AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   94 / 213

279K to 282K   out of 636.6K words

fuskar nan babu walwala sai kwarjinin kamala dana ibada ke fita. Maanal da haushin tsayawar tasu ya kumeta taja tsaki tana ƙoƙarin ƙarasa abinda take a laptop ta fito kawai taji an buɗe side ɗin da taken, ɗagowa tai cike da masifa dan son ganin wanene suka haɗa ido da AA da yay kicin-kicin da fuska. Itama dai tayi ƙyau sosai cikin lass da akaima doguwar riga, ta kafa ɗaurin zarah buhari sai veil ɗinta da yay dai-dai da tsarin shigar tata. Tana ƙoƙarin rufe laptop ɗin kawai ya duƙo cikin motar a kanta, kafin ta samu damar magana ya ɗagata cak ya fito da ita. Idan tace al'amarin AA bai fara girgiza tunaninta ba ma ai tayi ƙarya, yanzu banda ikkanci a titin ALLAH zai ɗakkota a mota da safen nan mutane nata kai-kawo. Koma tace a anguwarsu data tabbatar ko wani bai sanshi ba wani ya sanshi duk da ana rayuwa ne irinta ba ruwan wani da wani ɗin nan a anguwar. Da sauri kuwa nasa drivern ya fito ya buɗe masa ɗayan side ɗin da yaga ya zagaya, a ransa kuwa dariyar halin ogan nasa yake, yayinda suka matuƙar birgesa duk da yanata wani sinne kai. Ajiyeta AA ɗin yayi ya gyara mata rigarta ya rufe ƙofar, ita kam ai tamayi sumar zaune ne ko mi zatace oho. Dan sam tama kasa masa magana dan al'ajabi. Shigowarsa wajen da yake zaune hannunsa riƙe da tarkacenta da drivern Abah ya kwaso mata ya sata kallonsa ta gefen ido, sai wani ɓaɓɓata fuska yake kamar ba shine daren jiya ya gama aikata mata abin kunya ba. Aikinsa ya cigaba da yi batare daya sake kallonta ba yana cema drivern sa, “Muje” a daƙile.
     Yanda ya basar ya cigaba da aikinsa itama sai ta basar ta cigaba da nata aikin. Har suka iso Company wani magana bai shiga tsakaninsu ba. Kai babu ma wanda ya kula ɗan uwansa. Koda motar ta tsaya kuma kasancewar tana tattara kayanta shine ya fara fita. Tayi zaton zai yi tafiyarsa ne. Amma sai a mamakinta ya zagayo ta inda take ya buɗe mata. Koda ta fito kuma sai ya saka hannu ya amshi kayan hannunta harda handbag ɗin kamar jiya. Ya kuma kama hannunta da ɗayan hannunnsa. Nashi kayan kuwa sai drivern sa daya bisu da kallo yana murmushi ne ya tattara yabi bayansa da su.
     Yau ma cike da gulma wanda suka iso ke binsu da kallo suna kuma gaishesu da girmamawa. Yayinda wasu ke gwada son amsar kayan hannun AA ɗin amma sai ya girgiza kai kawai alamar (a'a). Kamar dai jiya harda masu leƙensu ta windows dan gulma. Suna shigowa kuma kowa ya nutsu aka shiga miƙa musu gaisuwa...
Yau dai kai tsaye office ɗinta suka nufa. An gyara komai fes an saka air freshener masu daɗi, shine ya kunna wutar office ɗin dake a kashe, har saman desk ɗinta kuma yaje ya ajiye kayan hannun nasa batare daya kalleta ba ya nufi hanyar fita, ita dai tana tsaye tana kallon ikon ALLAH. Har yaje ƙofar sai kuma ya dawo gabanta yaja ya tsaya. Cike da gargaɗi fuskarsa a tamke murya a dake ya ce, “Daga yau wannan ya zama first and last da zaki bishi in har ba tare da Abah ba. Azumin mi kikeyi kuma”.
     Yanzun kam kallonsa tai cike da mamaki, sai kuma ta tura baki gaba ta ce, “Na nafila mana”.
        “To sai kisan yanda zakiyi da shi tunda baki sanar min ba.” ya ƙare maganar da dalla mata harara ya juya zai fita..........✍️


_Oh oh AA rigima azumin ne kuma sai an sanar maka munga idi🏃🏃🤣_


*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣0️⃣


______________

*_LADIES COLLECTION AND MORE_*
08169307477
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,

LADY'S COLLECTION AND MORE

ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻

Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Less
Hijabs
Supplements
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko

08169307477

Address bayan gidan drugs katsina State

Kayan mu masu inganci ne sosae

Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯


***********
_______________

20


WANNAN SAƘONKU NE😊

LA'ILAHA ILLA-ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN!!

