AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   151 / 213

450K to 453K   out of 636.6K words

dafe wajen tana tura baki. Shahidah ta sanya dariyar mugunta, ƙasa-ƙasa tace, “Maganin mai gulma kenan”.
      Harararta Amal tayi. Shahidah ta taɓe baki. Sai kuma ta ɗan duƙo saitin kunnen Amaal ɗin tana faɗin, “Nifa tunda muka iso kallo ɗaya na mata nace lallai su Ajwaad sharpshooter”.
           Amal tace, “Na gaske kuwa. Dama irin miskilan nan ƴan babu sauƙi ne. Damƙa ɗaya sukema mace suyi bugun daga kai sai mai tsaron gida”.
    Baki suka gimtse suna dariya. Sai da Ammie ta musu magana suka nutsu suna sauraren lecture ɗin yanda ya kamata. Lokacin da ake tashi dan yin sallar la'asar da ƙyar Oum ta tada Maanal, tana idar da salla ta haye gado ta kwanta. Amaal zata tada ita Oum tace ta barta gara tai barcin anjima a samu ta tashi. Sun dawo an cigaba da lecture AA ya kira wayar Maanal dake hannun Amaal, ɗagawa tai, daga can ya furta, “Zuciyar Ajwaad!”.
     Murmushi Amaal tayi, cike da tsokana tace wannan ƙanwar Ajwaad ce, zuciyar Ajwaad ɗin na barci”. Idanu AA ya rumtse daga can, dan sarai ya gane Amaal ce duk da muryarta na kama data Maanal ɗin sosai. Kamar zai yi magana sai kuma ya katse kiran kawai. Dariya Amaal da Shahidah suka sanya.....

Ƙarfe biyar aka tashi daga walimar, aka maida Ameerah gida domin shiryota. Itama Maimoon aka wuce da ita sashen Oum dan shirya ta. Maanal dai ba'a san mi duniya ke ciki ba tanata barci. Gasu AA sun dawo gida ya shiga sashensu sai su Shahidah kawai ya samu da su Rufaidah, su Sumayya, su Mufeeda matan su Giɗaɗo su Nuwaira, duk dai yaran matan nan ƴaƴa da iyaye, ƙanne da ƴaƴaye sunata shan shaftarsu cike da nishaɗi da yin fashin baƙi akan lectures ɗin yau. Kaya kawai ya hau sama ya canja dan hayaniyarsu bazata barshi zama ba. Haka ya sakko ya sake ficewa ya barsu ransa duk kewar Maanal. Kwata-kwata ƴan awoyi ne bai ganta ba amma duk ya damu. Koda ya nufi sashen Oum ya fahimci bai shiguwa, dole ya haƙura nan ma ɗin ya nufi can waje inda su Fawzan suka saka tabarmi a bishiwun kan layi da kujeru...

         Maimoon da Najma sunsha nasiha a wajen iyaye, dan sashen Abah aka kaisu aka sakasu tsakkiya kowa na nashi duk da kasancewarsu jikoki. An musu addu'oi da gargaɗin zama lafiya da abokan zamansu kafin a fito da su. Najma an maidata sashenta Maimoon aka fita da ita gidan Hajiya Shuwa. Tarba ta mutuntawa akai musu, kowa na maraba da zuwan Maimoon ɗin. Tare da mata addu'ar zama mai ƙyawun hali daya banbanta da matar Ameer ɗin. Daga haka aka miƙata sashenta. Sai suma suka fara shirin kawo Ameerah. Itama dai tasha tata nasihar da gargaɗin iyaye da addu'oi. Itama haka aka kawota tana shan kuka, sashen Oum aka fara kaita suma aka tarbesu da girma da mutuntawa sannan aka kaita sashenta dake cike da dangin su Saheeba na ɓangaren su Mamy dana ɓangaren Babbansu da suka iso yau suma. Suna sama wai suna jiran a kawo musu amarya sukaji tsitt an shige da ita ɗakinta. Zasu fara ƙananun magana Hajiya Turai ta tsawatar. Dole sukai shiru sai ƴar gunguni da gulmar dake ƙara zafafa zuciyar Saheeba. .........✍️



