Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ta nuna farin cikin ganinsu ta kuma shiga kiran sunan yaran ɗaya bayan ɗaya da buɗe musu hannaye alamar suzo sai sukafi sakin jiki da ita. Da gudunsu kuwa sukaje suka shige jikinta suna dariya kamar sun santa. Dan su basu da wahalar sabo, in dai zaka jasu a jiki yanzu zasu sallama. Sai abin kuma ya dami Mamy taji kunya sosai. Sai bin yaran take da kallo dake nane da Aunty, itako sai nannan take da su kamar zata cinye. Basu sake kula Mamy ba kuwa. Ana haka sai ga AA ya kira video call. Yaran suka shiga ɗoki suna kiran Abie-Abie. Shi ko sai murmushi yake musu cike da kulawa da soyayyarsu. Labarin abinda Aunty tai musu suka shiga bashi, su Zarah bakin bai gama nuna ba sai murmushi suke saka shi.........✍️216
..........Haka dai ya biye musu sai da kowa ya gama bashi nashi labarin su duka huɗun sannan ya gaisa da su Aunty, godiya yay mata sosai, itako tana harararsa da daƙuwa. Wai dan mi zai mata godiya ita da jikokinta. Mamy ma ta amsa suka gaisa. Yanda batai masa maganar yaran ba shima bai mata ba. Haka yaran suka ƙara amsa suka koma gefe sun hana iyayen. Dama haka suke musu, wataran har gori suke musu idan sukai magana. Musamman Ahmad ya iya faɗin “Ai Daddy's ɗinmu ne dai”.
Suko suce ikon ALLAH ai mu daga sama muka faɗo. Haka AA ya biye ma yaran nan sunata shiririta har Babban Yaya da Yaya Fawzan suma suka samesa suka ɗora, da ƙyar suka yarda sukai musu sallama Khadee harda kukanta sai da Maanal ta goyata aka samu lafiya. Yaran nada shaƙuwa sosai da iyayensu bata wasa ba. Koda su kaɗai suka taso suke gani sai kakanni su oho.
Anan gidan suka kwana, washe gari suka shirya komawa Abuja Manaal bata jin daɗin jikinta. Aunty ta haɗa musu shatara ta arziƙi. Mamy kam sai kukan zuciya. Amma ta buɗe baki ta nema gafararsu suma ta gagara. Haka suka koma Abuja. Kwannasu biyar da dawowa suka fara shirin wucewa. Maanal ta ziyarci Mawaad Company har sau kusan uku. Ta duba komai yana tafiya dai-dai yanda ya dace. CFO dai ta ajiye aiki tuni. Su Zaharadeen sai wani bata girma suke. Yaqub daya kara samun girma a yanzu yana matakin Designer director shima har gidansa taje sukai zuminci da matarsa mai kirki, haka taita girmama Maanal taima Khadee da Zarah kitso dan dasu taje....
★★ Randa suka dawo Chaina mazan nasu ne da kansu suka je tarbosu. Ba kunya suka rungume su sannan suka koma kan yaransu. Sun iso gida Oum ta shirya musu beta dan yanzu sun canja wajen zama. Suna a gidan dake ɗaukar family ne gaba ɗaya. Sun sami Naufal yazo hutu, sai dai sunyi ƴar tafiya shi da Abah sai dare suka dawo. Tuni yara suka tare wajen Oum da Abah da Naufal. Su AA suka sami filin sharafin baje soyayya dan sunyi kewa. Maanal ma dai dauriya kawai take dan bata jin daɗi. Sun dawo da sati ɗaya jikin nata ya takura mata AA ya ɗauketa suka je asibiti. Gwajin farko aka gane ciki ne. Zo kaga murna wajen Abah, Oum, Babban Yaya, Yaya Fawzan da uban gayya AA. Haka Ameerah da Najma ma. Kowa addu'a sauka lafiya yake mata. Wannan karon dai kam laulayi take sosai tun a farkon cikin, sai da ya shiga wata na huɗu ta samu lafiya da ƙarfin jiki. Haka suka cigaba da rainon cikin nan kowa na bata kulawar data dace. Gefe AA na kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a zuciya. A haka ALLAH ya kaita watan haihuwa, wannan karon ma aka ciro mata baby girl mai kama da iyayenta. Hotunan baby ya cika wayoyin dangi, washe gari RK da Nuwaira suka isa Chaina da yaransu biyu suma kyawawa. Sosai su Oum suka farin ciki da zuwansu, nan fa suka haɗu aka sha shagalin haihuwar Baby. Bakin AA ya kasa rufuwa dan farin ciki. Ranar suna yarinya taci suna Ruƙayya, zasuma ce mata Urwa. Wannan karan kam RK ya shirya walimar da akaci aka sha aka gagije. Bayan suna maijego ta cigaba da jegonta kafin a koma filin daga. Suma su Ameerah suka fara nasu laulayin kuma.
