Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Babban Yaya cayay masa wani ɗaurin aure zasuje na ƴar abokin Abah ya bashi kayan jikinsa yace ya saka, duk da yayi mamakin ganin ahalinsu da abokansa da yawa a wajen bai samu damar tambaya ba. Yana zuwa ya rungume Oum ya sakar mata kuka, ALLAH yaso ma daga ita sai shi da AA da RK sai Babban Yaya ne a ɗakin. Itama Oum hawayen take, a haka ta daure ta goge nata tas sannan ta ɗago Fawzan ɗin ta zaunar, shima goge masa nasa hawayen tayi tana murmushi. Albarka ta dinga saka musu, tare da addu'oi masu nauyi akan wannan aure. A haka Abah ya shigo ya samesu. Cike da tsokana ya ce, “Ja'iri, har yanzu kukan farin cikin bai ƙare ba kazo ka tasa uwaka kana cigaba da yi”.
Dariya Oum tayi, su Babban Yaya na murmushi. Zama Abah shima yay, ya sanya musu albarka sosai dan shi kansa shi kaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki a yau. A nutse yayma Oum bayanin ai Babban Yaya, RK, da AA ne suka shirya komai suka kuma roƙi alfarmar ɓoye zancen har sai an ɗaura. Tariya kuma sai nan da sati huɗu Najma ta kammala jarabawarta. Albarka itama Oum ta dinga saka musu.
A falo ma dai da tsakar gida duk wani ahalin Darma yayi farin ciki da wannan aure. Hajiya Majdiya kanta sai da tai hawaye. Sai da su Mah-mah sukaita lallashinta dan harga ALLAH abin yazo mata a bazata kamar yanda ya zoma kowa ma....
★Babu wanda zai ce ga halin da Nibras take ciki game da wannan aure, an daiga uwarta ta iso da wasu danginta sun shige sashen. Fawzan kam baima tuna da wata ita Nibras ba balle ya leƙata yasan yaya take...
Sai dai abinda kowa bai sani ba koda Nibras ɗin taji wai an ɗaura auren Fawzan shiru kawai tai na ɗan lokaci, sai kuma ta ɗan taɓe baki batace komai ba dan hankalinta sam a nan ɗin yake ba duk da ƙirjinta sai da ta buga. Amma sai huɗubar da sheɗaniyar zuciyarta ke kissima mata tafi rinjaya a can. Sai da mamanta tazo ne su ransu a ɓace sannan ta sakar mata kuka da faɗin ita bazata zauna da Fawzan ba tunda ya ƙara aure miye-miye....
________★
Su Maanal dake gidan Shahidah ma labari ya iske su, duk da Maanal tasan da shirin itama sosai taji farin ciki, aiko nan suka zagaye Najma. Kowa da abinda yake faɗa na farin ciki har sai da ta sanya musu kuka dan abin yazo mata a bazatar ne itama. Sai da Didi Shahidah ta ɗauketa a cikinsu ta maidata ɗakinta. Babu ɓata lokaci ta sanyata tai wanka, acewarta bashi yiwuwa amarya ta zauna a haka dole taci gayu duk da ba yanzu ne biki ba. Aiko sai ga kiran Oum ma ya shigowa Shahidah. Tace za'azo ɗaukar Najma ɗin yanzu. Su kuma shirya dan itama Maanal da wuri za'azo ɗaukarsu saboda ana son zuwa dinnar da wuri a tashi da wuri.
