Author : Bilyn Abdull Category : Romance
haye ta kwanta rufda ciki itama. Sai wani sakin azababben ajiyar zuciya take yi da sauri-sauri, ta ƙanƙameshi hawaye na fita daga idonta a guje. ALLAH tana son AA, mahaukacin so ma da bata taɓama kowa ba a duniya. Bata tabbatar da hakan ba sai yanzu da take jinta a jikinsa. Kissing ɗin fuskarsa ta farayi zuwa kai da wuya da gadon baya a haukace, dama a buƙace take matuƙa da gayaran data sha. Kuma tunda suka dawo taƙi yarda da Yaya Fawzan kwata-kwata. Shima kuma bai nema ba dan yanzu kam ya gama ajiye ta inda ya dace da ita. Lokaci kawai yake jira.
Tun AA najin al'amurin kamar mafarki harya farka. Hannu ya kai ya jawota a bayansa ya sauketa gefensa. A tunaninsa Maanal ce, dan mafarki ta yake yi, sai dai ƙamshin sam bai masa kama da nata ba, hannu ya kai jikinta nan ma sai yaji ba ita bace ba. Dan wlhy ko a wane irin yanayin zai iya gane matarsa. Hannunsa Nibras data gama haukacewa ta kama zata kai ƙirjinta ya janye. Cikin mayen magani dana masifaffiyar sha'awar da yake ji ya buɗe idanunsa da ƙyar, luuu ya kalla Nibras ya lumshe su, kamar wanda ke aiki da magic sai brain nashi ta sake hasko masa fuskar, da sauri ya buɗe idanun again dai-dai tana matsowa zata shige masa jiki. Babu shiri ya turata da ƙarfi, sai kuma ya tashi zaune yana dafe kansa dake sara masa na ciwo. Da ƙyar ya iya kai hannu ya kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko'ina. Ya fisgi goran ruwa dake gefen gadon a bed side drawer ya ɓalle murfin ya juye a fuskarsa duk da sanyin da ruwan ke da shi bai damu ba. Dai-dai Nibras na sake matsowa tana hawaye da faɗin, “Dan ALLAH ka biya min buƙatata ko sau ɗaya ne. Sonka nake AA so mai tsanani da zai iya kasheni wlhy.......” wani irin hankaɗawa yay mata ta bala'i sai da ta wantsala ƙasa. Duk da jikinsa yayi week sosai haka ya ƙarfafa kansa ya miƙe, dan maganar da tayi ya fahimci wacece. Wani kalar tsatstsagewa zuciyarsa ta shiga yi. Ko ci kanka baice mata ba ya nufi ƙofa zai fita. Kawai ta tashi da gudu ta riga shi isa ta zare key ɗin jiki. Baya son yay mata magana, baya son kuma ya kalleta dan haka ya juya kawai zai je closet ya ɗauka wani key ɗin. Amma ƴar shegiyar nan ta taho a guje ta rungumeshi ta baya tana sakin kuka da cigaba da roƙonsa. Zuciyar AA ta gama zuwa maƙoshi, bai ma san ya fisgota a bayan nashi ba ya bugata da kujera ba. Ta saki wata kalar wahalliyar ƙara. Baibi takan ta ba ya wuce ya ɗauki wayarsa. Da ƙyar ya iya gano sunan Yaya Fawzan dan ko gani bayayi da ƙyau.....
★Kiran AA na shigima Yaya Fawzan dai-dai ya fito ɗakin Nibras yana mamakin ina taje kuma. Zuwansa na uku kenan bata nan shi kuma yana son ya amshi keys ɗin sashen ne data kwashe tun waccan ranar, sun rasa inda na ɗakinsa yake shi da Najma tun ɗazun. Shigowar kiran na AA ya saka shi dakatawa ya ɗaga. Koda ya kai kunne yanda yaji muryarsa sai da gabansa ya faɗi. A ɗan rikice yace, “Auta baka da lafiya ne?”.
Da ƙyar AA yace, “Lafiyata ƙalau Yaya, ina son ka saki matarka yanzun nan, sannan ka tattaro min su Abah kuzo sashena”.
Cikin mamaki da ruɗewa Fawzan Yace, “Wace irin magana ce wannan Auta, wace matar tawa?”.