Ai a wannan gaɓar Mamy tama rasa nacewa, UBANGIJI ya tabbatar mata shine maiyi da tsarawa bayinsa rayuwa. Ga dai masu cikama ƴaƴanta burinsu nan da ƴaƴaye. Wani lokacin a ɓoye take saka hoton yaran su shida reras da iyayensu uku da Oum da Abah sai su Maanal taita hawaye. Tayi mai isarta ta goge dan ko Aunty bata bari ta gane duk da aunty tana ƙyaletane kawai amma ta gane komai. Amma tunda tana ɓoyewa sai take barinta a hakan kawai...
★★ Urwa nada shekara ɗaya da rabi, yaran Ameerah da Najma da suka haima duk maza suma Abubakar, da Umar nada watanni bakwai-bakwai jikin Mamy ya rikice. Babu ɓata lokaci su Oum gaba ɗayansu har Abah suka nufo Nigeria. Kai tsaye Kano suka sauka, maimakon gida kuma asibiti suka wuce inda take kwance. ALLAH mai girma da ɗaukaka sun shiga ɗakin da take kawai ta zuba musu ido tana hawaye. Magana take son yi amma babu baki dan kwana uku kenan maganarta ta dakata. Haka taita kallonsu da idonta ɗaya tana hawaye. Su Naufal na zagaye da ita su takwas cas sai iyayensu a bayansu, Oum Abah da su Maanal na gefensu. Sai Aunty da yaranta suma. Ta kafe Abah da ido na tsawon lokaci sannan ta koma kan Oum, ta juya idanun ta sauke akan su Maanal ɗaya bayan ɗaya sannan ta maida kan su AA, tai ɗan murmushi ta maida kan su Naufal. Fin mintuna biyar tana kallon yaran sai tari, sai aman jini, abu kamar wasa dan danan aka nemo likita. Su kuma akace su fito. Cikin abinda bai wuce awa guda ba ALLAH yay mata rasuwa. Sai likita fitowa yay jiki a sanyaye...
Hawaye sosai Oum da su Maanal da Aunty keyi. Abah ya duƙar da kai kawai yay shiru, haka ma su Babban yaya idanunsu duk sun kaɗe hawaye na cika su. Sosai tausayin mahaifiyarsu ya kamasu na rashin neman gafarar mutane da batai ba. Duk da sunyi iya ƙoƙarinsu na ganin tayi hakan amma ALLAH bai bata iko ba. Haka aka ɗauki gawarta, zasu wuce gidanta da ita Baba Sardauna yace a kawota gidansa. Hakan ya saka su Babban Yaya jin daɗi, a gidan Baba Sardauna akai mata wanka aka shiryata, sannan aka sallaceta aka miƙata makwancinta na gaskiya. Ahalin Darma sun nuna dattako da kara sosai. Dan har na nesa sai da suka dawo har ma wanda basa ƙasar ƴaƴa da iyaye. Hakama su Ammie, su Hajiya Shuwa da ƴan uwa da abokan arziki duk sunzo. Tsohon shugaban ƙasa mai sauka ma yaje da tawagarsa. Manyan mutane darajar ƴaƴanta da tsohon mijinta sun taka rawar gani. Haka akai addu'ar uku gidan baba Sardauna cike. Ko abinci ba ƙaramin aiki yayi a gidan nan ba sai godiyar UBANGIJI. Dan rasuwa yanzu ta zama tamkar biki musamman idan kana da gata.