......A tunzure Maanal data cika tai fam da wannan mulkin mallaka ta ce, “Kamar ya nasan yanda zanyi da shi? Yanzu ibadar ce kuma dan zan yi sai na sanar maka?”.
        Sai da ya buɗe ƙofar sannan ya waiwayo ya kalleta, cike da izza ya furta, “Ya rage naki”. Daga haka yay ficewarsa. Harara ta rakashi da ita. Sai kuma tama ƙofar gwalo dan shi dai ai ya riga ya fice abinsa. Kujerar zamanta ta nufa ta zauna tana ƴar dariyar ƙeta. Dama babu wani azumi da takeyi, tayi hakan ne dan gujema halinsa na salon tattaɓata daya ɗauka. Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro ƙyaƙyawan bottle mai kama da cup ɗin nan na zamani dake cike da tea, sai gasashshen bread a ƴar bowl data sanyo batare da ko sanin Oum ba. Dan Inte tasa ta haɗa mata su. Hankalinta kwance ta fara aikinta tana karyawa. Sai zabga murmushi take da bata san na miye ba itama. Kawai dai ta tsinta kanta a cikin nishaɗin yin hakanne....
     Kusan ƙarfe goma takarda ta iso mata daga office ɗin HOD. Bata komai bace sai ta tafiyarsu. Komai an kammala, sannan iya su da zasuyi tafiyar an basu hutun zuwa aiki gobe, idan ma daga yau mutum zai wuce gidan duk an basu dama amma sai zuwa break bayan anyi zama da su, suyi shiri kawai dan jibi in sha ALLAHU ƙarfe biyar na yamma jirginsu zai ɗaga. Ajiyar zuciya kawai ta sauke a hankali, zata ƙarasa ayyukanta kawai yau ɗin ita kam bazata tafi yau ba. Ƙarfe sha biyu suka shiga meeting. Sai a lokacin taga sauran wanda zasu yi tafiyar da su. Ashe harda cikin manyan ma. Dan akwai CFO, sai CMO, WCD da sauransu..... Sunyi nisa a meeting ɗin kafin CEO ya shigo shida Assistant ɗinsa. Bayan sun zauna ya nema afuwar jikinrinsa, acewarsa yana da baƙi ne. Maanal na ɗagowa suka haɗa ido. Da sauri ta janye nata. AS ne yay musu bayanin abinda zasuje yi, dan kowa da fanin sa, tare da karanto musu dokokin tafiyar. Zasu yi kwana goma ne, kenan zasu dawo azumi nada kwanaki takwas, dan yau saura kwana huɗu a fara. Daga ƙarshe yace kowa zaiga alert na kuɗi a cikin account ɗinsa domin shirin tafiyar. Bayan komawa ya zauna AA ya dubesu a dakensa, idonsa ne ya sauka akan Maanal a karo na barkatai, sai dai yanzu ita ba kallonsa take ba, tana magana ne da Yaqub ƙasa-ƙasa, da'alana akwai bayanin da yake mata da bata gane ba a maganar AS. Shima janye nasan yayi yanayinsa na canjawa sannan ya fara musu nasa jawabin mai cike da gargaɗin daya saka Maanal ɗagowa ta dubesa, harara ya sakar mata a kaikaice, wani gefen kuma nasiha ce. Ya rufe da addu'a daga haka meeting ɗin ya tashi. A tare Maanal da Yaqub dake mata sallama suka fito, sai kawai jitai an riƙo hannunta, juyowa tai da sauri, sukayi ido huɗu kuwa da mai gayya da aiki. Wani banzan kallo yay mata, sannan ya zubama Yaqub wani kallon gargaɗi daya sakashi barin wajen da sauri.......

__________★

اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
_Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so._

