Author : Bilyn Abdull Category : Romance
zuciyarsa tai rauni, wai shima yau yayi aure za'a danƙashi ga matarsa ya bar Oum ɗinsa da yake manne da ita akoda yaushe, shike nan zai tashi daga saurayi ya koma magidanci. Da ƙyar su RK da jikinsu yay sanyi suma suka janyesa. Dan soyayyar Oum da yaran nan uku musamman Ajwaad na taɓa zukatan wannan Family ɗin matuƙa. Ɗagosa Oum tayi ta share masa guntun hawayen sannan ta kamo hannun Modibbo ta damƙa na AA a ciki, sai ta koma ta zauna tana riƙe hawayenta itama. Yau finally ta aurar da autanta yaranta sun gama auren fari sai kuma ga masu burin ƙarawa kamar yanda Fawzan yayi.
Da ƙyar su RK suka ja AA dake ta kallon Oum suka fita da shi. Sun wuce sashen Mamy, sai suka samu tana barci, anan ko maimakon AA ya samu faɗa da nasiha kamar a sashen Mamy sai su Maman Saheeba suka ɓige da habaice-habaice. RK ne kawai ya fahimci inda suka dosa, sauran ko basu kawo komai a ransu ba sai shi AA ɗin kansa. Dan haka baici komai ba ya miƙe yay musu sai da safe ya barsu da baƙin cikin sharesun da yay. Haka sukaita zage-zage da aibanta Oum da Maanal dama Darma Family gaba ɗaya har Maanal da danginta basu tsira ba. Sashen Abah shine na uku, daga shi sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain da Hassan ɗinsa, anan ma nasiha mai ratsa jiki iyayen sukai masa. Tare da jadadada masa haƙƙoƙinsa na miji akan matarsa. Sai dabaru na kula da mace ta yanda aure ke ƙarko da ikon ALLAH. Daga ƙarshe akai addu'a sannan suka taso, sai sashen Babban Yaya. Sun sameshi shi kaɗai a falo zaune yana shan shayi yana kallon labarai. Kama AA yay ya rungume tsam-tsam a jikinsa. Kafin ya ɗagosa yana murmushi ya riƙe masa fuska da hannaye biyu. Cike da raɗa Babban Yaya ya ce, “Finally yau Autan Oum ya mallaki Lilly na, zata maidashi babban mutum, nan da wata tara su haifa min ƙyawawan yara masu kama da su”.
Kunya sosai ta kama AA. Sai kawai ya sake rungume Babban Yaya hawaye na cika masa ido. Dariya babban yaya ya sake yi sauran na tayashi sannan ya zaunar da shi kusa da shi. Shima dai yayma AA nasiha da jadadda masa zama miji na gari a wajen Lilly. Ya rufe da addu'a mai ƙarfi. Daga nan sashen Fawzan suka nufa, shi kam sai Nibras kawai suka samu a falo. Duk tayi wani wujiga-wujiga da alama kuma leƙensu take ta window kafin su shigo. Bayan ta gaishesu cikin son danne kanta da ƙyar RK yace ta kira musu Fawzan. Tana miƙewa ma sai gashi yana sakkowa daga sama. Yana zuwa ya rungume AA, cike da raɗa yanda kowa baya ji ya ce, “Oh oh yau fa Autan Oum zai shiga daga ciki. Babu dokar Aba a kansa Lilly zata dinga masa TAWAI”.
Mintsininsa AA yayi, Yaya Fawzan ya ce, “Ouch wane muguntane wanan haka Auta?”.
Cike da shaƙiyanci AA yace, “Ƙanwarka ta koya min”.
Yanda yay maganar a fili ya sanya kowa dariya. Dan saika rantse bama shi yay zancen ba, babu wani fara'a a tare da shi. Yaya Fawzan yakai zaune yana faɗin, “Shike nan na yafe maka kaci albarkacin Lilly, zauna na maka nasiha dan bazan yarda da rashin mutuncin mijin ƙanwa ba lallasaka zanyi idan kai mata ko kallon banza eh”. Babu wanda bai dara ba yanzu ma. Kafin Fawzan yaci serious kamar ba shi ba ya fara ma AA nasiha shima, daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan ya sallamesu. Koda AA yace shi bazai masa rakkiyar ba? Sai Fawzan yay shiru, sai da yaga kamar AA ya ƙwaɓe fuska sannan ya miƙe yace “Muje taɓararre kawai. Yanzu dai zamu huta muma Lilly ta kwasa”.
