Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ɗin nan ba wani mutumin kirki bane ba, sunansa wai Sille, da shi kuma kowa ya sanshi. Irin ƴan jagaliyar siyasar nan ne. Yaron Minister Olermide ne. Tare yazo Abuja da shi daga Lagos. Dan hatta ita wannan motar da yake hawa Minister ɗin ne ya saya masa ita. Suna nan a cikin wani tsohon Company shi da yaransa abokan ta'addancinsa. Amma asalinsa dai tashin Lagos ɗin ne, baida uwa kuma sai uba. A yanzu haka kuma babansa baya zaune a Lagos ɗin, wanda ya bani bayanan yace bai san inda yake ba dan shi kansa Sille ɗin yanzu bai cika zaman Lagos ɗin ba sai Ministar zaije gida ne suke zuwa tare”.
“Okay thanks you. Amma babansa bahaushe ne?”.
“Tabbas ance bahaushe ne ɗan arewa, sai dai shima bai san ainahin jihar sa ba”.
“Ba damuwa zan tura maka saƙo”.
Daga haka AA ya yanke kiran. Yaya Fawzan ya ce, “Kai dawa haka Auta?”.
“Akan case ɗin nan ne na Daddyn Kaduna”. AA ya faɗa dan baya son ya faɗa musu komai har sai ya gama bincikensa. Duk sun gamsu, dan babban Yaya ma baice komai ba....
Shirye-shiryen babbar salla sun kankama. Su AA sunyi rabon raguna ha talakawa, da ma'aikatansu na office. Dama akwai wanda suka biyama hajji da suka tafi. Sannan sunyi rabon buhunnan shinkafa kamar yanda suka saba musamman a ƙauyukan Kano dama cikin birnin ta ɓangaren mabuƙata. Sannan nasu ragunan da za'ai amfani da su a cikin gidan dan hatta Anum dake ƙarama ana mata yankan rago ita kaɗai (Wata bishasha sai a novel😂, kai a zahirina fa yi ake walle masu kudi na hutawa😎)
A ɓangaren su Maanal suma sun sha gyaran jiki duk da dai da ƙyar AA ya lallaɓata taje wankin kai tare da su Najma. Mai ƙunshi tazo gida tai musu harda Maimoon data shigo nan. AA baice mata komai ba sai washen gari sun shagala da aikin cin-cin su cake da dai kayan fulawa dan gobe ne zasu wuce Kano acan suke babbar salla ya janyeta wai zata masa rakkiya. Sai kawai ganinta tai a shagon saloon. Tako tubure masa shi kuma ya haɗe fuska, a vip suka zauna aka fara mata kitson yana hawaye. Shi ko yay kicin-kicin da rai babu alamar wasa a tare da shi. Ya kuma ƙi lallashinta. Ita dai mai kitso na kallon ikon ALLAH. Dan wlhy ta zata ma ƙanwarsa ce. Duk da dai zuciyarta nata mata kai-kawo da wasu-wasin kamar fa matarsa ce da hotunansu sukaita yawo a media lokacin bikinsu. Bata da mai bata amsa, gashi ba abokan gulma a kusa. Dole tai gum tai aikinta yanda ya kamata. Ba wani mai yawa akai sosai ba amma ya mata ƙyau kitson. Sai da aka gama AA ya fara lallashinta tai banza da shi. Haka suka taho gida taƙi kulashi, shi kuma bai fasa tsokanarta ba. Koda suka shigo gidan kin komawa sashen Oum tayi sai bayan azhar. Lokacin ma har sun kusa kammala aikin dan harda masu aiki da kuma kwararrun bekers guda biyar da aka ɗakko....
