AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   195 / 213

582K to 585K   out of 636.6K words

su. Ruɗewa Maanal tayi saboda farin ciki. Sai tama rasa wazata fara kira tsakanin Babban Yaya da Yaya Fawzan. Yaya Fawzan dai wannan shine abinda dama ake fata, Babban Yaya kuwa rasa Anum yasa kowa ke ganin madadi ya samu. Kai sai kawai ta kira AA. Shima farin ciki yasa shi rikicewa, dama sun fita ne su ukun akan wani business ɗin Abah. Kawai AA ya haɗasu ya rungume. Suna tambayarsa mike faruwa ya kasa magana, sai bayan wasu sakanni ya iya musu bayani. Abinda AA yay tunani ne ya nema faruwa, dan Yaya Fawzan neman zubewa yay a ƙasa sai da suka riƙoshi. Sai kuka kuma. Yama rasa yazai fassara al'amarin, wai shine da ɗa, dama ashe yana haihuwa? Dama zai ga ɗan kanshi kafin ya koma ga ALLAH? Haka dama akeji idan akace matarka nada ciki?. Su kansu su AA yanayin Yaya Fawzan ɗin sai da idanunsu suka kaɗe. Haka suka wuce asibiti suka iskesu. Babu kunya Yaya Fawzan ya ɗauki Najma ya dinga juyi da ita, Babban Yaya dai yayi kawaici, sai da ya faki ido ya rungume Ameerah. Aiko RK ya samu nayi ya tasa Yaya Fawzan a gaba.
     Kafin wani dogon lokaci dangin da ƴan uwa sun gama jin batun waɗan nan ciki. Farin ciki kowa keyi, ana addu'a da fatan ALLAH ya saukesu lafiya. Abah da Oum ma har an gumtsa musu. Oum harda kukanta na daɗi, shi kansa Abah sai da ya share guntun hawaye...

       Kowa na farin ciki banda mutane uku da wasu tsiraru. Na farko Saheeba, hankalinta yayi masifar tashi har jininta ya hau. Nuratu na gefe na tayata kuka. Na biyu Nibras, ita kam a karo na farko yau yanke jiki tai ta faɗi tana kuka da ihu har sai da uwarta da ƴan uwanta sukazo. Ƙarshe ma asibiti suka wuce da ita dan neman some musu take yi. Su kansu ƴan uwan nata duk da maza ne hankalinsu ya tashi, dan bayyanar dai cikin matar Fawzan na nufin matsalar ta ƴar uwarsu ce. Uwarta kuwa data san komai sai hawaye take yi a ranta tana faɗin Nibras kin cucemu wlhy kin cuci kanki. Na uku Mamy da aka sallama daga asibiti yau, batare da sanin su AA ba RK yasa aka kawosu gidan ita da Aunty aka wuce sashenta da ita. Hakan kuma umarnin Oum ne da su Baba Sardauna. Dan sunce Mamy ta cigaba da zama a gidan kodan daraja da mutuncin ƴaƴanta guda uku. Sai dai shigowar tata gidan tazo mata da tangarɗa, dan tamkar saukar aradu haka taji wannan batun ciki har biyu daga surukan da bata so bata ƙauna. Hakan kuma na sake tabbatar mata ta faɗi, faɗuwa ta har abada Fateema tayi nasara ta har abada. Gashi tunda suka dawo gidan babu wanda yabi takansu, dan su suna can suna murna da farin cikin samun ciki, su Saheeba kuma na kuka. Itama sai Mamyn ta hau kuka wiwi. Aunty ko ta tsaya tana kallonta kawai, dan ita dai bataga abin kuka anan ba..
      A Zaria ma dai kishiyoyin Hajiya Majdiya hassada ƙiri-ƙiri suka nuna akan cikin Najma. Musamman Maman Yaseerah da abin duniya ya dama itama. Dan Abdull dai ya saki Yaseerah saki uku, yanzu haka ma shirin aura masa wata cousin sister ɗinsa akeyi yarinya ƙarama. Ana gama bikin kuma zasu bar ƙasar dan zatai karatunta ne a can waje. Har ma an kwaso kayan Yaseerah ɗin. Wannan takaicin kuma yasa Babansu Najma yay mata saki ɗaya, amma ya bata damar cigaba da zaman ƴaƴanta. Sai kuma batun tafiya da Hajiya Majdiya zuwa waje, dan zai yi wani harkar business na shekara biyar ya kuma ce bazai je ya zauna babu mace ba, itace kuma mai ƙananun ƴaƴa dake buƙatar makaranta, kuma su biyu ne kacal tunda an aurar da Najma dama uku ne da ita. Suko kusan takwas-takwas ne da su an zuba gasa saboda cin gado. Suna akan wannan fitinar na basu amince bane sai kuma ga batun cikin Najma ɗin ya fito, sai ƙurar ta ƙara sama. Oho ko kallonsu Hajiya Majdiya batai ba. Ta farin cikinta take ma, washe gari ta shirya ta wuce Abuja tunda tasan Oum bata nan. Sai Ammie aka bari da kai-kawo.
     Aiko zuwanta yama su Najman daɗi, haka suka haɗu ita da Ammie akan yaransu uku ga Hajiya Shuwa da tafi kusa da su itama tana nata ƙoƙarin. Duk da tana fama da Maimoon da itama dai take laulayin tumma watan jiya.
     Su dukansu sukan shiga gaida Mamy kowace safiyar duniya. Hakama su AA ɗin, daga wannan gaisuwar kuwa bata sake ganin kowa sai gobe. Saheeba da Nuratu kam koda wasa basu taɓa zuwa dubata. Bama su taɓa nuna sun san ta dawo gidan ba. Sai da Aunty tazo tai musu faɗa sannan. Koda suka fara zuwa kuma sai su gaida Auntyn kawai suyo gaba abinsu. Waɗan nan abubuwa suka taru sukai ma Mamy yawa matuƙa. Sai da ta zabga uban tagumi tai shiru, wani lokacin kuma taita hawaye sai Auntyn ta zauna tana mata nasiha...........✍️186



