AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   165 / 213

492K to 495K   out of 636.6K words

irinsu alkaki, cin-cin da sauransu. A table ta ajiye, tsakkiyarsu shi da Yaya Fawzan ɗin, sannan ta zuba shayin ta miƙama mijinta shi kuma ta ajiye a saitinsa tana faɗin, “Yaya bismillah ga shayi maganin sanyi”.
     Murmushi sosai Yayan Nibras yayi, yarinyar na wani irin birgesa, eh lallai dole miji yaji ya daina son ƙanwarsu kam, irin wannan mar'atussaliha haka. Najma da bata san yana yi ba ta zauna tana gaisheshi, ya ko amsa mata tare da mata murnar aure, yay musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a masu albarka. Kan Najma a ƙasa ta kasa amsawa dan kunya, daga ƙarshe tama miƙe zata bar musu wajen Yayan Nibras ɗin ya ce, “Kiyi haƙuri idan ba damuwa ki zauna. Dan nazo ne wajenku ke da mijinki”.
    Babu jayayya Najma ta juyo sai dai bata zauna ɗin ba ta tsaya tana kallon Yaya Fawzan alamar jiran umarninsa. ALLAH sarki Yaya F. Sai yaji wani irin sanyi da nutsuwa na ratsa masa gaɓɓai. Zuciyarsa na wani irin narkewa yay salon nasu na gado, wato lumshe idanu da buɗewa a kanta ya jinjina mata kai alamar amince mata. Sai itama ta lumshe masa nata idanun alamar godiya taje ta zauna. Ai sai yayan Nibras yay sumar zaune yana kallon tsagwaron girmama juna da soyayya mai natsuwa, tausayin ƙanwarsa da gaba ɗaya yake tamkar tazarar kudu da arewa tsakanin halayenta dana wannan amarya ya sake kamashi. Dan ya tabbatar ko yanzu tace zata gyara ta riga tayi loosing. Jiba fa gaishe da Fawzan ɗin ma batai ba, shi ko ko kallon inda take baiyi ba, sai ma ka rantse bai ganta ba a wajen..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣3️⃣


