauran kwalayen kaya da ba'a gama shiryawaba suna nan. Saman da yace zata samesa ta nufa, duk da zuciyarta na wani ɗas-ɗas na tsoro tadai dake. Shiru falon saman ko wuta ma ba'a kunna ba, sai da ta haska fitilar wayarta ma sannan ta kunna wutar. Zama tai a kujera tana fatan fitowarsa, fin mintuna biyar shiru, gashi tana son zuwa ta kwanta kodan kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu salla. Akwai fita idi da wuri, kuma tana son ya barta ta wuce gidan Didi ta yini. Fahimtar bafa fitowar zai yi ba yasa ta miƙe, ƙofar ɗakin ranar taje tai knocking. Shiru babu ko motsi, sai ta tura ƙofar kawai ta leƙa. Babu kowa a ciki sai uban sanyin ac. Ɗan jimm tayi a wajen, sai kuma ta shiga kawai zuciyarta na raya mata ta ajiye masa kawai idan ma wanka yake in ya fito ai zai gani ita kuma sai ta koma falo. Tana maida ƙofar zata rufe kawai ta ganshi tsaye a wajen ashe bayan ƙofar ya ɓoye. Da farko ma ita tsorata tayi, dan har zata fasa ƙara yay saurin faɗin, “Hy relax! Hajiyar tsoro”.
Baki ta tura sosai, kanta a ƙasa saboda daga shi sai towel a ƙugu ta ce, “Haa'a to miye na ɓoyewa anan ɗin?”.
Gabanta ya taka ya tsaya, sai ta matsa baya saboda kusancin nasu yayi dab da yawa. Ƙara matsowa yay, itama ta matsa, sai kawai abin ya saka shi nishaɗi ya cigaba da binta har suka dangane da jikin katakon mirror. Sai data runtse idanu, sai kuma ta ɗaura duka hannayenta a katakon tai baya da jikinta kamar zata jingina da madubin. Shima nasa hannayen duk biyu ya dafe katakon mirror ɗin da su ya shiga biyota yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata amma taƙi yarda da hakan. A yanda ya ranƙwafo ɗin da yanda take sai yay kamar zai kwanto a jikinta, ga fuskarsu dab da juna suna busama junansu nunfashi.
“I miss you Everbloom”.
Ya faɗa cikin raɗa yana hura mata iska a kan idanunta. Wani yarrr taji a illahirin jikinta. Dole ta buɗe idannunta dake wani mar-mar-mar. A cikin nasan da yake so suka shige, tai ƙoƙarin janyewa ya hana hakan. Dole ta shiga gaishe shi lips ɗinta na ɗan rawa. Matsar da nasa lips ɗin yay ya sumbaci nata kaɗan. Sai kuma ya sake ɗagowa yana kallonta. Cike da raɗa ya ce, “Na sha?”.
Kanta ta girgiza masa alamar a'a.
“Why?”.
Ya faɗa a hankali idanunta a cikin nasa. Itama a hankalin tace, “Ba yanzu ba”.
“Sai yau she?”.
Duk da maganar na mata nauyi ta daure cikin raɗan tace, “Sai randa aka kawo maka ni”.
Murmushi ya saki mai sanyi tare da lumshe idanun ya sake buɗewa a kanta slowly. Yanzun ma ƙasa-ƙasa yace “Anya zaki iya cika alƙawuran da kika ɗauka wannan ranar kuwa Besty?”.
Murmushi tayi da jinjina masa kanta, sai kuma tasa hannu ta rufe fuskarta. A haka ta ce, “In sha ALLAHU duk zan iya. Kai dai kawai kayi fatan zuwan ranar”.
Ajiyar zuciya ya sauke mai fita a hankali, sai kuma ya miƙe da ƙyau ya kamota kawai ya rungume a cikin jikinsa. Bata hanashi ba, itama tai luf dan zuwa yanzu ta ɗauka ɗamarar zama masa mar'atussaliha in sha ALLAHU. Sun jima a haka kafin ya ɗagota. Fuskarsu ya gaɗe a waje guda goshinsu, hancinsu na gogar juna. Ɗan sumbatar lips ɗinta ya sake yi kaɗan, sai kuma cike da shagwaɓa ya ce, “Please my Babie nayi missing ɗinsu ALLAH, nayi kaɗan?”.
Cikin tata shagwaɓar ta ce, “Ai matsalan kai baka san kaɗan bane, kuma ma fushi nake da kai”.
“Nasan kina fushi dani shiyyasa zanyi lallashi ai.”
