AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   122 / 213

363K to 366K   out of 636.6K words

da Maman Saheeba. Sai dai Nuratu babu lafiya wai tana ma asibiti an kwantar da ita. Dan tunda batun ɗaga bikin nata ya shiga kunnenta ta yanke jiki ta faɗi, tun kwana biyu da salla ta koma gida dan yin shiri biki dama. Baiwar ALLAH Oum, tana ji ta tasa ƴan hutunta gaba da bazasu koma ba sai anyi biki sukaje suka duba Nuratun. A can suka sami Mamy da Saheeba dan tunda rana suka tafi su. A mazan dai su Babban Yaya babu wanda yaje, shi AA ma baya nan yana Lagos, ya kuma ce bazai dawo ba sai ana saura kwana ɗaya....

________★

      Hakan kuwa ce ta kasance, ranar Alhamis ya dawo, a kuma ranar baƙin abokansa da bai san da zuwansu ba suka fara isowa. RK da Yaya Fawzan sun riga sun tanadar musu masauki. Anan ma gida tuni ƴan Kano sun fara isowa, zuwa yamma sai ga tawagar su Nene da sauran tarkacan Maanal, harda motocinta na lefe, sai kayan kawai aka sauke anan su a gidan Shahidah suka sauka. Dan itama Maanal can gidan Hajiya Shuwa ke shirin maidata.
     Ya subahannallah, kunga Maanal kuwa, tayi ƙyau harta gaji, ga ƙunshi ja da baƙi an zuba mata. Gashi yasha wanki duk da itama tasha kuka a wajen gyaransa. Ƙamshi ba'a magana ko kana nesa da ita ta gitta sai ka jishi. Bayan sallar zuhur Hajiya Shuwa da Ameerah suka kaita gidan Shahidah. Tuni ta faɗa jikin Nene tana murna, yaran kuwa suka zagayeta kowa na farin cikin ganin Mie-mie kamar yanda suke kiranta. Nene sai latsa jikin Maanal take tana santi. Su kansu su Amaal bakinsu ya kasa yin shiru. Dan gaskiya Maanal ta gyaru sai Masha ALLAH. Jin Ammie bazata zo ba Maanal ta samusu shagwaɓa, ta kira Ammien tana kuka. Lallashinta tayi da tabbatar mata nan da sati biyu zatazo in sha ALLAHU. Da ƙyar-da-ƙyar Maanal ta haƙura. Ranar kam ansha hirar yaushe gamo, dan su Maanal suna son junansu sosai.

      Washe gari juma'a Mothers event, na rana ne ƙarfe uku za'a fara. Kusan sha biyu sai ga su Aneesa sun iso daga Kaduna. Sosai Maanal tayi farin ciki, dan ba wasu ƙawaye tare da ita sai jikokin Nene da suma sai yau suka iso daga Kaduna ɗin. Isowarsu babu jimawa Najma da Maimoon, Batool, Lailah suka zo, suma sunce gara su dawo nan kusa da amarya cikin ƙawaye. Tare suke da akwatin kayan da zatai amfani da su. Kuma Uncle RK da AA ne suka saukesu. Sai da Maanal taji ranta ya sosu ganin AA koma ya nemeta, ba komai zata rama. Kamar wasa sai ga su Amraah suma sun iso, ashe Daddy ne ya tarkatosu kaf yace dole suzo ayi bikin da su.
     Ba ƙaramin girgiza sukatan su Nasiba yayi da ganin gidan Shahidah ba, dan ba taɓa zuwa sukayi ba har Amaal ma dake a cikin Kaduna basu taɓa zuwa gidanta ba. Su Shahidah kam tarba sukai musu ta mutuntawa, dan ko'a fuska basu nuna musu komai ba. Lokacin da suka iso ma har an fara shirya amarya, kowa kuma nata ƙoƙarin shiryawa sai kawai suma suka shiga ayari........✍️


To lokacin shoshalewa yayi, kowa sai ya tsuke ƙugu dan dole ne muyi rawar a ƙame ƙam🥱🤣🤣🤣🏃