_________★

AIRPORT

          Cike da farin cikin dawowarsa ƙasar haihuwarsa bayan dogon hutun daya sha na watanni uku yake fitowa a jirgin. Yayi fresh da shi dan ma tsufa ya cinye komai. Ƙarfarsa na gama sauka bisa ƙasa idonsa ya sauka kan amaryarsa, gefe kaɗan Oler ne da Rabilu sai sauran yaransa dai na siyasa. Sen... Bukar Kaugama yay wani murmushin jin daɗi mai cike da ma'anoni. Dan kuwa abu biyu ke ɗawainiya da shi, farin cikin dawowa ƙasarsa a gaɓar da zai mallaki ƴar shilar amaryarsa Maanal, da kuma kewar ƙasarsa ta haihuwa. Babu kunya amaryarsa tazo ta rungumesa tana masa barka da dawowa cike da farin ciki.
      Cikin irin nasu salon na manyan ƙasa ya wani ɗan bubbuga bayanta da ɗan mata ƙaramin kiss a gefen fuska sannan ya janyeta daga jikin nasa ya riƙe mata hannu. Sai lokacin su Rabilu sukayo wajensa suma. Fuskokinsu da farin ciki suke masa barka da zuwa. Shi ko yana amsa musu da kulawa. Basu wani ɓata lokaci ba suka ɗunguma inda jerarrun motocin da sukazo tarbarsa suke. Aka buɗe masa wadda tafi kowacce daukar ido shi da amaryarsa suka shige. Motocin na fitowa a airport ɗin tawagar uwargidansa na isowa itama tarbar tasa. Sunata sauri ganin sun makara, sai dai kuma basu dace ɗin ba. Drivern ta daya lura da motocin ne ya ce, “Ranki ya daɗe ai kamar ha Excellency ɗin ma can fa har sun fito”. Da sauri ta kalla motocin itama, tabbas kuwa motocin gidansu ne, sai dai motar da ta tabbatar yana a ciki tasan tana a gidan amaryarsa ne ajiye. A take ranta ya ɓaci matuƙa. Cikin fushi da jin zafin kishi tace, “Mubi bayansu”.
     Babu musu yay reverse, hakama drivern daya ɗakko yaranta shima, sai ma'aikatan gidanta, motar ƙawayenta ce ƙarshe, dan kuwa shiri tai na musamman akan dawowar tasa yau tare da shirya masa wani ƙwarya-ƙwaryar liyafa dan ranar tayi dai-dai fa Anaversary ɗin aurensu. Motocin su amarya na gama shiga maigadi zai maida gate ya rufe na uwargida suka iso. Dole ya dakata dan aguje suke. Fuskar Sen... Bukar da murmushi ya fito a motar, dan amaryar tasa ce ke zuba masa iskanci a motar, shiko ya narke mata. Da ƙyar ma ta bari suka fito. Sai dai me yana gama fitowa Uwargida ran gida na tsayawa a gabansa kamar wadda aka jeho. Hamshaƙiyar mace data amsa mace, dan kuwa sune manyan mata. Amma (iyayi na mutum nan yace bai son ƙiba🙄, shima kuma fa ƙaton gaske ne🥱). Yanda uwargidan ke kallonsa cikin ido dole ya ƙaƙaro murmushi tare da ɗan rungumota yana faɗin, “A'a ku kuma maimakon airport nan kuka yo?”.
       Itama a maimakon bashi amsa ɗagowa kawai tayi daga jikinsa, sai kuma ta kama hannunsa a dake ta ce, “Muje ko! Ga mutane a waje na jiranmu”.
     Gaba ɗaya daburcewa sen.. Bukar ya nema yi, dan kowaccensu da shirinta take an kai sunansa wajen teacher na zaure, ya kalla amarya ya kalla uwargida. Kowacce ta haɗe fuska abinta kamar dai a film. A ransa faɗi yake (wadda duk zata ɗaukeni gaba ɗaya daga hannunku ta kusa zuwa ai tula-tulan banza). Amaryar ƴar tsiyace ya sani, ita kuma uwargidan bata da yawan magana amma itama fa ba daga baya ba tasan ta inda take dafa shi duk rashin mutuncin da yake musu musamman ma ita da babu kalar da bata gani ba. Fuuu amaryar ta shige ciki ita mai zuciya, a zatonta ai zai biyota kamar yanda yake mata idan su kaɗai ne musamman ludayinta na akan dawo, (bata san yanzu akwai Manaal ba😂), wannan ya bama uwargida dama ta jashi suka wuce......

_________★

اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ.

Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum.
_Ya ALLAH! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya ALLAH! Ka karya su, ka girgiza su._
________★