★Yau ta kasance arfa, rana mai ɗunbin daraja da muhimmanci ga kowanne musulmi. Da farko AA ya hana Maanal ɗaukar azumi, amma ta dage kan zata iya. Dole ya barta dan harda kukanta. Cikin anincin UBANGIJI kuma har dai sha biyu babu wani damuwa. Duk shekara a Kano suke babbar salla, sai dai wannan shekarar anan Abuja zasuyi sai zuwa ƙarshen wata zasuje Kanon yin bikin ƙarshen shekarar musulunci in sha ALLAHU. Kayan shan ruwa sosai aka haɗa, sai kuma ga hadari. Dole aka kwashe zuwa cikin sashen Oum. Bayan yin sallar magrib kowa ya hallara babu Mamy, Oum tace Najma taje tai kiranta. Kamar AA zai yi magana sai kuma yay shiru, dan ya fahimci yau Mamyn a fusace take. Ɗazun nan ta gama zageshi tas akan batun Documents ɗinsa. Ta kuma tabbatar masa da rantsuwa cewar zata amsa ita da kanta a cikin satin nan. Bai wani fahimci inda ta dosa ba shi kam.
Babu wani jimawa Najma ta dawo, sai da takai zaune sannan ta ce, “Oum tace muci tana da uziri”.
Babu wanda bai kalli Najma ba, ita ko tai kamar bata ga kallon da kowa ke mata ba. Manaal tai murmushi, hakama RK da Nuwaira. Abah kam sai ka rantse bai ji ba ma. Sai da Oum ta yunƙura zata tashi ne a dake ya ce, “Koma ki zauna”.
Babu yanda ta iya ta koma ta zauna suka fara buɗa bakinsu. Bayan sun kammala mazan suka wuce massalaci, su Maanal kuma suka fara gyara wajen. Ƙasa-ƙasa Maanal ta ce, “ALLAH Najma baki da kirki, maimakon ki rufa mata asiri”.
“A hakan ma ai na rufa mata, harda zagina fa tayi, ALLAH matar can kamar ta fara haukacewa. Ni bana ma zaton tayi azumin fa shiyyasa ta ƙare da borin kunya”.
Dariya Manaal tayi ƙasa-ƙasa..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣9️⃣
______________
........Washe gari safiyar salla, kowa a gidan Darma ya wayi gari cikin farin ciki. Sai dai wasu ba farin cikin sallar bane a ransu. Musamman Mamy da a yau ne take shirin aiwatar da aikinta akan Abah. Ta gama shirya komai dan yau da asubar fari ta tashi da kanta tai ɗan girki a sashenta. Ta haɗa komai ta bama Haule da za'a barsu a gida su haɗa abincin. Ta mata gargaɗi da jan kunne mai tsanani tare da barazanar datai matuƙar firgita Haulen....
_______★
A ɓangaren Saheeba ma hakan take. Ta gama nata shirin tsaff akan yanda zata gudanar da aikin kowa ya tafi yanda ya kamata. Dan haka ta langare bata da lafiya bada ita akai shirin zuwa idi ba. Suna fita ta miƙe ta fice zuwa sashen Oum wajen masu aikin haɗa abincin salla....
______★
Ba'a gidan Darma kawai ake shiri ba. Anan ɓangaren Sille ma ya shirya tsaff da kayan aikinsa domin zuwa gidan na Darma. Hakama mahaifinsa Mabera ya iso daga Kaduna tun a daren jiya. Shima a yau zai je gidan Darma kai tsaye kamar yanda suka tsara. Dan haka kai tsaye daya kammala shirin massalaci sai ya nufi massalacin da su Abah ke zuwa sallar idi. Akan idanunsa suka iso kuwa. Yay wani irin makirin murmushi dan yasan yau sunanta ranar ɗaukar fansa. A kusa da su kaɗan ya zauna batare da su sun ma lura da shi ba.....
Anan kuwa gida Sille ya iso shima. Da taimakon Haule ya shige sashen Mamy har cikin bedroom ɗinta. Bayan ya ajiye kayan aikinsa ya shiga closet ɗinta ya fara bincike filla-filla.....