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣3️⃣


______________


.......Gaba ɗaya AA mamakin ganin sabon bikin da suka shirya yake yi, dan Oum kanta da su Hajiya Majdiya ko lokacin kansu basu da. Shima sai abun ya fara sakashi nishaɗi da jin karsashin ango fa yake sabo fil-fil a leda, dama a wancan karon bai gayyaci kowa ba saboda bai kawo Bestyn tasa ce zata zama matarsa tasa ba, shiyyasa ya sallama komai babu wani shiri da yayi.. Al'amarin Oum ɗin tashi da ƴan uwansa bai gama girmar kansa ba sai da Fawzan ya kaisa masaukin da suka tanadarma abokan nashi, yaje ya sameshi harma da wanda baiyi zaton gani ba. Aifa nan suka tasashi gaba da mitar rashin sanar musu auren nasa, dan sai da suka iso suke jin ai an rigada an ɗaura sure tun kafin salla. Bashi da bakin bayani sai kawai ya bar Yaya Fawzan da musu sharhi...

  ________★

A can gidan Didi Shahidah kuwa wani shegen kwalliya mai natsuwa akema Maanal, komai dai-dai misali ba'a cika shi da shirme ba. Dan mai kwalliyar ƙwararriya ce tun daga Lagos Hajiya Shuwa ta ɗakkota dan komai daya shafi amarya itace keyi. Hatta kayan da Manaal zata saka duk shirin Hajiya Shuwa ne. Matar ta gogu da sanin takan duniya ne ƙwarai da gaske. Ƙarfe biyu da arba'in an gama shirya amarya Manaal cikin doguwar riga na lass daya tsaru da ɗinki matuƙa. Fitet rigace a ciki har ƙasa ta wani irin fidda ainahin surarta tamkar zane a takarda, sai akai wata a sama tamkar after dress sai dai itama da lass ɗin akayita ta sauka har tana jan ƙasa. Matuƙar zaunuwa ɗaurin kan Maanal ya zauna. Sarƙa ƴan kunne zuwa bangles kam ba'a magana. Dan dan ƙareriyar sarƙa ce da akama ma wani irin adon fararen stones ya rabba. Dole ka kalla wannan amaryar ka sake kallo dan takai zama abin kallon. To dama Maanal gidan gayu ce, balle yau ɗin ta dabance a gareta. Ita kanta sai take jin kamar ba ita ba. Lokacin da mai kwalliya da Hajiya Shuwa data iso suke fito da ita falo sumar zaune su Basira sukayi, su Zeezah kuwa suka shiga faɗin, “Woowww!!“ Suna miƙewa. Kafin kace mi hasken camara ya fara hasketa tako ina.
         Dai-dai nan motar ɗaukar Maanal ke isowa, dan yau ba ango ne zaizo ɗaukarta ba. Babban Yaya da kansa ne yazo ɗaukar ƙanwarsa, a tare dashi akwai Uncle Najeeb (ƙanen Abah da suke uwa ɗaya uba ɗaya kun dai gane wanda akai bikinsu da su AA).
         Sai da kowa ya gama fita suka shiga motocin dake can waje suna jiransu dan Babban Yaya ne kawai ya shigo ciki sannan Amaal da Hajiya Shuwa suka fita da Maanal. Babban Yaya dake murmushi ya ce, “ALLAH na gode maka, yau ga Lilly ta fito a amryar ta, amaryar ma ta Auta”.
     Dariya Amaal da Hajiya Shuwa sukayi, Uncle Najeeb ma ya murmusa dan shima dai gwanin tsare gida ne. Kan Maanal da idonta ya cika da hawaye a ƙasa ta rissina ta gaishesu. Kafin Amaal ta sanyata a motar. Amaal ce kawai ta zauna tare da ita, Hajiya Shuwa motarta ta shiga sai ta ɗauka su Nene.
      Masha ALLAH waje kam ya haɗu, dan ko makaho ya laluma yasan an gyara wajen. Ga ƙaton symbol da ke rubuce da sunan AA dana Maanal ɗin, yayi ko masifar ƙyau duk da babu hoto a jiki dan Alaj AA ya hana. Abinka da manya komai yana tafiya cikin natsuwa da tsari, dan sai da mutane duk suka shiga sannan Oum ta fito ita da Hajiya Majdiya cikin kwalliya domin shiga da amarya. Ango dai ba yanzu ba kamar yanda aka tsara.
      Wani irin rungume Maanal Oum tayi, jitake kamar yau ne aka ɗakkota daga KD aka kawo musu. Ga madarar ƙyau da Maanal ɗin tai mata. Hajiya Majdiya dake murmushi ta shiga haska musu camara. Kafin itama ta rungume Maanal ɗin.