Bayan addu'ar bakwai suna shirin wucewa aka sake wata rasuwar. Babu ya rasu a Giro. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, sosai su Maanal sukaji rasuwar nan suma. Haka aka ɗunguma akai Giro kuma. Ba'a biznesa ba sai da suka isa. Harda su AA da su Babban Yaya, su baba Sardauna duk aka sallaceshi aka kaishi gidansa na gaskiya. Nan ma kwana su uku sai da akai uku sannan suka wuce aka bar su Maanal kawai da su Ammie, Amaal, Shahidah. Sai da akai bakwai har ma suka ƙara kwana uku akai sannan sukai shirin barowa. Koda aka raba gonakin gadon daya bari haka suka ɗauka suka bama Sailuba su da Sule dake kuka matuƙa kamar ransu zai fita. Haƙila kam tayi gaba babu wanda yasan inda take. Wasu suce tana Lagos, wasu suce tana Tafa, ALLAH dai kaɗai yasan tana ina sai ita.
Su Maanal sun taho sun bar ƴan Giro da kewa. Dan sun san yanzu kam ganinsu zai musu wahala ai. Tunda dama dan mahaifinsu suke zaryar zuwa. Yanzu ko babu shi sai ta ALLAH kuma. Sun dawo Abuja juma'a su Maanal suka koma Chaina Lahadi........✍️217
..........Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun canja, su AA sun dawo Nigeria gaba ɗaya, sai dai sun sake gida dan Abah da su kansu basa son tuna komai daya faru a waccan. Sabuwar rayuwa, sabon family, sabon muhalli.
Kyawawan hamshaƙan manyan mata ne guda uku zaune a wani katafaren falo da yaji kayan more rayuwa na haƙiƙa bana yaku bayi ba. A kallo ɗaya zaka tabbatar da kuɗi, tsafta, gayu da ƙwalisa sun zauna. A shekaru duk bazasu wuce 35 ba. Hira suke cike da nutsuwa da fahimtar juna. Kowace da murmushi mai ƙayatarwa akan fuskarta. Yanda suke hirar ƙasa-ƙasa suna kallon hanyar stairscase da akai adon falon da ita tamkar ba'a Nigeria ba zai baka tabbacin gulma suke ko hirar da basa so aji.
Kamar kuwa hakan ne dan wani matashin dattijon mutumi da zai iya haura hamsin na ɓullowa alamar zai sakko falon da suke daga upstairs sukai shiru. Sanye yake cikin ƙananun kayan zaman gida na shan iska. Duk da shekaru sun turza ƙyawun haibar da cikar kamalar na nan, ga wani furfura ɗai-ɗai datai masa ado a saman kai da gemunsa.
Ganin yanda matan suka haɗe kai a ƙasa ya ɗan kallesu da yanayin nan nashi na rashin sakin fuska ya furta, “An dasa gulmar ko?”.
A tare suka kalleshi, Ameerah ta ɗan waro idanu da faɗin, “ALLAH Big Daddy mu bama gulmar kowa, hirarmu muke yi”.
“To ALLAH yasa, ai nasan hali ne, musamman idan naga Lilly da Najmah na wani sinne kai”.
Dariya Maanal da Najma suka sanya. Cikin haɗa baki wajen kare kansu. Shima sai ya ɗan murmusa da faɗin, “Okay shike nan. Har yanzu su Fawzan basu shigo bane?”.
Manaal tace, “Sunce suna gab, wai sai sun sauke Uncle R a gida sannan”.
“Humm daga nan kuma Nuwaira ta riƙesu sai sunci abinci ba. Ina yaran nan ko suna waje”.
“Suna kitchen kaf ɗinsu, Ni bamma san wane tsiyar suke ƙullawa ba wai kar muzo sai sun gama.”
Ɗan jimmm Babban Yaya yayi sai kuma ya kaɗa kansa yana nufar hanyar fita da faɗin, “To idan tayi wari maji, ni bari naje massallaci kuma ku tashi salla.”
Da to duk suka amsa, Najma ta nufi hannayar kitchen taima yaran knocking. Tace su buɗe, cikin haɗa baki sukace su dai a'a.
“Ikon ALLAH wai ubanmu kukeyi?”.
“Mah ke dai kawai kije kiyi zamanki abinki, idan mun gama su Yaya Naufal sun dawo daga inda sukaje zaku gani”.
“ALLAH ya shiryeku to, sai ku fito kuyi salla”.