______________



........Shigowar Haule ce ta taimaki Mamy, ita ta kamata da ƙyar ta hau da ita a saman gado bayan ta bata ruwa tasha, kamar hawayenta jira suke Haule ta fita suka fara zuba sharrr, karo na farko kenan da duk fara wannan kai-kawon da badaƙala hawaye suka zuba a idanun Mamy kamar haka. Zuciyarta ta daɗe kafin tai babban motsi a cikin ƙirjinta. Tama rasa yanda zata fassara al'amarin. Junaid fa yana raye, Junaid dai Junaid data gama rufe babin rayuwarsa gaba ɗaya kuma tayi imani da hakan. Tayama za'ace mata Junaid yana raye? Sannan wannan yaron wai ɗan nan ne data haifa ita kaɗai bayan ta raini cikinsa ita kaɗai, taje ta yarda shi cikin tsakiyar dare ita kaɗai. Mi rayuwa take son nuna mata ne a wannan gaɓar? Mi tarihi yake son dawo mata da shi ne? Wane waiwaye ake son bayanta tayi a lokacin da tagama yarda tayi gaba, gaba irin na har abadan. A yanzu fa itace matar Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Fadeel Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Fawzan Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Jiga-jigan murahu uku fa gareta, tare da basamudiyar tukunya a samansu. Hakan na nufin yanzu a kan gaɓar yin GUDU DA WAIWAYE zata kasance? Sai wasu hawayen sharrr-sharrr. A hankali ta lumshe idanunta dake tsaye ƙyam suna kallon zanen haɗaɗɗen pop ɗin rufin ɗakin, tamkar ana tariyar film tuninta ya fara komawa baya-baya harya tsaya cak a inda take buƙatar ganinsa...
      (Idan masu karatu basu manta ba mun tsaya a tunanin Mamy na waccan ranar dai-dai inda Junaid ke matsayin malamin su....)
    _____Matuƙar gundura da halayyar Uncle Junaid ƴan ajinsu sunyi, dan haka sukai gangamin kai ƙararsa wajen principal. Sai dai maimakon su ciwo nasara ɗan karen duka suka ciwo. Wannan abu da akai musu ya ƙona ransu matuƙa, dan haka manyan ƴan iskan cikinsu irinsu Kamila da ire-iren ƙawayenta da samarinta suka haɗa meeting a wajen makaranta domin maganin Uncle Junaid. Sai dai basu samo hanyar da zasu aiwatar da shirin nasu cikin sauƙi ba, dan sun aminta koda an gane sune bayan sun aiwatar ɗin ba damuwarsa bace, iyaka dai ace za'a koresu ai daga makarantar. Sun haɗa tsahon kwana uku suna neman hanayar data dace, sai a ranar alhamis ɗin ƙarshen sati wani a cikinsu ya samo mafita. Kamar yanda suka saba bayan an tashi sun fito zasu tafi gida suka wuce inda suke haɗa meeting ɗinsu. Wanda ya samo mafitar ya zayyane musu komai, babu wanda ya musa hakan yay musu ɗari bisa ɗari, dan kuwa basu da wata hanya idan ba wata a cikin matan ta ƙulla soyayya da Uncle Junaid ɗin ba. Dan haka a cikin su Kamila akace wacece zatayi?. Da farko duk shiru sukayi, sai zuwa can wanda ya kawo shawarar yace, “Babu wadda zata dace da wannan aikin sai Amila (Haka suke kiran Kamila a lokacin) dan itace keda innocent face da bazata tona ma kanta asiri ba, kuma sai yafi aminta da ita sosai, bakwa ganin yanda dama yake ƙoƙarin son ganin ta gane karatu a duk sanda yayi”.
     Anan ne wanda ke matsayin saurayin Kamila yace bai yarda ba, aka kaɗa dambu taliya yace bai fa yarda ba, har abin yaso zame musu rikici aka tashi baran-baran babu wata matsaya. Har aka dawo hutun ƙarshen mako babu dai-daito, satin ma ya kusa ƙarewa, tsautsayi yasa ranar juma'a Uncle Junaid ya basu assignment ya kuma tabbatar musu duk wanda baiyi ba zai sha mamaki. Bako suyin ba dan gadara, aiko ranar Monday ya amsa, da yake shima muguntar ya shirya saboda ya tsani yaran dan basu da kunya a cikin ajin ya duba assignment ɗin nasu yay amfani da period ɗinsa gaba ɗaya, ya kuma amshi ta malamin da zai shigo next. Haka ya zage ƙwanji yaci uban wanda basuyi ba daga mazan har matan, babu abinda ya dame shi da ƙanƙantar shekarunsu, dan a lokacin kaf ɗinsu basu wuce 15+ ba. Sai da ya jigatasu iya jigatawa da punishment, musamman ƴan group ɗin su Kamila sannan ya barsu, tare da basu suspension na sati biyu.
      A cikin wannan suspension ne suka ƙulla yanda Kamila zata shiga jikinsa dan saurayinta ya amince, itama kuma ta amince. Dan haka sai gasu sun dawo makaranta ranar da suspension ɗin ya ƙare kowa da iyayensa, sai dai Kamila ita ɗaya tazo ta zabga ƙarya wai babanta yayi tafiya shida mamanta kakarta kuma bata da lafiya. Har za'a sake komar da ita sai cikin iyayen sauran ya hana, yace ai ɗa na kowane shi ya wakilci baban nata, tunda har tai hankali ma ta dawo ai Alhamdullah. Wannan shine mafarin dawowar su makaranta, suka kuma nuna sun nutsu saboda nasihar da akai musu iyaye da malamai, idan Uncle Junaid ya shigo zakaga sun bashi dukkan hankalinsu, duk aikin daya bayar na aji ko na gida basa lattin yi koda baiyi dai-dai ba, a haka Kamila ke saka wasiƙar soyayya ma a nata littafin ma Uncle Junaid. Bai taɓa nuna mata yasan tanayi ba, duk da kuwa yana ganin