      Ashe daga wajen hall ɗin wasan yara ne. Sai ka shiga daga ciki zaka tabbatar da eh an shirya bikin ƴar gata. Mata ne zalla a cikin hall ɗin, ƴammata da manyan iyaye da sukafi kowa yawa. Yara ma ɗai-ɗai ne a wajen. Tunda mc ya fara zubama amarya kirari hall ɗin yay tsitt, kowa ya zubama ƙofa ido musamman ta ɓangaren Darma Family da dangin Mamy, dan daga ƙarshe dai sun ajiye komai a gefe acewarsu sai an gama biki suma sun shigo tawagar dan suna son komai ayi akan idonsu ta yanda idan na Nuratun ya tashi ba'ayiba su sami nayi ƙorafi. Hajiya Majdiya ce ta fara shigowa, bayan kusan minti ɗaya ƙofar ta sake zuge kanta Oum da Maanal suka bayyana. Oum na riƙe da hannun Maanal ɗin. Tuni hall ɗin ya ɗauka ƙananun ƙunƙuni na ambaton Masha ALLAH dan harga ALLAH ko maƙiyi yasan Manaal tayi ƙyau sosai. Mamy kam da ƴan uwanta babu wanda bai ji abu ya sokar masa ƙahon zuciya ba.
       Oum ta zaunar da Maanal a kujerar da aka tanada domin ita, ta ɗan gyagygyara mata rigarta kafin tai shirin barin wajen. Hannunta Maanal ta riƙo cike da shagwaɓa, Oum ta juyo tana kallonta. Sai kuma ta dawo ta riƙe hannunta cike da kulawa tace, “Miya faru?”.
      Idon Maanal cike da hawaye ta ce, “Oum dan ALLAH ki zauna tare da ni anan, ko Didi ta dawo, bana son kowa na kallona”.
     Murmushi Oum tayi sosai, tare da kai hannu ta ɗaukema Manaal ɗin ƴan hawayen da suka taru mata a gefen ido. “Yau ranar farin ciki ce Baby na ba ranar kuka ba, ki yi haƙuri yanzu Auta zai iso shima bake kaɗai zaki zauna ba ai. Kin taɓa ganin amarya ta zauna da mamanta ai sai a mana dariya ace ango yaƙi zuwa”.
        Yanda Oum ɗin ta faɗa sai ya bama Maanal dariya. Murmushi ta saki mai sanyi daya wani mata ƙyau. Oum ma sai ta murmusa tana tashi. Sosai Maanal ke jin idanu sun mata yawa, sam bata ƙaunar kallo, takurata yake yi. Tana ɗan bin mutane da kallo ƙasa-ƙasa itama ta hango wani kallon tsana da Mamy ke mata ita da danginta. Sai kawai yanayin nasu ya bata ƙarfin gwiwa taji wata dakewa ta musamman ta risketa. Aiko sai ta ƙara dakewa ta ƙawata fiskarta da murmushin da ya tsaya musu kuwa a ƙahon zuciya. An fara buɗe taro da addu'a, sai ɗan abinda ba'a rasa ba aka sanar da isowar tawagar ƴan discussion house. Hauwa'u Jidda, Ummul-Adnan. Ummu Fharuk. Oum Zarah. Maman afrah. Hafsy gayu (Mmn Ajmaal) (ر قية موس). Daddy's girl (Aysha). Hafsy Gayu. Leila. Mrs lawal. Mrs Bash. Fiddausi sani. Aunty Saliha. Aunty maryam. Maman faruk. Saraunia. Sharifa Ahmed. Maman meema .Oum shuraim. Mrs Affan. Maman Fa'izz. Meeno. Oummu nawal. Zubaida chiroma. Oum zarah & muhd. Fattu. Maman Hameeda, Aminatu, INDOBATIK NG. (Kai kuna da yawa, amma dole a dinner na antayo sauran😄👍🤏.)
    Ohhh ohhh zokaga mutanen nawa yanda suke shigowa cikin nutsuwa da ƙasaita, ƙyau iya ƙyau wanka iya wanka. Su ɗin na musamman ne, dan haka wajen zamansu ma ya kasance na musamman dan dama an tanada musu shi. Kamar jira suna gama zama ango ma ya iso da tawagar abokansa. Tuni kallo ya sake komawa sama wai shaho ya ɗau giya. Uhhhm uhhmm inji mai ciwon haƙori, kunga angonku kuwa, nace kunga ango AA Darma kuwa? Ya subahannallah, tabbas ranar aure daban take ga kowanne mata da miji. A yanda tsarin yake amarya ce zata je da kanta ta taro ango. Dan haka AA da tawagarsa suka tsaya a waje, Shahidah ce ta kama hannun Maanal suka iso har wajen ƙofa, sai da aka tsayar da Maanal MC ta gyara mata zaman rigarta sannan akace da ango bismillah ya shigo.