Lokacin da suke ficewa idon Fawzan ya sauka akan Nibras dake ɓoye ƙarƙashin bene tana kuka sosai. Kansa kawai ya girgiza yay gaba hannunsa riƙe dana AA. Shima AA ɗin sarai yaga Nibras ɗin, amma ya basar kamar bai ganta ba. Sauran ko babu wanda ya lura sam..
Wani irin daddaɗan ƙamshi mai sanyaya zuciya da sauke gajiya ne ya fara musu sallama a falon, musamman ga AA daya fara shiga. Gaba ɗaya falon ya ɗauki wani irin ƙyau mai ƙayatarwa daka kallesa ka san a lallai gidan amarya kazo. Duk zama su RK sukai kowa na sauke numfashi, dan ba ƙaramin daɗi ƙamshin gidan yay musu ba. AA zai zauna Yaya Fawzan ya ce, “A'a ango tashi kaje kazo mana da amarya muna nan”.
Ɗan jimmm AA yayi, sai kuma ya miƙe dan harga ALLAH soyay daga iya nan suyi sallama su koma shi kaɗai yaje ga matarsa. Amma bazai iya ba yana jin nauyin Yaya Fawzan ɗinsa. Tsayawa yay a ƙofar ɗakin ya zubama handle ɗin ido na sakanni, dan Amaal ta tura masa text cewar Maanal ɗin na nan ƙasa. Sai kuma ya sauke numfashi a hankali sannan ya murɗa handle ɗin kamar baya so ya tura kai ciki da sallama ƙasa-ƙasa. Zuwa yanzu Maanal na kwance ne dan ta gaji da zaman, ga tsoro na shigarta haka kawai, ta kira Didi Amaal tace su dawo dan ALLAH tsoro take ji, shine tace mata ta daure na ɗan lokaci ne gasu AA ɗin nan shigowa. Tun tana kallon ƙofa harta zame ta kwanta idanunta a lumshe ta faɗa tunanin duniya da nazarce-nazarcen ruguntsumin cikinta. A wannan yanayin taji an buɗe ƙofa, kafin ma ta nema ba'asin wanene sassanyan ƙamshin turarensa ya shigo mata hanci duk da yanda nata ke tashi da wanda aka sanya ma ɗakin ma. Luff tayi kamar mai barci tana ƙoƙarin saisaita numfashinta har ta fahimci isowarsa inda take ya tsaya cak. Shiru bata buɗe idanun ba, yana daga tsaye shi kuma ya zubama ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yake gani kaɗan raunanan idanunsa. Kallon fin minti guda sannan ya wani fusrzar da iska mai nauyi sakamakon saukar idanunsa akan ƙugunta daya wani bada shep ta hanyar fidda lafaffen cikinta zuwa cikar ƙirji dana ƙugun dan lafayar mai kwantawa ce a jiki. Sannu a hankali kamar wanda baya so ya duƙo yana kai hannu ya yaye fuskarta da ƙyau, cike da raɗa ganin taƙi buɗe idanun ya furta, “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki Madam pretender”.
Baki Manaal ta ɗan cuna a karo na farko, amma still taƙi buɗe idannunta. A karo na farko yay murmushi kaɗan, sai kuma tunawa da ana jiransu yasa shi sake furzar da numfashin ya ce, “I'm sorry drama queen. Ajiye shagwaɓan muje wajen su Yaya Fawzan mu dawo duk sai ki tattaro kiyi min harta shekara 8 da suka wuce da nayi missing duk zan ɗauka a yau ɗin nan koda ina faɗuwa ina tashi ne”.