wasiƙun kuma yana karantawa. Har sai da ya kammala hidimar ƙasarsa lokacin zasu shiga ss2, basu san ya kusa gamawa ba sam, aiko sunyi baƙin ciki sosai musamman Kamila dan a wannan gaɓar fa da gaske ita ta fara jin son Uncle Junaid ɗinne. Aiko haka ta rubuta masa wasiƙa mai ban tausayi ta bayar aka kai masa, ta kuma tabbatar masa in har yabar makarantar itama ta barta kenan. A karo na farko daya saka aka kira masa ita kenan, koda taje ta samesa a ƙasan bishiya da yake zaune tana duƙawa gabansa sai ta fara kuka. Tsayawa yay kawai yana kallonta na tsawon lokaci, kafin zuwa can yay kiran cikakken sunanta. Kanta a ƙasa ta amsa masa. Sake kiran sunanta yay a karo na biyu, yanzu kam sai ta ɗago tana kallonsa. Shima kallon nata yake a cikin ido, kuma sosai yaga soyayyar da take masan, sai yay murmushi da faɗin, “Kamila shekararki nawa?”.
       “Sha biyar da wata bakwai”.
   “Miyasa kike sona?”.
Shiru tai na tsawon lokaci tana wasa da yatsun hannunta. Kafin a hankali tace, “Zan gaya maka gaskiya, amma dan ALLAH kada kayi amfani da hakan kace bazaka soni ba ko zaka hukunta ƴan uwana.....”
     “Karki damu ina saurarenki, na miki alƙawarin kuma bazanyi komai ba, idan kuma har na gamsu zan amshi soyayyarki”.
    Cikin farin ciki matuƙa da jin kalamansa ta warware masa komai na shirinsu, ta kuma rantse masa ita sonshi take a yanzu da gaske. Ko karatu yace ta bari a yanzu zata bari suyi aure”.
     Shi dariyama ta bashi sosai. Shi yana shekara ashirin da huɗu a lokacin ita tana sha biyar da wata bakwai take maganar aure. Yo a gidansu yace ma aure yake so ai maybe sai an zanesa tsaf, dan ƙa'idar babansu sai ka gama karatu kayi hidamar ƙasa ka fara aiki da kasuwa, ka kuma cika shekara talatin ciss a duniya sannan ake maka aure. Amma yayunsa biyu hakan, kuma sun girmesa sosai, a yanzu hakan ma akwai mata biyu a tsakaninsu. Amma zai amsheta dan zatai masa amfani. Ya amshi soyayyar ta, ya kuma bata ƙaramar waya yace ta ɓoye zaiyi magana da ita idan ta koma gida kafin ya samu lokaci yazo gidansu. Tayi murna da hakan sai dai maganar zuwa gida ta tayar mata da hankali, dan tana tsoron kar yaje gidansu yaga ita ba ƴar kowa bace ya canja shawara. (Wlhy ƴan uwa mu kiyayi raina tushenmu. Dan an haifeka a ƙauye, ko iyayenka talakawa ne, ko sunada wata nakasa ta jiki kama dinga jin inama basu bane iyayenka, ko kaita ƙoƙarin hidden wannan ni'imar da ALLAH ya baka kuskurene. UBANGIJI ya fimu sanin abinda ya dace damu, haihuwarka a birni ko gidan masu kuɗi ba shine nasarar rayuwa ba, babbar nasarar nagartattun iyaye da zasu baka tarbiyyar da wataran zaki fito cikin birnin kifi wanda aka haifa a ciki komai, ko ka fito cikin gidan talakawan, kafi wanda aka haifa gidan arziƙin komai. Ku koma tarihi mana, suwaye ANNABAWAN mu. Yo ko a wannan duniyar kabi silsilar su masu arziƙi zaka samu a asali ai talakawane kuma suna da ƙauye, hakama wanda aka haifa a cikin birni, kai su kansu biranen fa da ai ƙauyuka ne, yau da gobe ce ta maidasu birane. Maida hankalinki wajen samun dawwamamen birni da yafi ko ina ƙawa da ni'ima wato aljanna dan shi wannan na duniyar na zaman ɗan lokaci ne, shi wannan arziƙin da muke fafutukar nema wasu ta hanyar halak wasu ta hanyar haram rana ɗaya zai zama tamkar bamuyi ba. A DUK YANDA UBANGIJI yayimu mu gode masa muyi alfahari da wannan NI'IMAR sai ya ƙara mana da wadda ta fita tunda ba biyansa muke ba balle muce ya mana yanda bama buƙata. Yau ina fir'auna, mi mulkinsa da izza ta amfana masa? Ina Qaruna, mi dukiyarsa da alfaharin arziƙi ya tsinana masa. Ina mutanen Annabi Luɗu, mi saɓonsu ya amfana musu. Ina jiga-jigan tsinannun kafiran makka irin su Abu lahab, mi gadararsu da rigima da son ƙuntata MANZON ALLAH ya tsinana musu. Idan zamu zama na ƙwarai mu zama, dan babu mai tayaki kwanciyar kabari ko amsar sakamakon hisabinka a ranar sakamako. Hasalima masu taya maka ka aikata ɓarnar kai da su tsine-tsine zaku dingama juna, to miya amfanin alaƙar da ba'a gina domin ALLAH ba. Miye ribar ɓata lokaci a burge wanin da bai isa baka ko hanaka ba. Yanda aka haliccesa kaima halittarka akayi. Duniya gidan kashe ahu ce, yanda kaga kasuwa na cika a hankali kowa ya tafi idan dare yayi haka wannan duniyar zata kasance. Riƙe da gaskiya, sai UBANGIJI ya riƙe maka kaima).
     Wannan bada waya itace tsushen komai tsakanin ta da Junaid, daga nan kuma komai ya fara. Farawar da take tunanin ta kawo ƙarshenta a wata gaɓar samun yanci da cigaban rayuwar da shine sanadinta duk da ba'ayita ta hanya mai ƙyau ba. Sai gashi komai na ƙoƙarin canjawa, bayan data juyama baya da yaƙini da yarda na ƙoƙarin komawa gabanta. Gaban nata ma a gaɓar da take ƙoƙarin tsayawa da ƙafafunta..........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣4️⃣