......An sallami Mamy da sati biyu suma su Gwaggo aka sallamesu. Babu wani ɓata lokaci aka wuce da su gida Giro kawai bisa rakkiyar su Maanal, Amaal, Shahidah, Ammie. Sai AA, Mijin Shahidah da Mijin Amal da yaransu duka. Sai Hameed da Waleed da Daddy shima.
     Su dai mazan a ranar suka shirya zuwa su dawo. Amma su Maanal za'a barsu acan suyi kwana biyu harda Ammie. Da yake tafiyar safe sukayi ƙarfe sha ɗaya a Giro tai musu. Dan jirgin yawo suka hawo kawai saboda samun sauƙi basai sun je Sokoto ba. Zo kaga ihu da farko wajen mutanen gari jirgi ya sauka Giro. Sai sukai tunanin za'a sake maimaita abinda ya faru ne kwanaki. Sai daga baya suka fahimci mike faruwa kowa ya nutsu, wanda suka gudu suka dawo aka zagaye jirgi.
     Tunda aka fita da su Gwaggo gari ya ɗauki zance ai Asiya ce da iyalanta duka da mazansu. Zo kaga yanda ake ma su AA tarbar mutuntawa kamar wasu shugaban ƙasa da tawagarsa. Su Maanal kam kamar a ɗaukesu a goya. Sosai hawaye suka zuboma Ammie, ashe zata ga wannan ranar a rayuwarta? Ranar da zasu zama taurari a tushen haihuwarsu ita da zuri'arta. Kai duniya kai duniya budurwar wawa kenan. Wanda ma bai shigo cikinta ba jiran zuwansa take ta kuma tanada masa fili. Dan lokacin da kake gama taka rayuwar wani ma lokacin ake haifoshi.
     Babu tun a rayuwar asibiti bai iya ko haɗa ido da Ammie da ƴaƴan nasa ma saboda kunya da nauyi, balle yau da suka taho a jirgi ɗaya, sai su su Amal ɗin ne ma keta kaffa-kaffa da shi dai uba dai uba ne duk lalacewarsa. Wannan shine karo na farko na zuwan Daddy, mijin Shahidah dana Amaal Giro. Sai Waleed da Hameed. Shi ko AA na uku harda wanda yazo suna ƙananu. Kwanan nan kuma yazo da su Baba Sardauna.
         Kowa daya shigo sai kaga ya ɗanyi turus da ganin Sule dake kwance yana fama da jiyya. Dan kwana biyu da sakin ƴan Giro shima aka sako shi daga prison shi da abokansa tun kamawar da akai musu ɗin nan. Ya rame sosai yayi baƙi sai haƙora a gaba kacakau kamar ba Sule ba. Kai daka ganshi kasan maza sun jigatu a hannun Maza.
     Cikin ƙarfin hali Sailu ta zauna a kusa da shi tana kuka. Shi ko ya zuba ma su Maanal ido kawai. Suma dai kallonsa suke, amma basu ce komai ba har aka kawo tabarmi aka shimfiɗa musu anan sashen nasu Gwaggo. Mazan suka zauna, suma su Shahidah suka zauna a gefe da Ammie. Kafin kace mi jama'ar gari har an kawo musu ruwan roba da su Malt... Dan Suru aka garzaya aka sayo musu. Tako ina kuma sai yanka kaji da zabbi