Ana wucewa da Najma kuwa itama Maanal aka hau shiryata, dan zuwa lokacin la'asar tayi. Sai kawai ƴar shagwaɓar ta kama musu kuka. Dan wlhy jitake tamkar yanzu ne za'a fara kaita gidan su AA ɗin. Haka dai aka gama shiryata cikin atamfa datai matuƙar ƙyau ta kuma samu ɗinki na nutsuwa. Uncle Sadeeq, Daddy da ya zo ɗaurin auren Najma ya wuto nan, Uncle Ahmad mijin Amaal, sai su Nene sukai mata faɗa da nasiha mai matuƙar ratsa jiki da ɓargo. Daga ƙarshe suka sanya mata albarka da fatan alkairi a rayuwar aurenta. Ƙarfe biyar saura haɗaɗɗun motocin ɗaukar amarya daga manyan yaran Abuja suka iso ƙofar gidan Didi Shahidah. Ya subahannallah tsarin ya matuƙar haɗuwa, motar amarya a tsakkiya tasha flowers. Su Nusaiba dai ai tun jiya sun gama mutuwa a tsaye. Daga uhhm sai uhhm kawai kake ji a tsakaninsu. Haka suma rukunin ƙannen Huznah, abin duniya ya ishesu sai ƙiyastawa suke a ransu da yanzu fa Huznah ake ma wannan hidimar.
A nutse Nene ta saka Maanal dake uban kuka a motar RK dan shine zai ɗauki amarya shi da Fawzan. Surukan Nene sai zabga guɗa suke, masu hotuna nayi masu videos nayi. Har motocin suka iso gidan Darma Maanal dake kwance jikin Nene na hawaye, dan yanzu kam tasan ba wasan yaran da akai a watannin baya bane zaman aure ɗan gaske aka kawowa yi a karo na biyu wannan gida. Har ciki motar amarya ta shiga, su Ummah tsoffi suka fito da kansu suka tarbi amarya. An fara kaita sashen Oum, Oum ta rungume abarta tana share hawayen farin ciki, Babynta ta dawo kusa da ita a karo na biyu matsayin matar ɗanta. ALLAH zai cika mata burinta. Bayan addu'oi aka fito da ita aka nufi sashen Mamy. Anan kam dai cike da bariki su Hajiya Turai suka tarbesu, sai dai Babu Mamy, dan tana can kwance a gado an saka mata ƙarin ruwa. Dan faɗuwar datai ɗazun sume musu tayi, shine Hajiya Turai ta kira wata ƙawarta Nurse tazo kamar ƴan zuwa biki, itace ta duba Mamyn ta tabbatar musu jinjinta yayi masifar hawa, dan haka bayan ta farfaɗo da ita tai mata allura mai ƙarfi aka saka mata drip kuma. Shine suke ɓoyewa dan basu son ko Abah yasan halin da ake ciki. Babu wanda ya tambayi rashin ganinta a wajen tunda ansan yanda takema Oum kara. Su sukai addu'oi duk da basu kai ciki ba. Daga nan aka dawo da Maanal sashenta. Bayan an sakata tayi alwala aka shiga da ita ciki bakinta da addu'a. Anan bedroom ɗin ƙasa suka ajiyeta bisa umarnin Nene...
Gaba ɗaya yaran Hajiya Yaya dana Hajiya Basariyya sun gama sumewa a tsaye. Karo na farko na rayuwarsu suka fahimci ashe ubansu yaron masu arziƙi ne kawai, dan wlhy a dukiya irin ta wannan gidan da ginin kawai suka gani mahaifinsu ba komai bane. Dan wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saka motar 90m ba komai bace a lefe da sukai. Dole Huznah da Hajiya Basariyya ke haukacewa kambuuu...
Basu ƙara raina kansu ba sai da aka fara shigowa da wasu irin haɗaɗɗun manyan bowl glass na abinci, yo in banda kasada irin ta mai kuɗi a ranar biki zaka fito da kayan gilashi matsayin kwanon bada abinci ga ƴan biki. Lemuka kam kala-kala ba'a maganar su coc.. fanta... Da ire-iren su ƴan biyu sha biyar, kai jama'a, ashe jiya da suke jinjina kwalliyar mutanen ƙaramin wasa ne, yau da take ranar dinnar zasu baza ido susha kallo ɗan gaske. Mamaki ya ishesu ta yanda su Ammie suka san waɗan nan mutane haka? Wai harma ace shi AA yama Maanal fyaɗe. Duk da ƴaƴan Ammie kaf ƙyawawa ne matan manya, amma yanda ƙasar nan ta koma ta bani gishiri in baka manda, auren ƙwarya tabi ƙwarya mai kuɗi ya aure ƴar talaka tsananin rabo ne wlhy, indai iskanci ne a sheƙe aya zasu yarda da ƴaƴan malam Shehu, amma a fagen raya sunnar MANZON ALLAH ba wannan maganar, in kikai wasa ma sai dai ki tsinta shagalin bikinsa na yawo a social media. Koki zama cikin ƴan aikin shirya bikin.