     Idan Maanal tace yanda taga fuskar AA hankalinta bai tashi ba ƙarya tayi, ita shaida ce tun suna ƙanana ya tsani yaga tana kula wani, ko ƴan uwansa su Fawzan dan baida yanda zai yi ne kawai. Addu'a ta shiga karantowa a zuciyarta ita dai, dan yanda ya damƙi hannun nata ma ji take kamar ta fasa kuka. Suna shiga office ɗinsa a kusan tsakkiya ya sakar mata hannu, batare dako kallonta ya sakeyi ba ya wuce kujerarsa ya zauna. Aikinsa ya cigaba da yi tamkar yama manta da ita. Itama tun tana basarwar harta koma satar kallonsa, tama kai ta zuba masa idanun kai tsaye. Kusan mintuna ashirin taji ƙafafunta na neman sagewa, zuciyarta kuma nata angizata akan taje kawai ta bashi haƙuri, dan itama abinda yay ɗin ya sake fargar da ita alaƙarta da Yaqub fa dole ne ta tsaya a iya matsayin daya dace, ba kamar ada da suka ɗan fara ba kodan darajar aure da kare mutuncin wanda yake a matsayin mijin nata kuma ogansu a ma'aikatar gaba ɗaya. Sai kuma nasihar Ammie da Nene da ma Oum take mata faman kai-kawo a rai, basuce ta wulaƙanta kanta ba, amma sun gargaɗeta ta sauke nauyin dake kanta musamman a gaɓar data san abu kuskurenta ne. Gyarawar tata shima zaisaka ya gyara nasa kura-kuran su gina ƙyaƙyƙyawar rayuwar aure mai nagarta, dan ita wannan rayuwar tasu ta yanzu tana da banbanci da wadda sukai a baya ta ƙuruciya musamman ga ita dake ƙarama sosai, tunda ko acan bayan tasan nagaba yay gaba, kawai dai ita dashi haɗuwar jini ce bawai abotar kai da kai ba. A hankali ta fara takawa zuwa inda yake tamkar mai koyan tafiya, maimakon zama a visitors chair kai tsaye inda yake zaune ta zagaya. Kusa da shi kaɗan taja ta tsaya, hakan datai ya saka ziciyar AA ƙara gudu a ƙirjinsa, dama can bawani aiki yake yi ba, dan ji yay bama ya fahimtar komai. A yasan shima yana da kishi mai karfi a kanta, dan haka yake so ta gane kuma ta kiyaye, duk da kuwa sanin hakan a gareta game da shi ba sabon abu bane ba ai, amma ya fahimci kamar ta manta ne....
       “AA!”.
  Ta kirashi da sunan da abakinta ya fara jinsa, ga shi nan kuma ya bisa dan wasu da yawa a yanzu bama su iya tantance ainahin sunansa sai AA Darma kawai. Duk da harbawar da zuciyarsa ta shiga yi a ƙirjinsa saboda tasirin kiran sunan nasa da tai bai kalleta ba, aikinsa kawai yake kamar gaske. 
         “Besty fushi fa ba ƙyau!”.
    Ta faɗa tana leƙa fuskarsa cike da shagwaɓa. Nan ma tamkar dutse haka yay mata shiru. To itama fa zuciyar tata ta fara hawa, dan haka tai shiru kawai tana kallonsa. Tsahon mintuna uku taga ba kulatan zai yi ba kawai saita nufi barin wajen. Karan farko ya ɗago ido ya bita da kallo, itako ta wuce fuuuu alamar dai itama ta hau sama. Shima ai yasan yanda ya tsani yay magana ai masa shiru haka itama ta tsani ɗabi'ar. Har ita zai nunama zuciya da kishi, ita jiya ba ɗaukarta yay ya kaita wajen budurwarsa ba dan wulaƙanci, amma mitace masa, sai shi dan kawai ya ganta da abokin aikinta, to shike nan kuma bazata dinga mutunci da mutane ba'a Companyn?.
      Tana gama fita yay wani irin watsar da file ɗin hannunsa akan desk ɗin, sai kuma ya buga shi ya juya kujerar ya kalla bangon wajen daya kasance glass....

    Manaal na shiga office ɗinta kayanta ta tattara tsaf tai fitowar ta. Duk inda ta gitta gaisheta akeyi, ita sai suka ma ƙara bata haushi. ALLAH ya sota sanda ta fito harabar kamfanin duk ana ciki, sai securitys ne kawai ke ɗan kai-kawo. Suma duk wanda ta gitta sai ya gaisheta, drivern AA dake cikinsu yana hira yana hangota ya taso da sauri, gaisheta yay, tare da faɗin bara ya ɗakko mota. Amma sai sai tace da fa shi karya damu su Abah na jiranta a waje. Jin tace Abah ya sashi dakatawa, haka ta fita a ƙafa a kamfanin.
        Tun fitiwarta harabar kamfanin sosai idon AA ya sauka a kanta, har maganarta da drivern sa da gaisuwar da securitys suke mata duk ya gani, kawai dai baya jin mi suke faɗa ne. Ji yay zuciyarsa ta ƙara hasala. Da ga zaunen da yake bazai iya ganinta ba yanzu saboda ta fita a kamfanin, dan haka ya miƙe tare da matsawa jikin gilashin. Sai ko ya hangota ta tsaida wata taxi ta shiga. Idan AA yace zuwa yanzu zuciyarsa batai kumburar da take neman fashewa ba yayi ƙarya. Shi yarinyar nan zata wulaƙanta da mutuncinsa a garin nan tana matarsa ta shiga taxi, shi zatama laifi ta fishi zuciya kuma. (Amma ai ta zo lallashinka kaƙi kulata) Wani sashe na zuciyarsa ta faɗa. Ji yay kamar ya kaima zuciyar naushi, amma dai ya daure, wajen ya bari gaba ɗaya, sai ma ya koma rukunin kujeru ya zauna, dan yasan ko aikin yace zai cigaba shirme kawai zaita tafkawa.........✍️

حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
_ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro._





*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA

94 / 213

Chapters