A fusace AA yace jakar da aka aura maka ta farko, dan igiyar aurenka ce kawai zata zama shamakin hanani abinda nayi niyyar yi yau. Tsinketa ne kawai zai bani dama dan itace kawai tai mata GARKUWA a waje na. Dan haka ina roƙonka dan girman ALLAH ka saketa koda itace alfarma ta ƙarshe da zakai min a duniya”.
Rawa kawai jikin Fawzan ya kamayi, shi mutum ne da sam baya son tashin hankali. Amma zuciyarsa ta gama haska masa akwai babbar matsala, dan yasan wanene Ajwaad. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi batare da sake yin wani dogon nazari ba ya ce, “Ajwaad raina fansa akan ku zuri'ata. Duk da ban san mike faruwa ba bazan tambaye ka ba, na saki Nibras saki ɗaya, saki biyu, saki.....”
“Ya isa Yaya hakan ma ya wadatar. Nagode da wannan alfarmar. Saura dan girman ALLAH ka tattaro min su Abah yanzun nan”.
Kafin ma Fawzan yace wani abu AA ya yanke kiran. Dai-dai Nibras na rarrafowa inda yake ta riƙe ƙafarsa tana kukan wahala da cigaba da roƙonsa ko sau ɗaya yayi amfani da ita, idan ba haka ba mutuwa zatayi wlhy. Hankaɗeta yay da ƙafar yabi takan hannunta ya wuce closet ɗinsa bai damu da ihun wahalar data saki ba. Wani tafkeken belt ɗinsa na ainahin fata ya ɗakko a inda suke a tsare cikin drawer na glass dake tsakiyar closet ɗin, harda su link na hannu, agoguna, da glasses. Gashi kamar a buge amma yana jin ƙarfi kaɗan, ko yaya mace da namiji ma ba ɗaya suke ba balle AA kallo ɗaya zakai masa kasan ko mazan ne a gabansa mai kada shi sai ya shirya. Wani irin zubama Nibras belt ɗin nan ya shiga yi. Ta fasa gigitacciyar ƙara mai ihu tana miƙewa, ina ya sake lafta mata yana taɗeta da ƙafa ta zube ƙasa. A duniya ya tsani yaga ana dukan mace, amma wlhy yau sai ya kakkarya wannan ƴar iskar ta yanda bazata sake moruwa ba a rayuwarta wannan alƙawarinsa ne. Dukanta yake babu tausayi ko ragi, a kallo ɗaya zaka fahimci sam baya cikin hankalinsa ma saboda fushi, AA akwai zuciya, kafin yayi fushi irin haka ne akan daɗe dan sai an kaishi maƙura, amma idan fa ya birkice ɗin nan bayaji baya gani sam.....
Cikin barci Maanal take jiyo ihu, ta buɗe idanu a hankali, wani ihu da Nibras ta kwaɗa mai gigitarwa ya sata zabura ta tashi zaune. Dan gadon yaran dake gefenta ta kalla, har sun tashi suma dan Muhammad ma da baida yawan kuka harya fara ƙunƙuni. Kasancewar bango ɗaya ne tsakanin ɗakin nata dana AA tana jin yanda ake buga ƙofar da bangon kansa, ai dole ta fasa ɗaukar Muhammad datai niyya ta fita da sauri, har tana buge wajen cs ɗinta sai da ta dafe wajan da hannu.
Tabbas anan ɗin ne, kuma ɗakin AA, mace kuma yake duka. Maanal ta jima bataga abinda ya ɗaga mata hankali irin yau ba, wacece haka a ɗakin mijinta har yana duka. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ƙofar tai ƙoƙarin buɗewa amma a rufe gam, ta shiga bugawa tana kiran sunansa amma ina, sai ma Nibras da jin muryar Maanal ɗin ya saka shiga ƙwala kiran sunanta tana faɗin, “Na shiga uku Maanal ki taimakeni zai kasheni, wlhy kasheni zai yi Maanal..”