Da to suka amsa mata, sai da suka tabbatar tabar jikin ƙofar sannan suka fito. Oh oh Masha ALLAH, ƙyawawan ƴammata ne guda huɗu duk masu kammani ɗaya. Ɗaya duk ta fisu girma, sai biyu kamar tagwaye, sai ƙaramar da bata kaisu ba. Babbar zata iya kai 17years, Maryam kenan da suke kira Norah babbar ɗiyar Uncle RK, sai tagwayen su biyu da zasu iya kaiwa 15years Khadee da Zarah kenan, sai ƙaramar da zata iya kaiwa 13years Urwa kenan (Ruƙayya) kai daka gansu kaga ƴaƴan madara malam, ga ƙyau ga nutsuwa kamar ƴaƴan larabawa. Ɗakinsu suka nufa dake sama ɓangaren Babban Yaya, dan itama Norah tuni ta dawo nan gidan. Babban ɗaki ne da gado huɗu kowa da nata. Haka sukai alwala sukai salla. Suna idarwa suka sakko ƙasa, dai-dai iyayen na sakkowa suma. Suka gaishesu a nutse, sai kuma ga sallamar wasu magidantan su biyu masu kammani guda. Ɗaya zai iya kaiwa arba'in da tara, ɗaya kuma arba'in da biyu haka zuwa da huɗu ma. Sanye suke cikin yaduka da sukai musu ƙyau suka fidda kamalarsu da nutsuwa. Ai da gudu yaran suka sakko a stairscase ɗin suna faɗin, “Oyoyo Abbah! Abie Oyoyo.”
Murmushi ne sosai a fuskar AA da Yaya Fawzan, yaran suka iso gabansu suka rirriƙe musu hannuwa. Suko suka shashahafa musu kai suna amsa gaisuwar da suke musu da sannu da zuwa. Kwanansu uku kenna a Kano, sun je wani aiki ne. Dai-dai nan Babban yaya ke shigowa da wasu samarin matasan yara har su biyar cif. Masha ALLAH yaran gwanin sha'awa. Akwai babban saurayi da zai iya kaiwa 25years, sai wasu dake kai ɗaya kai daka gansu kasan ƴan biyu ne da zasu iya kaiwa 17years, sai ƙanana da zasu iya kaiwa 12years haka. Manyan ledojin shopping ne a hannunsu alamar daga can suke. Suma tuni suka ajiye ledojin suka zo suka maƙalƙale iyayen nasu suna musu sannu da zuwa. Sai da suka gama sannan Yaya Fawzan da AA suka rungume Babban Yaya suma. A lokacin ne kuma matan ke isowa na musu sannu da zuwa. AA ya wani kafe Maanal da kallo cike da shagwaɓa. Ido ta ɗan kashe masa tare da masa nuni da yaran da su Babban Yaya. Koda ya ɗan juya sai yaga ido yaya Fawzan a kansa. Ido AA ya ɗage sama da ɗan harararsa sannan ya duƙo cike da raɗa ya ce, “A dai rage gulma Abban yara”.
AA bai rufe baki ba Yaya Fawzan ya amshe da faɗin, “Adai rage taɓara Abien yara”. Murmushi Babban Yaya yayi yaja hancinsu a tare da dungure musu kawuna. Sai yaran suka sanya dariya. Wannan ba sabon abu bane ba a wajensu. Su Maanal kam murmushi kawai sukai kowacce taja mijinta suka shige ɓangarensu.
Suna shiga ɗaki AA ya rungume Maanal yana faɗin, “I miss you bestie”.
“Miss you too Bestyn Besty”.
Ta faɗa tana murmushi da ɗago fuskarsa ta manna masa kiss. Zata janye ya cafke lips ɗin nata ya shiga sumbata. Tun kamar abin zai tsaya iya nan har aka ɗauki wata hanyar, dan da gasken sunyi missing junan, kwana uku a wajen AA da Maanal ai kamar shekara uku ne. A hakama koda yaushe ana manne da juna ta waya da video call. Basu gane kansu ba sai da suka gama faranta ran juna, sannan sukai sabon wanka suka fito, ta taimaka masa ya shirya itama ta canja shiga. Sallar la'asar ta saka shi fita, ita ko tayi a ɗaki sannan ta fita ta samo masa fruits dan yace sunci abinci gidan RK. Ana kuwa idar da sallar la'asar ya shigo. Dan haka ta kawo masa fruits ɗin, yana fara sha da ƙoƙarin kunna television tana jikinsa ita kuma yace, “Besty wai saura kwana nawa a fara bikin nan na su Barru ne?”.