Kafin ma ta samu damar sake cewa wani abu ya mamane lips ɗinsu waje guda. Cike da nutsuwa da kewa ya fara sumbatar ta. Itama dai yau jin abun tai har tsakar kai, bama tasan ta fara bashi haɗin kai ba. Ya subahannallah ji AA yay kamar ana masa kiɗan general a sama. Baima san ya kamata ya ɗaga gaba ɗaya ya zaunar akan katakon mirror ɗin ba ya wani riƙe kanta da duka hannayensa biyu. Yi yake kamar zai haɗa har lips ɗin nata ya cinye kawai. Sunfi mintina shida a haka kafin ya haƙura ya rungumeta, itama rungumesan tayi tsam suna sauke numfashi a tare. Wata irin nutsuwa da farin ciki na zagayesu. Duk da shi dai oga AA ta ƙarƙashin ƙasa gobara ce ke niyyar tashi. Amma dai yanata ƙoƙarin tausar zuciyarsa da lallashin gangar jikinsa. Sai ALLAH ya taimakesa ya ɗan samu lafawar yanayin nasa a wannan rungumar. Maanal ce ta fara ƙoƙarin janye jikinta, bai musa ba shima ya barta. Sam taƙi yarda ta kallesa, kanta a ƙasa, jitake kamar ta nutse a wajen dan kunya. Cikin wani irin nishaɗi AA yaja hancinta kaɗan tare da sumbatar gefen fuskarta sannan a raɗa yace, “Sarkin kunya”. Murmushi tayi tana ƙara duƙar da kanta. Shima sai ya bar wajen yana murmushin. A zuciyarsa ko mamakin canjawarta yake yau. Dan zai iya cewa bata taɓa bashi haɗin kai yayi yanda yake so cikin salama irin yau ba. Duk da dai kunyar na nan babu abinda ya canja. Jallabiya ya sanyo a jikinsa, sannan ya dawo inda take. Cak ya kamata ya sauke daga saman mirror ɗin, sai kuma ya kama hannunta suka nufi bakin gado. Sai da ya zaunar da ita sannan ya zauna shima. Cike da kulawa ya ce, “Bani abincin yunwa nake ji”.
Kanta kawai ta jinjina masa, ta jawo basket ɗin abincin ta zuba masa kunu, sai farfesun naman talo-talo da sukayi. Sai uban ƙamshi yake gashi gwanin sha'awa a ido. Kunun kawai ya amsa, naman ya buɗe mata baki alamar ta bashi. Ƙaramar harara tai masa, sai ya shagwaɓe fuska. Ta dungure masa kai tana murmushi. “ALLAH Besty ka canja hali”.
Murmushi yayi mai ƙayatarwa, zai yi magana ta zuba masa naman data ɗebo a bakin dole yay shiru ya shiga taunawa. Sai wani kallonta yake, dan ji yake kamar an canja masa ita. Alhamdullah addu'arsa ta amsu kenan. Dan kusan a ittikafin nan addu'oi sa akan Maanal ne. Yaci naman sosai, itako da ya nuna zai bata tace masa ta ƙoshi taci abinci. Bai takura mata ba. Wani ƙyaƙyƙyawan leda dake gefen gadon ya jawo gabanta.
“Ga kayan sallarki tashi ki gwada”.
“A ina ɗin?”.
Ta faɗa tana waro idanu waje. Cike da tsokana yace, “A gabana mana, ba mijinki bane?”.
“Hu'um ALLAH bazan iya ba. Kadai bari naje sashen Oum duk wanda na gwada zan maka hoto”.
Murmushi yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan laɓe baki yana fara fiddo kayan da faɗin, “Ni za'ama wayo kenan. To naƙi ɗin”.
A marairaice ta ce, “Please Yaya AA”.
Dariya yayi, sai kuma ya dakata da fiddo kayan yana kallonta. “Ni dai wannan yaya da aka saka min bai ma ko dace da ni ba. A kirani da Besty na nafi so”.
“Oh dama ka samu nake cemaka Yayan”.
“Na yafe bana so. Tunda dama badan ALLAH kika fara faɗa ba ko a waccan ranar”.
Kanta kawai ta juyar tana murmushi batace komai ba, sai kayan data fara amsa tana dubawa. Kala biyar ne, duk kuma sunyi ƙyau dan sun sami ɗinki na nutsuwa kuma mai ƙyau. Godiya tai amsa sosai da addu'a. Yaji daɗin addu'ar tata kuwa... Dai-dai nan Oum tai kiran wayarsa. Yana ɗagawa tace, “Auta turo min yarinyata tazo ta kwanta da safe ba wani isasshen barci za'a samu ba”.
Sai da ya ɗan murmushi yana kai hannu ya shafa fuskar Maanal ɗin sannan ya ce, “Okay Oum gata nan zuwa”. Daga haka ya sauke wayar. Kayan ya maida a ledan ya ce, “Tashi muje na rakaki kafin Oum ta biyo sahu”.
Dariya Maanal tayi, shima yana murmushi suka fito hannunsa ɗauke da ledan ita kuma basket ɗin. A compound daga can jikin motoci Maanal ta hango Najma da Yaya Fawzan. AA da sam hankalinsa bai kai wajen ba ta taɓa. “Besty kalla”.
Juyawa yay ya kalla inda ta nuna ɗin, aiko yay wani tsai yana kallon ikon ALLAH. Maanal dake murmushi tace, “Mika fahimta?”.
Maimakon bata amsa sai ya kama hannunta suka nufi wajen. Babu zato kawai su Yaya Fawzan suka gamsu. Daburcewa Najma tayi, dan suna tsoron AA sosai saboda ba sabgarsu yake shiga ba. A ɗan rikice taima Maanal alamar miyyasa ta bari yazo. Murmushi Maanal tayi,