Gigicewa Maanal ta sake yi tana jijjiga ƙofar, tama rasa miyya kamata tayi, key ne ya faɗo mata, da ɗan gudu ta koma ɗakinta wajen cs ɗinta na mata zafi saboda ta buge shi. Kasancewar ta san inda suke ɗakkowa kawai tai, ga twins sun rikice da kuka na bala'i amma batabi takansu ba ta sake ficewa, idannunta sun mata nauyi, barci take ji saboda abinda suka bugar da ita da shi, tsabar ƙarfin jini ne kawai kuma da yake ta kwanta da wuri barcin ya ragu mata sosai. Yanda hannunta ke rawa da ƙyar take iya gwada keys ɗin, a lokacin ne su Abah ke shigowa sashen. Tun daga ƙasa ihun Nibras ya ratsa su, da gudu suke rige-rigen hawowa steps ɗin. Dai-dai Maanal ta samu key ɗin ya shiga ta murza. Tana tura ƙofar suna ƙarasa hawowa.
Da rarrafe Nibras ke fitowa a ɗakin duk ya fasa mata jiki da belt, danma ta samu ta hmmka kimono ɗinta da ƙyar ta rufe jikinta da anyi abin kunya. Cigaba da dukanta AA yake a hakan ma, Maanal na ƙokarin masa magana amma ko ganinta bayayi, su Abah da suka hawo kuma duk wanda yay yi ƙurin zuwa ceton Nibras sai Yaya Fawzan ya riƙeshi ya hana. Oum na kuka da kiran sunan AA amma baya jinta. Ga Maanal ɗin ma na kuka tana hanashi, ƙarshe dai ta shiga tsakkiyarsa da Nibras cikin matuƙar ƙaraji tace, “Ajwaad!! Wai mi kake yi haka?! Matar Yayanka ce fa!” sai kuma cikin sanyin muryar kuka ta cigaba da faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri kada ka kasheta kasa kanka a masifa muma ka saka mu...”
Cikin rufewar idanu da matsanancin fushi ya ce, “Tashi min a gana kona haɗa dake kema!!”.
“Ka haɗa dani ɗin, nace ka haɗa dani ɗin, sai me idan ka haɗa dani, mace kake ma irin wannan dukan kamar ka samu ƙato”.
“An mata ɗin, wlhy idan baki tashi min a gaba ba zan mareki kema. Kuma dukan wannan jakar jahilar yanzu ma na fara!!”.
Hannu ya ɗaga zai maretan kuwa, dan idon AA a rufe yake halin yanzu baya gane komai. Ita kuma sarkin taurin kai ta tsaya masa ɗin ya mara. Yana gab da sauke hannun nasa a fuskarta Yaya Fawzan yazo ya riƙeshi. “Haba Ajwaad Bestyn taka zaka daka?”.
“Tunda bata da kunya bakinta ya iya tsiwa sai me idan na daketa Yaya, tasan mi banzar nan tamun da zatazo tana bani umarnin abinda zanyi ita kuma”.
Cike da tsiwa Maanal ta buɗe baki zata sake magana Yaya Fawzan ya mata tsawa. “Yima mutane shiru Lilly, stupid, kika ƙara magana zan ɓata miki rai”.
Shiru Maanal tayi, dai-dai nan suka ji dariyar Nibras da babu wanda ya kula tabar wajan hankalin kowa ya koma ga rikicin AA da Maanal. Da sauri duk suka juya saboda dariyar tata da kukan twins. Ai babu wanda bai waro idanu ba.........✍️208
.......Nibras da gaba ɗaya kamar wadda ta haukace ta nufi wajen ƙarfen da glass da akai adon upstairs ɗin ta tsaya, cikin bushewar zuciya ga jini na zuba mata a inda ya jijji mata ciwo amma tana dariya, tace, “Ajwaad bani ka daka ba? To wlhy kaima sai ka ɗanɗana raɗaɗin wannan dukan a jikinka dan sai na kashe waɗan nan shegun yaran, sai dai ka sake mata cikin wasu ta haifo maka. Mugu azzalumi, kuma sonka bazan daina faɗar inayi ba ko za'a kasheni. Komai tsahon shekaru kuma sai na amfana da wannan lafiyayyen jikin naka, sai na ɗanɗanaka Ajwaad wlhy”.