______________


..........Da gidan Chalawa Sabuwa gidansu ta wuce tana kuma wiwi take sanar da iyayensu abinda ke faruwa. Wai Chalawa yasa ƴan sanda sun tafi da Nazeefa da Yazeed wai sune sukai musu sata. Suma zancen ya girgizasu, sai dai basuce mata komai ba. Hasalima mahaifiyarsu catai ina ruwansu. Suje can su ƙarata ita da ƴar uwar tata. Yanda basu tanka ba a na baya yanzun ma babu ruwansu. Baban kuwa cayay tabar masa gida, idan ba haka ba zai ɓata mata rai. Haka ta baro gidan kuwa dan suna tsoron Mamansu bata da wasa, yanzu ne ma da tsufa ya kamata wasu abubuwan take kallo ta kauda kai. Amma jajirtacciya uwa ce mai tsayayyen ra'ayi akan zuri'arta. Kawai dai ko yaya sai ka samu fanɗararre a cikin ƴaƴa, to su kamar ma Sabuwar ce fandararriyar dan Hajiya Yaya iyakar tujararta a gidan mijinta ne, shima sai da akai mata kishiyoyi...
      Daga nan gidan police station ta wuce inda take tunanin an kai su Nazeefa, sai dai kai tsaye suka nuna mata bama su san case ɗin ba. Ta buƙaci ganin dpo sukace baya nan. Can sai ga kofur Hamza, tai masa magana tana kuka da faɗin ai sune sukaje suka kamasu yace shi baima taɓa ganinta ba sai yanzu. Wannan abu ya rikitama Sabuwa hankali. Ta dinga rantsuwa da kuka tana tabbatar da Kofur Hamza ne shiko yay mirsisi, sauran ƴan uwansa ma suka goya masa baya wai shi bama ya gari ai yanzu ya dawo. Neman haukata Sabuwa suke, dan haka ta ɗauka waya tana kiran mijinta amma fin sau goma bai amsa ba. Sai zuciyarta ta sake dagule wa. Har wani bishi-bishi take gani sanda ta baro ofishin ƴan sandan, dan tana matuƙar so da ƙaunar Nazeefa. Koda ta iso gida bata samu mijin nata ba, dan mai aikinta ma tace ai tunda suka fita tare bai dawo ba. Wannan abu ya sake ƙona mata zuciya da ruhi, sai kawai ta zauna a ƙasa a falo ta zuba uban tagumi....