________★
Anan Kaduna kuwa abubuwa biyu ne zuwa uku ke shirin faruwa a lokaci ɗaya. Naƙudar da Nazeefa ta fara batare da sanin kowa ba. Sai shagalin girka abincin salla da akeyi tsakanin ɓangaren Ammie da Hajiya Yaya. Kafin kowa ya fito cikin shirin gayunsa kamar kowace sallar suka wuce massalaci. Ana idar da salla gida sukai yinƙurin nifowa. Banda Hajiya Basariyya da Huznah. Acewarta zasu je su fara gaida Yayanta ita da Huznah ɗin. Su kuma sauran yaran sai gobe.
Babu wanda ya kawo komai a ransa har Huznah ɗin. Su Ammie suka wuce gida dan masu aikin raguna sun kira sun iso. Yaran kowa ka kalla yana cikin ɗumbin farin ciki mara misali. Su kansu yaran Hajiya Basariyya da alama tafiyar uwar tasu anguwa tai musu daɗi, dan suna isa gidan maimakon sashensu kai tsaye sashen Hajiya Yaya suka bi ƴan uwansu domin cin abinci....
_____★
Sosai gaban Huznah ya shiga faɗuwa, ganin maimakon gidan kawunsu da Ummin tasu ta faɗa sun nufi hayar wani gida daban. A ɗarare ta yarda suka shiga gidan. Matar gidan ƙabila ce, ta fito ta tarbesu cike da farin ciki. Aka saukesu a falo aka kawo musu ruwa da lemo. Babu abinda Huznah ta taɓa sai ma gabanta ne dake faman faɗuwa matuƙa. Bayan Hajiya Basariyya sun gaisa da matar sai take kallon Huznah, ta ce, “Itace wannan za'a zubar ma cikin?”.
Hankali kwance Hajiya Basariyya dake murmushi ta ce, “Ƙwarai itace”. Huznah kam wani irin faɗiwa gabanta yayi, ta kalli mahaifiyarta ta kalli matar jikinta na rawa. Bama tasan bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Ummi zubar da ciki kuma?”.
Hararrata Hajiya Basariyya tayi, a kausashe tace, “Ai kema kin san abinda zai biyo baya kenan, dan bazan taɓa haɗa jinin da ɗan Sani ba har abada.”
“Amma Ummi ya kai wata biyar fa”.
“Koma wata sha biyar ne dan ubansa sai yabi rariya. Oya Doctor zaki iya fara aikin ki dan banda isashen lokaci kin san yau muna bikin salla, yanzu ma nace zanje ziyara ne
Na zaɓi wannan ranar ne saboda hankalin mutane bazai kai kanta ba musamman ma ubanta da ƴan sa idon matansa.”
“Baki da damuwa Hajiya, komai zai tafi yanda ya kamata. Awa ɗaya ta ishemu dan allurar idan anyi zata ɗauki mintuna talatin ne ma shiyyasa. Idan kuma kin yarda da an mata zakije gida to, na tabbatar sanda zaku isa jinin bai fara zuba ba.”
“A'a babu wata damuwa ayi mata anan, so nake ayi komai a gama dan idan mun tafi zan kaita wani waje ne ta zauna sai dare sannan ta koma gida ta gama dawowa hayyacinta”.
“Haka ma dabara ce kam.”
Kuka sosai Huznah keyi, maganganun Sageer na dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Ta zamo a kujerar ta dur ƙusa a gaban Hajiya Basariyya tana kuka. “Ummi dan ALLAH na roƙeki kada ki zubar min da cikin nan. Wlhy ubansa bazai taɓa yafe mana ba dan yaji a jikinsa hakan zata iya faruwa. Ya kuma tabbatar min wlhy sai yabi kadin cikinsa. Koba haka ba ma wlhy Ummi nima ina son cikin, nasha wahala sosai a laulayi. A kwanakin nan ne kawai kike gani na da lafiya kamar haka. Dan ALLAH kiji ƙaina ko tausaya min babyna har ya fara motsi. Motsinsa da nake ji yasa nima na fara jin ƙaunarsa har bazan iya cutar da shi ba.....”