Babu wanda kalaman Nibras basu gigita ba a falon. Yaya Fawzan ya ɗan lumshe idanunsa yana kauda kai, wlhy ba kishin AA yake ba, nadamar auren Nibras na tsahon shekaru yake ji a zuciyarsa. A fusace AA ya nufeta, Babban Yaya ya riƙesa, Abah da gaba ɗaya zuciyarsa ke bugawa daga shi har Oum murya a sanyaye ya kira sunan Nibras. Amma sai cikin tsawa catai, “Abah ka barni, ka ƙyaleni bashi yace ya iya mugunta da taurin zuciya ba, shekara nawa ina nuna masa abinda ya dace yana wani basar dani shi mai taurin kai, to zan kashe yaran, ba shike nan ba naga ta ɗanyen kai. Idan kuma yana son rayuwarsu sai ya zaɓa amsar soyayyata ko su mutu....”
A fusace AA ya ce, “Wlhy kema da sai na kashe ki, na kashe uwarki da kaf zuri'ar gidanku. Idan kuma ke kin cika ƴar halak ce ki kashe su mana!!”.
Ƙoƙarin kuwa watsa su tayi downstairs, ai da sauri Maanal ta zube ƙasa tai kneeling tana kuka da roƙonta, hakama Oum kukan takeyi. Dai-dai nan su Umma suka shigo, dan a gabansu Fawzan ya kirata a waya, sai tace musu tana zuwa. Jin shiru sosai gashi ta fita a ruɗe ya sakasu aiko Rufaidah ta duba, sai ta koma a rikice take sanar dasu babu lafiya gidan fa a sashen AA. Shine suka taho, sai ga su Saheeba ma da Ameerah, dan yanda Babban Yaya ya fito suma ya rikitasu, Najma ma haka jin shiru ga yanda Yaya Fawzan ya fita yasa ta fito. Saheeba uwar gulma ta kira Nuratu dake sashen Mamy tace su fito gida babu lafiya. Uwangale muguwa tana zuwa taga mike faruwa ta koma ta cicciɓi mamy tasa a wheelchiar ɗinta ta turota suka taho sashen AA
Tsoro kuma ya hanata magana ga barci a idonta.
Ganin fa al'amarin babba ne Umma tai kiran su RK dake sashen baƙi a waya. Sosai ake lallashin Nibras ga ƴan biyu na kuka na tashin hankali saboda riƙon mugunta datai musu. Amma taƙi sauraren kowa wai wlhy sai AA yace yana sonta sannan. Shi kuma yace sai dai ta mutu. Humm ahalin Darma basu taɓa ganin masifa makamanciyar wannan ba a dukkan abubuwan da suka faru da su a rayuwarsu. Wannan wane irin shaiɗanci ne kuma? Anya brain na Nibras yana lafiya kuwa. Shegiya shiru-shiru da ita ashe sheɗaniya ce mai zaman kanta.
RK ya fahimci zuciyar Nibras fa a bushe take, sai kawai yace a samo katifa asa a ƙasan, hakan kuwa akayi, saman ya fara haurawa cikin ƙaraji tace, “Wlhy duk wanda ya hawo upstairs ɗin nan a cikinku sai na saki yaran nan ƙasa sun ragargaje”.
Cak RK ya tsaya a step na biyu daya taka, sai kuma ya kalleta da ƙyau yana jingina da bango. Ya ce, “Nibras ke musulma ce anya kuwa?”.
“A'a bamagujiya ce”. Ta bashi amsa a gadarance.
“Da alamar hakan”.
Ya faɗa cikin jinjina kansa.
Alama yay ma Babba yaya dake ta saitin inda yake ya cigaba da jan Nibras da magana. Ita kuma tana mayar masa cikin zafi, Abah na riƙe da AA dan jikinsa tsuma yake kawai, burinsa ya kama Nibras ya ɓalla ɓas kawai. Oum na rungume da Maanal dake durƙushe tana kuka sosai ga wajen cs ɗinta na mata azaba, tana jin kukan yaranta har cikin ranta. Yaya Fawzan kam ya kifa kansa ne a kafaɗar Abah ta ɗayan gefen shima yayi shiru.
Karaf idon Nibras ya hango mata alamar da RK kema Babban Yaya da hannu, da sauri ta juya tana kallon Babban Yaya, ta ce, “Wlhy idan kuna son yaran nan kada wanda yazo inda nake”.
Tsayar da babban Yaya daya fara fusata shima Abah yayi, sannan ya dubi Nibras cike da lallashi ya ce, “Daughter Please ki saurareni, yaran nan basu ne suka miki laifi ba, kiji tausayinsu kinji. Kalla yanda suke kuka, kalla yanda mahaifiyarsu ke kuka.....”