ake dan a dafa musu. A taƙaice dai Ammie da iyalanta sun zama Cele a Giro saboda ƙwatosu da su AA sukai a halaka. Gaisuwa kam mutane sai shigowa suke suna yinta cikin girmamawa. Ita kanta Ammie wasu ma bata ganesu. Wasu ko bata sansu ba ma. Matan gidansu kansu da suka zama gaba-gaba wajen wulaƙanta ta yau sai gasu suna zuwa suna gurfana a ƙasa wai gaisheta. Kai wannan al'amari da ban mamaki yake ya subahannallah.
     Abinda ya bama su Ammie mamaki babu mai kula su Gwaggo balle tambayarsu yaya jiki. Kowa yazo kawai su yake gaisarwa da jera godiyar abinda akai musu da neman gafarar su Ammie ɗin. Kafin azhar an cika musu gaba da kwanika daga gida-gida. Kuma ko'ina ka buɗe nama ne da fura ziryan. Ita Maanal ma dake fama da kanta sai ƙamshin naman suka fara hawa mata kai. Ita dai Amal normal ne. Tun tana daurewa har ta miƙe yin amai. AA da hankalinsa ke kanta gaba ɗaya dama tun ɗazun daya fahimci tana yamutse-yamutse babu ko kunya ya miƙe yana tambayarta da sauri. Ina aman ya riga yazo mata, haka ya riƙeta tayi anata mata sannu, ya wanke mata baki ya kamota suka dawo sai Ammie aka bari da saukar da kan jin nauyi. Daddy kuwa murmushi kawai yayi. Su Gwaggo da Sailu da mutanen gida sunata gwalo idanu. Su Uncle Sadeeq ma dai murmushi suka dinga yi ƙasa-ƙasa suna tsokanar AA shi da mijin Amaal. Sai shima dai ya dinga murmushin kawai. Maanal ma dai sata a gaba su Shahidah sukai musamman Amal. Sai da Ammie ta ƙwaceta.
       Su AA sun fita salla, su kuma sukai shirin yi anan, aifa sai mutanen gida kowa ya dinga nuna suzo suyi a ɗakinsa. Ita Ammie har ma abin ya bata dariya. Gwaggo ana son yin magana babu dama, haka su Ammie suka je sudai sukai sallarsu, jin kuma anan za'a barsu sai jibi zasu tafi dan danan aka gyara musu ɗakin wani yaron gidan da zaiyi aure ya gina yayi plaster harda fentinsa na farar ƙasa. Danƙara-danƙaran katifu aka saka musu har biyu a ciki...
      Sailu da Gwaggo na ganin an wuce salla suka faki ido suka ja kwano ɗai-ɗai na nama da fura sukaci sukai nak. Haka shima Sule jikinsa har rawa yake dama yunwa ce gaba-gaba a ciwon nashi. Shima dai Babu ya ci kaɗan ya koma ya kwanta. Sai lokacin Sailu ke tambayar ina Haƙila. Sule yace shi tunda ya dawo gidan ma bai ganta ba. Daya tambaya ƴan gidan sunce tunda abin nan ya faru data bar gida bata dawo ba har yanzu. Hankalin Sailu ya tashi sosai, ta shiga ɗaki ta lalubo wayarta, sai dai babu caji. Haka ta bayar aka kai mata.