        Fin minti ɗaya bashi da niyyar motsawa, sai da RK ya tsungunesa. Hararrasa yayi kaɗan, kafin ya motsa a nutse ya shigo cikin hall ɗin. Wani irin shaaaaaah zuciyarsa tayi sakamakon saukar mayan oily fararen idanunsa masu kamar an watsa madara akan Maanal dake tsaye kanta a ƙasa. Tuni wani kirari da mc ta jeroma AA ɗin ya saka Maanal ɗaga idanunta slowly ta sauke a kansa itama, shima dai kallonta yake, zuciyarsa na ambaton sunan ALLAH maƙagi gagara misali daya mallaka masa wannan ƙyaƙyƙyawar halitta matsayin iyalinsa, lambunsa na hutawa. Mc ta kama hannun Maanal suka tafi a hankali har inda AA ke tsaye, wani irin lumshe idanu Maanal tayi, ta sake buɗewa a lokaci guda tare da motsa lips ɗinta kaɗan ta ce, “Barka da isowa mijin Maanal”.
       Shima cike da tasa ƙasaitar ya motsa nashi lips ɗin ya furta, “ALLAH yay miki albarka matar Ajwaad”.
       “Auuuwwwww!!”.
   Mc ta faɗa cike da salon iskanci daya saka hall ɗin ɗaukar hayaniyar ƙananun dariya. Mc ɗin kaɗai taji abinda suka faɗa, amma yanda tai ɗin sai mutane sukai tunanin wasu manyan magana ne daban. Cike da nutsuwa Maanal ta buɗe masa hannayenta kaɗan alamar yazo gareta ta rungume shi tana wani irin murmushi mai sanyi, AA da gaba ɗaya yaji yana narkewa ya shiga takowa a hankali garetan, yana gab da isowa ta wani juya masa baya da sauri tana sake ƙawata murmushinta, sai kuma tasa duka hannayenta ta rufe fuskarta. Miza'ai in ba dariya ba. AA ko ya wani kalar basarwa yana cije lips, batare da yace komai ba ya ƙaraso kusa da ita suka jera. Batare da ya riƙe ko hannunta ba suka shiga takawa a hankali har mazauninsu, sai lokacin ya taimaka mata ta zauna tare da gyara mata rigarta sannan shima ya zauna. Hannunta ya kamo a hankali cikin nasa ya rumtse. A tare suka saki ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ƙasa-ƙasa ya ce, “I miss you my half. Irin wannan ƙyau haka ai sai kisa na hana bikin”.
      Maimakon ta bashi amsa sai tai murmushi kawai tana risinar da idannunta ƙasa. Dan wani annakirin kallo yake mata mai matuƙar ratsa ɓargon jiki. An cigaba da gudanar da abinda ya tara mutane. Matuƙar ƙawatarwa taron yayi, komai ya ƙayatar yanda ya kamata. Anci ansha amarya tasha kyaututtuka wajen iyaye su Umma matar babba Sardauna, su Mah-mah, su Gwaggo Khadijah, su Mom mahaifiyar Abah kenan. Mamy ma ta daure ta bayar😜 bisa shawarar babbar yayarsu. Sannan aka dawo kan ƴaƴa su Hajiya Majdiya, kai harda ƴammata da ƴaƴaye abin masha ALLAH. Daga ƙarshe Oum uwa maba da mama data saka nata sai da zukata suka girgiza. Gab da magrib taro ya tashi lafiya. 
      Yanzu ma dai Babban Yaya da kansa ya maida Maanal, wannan tsari ya taimaki Maanal inji AA a zuciya, dan yanda yake jinsa ALLAH daga hall ɗin bikin zai iya wucewa da ita ya sauke matsalarsa, bai taɓa jin bazai iya jurewa ba irin yau, yanda Maanal tayi masifar ƙyau, ga wani irin ƙamshi mai marmasa gaɓɓai da ɓargon jiki. Ko a wannan zaman harga ALLAH girmama iyayensa dake cike da wajen da yayye ya sashi tsayawa a riƙe hannun kawai, shima a ɓoye yayi. Ya rabba! In ko haka wannan gyaran jiki yake to yata buɗe bakin aljihu kenan duk bayan sati biyu anama Maanal ɗinsa. Shi yasan Maanal kyakkyawa ce, sannan akwai tsafta da son gayu, amma a yau ta sake komawa wata ta musamman a cikin idanunsa. Ƙamshin da take kawai ji yake kamar zai suma. ALLAH ya dinga roƙo ya bashi ikon juriya yay kawaici. Dan yayi alƙawarin duk yanda suka tsara bikinsu shi mai biyayya ne..........✍️