🤭🤭🤭Saheeba ayi hakuri dai



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣9️⃣


______________



.......Dan ana cewa an shigo da amarya ta duƙe ƙasa sai hawaye. Dama yau haka ta yini cikin ɓacin ran nan, koma ace tun daren jiya data gama shirya ma Babban Yaya kanta ya zabga mata tsiya ya kulle kansa a ɗaki, bugawar duniya yaƙi ya buɗe dole ta haƙura taje ta kwanta tana matse ƙafafu da kwasar kuka sosai, dan shaye-shayen abubuwa tai emargency a tunaninta tunda Yaya Fawzan ya sasantasu zai nemeta balle taga kusan wata guda, yanda ta sanshi da mace. (😂Saheeba kinyi Gwari, Babban Yaya amarya yakema tanadin betar nan🤭🏃).
          
      Duk wannan bidirin da ake na kai-kawon amare Hajiya Maanal bata san anai ba. Dan bata tashi farkawa ba sai kusan goma. Shima yunwa ce ta isheta a cikin barci dan yinin yau duka bazatace ga tsayayyen abinci da taci ba. Madara kawai take ɗurama cikinta in ma taji yunwar ta isheta. Ganin ta tashi Ammie tace ta wuce ta tafi sashenta mijinta tun ɗazun yake zarya. Cikin rashin damuwa tace, “To Ammie tashi muje, kin san dai kin min alƙawari zaki kwana a sashena idan kika zo, jiya ban san kinzo ba kinga yau sai ki je can ki kwana ki cika alƙawari”.
        Ammie da taɓarar Maanal ta girmeta ta ce, “To naji, tashi kije zanzo idan na gama abinda nake yi.”
    Shiru Maanal tayi kamar dai bata yarda ba, sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Ammie idan naji shiru zan dawo fa. Ina su Didi?”.
       “Waɗan nan sun wuce babu jimawa su da su Rufaidah. Sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu”.
    “Acan su aunty Rufaidahn zasu kwana suma?”.
    Ammie tace, “Eh”.
Ajiyar zuciya Maanal tayi, tare da ɗaukar mayafinta da wayarta ta fita. Ammie ta bita da kallo tana murmushi. A ranta kam jinjina wa take wai Maanal da ciki, lallai za'aga iyaye kuwa sarakan wauta. Dan ga uwar har uban autanci ya sakasu zama sai a hankali. Ta wani fannin ma gara AA ɗin. Amma Maanal humm ALLAH dai ya ƙyauta. Yanayin rainon da Ajwaad ɗin yay mata da su Babban Yaya da Oum dama su Shahidahn yasa ta tashi a muguwar shagwaɓaɓɓiya, al'amarin can ne ma daya gitta fa ya ƙarfafata harta zama jaruma akan rayuwarta. Ta riga ta taso ne a tsakkiyar gatan da a lokacin ita ce ƙarama gaba ɗaya a tsakaninsu. Kowa ya kwaso gatansa Maanal ce dai. Shiyyasa har yanzu bata kallon su Hameed a ƙanenta, wani lokacin ma Hameed ɗin ne ke haƙura ya zama Yayan, balle yanzu daya yake neman isketa a tsaho da girman jiki Abinka da namiji...