Ba ƙaramin zama galala Hajiya Basariyya tayi yana kallon Huznah ɗin ba. Sai kuma ta shiga faɗin, “Eh lallai Huznah yanzu na sake yarda kin auri Sageer. Yanzu ni kike faɗawa haka, ni uwarki har ni kike sanarma Sageer zai bi kadin cikinsa, ke kuma kina son Babyn ki. To shike nan bari na ɓarar da shegen ciki in yaso ke da Sageer ɗin ku haɗu ku kaini kotun ALLAH ya isa. In ce dai shike nan”.
“Ummi ba haka nake nufi ba dan ALLAH kiyi haƙuri, kiyi haƙuri koma miye kiyi min amma dan ALLAH banza zubda cikin nan na tuba”.
“Aiko sai dai ki mutu, ciki babu fashi sai na ɓarar da shi dan ubanki. Kuma kika sake min magana sai na tsine miki!!!”.
Wani irin komawa baya Huznah tayi jikinta na rawa kar-kar-kar........
_________★
Anan gidan Darma komai su Haule sun haɗa sun shirya kamar yanda aka saba. Dukkan abinda Mamy ta bama Haule ta shirya komai a inda Abah zai zauna. Haka ma Saheeba komai sai da ta tabbatar ta saka a gurbin daya dace. Kafin ta wuce sashensu dan bata buƙatar mutanen gidan suzo su sameta....
An idar da salla, kowa ka gani yana cikin farin ciki. Kamar yanda aka saba ahalin Darma sai da sukai hotuna sannan suka shiga motoci suka kama hanyar gida. Duk Mabera na kallonsu kuwa. Sai da suka wuce da kamar mintuna goma sannan shima ya shiga mota yabi bayansu. Sai faman zuba murmushi yake yi dan fuskar Kamila kawai yake hangowa a wannan gaɓar..........✍️
Kunga page ɗin nan kuyi hakuri da shi a hakansa. Wlhy aiki yamun yawa na kasa kaishi yanda nake so. Muhaɗe kawai ranar Monday idan ALLAH ya kaimu. Ina fatan zakuyi salla cikin aminci da ƙoshin lafiya. Karka a manya dani a addu'a awajen sallar idi, da kuma kai da ƙafafu ehe. Ayi salla lafiya. Ina sake bada hakuri da gajartar page ɗin nan na karshe ku bini bashi😘😘😘.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣0️⃣
______________
........Koda ahalin Darma suka iso gida matan ne kawai suka shige ciki. Amma su Abah duk nan waje suka tsaya suka gaggaisa da sauran mazan anguwa da Baba Imam dake musu yankan raguna. Sai da aka kammala yankawa masu gyara zasu fara sannan suka shiga ciki.
Gaba ɗaya sun sami ahalin gidan a sashen Oum, abinda yaba Abah da AA mamaki harda Mamy. Kuma yau sai faran-faran take da kowa. Dan suna zaune ne ma suna hira da Oum su kuma su Maanal na hotuna. Saheeba ma ta fito tanata wani yamutse-yamutse ita adole wai mara lafiya. Zaman cin abinci akayi, gaba ɗaya hankalin Saheeba nakan Maanal. Mamy kuwa da kanta yau ta zubama Abah abinci, komai baice ba, bai kuma gwaleta ba dan tasan itama bazaiyi hakan ba kodan yara. Tana kammala zubawa kamar kowa yay bismillah ya fara cin abincinsa. A kusan tare Mamy da Saheeba suka sauke ajiyar zuciya, dan itama dai Maanal ta fara cin nata hankali kwance. Haka sauran ma. Ran Oum fes yau Mamy ta saki ranta family ya cika yanda take fata. Gashi anata hira da raha gwanin sha'awa. Suna gab da kammala cin abinci Bola ya shigo sashen Oum ɗin bayan ya nema izini, cikin girmamawa ya sanar ma Abah yana da baƙo. Dan shiru Abah yayi na mamaki dan yasan baiyi da kowa zaizo a yanzu ba, mafi yawanci ma a ranar babbar salla sai irin bayan azhar ɗin nan suke fara yin baƙi. Amma sai bai ce komai ba ya miƙe ya fita.