“Bai wuce sati uku ba fa, shiyyasa nake son a next satin nan ma mu shiga Dubai ɗin nan, gashi kai kuma kanata ciccijewa.”
“Am sorry ba cijewa nake ba, kawai kai-kawon nan ne ya riƙeni, amma Alhamdullah ai na kammala. Ke da waye masu tafiyar?”.
“Ai Mamma (Ameerah) ne kawai da Mah (Najma) sai yaran nan da suke ta naci yammatan, sai Aunty Sakina”.
“Oh Shahidah da Amaal dai ba damar zuwa kenan?”.
“Kai Besty, gamu kuma mi zasuje suyi suda zasu aurar da yara. Ai su ƴan kallone mune masu shirya komai”.
“Hakane kuma amariri iyayen amare, nima ALLAH ya kaini randa zan aurar da nawa yammatan huɗu”.
Murmushi Maanal tayi da faɗin, “Norah kam ai tana hanya, dan naga ita da Naufal da gaske suke kam. Sai dai Khadee da Zarah ai kwa ɗaga mana ƙafa da saura 15years da. Urwa kam ai ba'a magana balle su twins maza”.
Cike da farin cikin zancen Norah da Naufal AA ya ce, “Amma ALLAH yay ma yaran nan albarka, haka nake fatan Muhammad da Ahmad su dai-dai da Zarah da Khadijah in sha ALLAHU”.
“To ALLAH ya tabbatar, kuce duk ƴar gida zakuyi kenan”.
“A in sha ALLAHU haka muke fata Besty”.
“ALLAH ya bamu tsahon rai mai albarka kamar su Oum, wai yaushe zasu dawo ne wlhy kewarsu muke. Yau yaran nan suma tunda safe naga sun tashi suna gyara sashensu, kuma gasu can sun maƙale a kitchen bamu san uwar mi suke ba”.
“Gyara fa dai?”.
“Wlhy kuwa”.
“To kodai su Oum na shirin dawowa ne jikokinsu kawai suka faɗamawa? Amma jiya munyi waya Abah ke cemin babu rana balle wata, ni harma naji haushi, dan na rasa mi suke a Yola ɗin nan ga zafi ma”.
Kafin Maanal tace wani abu kawai sukaji hayaniyar yaran tayi yawa. Tashi AA yay da Maanal suka fito. Mi zasu gani Oum da Abah na shigowa. Maanal ta kalla AA, AA ya kalla Maanal. Sai kawai suka nufi staircase. Dai-dai su ma su Yaya Fawzan da Najma, Ameerah da Babban Yaya na fitowa.
Yaya Fawzan yace, “Dama bayin ALLAHn nan dawo zasuyi aka ɓoye mana sai jikokinsu”.
Murmushi Babban Yaya da AA sukayi, Babban Yaya yace, “Ga alama kuwa Abbah”.
Sakkowa sukai a tare, su Naufal na zagaye da su Oum daketa farin ciki. Duk da akwai jin daɗi tsufa sosai ya bayyana garesu. Dan kan Abah da sajensa duk sun zama furfura. Hakama Oum. Cike da tsokana suka buɗema su Babban Yaya hannu alamar oyoyo. Sai duk suka juya irin su sunyi fushin nan. Dariya yaran suka saka da su Aban, sai kuma suka fara lallashinsu. Suma duk sai suka murmusa suka juyo. Su Maanal ne suka fara zuwa ita da Najma da Ameerah suka rungume Oum, sannan Babban Yaya da su Yaya Fawzan suma suka rungume Abah. Kowa ka kalla kasan yana cikin farin ciki, satin su Oum biyu kenan a Yola daga bikin yarinyar Uncle Lamiɗo da akai aka kai can suka maƙale a asalin ƙauyen su Baba Sardauna na rugar Darma harda su Baba Sardauna ɗin wai zasu huta, suko suka shiryo suka dawo shine sai yau suke ganinsu.
Sai da su Abah