       Su Daddy sunje sun gaisa da maigari. Inda a can mutanen gari suka taru cike ana musu godiya, da sake neman afuwar su akan abinda akaima matansu a shekarun baya. Daddy ne yay magana. Ya ce babu komai ya wuce, abinda ya faru kuma yana cikin ƙaddararsu ne. Sai dai magana ta gaskiya a wancan karon ba'aima Maanal fyaɗe ba. Makirci ne aka shirya kawai kuma ba kowa bane face Gwaggo da Sailuba. Amma Maanal takai mutuncinta gidan aurenta. Dan haka a yanzu ma suna son maigari yasa azo da su Gwaggo dan su warware komai ta yanda kowa zai sake shaida wa. Maigari kam ya yarda da wannan shawara. Nan take ya aika a kira Gwaggo da Sailuba harma da Babu. Sai dai yanayin jikin Babu ɗin yasa shi sai a mashin aka ɗakkoshi duk da tafiyar ba wata bace ba. Suma su Maanal sun tafi can gidan maigarin. Ganin haka mata suka dinga fitowa a gida kowa yana son yaji yaya akayi.
      Duk wanda ya kalli su Gwaggo yasan a rikice suke, musamman daya kasance basu san dalilin kiran ba sai da maigari ya maimaita musu. Sailu duk ta rikice, ita tsironta kada su AA su tona musu asiri ace suna da ƙanjamau, an kuma yi musu fyaɗe. Dan haka ta fashe da kuka wiwi tana faɗin, “Wlhy ni dai duk ba laifina bane ba, tsohuwar nan ce ta tsara komai. Dan tun farko ALLAH ya jiƙan innata itace ta sameta tace tana son ahaɗa aurena dana Habibu dan tana son ta fitar da Asiya a gidan. Tace idan har Innata ta yarda zata bata kuɗi dubu ɗari. Dan lokacin ita Innata ta tsorata ance mata Habibu na neman mata. Haka ta kakkareshi har Innata ta yarda jin kuɗi masu yawan gaske. To bayan amma yi auren bata bata ba dubu ashirin kawai ta bata, shine ma abinda yasa har sukai faɗa Innata taso rabani da Habibu na ƙi saboda inada ciki lokacin kuma ya kaini can Kano ina jin daɗin zaman. Duk wani asiri da muka dingama Asiya da Habibu dan su rabu itace mai amsowa, munci nasarar haddasa rashin zaman lafiya a tsakaninsu dan ko ganin Asiya Habibu baya son yi, amma Asiya na samun taimako a gidan makwaftanmu su Hajiya Fateema, shine hankalinta ya tashi suka haɗa kai da kishiyar Hajiya Fateema ɗin aka kawo wani yayima Maanal fyaɗe dan a rusa auren su Shahidah da aka shirya yi da ƴaƴan Hajiya Fateema. Koda yake ita kishiyarta tace mana wai ƴaƴanta ne bana Hajiya Fateema ba. To nidai ban yarda ba tunda basa kama da ita da Hajiya Fateema ɗin suke kama yaran duka. Amma dan kawai a saki Asiya na samu yanda nake so na yarda. Gidan Malam Sango ta amso asirin na nan gefen gari da aka kashe kwanaki. To shine kuma reshe ya juye da mujiya akace Autan Hajiya Fateema ne yayi fyaɗen. Lokacin da Ajwaad ya kama mu muna magana da Hajiya Kamila kishiyar ita Hajiya Fateema muka gudo gida muna magana Baba marigayi yaji shine ya shigo yana salati Gwaggo ta tureshi ya faɗi kansa ya bugu shine sanadin mutuwarsa......”
        Atake waje ya ɗauki salati, Gwaggo ta shiga kuka da gyagygyaɓin ita wlhy bada sani ko niyya tayi hakan ba har Baba Haruna ya rasu. Ina ai waje sai ya hamitse aka shiga tsinema Gwaggo da Sailuba. Musamman yanda bayan sun dawo Giro an gama kukan mutuwar Baba Haruna suka ƙullama su Ammie sharri kuma kowa ya tsanesu har sai da suka gudu suka bar gari. Kuka sosai Babu yake yi na fitar hankali yana roƙon Ammie gafara da su Maanal. Su Maanal since sun yafe masa, suka shiga kuma kwantar masa da hankali da lallashinsa har ita Ammien tunda koba komai dai ƴaƴanta ne. Hasali ma shi ta buɗe ido take kallo a matsayin ɗan uwa uwa ɗaya uba ɗaya. Su Gwaggo kam ko kallo basu ishi su Maanal ba. Bayan an gama tattaunawa a wajen maigari su AA nayin sallar la'asar suka wuce aka barsu anan su. Duk da AA ya daure ne kawai dan kar ace yayi rashin mutunci, amma magana ta gaskiya baiso barin Maanal ba dan ya fahimci bata jin daɗin jikinta sam. Amma haka suka taho suka barosu bayan yasa an kwaso musu ruwan roba da abubuwan ciye-ciye himili an jibge a ɗakin da akai musu masauki. Su Hameed ma sunƙi zama sunbi Daddy.........✍️187