Sai da kowa yaci ya ƙoshi dan kayan alatun da aka kawo musu duk ƙoshinka ka gani sai ka ci. Maanal ce kaɗai bata iya taci komai ba. Dan ita yau babban tashin hankalinta ace ita da AA zasu kwana. Addu'a take ALLAH yasa anan su Nene zasu kwana...
Bayan sallar Magriba mai kwalliya ta iso tare da Hajiya Shuwa, atake ta saka Manaal tashi ta shiga sabon wanka da wasu irin haɗin turarurruka masu ƙamshin tashin hankali, data fito kuma aka saka wani a wuta aka lulluɓeta da ƙaton bargo ta ƙasa kuma ta zauna a kujerar tsuguno. Tafi mintina talatin aciki dan Hajiya Shuwa tana ɗagawa tana ƙara turaren ne a cikin rushin. Sallar isha'i da ake kira ta bata umarni tashi tayi, Maanal tai sallarta a tsanake sannan ta zauna mai kwalliya ta fara nata aikinta.
Suma dai su Shahidah suna can suna nasu shirin dan Oum da kanta ta samesu, ta kuma tabbatar musu anan zasu kwana baza'a bar Maanal ita kaɗai ba karma suce zasuje gidan Shahidah jiyama tayi shiru ne kawai saboda Maanal zata kwana can
Murmushi Nene tayi, tare da sake jinjina karamcin Oum. Hummm jama'a, nace kunga yanda ake zane muku fuskar amaryarku. Abin ba'a magana dan tayi mahaukacin ƙyau na'a tsaya aita kallo. Su kansu su Amaal sai hotuna suke zuba mata. Sosai tai ƙyau komai ya fita da fitarsa, sai ƙamshi take zabgawa kamar a kamfanin turare. Kora su Amaal waje Hajiya Shuwa ta sake yi, suka fara shirya Maanal ita da mai kwalliya da wadda tai ɗinkin Maaanal ɗin. Wato jama'a, Material ne aka samu akama wani shegen ɗinkin doguwar riga na tada kan maƙiyi, aka bisa da stones masu shegen walƙiya da ƙyalli ta yanda in aka kashe fitila suke wani bada kala. Idan baka da lura ma bazaka taɓa cewa Material bane saboda yanda aka tsara mata ɗinki. Gashi ya wani masifar bin jikin Maanal ɗin tamkar an zanata a takarda. Komai ya fita da tashi fitar. Cikakkiyar ƴar gatan amarya kenan. Hajiya Shuwa ta sake binta da ƙamshi bayan an zuba mata ɗauri dasu ƴan kunne da sarƙa. Ita kanta Maanal jinta take tamkar ba ita ba, kamar wata Maanal ɗin ce aka canja. Takalma kawai ta sanya Hajiya Shuwa tace suje a haka after dress a saka idan zasu shiga hall ɗin. Dan rigar tayi bala'in fidda komai na surar Maanal shiyyasa ma akai after dress da za'a ɗora saman su. Duk da itama after dress ɗin ba wani mai kauri bace ba, telar datai ɗinkin ce ta dinkata itama kuma an bita da adon Material ɗin ne kamar dai kayanta na jiya. Wato Hajiya tasan takan tsiya, ita tasan miyyasa tace Maanal ɗin ta fita a haka..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣5️⃣
______________
........Amaal ce ta kama Maanal ta fita da ita dan Oum ce tai kiranta a waya akan a fito da Maanal ɗin su AA har sun iso. Hakama mutane duk sun shiga motoci dan tafiyar gaba ɗaya ake son yi a jere a tsare kamar yanda aka tsara wajen dinner ɗin.