“Abah kukan daɗi take yi ai, ita ba tana jinta wata shegiya ba, ta mamaye zuciyar Ajwaad ta hana shi kallon kowacce mace. To itama tana da zaɓi, kodai ta saka mijinta yace yana sona, kota rasa ƴaƴanta. Dan haka Maanal tunda sai kin bashi umarni yake ji bismillah”. Tai maganar tana yima yaran wani mugun ruƙo daya saka su tsagewa da sabon kuka. Rawa sosai jikin Maanal yake, tsabar yanda ta ruɗe batama san tabar jikin Oum ta koma gaban AA ba tai kneeling. Tana kuka mai ban tausayi, ta ce, “Yaya Ajwaad dan ALLAH, dan girman ALLAH kace kana sonta karta kashe min yara. Ka tausaya min Besty”.
A zafafe ya ce, “Har abada! Nace ina son wannan dabbar, ki barta idan ta isa ta kashe su mana”.
A fusace Maanal ta miƙe tsaye, cikin rufewar ido da ƙaraji ta ce, “Saboda baka san zafin haihuwar ba, baka san wahalar ɗaukar ciki ba. Kalla-kalla yanda take azabtar min da yara ƴan kwanaki goma sha uku kacal a duniya amma kake faɗin har abada ka faɗa mata kalma ɗaya. Anya kana da tausayi Ajwaad? Wane irin busashiyar zuciya ce wanna.....”
Ta ƙasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙe ta. Wani irin zafi kalamanta suke masa a zuciya, kodan zuciyar tashi a sama take dama, sannan yanda tayi sai yake ganin kamar ma babu kishinsa a ranta, rashin kishi kuwa na nuna babu soyayya. Eh bai san zafin haihuwa da rainon ciki ba, amma duk raɗa ɗin da taji yayi imani da ALLAH ko baiji kwatankwacin nata ba shima ya azabtu ai, saboda koda can idan ciwon kai tayi sai yaji a jikinsa balle rainon gudan jininsa.
Wani kalar zuba mata idanunsa da suka ƙara kaɗewa yayi sosai, cikin ƙunar rai har furucinsa na nuna wa ya ce, “Saboda baƙya so na da ƙaunata har kike biyema wata wawuya na amsa ina sonta bayan kin san minene matsayinta a wajena, Maanal saboda baƙya kishi n......”
“So!! kishi!!? Har wani maganar kishi da so kake a wannan gaɓar Ajwaad, to naji bana sonka, bana kishin naka ƴaƴana kawai na sani, kuma wlhy idan aka kashe min su a dalilin taurin kan ka sai na barka na har abada!!!”.
“To ki barni mana, idan kin barni sai me?? Na ce sai me??? Zan mutu ne??”.
Yanda yake maganar yana wani irin turata zaka san AA baya cikin hayyacinsa kamar yanda itama ta fita a nata hayyacin. Gaba ɗaya Oum sai ta ƙara ruɗewa, haka ma su Abah, wannan wace irin masifa ce kamar waɗan da asiri ke ci. Magana Abah da Oum ke musu amma basa jinsu. Maanal tsiwa, AA zuciya. Sai da Babban Yaya abin ya kaishi bango yay musu tsawa. Cikin nunasu da yatsa ya ce, “Duk wanda ya sake magana a cikinku ALLAH sai na mareshi. Wane shirmene wannan? Kanku kuke son kunnawa fitina kome? Ga abinda ke da muhimmanci amma kuna neman ɗaukar wata hanyar ma daban ya rabbi.”
Cikin kuka Maanal ta ce, “Yaya so yake ta kashe min su, kawai yace yana sonta ta bani yarana shine abu mai wahala. Wlhy ta kashesu nima mutuwa zanyi”. Sai kuma ta matsa da sauri tai kneeling tana fuskantar Nibras tana roƙonta cikin haɗe hannaye da kuka. Babu ko ɗar Nibras da ranta ke mata fes da yanda suke fitina ta taɓe baki da faɗin, “Kima daina wlhalar da kanki Maanal, rayuwar ƴaƴanki ko mijinki yace yana sona, yanda kuma