.......Bayan wucewar su AA mata suka cigaba da shigowa ganin su Ammie da musu sannu da zuwa harma da neman yafiya. Duk wanda yazo Ammie amsarsa take hannu biyu. Matan gidan dama suna zagaye da su anata bama Ammie labarai na bayan rabuwa. Su dai su Shahidah sai sun gadama suke kulasu. Musamman ma Amaal da Maanal da sukafi kowa shaƙa dan sunfi Shahidah fushi. Ita Shahidah kusan halin Ammie ne da ita. Amaal da Maanal kam babu ragi babu ragowa.
    Gaba ɗaya Gwaggo da Sailuba sun tsangwami kansu. Gasu Maanaal basu wani kulasu Babu kawai suke tattali. Haka zasu zauna da shi suyi hira. Washe gari sai ga Sule yazo har sashen ya gaishesu. Ya kuma gabatar da kanshi a matsayin ƙaninsu. ALLAH sarki Ammie duk da a kallo ɗaya ta fahimci Sule baya ji hannu biyu ta amsheshi ta kuma saka shi ya zauna suna hira. Ita Maanal ma tana barci sai da ta farka taga Sulen a ɗakin. Da farko haɗe fuska tayi, koda ya gaisheta sama-sama ta amsa ta tashi ta fita yo brush. Da hantsi zasu fita gaida mutane cikin gari haka ya bisu. Sai da suka dawo kuma Sailu zatai musu hauka Manaal ta buɗe mata idanu. Sai ta koma tai lakwas. Aiko mutanen gida sukaita dariya. Sai da suka shiga ɗaki takema Sule faɗa wai Maanal na mata rashin mutunci bai rama mata ba yace, “To babbamu mi kike so nai mata. Koba komai fa yayata ce, sannan ni so nake suce zasu tafi dani gidansu dan na gaji da zaman wannan ƙauyen wlhy. Kina ganinsu ƴan gayu sai raba sabbin ƴan dubu-dubu suke kamar basu san ciwon kuɗi ba sannan ki sani na ɓata al'amarina. Kawai kema ki fara musu biyayya ku zauna lafiya, naga badan su ba da yanzu kuna barzahu dan mutanen can da suka kamaku da kasheku zasuyi ai.”
       “Wai Sule ni kake gayawa haka? Kai mai ƴan uwa ko? Naga ga wadda kuke ciki ɗaya nan ba'asan inda take ba amma ko'a jikinka ”.
      “A kece dai baki san inda take ba, yo ya wuce ɗakin samari suna fafaketa. Kinga Babammu, idan fa bazaki saka min ido ba ki daina damuna akan lamarin mutanen nan, ƴan uwana ne dai ba ƴan uwanki ba ehe”.
     Daga haka ya buga takalminsa yay gaba. Sai kawai Sailu ta fashe da kuka. To ita Sule na mata haka tun yanzu idan kuma ƴan gari sukaji ainahin abinda ya faru da su na batun fyaɗe da cutar ƙanjamau fa? Wannan abu na tayar mata da hankali...

     WASHE GARI su Maanal suka cika kaf samarin yaran gidansu dama magidanta da alkairin kuɗaɗe suyi jari, suma matan haka dan harna ma'auri sunzo suma kuma sunje musu har wanda ke wasu ƙauyukan kusa da su suna aure. Sannan suka ajiye kuɗi masu nauyi akan ayi gyaran gidan musamman sashensu. Sai suka saka ɗan maigari da Sule. Shima kuma Sulen sun bashi kuɗi akan ya dogara

195 / 213

Chapters