AA na zaune da Oum suna magana a compound sai Yaya Fawzan a tsaye da isowarsa kenan wajen Maanal ta fito. Oum data fara hangota ta ce, “Baby ta tashi kenan”. Inda Oum ɗin ke kallo ya kalla. Shi dai Fawzan hankalinsa nakan waya ne dan suna charting da Najma. Lallaɓata yake ta fito ta samesa a mota ita kuma tace kunya take ji dan tare take da dangin babanta a sashen. Ga kuma ƙawayenta suma.
     Ganin yanda Maanal ke ɗan dafe bango Oum ta ce, “Auta tashi kaje ka kamata barcin can bai saketa ba. Da alama Ammienku ce ta korota”.
      Murmushi AA yay da jin ƙaunar Ammie a ransa. Dama shigar da yay sau biyu taso tada Maanal ɗin Oum ta hana. Yanzu kam taga ba Oum ɗin ta koro masa ita. Ji Maanal tai kawai an riƙota, dan haka ta ɗago tana kallosa da lumsassun idanunta. Wani yarr yaji a jikinsa dan idanun sunyi kamar wadda tasha wani abin maye. Sun kuma ƙara girma. Dama abu kaɗan ke takalo ƴan maza ai. 
       A cikin maƙoshi ya ce, “Miyasa baki kirani a waya nazo na goyaki ba?”.
        Jikinsa ta shige ta rungumesa, muryarta na fita cikin sanyi da yanayin wanda ya tashi a barci ta ce, “Ba Ammie ce ta koroni ba. Besty yunwa nake ji, muje zanci abinci”.
     Tausayi ta bashi, cikin sauke ajiyar zuciya ya ɗagota daga jikinsa dan yasan su Oum na kallonsu, cike da kulawa ya ce, “Baki ci abinci ba yau halan?”.
     Kai ta jinjina masa, sai kuma fuska a yamutse tace, “Ka goyani nidai muje naci”.
      Sashen da su Oum suke ya kalla, sai yaga Oum ta tashi ma bata wajen, sai Yaya Fawzan, ya wani ɗage masa gira kuwa. Hararasa AA yayi ya ɗauke kai, ya juya Maanal da sam bataga Yaya Fawzan ɗin ba ta haye bayansa. Fawzan dake ɗaukarsu video yay murmushi. Haka ya dinga binsu da camara har suka shige sashen su...
  