A gurguje, zamuyi shagalin bikin kawai idan an kammala sai mu koma sauran ɓangarorin yanda abin zaifi tsari🏃🏃




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣4️⃣


______________



.........Washe gari asabar ɗunbin al'umma suka shaida ɗaurin auren Fawzan Aliyu Abubakar Darma. Da amaryarsa Najma akan sadaki 1mil cass da AA ya biya. A lallai su Baba Sardauna sun girgiza zukata da yawa. Abune a bazata, bazata mai ban mamaki da wani bai taɓa hasasowa zai yiwu a family ɗin ba. Musamman ta yanda babu wata alaƙa makamanciyar haka a tsakanin Fawzan ɗin da Najma. 
        Su Mamy na bedroom suna tattaunawa ana ƙara tausar Maman Saheeba da tun jiya take ƙananun magana da ita kanta Mamy ɗin kawai Saheeban ta faɗo musu kamar wadda aka jeho. A tare suka juyo suna kallonta. Babbar yayar su Mamy ta ce, “Haba Saheeba miyyasa baƙya sanin kin girma ne. Wane gudu kenan keda ke da ƙaramin ciki”.
     Cikin hakki Saheeba ta ce, “Gwaggo bazaki gane ba, kuna nan ciki baku san mike faruwa ba. Aure aka ɗaurama Yaya Fawzan”.
          A tare suka miƙe, Mamy ta ce, “Fawzan kuma? Wanne kenan? Ba dai nawa ba?”.
       “Tabbas shi kuwa Mamy, kuma da Najma”.
      “Wacece Najma?”.
Mamy ta sake tambaya dan duk ta ma rikice. Kai tsaye Saheeba tace, “Ƴar Aunty Majdiya dake gidan nan mana”.
     Yuuu-yuuu Mamy ta dinga gani a cikin idannunta, lips ɗinta na rawa tama kasa fusta abinda take son fustawa. Babu zato sai gata a ƙasa wanwar ta baje.....

Tofa Mamy ta baje a ƙar ku kawo ɗauki😮‍💨🏃🏃😌

  _______★

A ɓangaren su Oum kuwa wani irin farin ciki ne mara misali zagaye da su. Dai dai Oum na share hawayen farin ciki, lokacin su Fawzan suka shigo shima idanunsa sun kaɗa sosai dan ana ambata ɗaurin auren da sunansa bai san hawaye sun zubo masa ba. Abu ne na bazata, bazata irin wadda ba'a taɓa masa ba a rayuwarsa. Dan koda AA yace zaima Abah magana a haɗa da bikinsa a waccan ranar bai wani ɗauki abin serious ba. Yau kuma

122 / 213

Chapters