A karo na farko Maanal taji zuciyarta na dukan tara-tara, tsakanin jiya da yau ɗin wani shakkar kasancewarta waje ɗaya da AA take yi, dan jiya wasu abubuwa masu nauyi ta dinga karanta a cikin ƙwayar idanunsa. Haka dai aka fito da ita babu yanda ta iya. Duk da kanta a ƙasa yake, an kuma rufa mata net har fuska hakan bai hanata jin idanun mutane a kanta ba, ga camaras na wayoyi da aketa binta da su, ji take kamar tai kuka. A dai-dai jikin falleliyar motar da RK ke tsaye ya juya musu baya da alama waya yake Amaal ta tsayar da ita. An riga da an buɗe musu dan haka ta taimaka ma Maanal ɗin da zuciyarta keta harbawa da sauri-sauri ta shiga. A hankali AA dake zaune a cikin motar yana binta da wani kallon ƙasan ido ya wani kalar lumshe idanun nasa daddaɗan ƙamshin turarenta na rige-rigen shige masa hanci. Itama dai nasa ƙamshin ne ya gama gauraye nata hancin tare da sanyin ac da motar ta ɗauka. Itama samun kanta tai da lumshe nata idanun nunfashinta na ɗan rawa. Sam bata yarda ta kallesa ba, har aka motsa da nufin tafiya, amma ta gaisheshi ƙasa-ƙasa, bataji ya amsa ba itama kuma bata sake magana ba. A bazata, matuƙar bazata taji shigar tattausan hannunsa da yay ɗan sanyi saboda acn da yake a ciki cikin nata hannun mai ɗumi da laushi, bata gama dawowa a hanyyacinta da riƙo hannun nata da yay ba taji saukar tausasa lips ɗinsa akan bayan hannun nata ya sumbata. Yanzu kam babu shiri dole ta ɗago ta kallesa, a cikin nasa dake mata narkakken kallo suka shige, sai ya sake shanyesu cike da ƙasaita ya motsa lips ɗinsa a raɗa ya furta, “You look great Mrs AA Darma, sai dai bazan taɓa iya barinki shiga a haka ba ina da matsanancin kishi kinfi kowa sanin hakan. Ke ɗin tawace ni kaɗai har a aljanna in sha ALLAHU”.
Sosai furucin nasa taji ya daki zuciyarta da girman gaske, dan haka ta samu kanta da lumshe nata idanun tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa har yanzu dan wani yarrrr take jin tsigar jikinta na tashi saboda yanda yake murza shi a wani irin hankali. Lallausan murmushi ya saki a karo na farko, duk da iyakar laɓɓansa yay abinsa hakan bai hanata jin fitar ɗan sautinsa ba. Shi ko sai ya wani ja idannun luuuu kamar zai lumshe yana mai kauda kansa gefe kaɗan har lokacin fuskar tasa da ɗan murmushin. Ita dai hannunta ta janye daga cikin nasa, bai kuma hanata ba. Jikinsa cike da kasala ya koma jikin kujerar ya kwantar da bayansa tare da gyara zamansa. Daga haka bai sake magana ba har suka iso hall ɗin da akai matuƙar ƙawatawa, dan tun daga farkon shigowa street ɗin zai baka tabbacin ana wani babban taro na manya. Dan kuwa duk wani ɗan tara dake ji da kansa a cikin Abuja musamman ƴan siyasa da ma'aikatun gwamnati dama abokan kasuwa sun halarci wannan dinner, hatta da shugaban ƙasa ana saka ran zuwansa (saura wani yace Tinbunu nake nufi🙄 to Shugaban kasar Naya Ramadhan B. Hameed Taura😏).