      Baki buɗe Maman Yaseerah ke kallon Hajiya Basariyya, dan suna a compound ɗin ne zaune suma sunata gulmar abubuwan dake faruwa a gidan. Dan yau dai anan zasu kwana jiya Abdull rashin kunya ya zuba musu ashe. Harda marin Yaseerah a gabansu dan tayi magana. Mamanta tace tazo su tafi Yaseerahn tace aa. Shine suka baro gidan ransu a ɓace da sassafe ko sallama basuyi da ita ba. Sun zata zata biyosu amma har dare yau ko gidan bikin ma bata leƙo ba. Kuma shi Abdull ɗin yazo dan ɗazun sun ganshi har cikin gidan ya shigo ma.
        “Yau naga iskanci ganin idona? Kaga tantiriyar yarinya”. Cewar Hajiya Basariyya ranta fal baƙin ciki da hassada. Maman Yaseerah ta ce, “Hummm, aini abin ma ya girmi kaina. Jiba fa ɗazun abinda yay akan ɗakko mana abinci da tai. A dole yaron nan yaƙi Huznah dan ya shawu matuƙa gaya. Jarabahhh”.
       Takaici ya hana Hajiya Basariyya sake magana. Sai kallon sashen su Maanal ɗin take, jitake kamar tabi bayansu taga mike cigaba da faruwa kuma. Oho Maanal da AA ɗin ma basu san sunayi ba, sunyi gaba sun barsu da hasashen zuciya mai dawwamar da takaici. To ashe bama su kaɗai ba. Harda Nuratu da Hajiya Turai dake can suna nasu zaman idonsu ya gane musu komai. Nuratu harda hawayenta. Tana sake tabbatarma zuciyarta bazata taɓa yafema Maanal ba sai ta mata illa wlhy. Dan ko auren AA tayi tarigata shanye komai ai..
     A can ma sashen Nibras da ƙawarta suna a window ɗin bedroom ɗinta ne suna kallon komai. Dama tun ɗazu suna kallon AA ɗin ne da Oum, ƙawar tata na sake tunzurata da jinjina ƙyawun AA ɗin da ajinsa. Can kuma sai ga Fawzan. Yayinda hankalin Nibras ke akan AA ita ƙawarta nata akan Fawzan yake a ranta ayyanawa take (Shasha mijinki ma mijine ɗan gaske. Miye marabarsa da ƙanin nasa? Sai dai ya nuna masa miskilanci da murɗewar jiki. Ni ko mijin naki na samu wlhy dafewa zan. Kuma ko yanzu ma zan gwada sa'a ta, kina yin waje zan shigo a madadinki wlhy. Wannan daular dolene a cita dani tunda ke baki san inda ke miki ciwo ba keda uwarki. Koda yake ita kishi take tayaki bata san haukan dake a zuciyarki ba nason kanin mijinki dana tabbatar ko kallo baki isheshi ba yanda yake ji da kansa ɗin nan). Can kuma abinda ya faru tsakanin AA da Maanal itama sai da ya motsa mata zuciya ya tafi da imaninta. A ranta ta sake ayyana (dole ki haukace ƙawata, da ganin guy ɗin nan dan son rayuwa ne. Yanda yake a murɗen nan kuwa zai matuƙar bada ma'ana a shimfiɗa. Sai dai itama matar tasa ta haɗu wlhy sun matuƙar dacewa da juna. Wanda keda wannan zillaziyyar black beauty ɗin mai dirarren jiki babu yanda za'ai kam ya kalleki koda kike fara tas, dan mazan da suka san sirrin baƙar mace da wahala kiga farare na zame musu koda abin kallo). Zungurin da Nibras tai mata ne ya maidota a hayyacinta.
       “Ikon ALLAH wai mi kike tunani haka?”.
     “Hummm ta yanda zamu ɓulloma guy ɗin nan mana. Da alama na fahimci yana son matar nan tashi. Duba fa a filin subahana ya duƙa ta ɗane bayansa”.
       “Humm kaɗan ma ai kika gani, yarinyar nan ai shegiya ce ta bugawa a jarida. Wlhy idan muna zaune gaba ɗaya baya jin kunyar kallonta. Abinci a plate ɗaya suke ci har a gaban surukanmu. Haka zakiga suna laluben juna ta ƙasan table. Wlhy wani lokacin sai naji kamar na zuba mata guba ta mutu mu huta”.
     “A'a rufama kanki asiri hakkin rai ba wasa ba. Mudai rabata da mijin ki mallakesa ta ƙara gaba hakan ya wadatar”.
        “Hakane, abinne da takaici wlhy, ga wata shegiyar kuma ta ƙaru.”
     Dariya ƙawar tata tai da faɗin, “Kina fa son mijinki wlhy matar nan. Sha'awar ƙaninsa ce kawai ke rinjayar zuciyarki”.
      “Sha'awa kuma?”.
  “Kwarai ma kuwa. Dan tabbas da ace zai yadda ya kasance dake ta bayan fage kema zaki ji kina son cigaba da zama da yayansa. Dan ba son Fawzan bane bakiyi, kawai dai ƙarfin sha'awar kasancewa da AA ce ta danne soyayyarsa, saboda kishinsa a bayyane yake cikin idanunki”.
     Shiru Nibras tai tana kallon ƙawar tata da tunani, dan maganar ta shige ta kwarai da gaske. Dan tabbas tana jin kishin Najma sosai a ranta. Idan taga Fawzan na rawar kai a kan yarinyar jitake kamar ta kamashi da duka. Idan kuma ta tuna zaifa kwanta da yarinyar daga yanzu zuwa ko yaushe tana jin ƙirjinta yay mata nauyi sosai...........✍️


Tofa Nibras ya take ne🤭🤣.

Kumin addu'a na dage da baku 5pages ɗin nan mu samu mu gama. ALLAH na fara gajiya🤭🏃🏃