   ★A lokacin da take nan tana damuwa da halin da ƴarta take ciki, a ɓangaren Mabera shi yana can yana kai-kawon lissafin yanda aikinsa zai tafi dai-dai. Dan kuwa tafiya da Yazeed da Nazeefa, shigowar ɗan gidan Darma a harƙallar gaba ɗaya ya gama ƙwaɓa masa shirinsa. Dole ya sake sabon lissafi gudun kar yay gaggawa, ka da kuma yayi garaje. Domin shi kaɗai yasan miya gani a cikin idanun wannan hatsabibin yaron ɗan gidan Darma, tabbas yasan barewa bazatai gudu ɗanta yay rarrafe ba. Sannan wannan yaron shi ake kira da ɗan gado har ya zarta. Bafa a banza ya ɓiyema ganin Aliyu Darma ba na tsawon shekaru. Duk da a yanzu next shirinsa shine bayyana a  gabansa ai ba irin wannan yake shirin yi ba...
     Tun a ranar ɗaurin auren Yazeed da Nazeefa da yaci karo da fuskar Darma da zaratan mazajen yaransa uku zagaye da shi hankalinsa yay matuƙar tashi, dan ya rasa ta ina alaƙar ta ƙullu a tsakanin Chalawa da Darma, dan a kaf sanin da yay masu na tsahon shekaru babu wata alaƙasa, sai ta business data ɗan ƙullu watanni da suka wuce, wanda sarai yasan Chalawan ya jima yana bibiya kafin ya samu hakan. Sai daya zurfafa bincike ya gano amaryar Chalawa ce igiyar zaren ƙulluwar alaƙar, abinda bai taɓa zuwa masa a lissafi ba, duk da kuwa yana biye da komai na rayuwar gidan Darma. An kuma bashi ƙafa ne a dalilin komawar amaryar Chalawa ƙauye da yaranta, daga haka yay tunanin komai ya ƙare ata ɓangarenta kamar yanda ɗansa ya tabbatar masa ashe-ashe ba haka bane ba.. shigowar kira a wayarsa ya katse masa tunani, ya ciro wayar yana dubawa, ɗansa ne, kuma zuciyarsa. Dagawa yay, tare da faɗin, “Son”.
      “Yea Baa. Ykk?”.
Yaron ya faɗa daga can. Mabera yay gajeran tsaki da faɗin, “Bana lafiya Son, dan wasana ake shirin buɗe min”.
      “Wanene da wannan gangancin. Halan bai san ka mallaki ɗan zaki ba?”.
      “Tabbas bai sani ba, dan cikin ƙwaryar kawai ya sani, ainahin kalarta zanenta ya ɓoye masa, musamman daya kasance an bita da fenti”.
      “Ai ko lokaci yayi da za'a kankare fentin, domin yasan da ainahin ƙwaryar da ake kai masa niƙan tuwo”.
     “Karka damu wannan aiki na ne, idan ina buƙatar shawara dama dole zan taɓoka.”
          “Haka ne Baa, nima ma kira ka ne akan matar can. Ta saka bincike akan ni da kai, yau kuma na tabbatar zuwa yanzu amsoshinta sun risketa”.
     Wata shegiyar dariya Mabera ya kwashe da ita, kafin ya ce, “Miyasa baka gaya min ba?”.
      “Saboda ba wani mai muhimmanci bane ba Baa, ai kai sarki ne ba kowane tarkace bane ya kamata yazo kunnen ka”.
     “ALLAH yay maka albarka ɗan Baabansa. Yanzu yaya ake ciki?”.
     “Nasa an bata dai-dai da abinda take buƙata, dan ina son mu tafi step 2. Sannan yaron nan na gaji da ganinsa yana yawo akan ƙafafunsa Ra'iz a cikin kujerar guragu, ya kamata shima ya ƙarfi nasa hisabin. Amma kafin hakan ina son shima na ɗan tatsesa kuɗaɗe akan video ɗin dana taɓa

165 / 213

Chapters