Cike da tsari da nagarta motocin suka kayantu a ƙofar hall ɗin, mutane suka fara fita a nutse suna shiga ciki, ango da amarya dai sai kowa ya gama shiga. Babu zato a karo na biyu Maanal taji AA na zame mata ɗan net ɗin da aka yana mata a kanta zuwa fuska, idannunta kawai ta lumshe zuciyarta na luguden daka, musamman saukar hannunsa a haɓarta dole ta sake matse idanun tsam. Babu zato ko tsammani taji saukar lips ɗinsa a saman nata lips ɗin. Ba gigicewa kawai ba jitai ita kanta motar da suke ciki kamar tana nutsewa a cikin ƙasa ne. Dole ta buɗe idannunta da sauri tana ƙoƙarin tureshi. Sai aka samu akasi hannun nata ya sauka a saman ƙirjinsa, ya kuma saka nashi ya riƙe ya hanata janyewar datai saurin son yi. Ɗayan kuma ya riƙe mata fuska ta yanda ta gagara janye lips ɗin nata. Sai da ya shanye lipstick ɗin da aka sanya mata yay mata masifar ƙyau kuma sannan ya janye nasa baya a hankali, sai dai har lokacin fuskokin nasu na'a gab-gab da juna kowa na busama ɗan uwansa numfashinsa. Ita dai idannunta dake cika da hawaye a rufe suke, wata irin kunyarsa take ji mai tsanani, ga tsoron yanda take ganin idanunsa a juye kuma a ƙanƙance alamar yana cikin wani yanayi mai girman gaske. Shi ko fuskar tata yake kallo kai kace yau ne ya fara ganinta, shi kaɗai yasan mi yake ji. Amma da yake gwani ne a kamewa ya fuske a binsa sam babu ko ɗigon zaƙuwar a kan fuskarsa da idanunsa a zahiri. Maimakon ma barin kunyar tata ta cigaba da tasiri a kofa zuciyar tasa sai yay yunƙurin ɓadda sawu ta hanyar kauda yanayin nasu gaba ɗaya.
“Miyasa kika bari suka sanya miki bayan kin san bana son kina sakawa a duk sanda zaki fita?”.
Ya faɗa da wata irin murya mai sanyi da zurfi ta yanda ita kaɗai ta iya jinsa. Dan koda ace da wani a kusa da su bazai ji abinda yace ɗin ba. Kauda fuska kawai Maanal tai ƙoƙarin yi gefe tana haɗiye hawayen dake neman zubowa daga idannunta na matsanancin haushi da firgici. Amma sai tayi jarumtar hanasu. Eh tabbas ta sani, dan sun sha yin faɗa a shekarun ma ƙuruciya idan ta saka janbaki idan zasu fita, yata takura mata kenan har sai ta goge, a wasu lokutan ma sai dai taji kawai yasa tissue ya kwashe mata shi da kansa, suyita faɗa dan ita harga ALLAH tana son jambaki, gata kuma dama ma'abociyar son kwalliya. Idan kuma ta saka shegen ƙyau yake mata musamman na yau ma dan ALLAH ya bata wasu kalar lips masu ƙyau da fitattacen shaf tamkar an zana mata shi. Gasu da zagayayyen baƙi kafin pink a tsakkiya, dan ko bata saka jan bakin ba sai kaga kamar ta saka ɗin ma a haka. Yanzun ma duk da ya shanye sai lips ɗin na nan da ƙyanzu kamar ma da lipstick ɗin har yanzu.
Yanda ta kauda kai sai shima bai sake magana ba, sai ma ƙoƙarin warware after dress da Hajiya Shuwa ta bashi yayi tare da warware ta. Sosai rigar ke wani irin ƙamshi mai daɗin gaske. Kaɗan ya ɗaga daga zaunen da yake ya ɗan ranƙwafo kanta. A wannan gaɓar kam numfashinta neman ɗaukewa yay, dan kusancin nasu mai girman gaske ne ta yanda wanda ke a nesa dasu ma zai iya ɗauka rungumeta yayi. Shi ko ko'a jikinsa ya yafa rigar a jikinta sannan ya koma mazauninsa ya zauna. Dai-dai nan kuma aka basu damar fitowa. Shine ya fara sauka, sannan ya zagaya ta inda take ya buɗe murfin. Hannu kawai ya miƙa mata batare da yayi magana ba, ita kuma tai shiru taƙi motsi balle ma ta bashi hannun nata, hasalima kanta a ƙasa yake har yanzu.
Hannun nata kawai ya kamo cikin nasa, dole