*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣0️⃣


______________


.......Washe gari amare sun kwana sun hantse a ɗakunansu Najma ma nada biyu. An tashi da shirye-shirye lunch da aka canja dinner da shi saboda wasu dalilai. Za'a fara ƙarfe ɗaya a tashi 4. Zuwa biyar ai buɗar kai. Zuwa sha biyu mai kwalliyar data ma Maanal a bikinta ta iso. Dan itace zataima amare. Sai da ta fara yoma Maimoon sannan ta shigo nan yima Ameerah da Najma da aka kawo nan sashen Maanal dan anan zasuyi shiri.
      Ya subahannallah jama'a kunga amaren kuwa. Nace kunga amaren na Babban Yaya da Yaya Fawzan kuwa. Auwwww itafa amarya kota gunki ce daban take mutanena. Matuƙar ƙyau sun fita da fitarsu. Dogayen rigunansu na lass zanen iri ɗaya, sai dai kowanne da kalar nashi. Maanal ta sakasu gaba da hotuna da tsokana harda videos. Mai kwalliya dake musu dariya tace, “Ai kema yanzu zan matseki na miki tunda baki gama amarcin ba”.
      “A'a Aunty rufa min asiri, ga dai amare nan sabbi fill a leda. Ai yau Babban Yaya da Yaya Fawzan nada bidiri”. Ta ɗagawa su Najma gira. Gaba ɗaya sai Najma taji ta sake tsurewa. Dama Yaya Fawzan duk ya rikita mata lissafinta, dan tun jiya data biye masa bazai ɗaga mata ƙafa ba. Dan hoha ya fito ya nuna mata a matse yake. Badan harda iyaye a wanda ke tare da ita ba ALLAH babu abinda zai sa ya barta ta sani. Ita dai uhum bata sake cewa ba tunda ya tura mata wannan vn ɗin. A jiya proud ɗinta ya ɗauke, wanda taita addu'ar yafi haka kwanaki amma addu'ar tata bata karɓu ba dan ta fara tun kwana biyu kafin a kawota. Ita dai Hajiya Ameerah da sauƙi, da yake shi babban Yaya babba ne yana ɗan fiskewa. Dan tunda ma aka kawota gidan bata ganshi ba sai yanzu ne dai zasu haɗu. Sai waya daya kirata sukayi jiya da daddare. Kuma gaisuwa ce kawai da ƴar hira sama-sama dan har yanzu bata iya sakewa da shi sosai. Mai kwalliya na fita bayan tama Maanal ƴar kaɗan a fuska Najma ta jawo hannun Maanal ta zaunar a tsakkiyarsu. Idanunta na cikowa da ƙwalla tace, “Dan ALLAH Maanal ba rashin kunya ba ki faɗa mana da wuya ko? Wlhy gaba ɗaya a tsorace nake. Dan Yaya Fawzan yace nama shirya babu ɗaga ƙafa. Har bana son yau ayi buɗar kan nan”.
      Dariyar mugunta ce ta zoma Maanal, tadai dake da ƙyar tana kallon Ameerah da itama ta zabga tagumi. “Kai ALLAH ku kwantar da hankalinku babu komai fa.”
     Ameerah tace, “Daina cewa babu komai Maanal, kefa har ɗinki akai miki kika sha jiyya ta kwanaki. Yaya AA dake ƙaninsu fa kenan, ta bakin Najma ALLAH koni bana son a gama bikin nan yau sam”.
     Yanzu kam kasa haƙuri Maanal tai ta shiga kwasar dariya mugunta fal ranta. Saida tai mai isarta taga suna shirin mata kuka sannan ta tsagaita. Wata na ƙoƙarin zuwa mata ta kare bakinta da hannu tana faɗin, “Shike nan na bari na bari. Kun san ALLAH ku kwantar da hankalinku. In sha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Sannan ku auna shi Besty fa saurayi ne maybe shiyyasa bai bini a hankali ba. Amma su Yaya sun san komai in sha ALLAHU zasu biku a hankali”. Sai kuma ta kwashe da dariyar tana miƙewa, tace “Ƴan iska kuna son soyayya amma kuna tsoron first night. Ai yau wasu zasu sha kuka”. Rige-rigen ɗaukar pillow Ameerah da Najma sukai tare da jeho mata. Ta fice da gudu tana dariyarta batare data lura da AA ba. Sai da ya kamata ya riƙe sannan...
    A ransa faɗi yake, (Ni ɗan Aliyu da Fateema naga takaina, ya rabbi indai da wannan ciki da muke hasashe ALLAH ka bashi kariya daga ɓare-ɓaren Besty). A fili kam kallonta kawai yake tana dariyar ƙasa-ƙasa kanta a jikinsa. Dan ko taso ta tsagaita data tuna yanda idanun su Najma sukai zuru-zuru sai taji wata tazo mata sabuwa. Kamata yay suka haye sama har

151 / 213

Chapters