Tunda Abah ya fito idanunsa akan mutumin dake tsaye a jikin motarsa ya juya baya yana waya. A haka dai ya ƙaraso yana nazari da tunanin to wanene wannan haka?. Dai-dai yana ƙarasowa tamkar amma Mabera magana shima ya juyo, sukama juna kallon ido cikin ido. Abah ma sai ya rasa abin cewa, kallo Mabera kawai yake yi tamkar ya samu television. Yayinda Mabera ke dariya da kallon Abah ɗin shima, sai kuma ya tako a hankali kusa da Abah yana faɗin, “My Darma badai ka suma bane?”.
Abah da mamaki ya kashe a tsaye ya ce, “Humm Mabera dole ne na suma ai, wai kai ɗin ne dai a gabana ko mafarkin dana saba yine dan ALLAH?”.
Kai tsaye Mabera ya rungume Abah tare da masa raɗa a cikin kunne ya ce, “Idonka biyu My Darma, Maberanka ne dai tsaye a gabanka”.
Rugumesa shima Abah yayi, kafin su saki juna yana kallonsa da ƙyau ya ce, “Mabera dama kana a duniyar nan a raye? Amma tsahon shekaru baka babu labarinka? Kasan irin neman da nai maka a rayuwar nan kuwa?”.
“Humm Aminina kai dai kawai a rufe rufau. Wani ƙulli ne ya ƙulleni mai girman gaske, sannan aka sakani a ramin da duk ihuna babu mai iya jin kuka na”.
Abah dake kallonsa ya ce, “Halan a wajen jaye-jayen ka ne?”.
Dariya Mabera yayi kawai, Abah ya ce, “Ai na sani, nasan bazaka canja ba. Kaga na barka a waje muje ciki dai”.
A yanzun ma dariya kawai Mabera yayi, a kaikaice kam sai sake bin gidan yake da kallo yana jinjina kai. A zuciyarsa yana ayyana, (Ta tabbata dai Darma yafi ƙarfina kamar yanda yasha gaya min. Duk da an haifeshi gidan kuɗi, nima an haifeni gidan kuɗin. Kuɗina da nashi muka fara dasa kasuwa na yaye komai amma hakan bai hanashi cigaba da zama a samana ba. Kenan kalmar daya gaya min ta har abada yafi ƙarfina, zai kuma cigaba da fin ƙarfina har ƙarshen numfashin mu ta tabbata)..
Taɓawar da Abah yay masa ce ta dawo da shi hayyacinsa, Abah ya ce, “Bismillah shigo mana, nan fa gidanka ne”.
Murmushin yaƙe Mabera yayi, ya shigo katafaran falon baƙin Abah na sashensa, wanda aka narkama uwar dukiya da kayan ƙawa. Kai daka gani kasan kazo gidan da nera ta zauna. Komai babu hayaniya, amma daka gani kasan an zuba kayan kuɗi. Zama sukayi Abah ya ɗauka kan waya ya fara neman Oum.
Kusan mintuna goma da fitar Abah kenan, dan kowa ma ya tashi daga gaban abinci anata tattare kayan sai ga kiran Abah ɗin a wayar Oum. Tana ɗagawa yace a kawo ma baƙonsa abinci, sannan anjima kaɗan dukan su suzo sashensa a falon baƙi su gaisa da baƙon nashi.
Abinci Oum ta saka aka shirya, su Haule suka tafi kaiwa sashen Abah. Koda Haule taga Mabera rikicewa tayi, har ta kusa faɗuwa ga kaya a hannu, ba ƙaramin bugawa zuciyarta ta shiga yi ba ganin mai kama da Sillenta, sai dai wannan kawai ya fishi manyantar shekaru. Bata taɓa sanin Sille nada mahaifi a raye ba balle ma ta kawo a ranta akwai alaƙa. Yanda taɗan rikice