Shiru nan ma tayi, sai dai ta buɗe idannunta a hankali ta sauke a kansa, suka ɗan zubama juna ido, sai kuma ta janye nata tana tashi zaunen a nutse. Taimaka mata yay batare daya janye nasa idanun ba ya miƙar da ita, sai kawai ya sanyata a jikinsa ya rungume. “Alhamdullahi! Alhamdullahi! Alhamdullahi!” ya jera har suka uku a jere yana sauke ajiyar zuciya. Cikin raɗa ya sake faɗin, “Ya rabba nagode maka daka nuna min wannan rana, kai ne ka bani ita tun tana ƙarama, ka jarabceni da kuɓucewarta a gaɓar dana gama sakankancewa, ka dawo min da ita a lokacin dana gama sallamawa na rasata, ka bani ita a randa na gama yarda tawa rayuwar ta ƙare kenan gaba ɗaya. Yau gashi ka shigo da ita a cikin gaba ɗaya duniyata a gaɓar da nake cikin matsanancin zumuɗi, ƙagare, farin cikin kasancewar tamu. ALLAH kai mata albarka, ya rabbi ka tausasa min ita ta zame min mar'atussaliha. Ya rabbi ka ƙarfafa min ita ta zama uwar ƴaƴana jajurtacciya, ya rabbi kai mata rahama mara yanke wa, ka tsare min ita daga kowanne irin sharri na fili dana ɓoye, ka baibaiyeta da alkairinka da rahamarka, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Khadijah, kasa ta zama mai koyi da Nana Ai'sha. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Hafsah. Ƙasa ta zama mai koyi da Nana Saudah, ƙasa ta zama mai koyi da Nana Zainab. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Faɗima. Ƙasa ta zama kai koyi da Nana Asiya, ƙasa ta zama mai koyi da ɗabi'un salihan mata bayin ALLAH duka da sauran matan MANZON ALLAH daban ambato ba da jaruman mata da sukai ma addini hidima tako wace fuskar alkairi. Ya rabbi kasa tai koyi da ƙyawawan halaye, haƙuri, juriya, jarumtar Oumna. Ya rabbi ka zama shaida, ita ɗin ta musamman ce a gareni, irin musamman ɗin da baki bazai iya ma furta wa ba.....”
Tsam-tsam Maanal ta sake rungumeshi hawaye na sauka mata. Fin minti uku suna faman sauke ajiyar zuciya sannan ya janyeta da ƙyar ya share mata hawayen ya gyara mata lulluɓin lifaya ɗin ya kama hannunta a jikin nashi yaja suka fice. A haka suka fito daga bedroom ɗin kamar makaho da ɗan jagora har cikin falon. Sai a lokacin Maanal ta fahimci basu kaɗai bane ba. Zaunar da ita yay sannan shima ya zauna kusa da ita. Cike da girmamawa yace ma Yaya Fawzan “Gata”.
Murmushi yaya Fawzan yayi mai faɗi, sai kuma ya kalla Maanal ɗin yace, “Lilly!”.
Jin muryar Yaya Fawzan yasa Maanal amsa masa da “Na'am Yaya F”.
“ALLAH yay miki albarka. ALLAH yay miki albarka! ALLAH yay miki albarka!. Nagode ma UBANGIJI daya kaimu wannan rana cike da lafiya da tsohon rai. Dan gaskiya dana mutu banga wannan ranar ba dole ne ma na dinga muku fatalwa banga ƙarshen movie ɗin ba”.
Murmushi su RK suka shiga yi, Yaya Fawzan ya cigaba da yiwa Maanal da AA nasiha da addu'a yanda ya kamata. Kafin su RK su amsa kowa yay tashi a taƙaice. Daga haka suka miƙe bayan RK yazo gaban AA ɗin ya ajiye wani haɗaɗɗen basket da akai ma wani irin ado da flowers a sama aka kuma rufesa da net. Shine da Nuwaira suka haɗashi, Sai kuɗi da suma akai ma wani irin nannaɗar ado a wata flower ɗin daban, daloli su kuma wai na sayen baki. Daga haka sukai sallama suka fice. AA ya ɗan rakosu wajen sashen. Sai Yaya Fawzan ya maidashi ciki yana faɗin, “Koma ciki mun yafe bama son rakiyar, dan nasan ma badan ALLAH zakayi ba Auta, maybe ma jikake kamar ka koromu waje kawai. Dariya sauran suka sanya sosai. RK ya matso saitin kunnen AA ya raɗa masa, “Adai bi min daughter a hankali yarinya ce dan ALLAH. Dan wannan fitinar dake cikin idanunka ma ta isa firgitata”.
Harararsa AA yayi, RK ya bar wajen yana dariya. Sai kawai yaji an riƙo masa hannu. Dariyar ya tsayar tare da juyowa. Ganin AA ne ya riƙosan ga wani irin kallo da yake masa sai shima ya zuba masa nasa idanun. Tsohon mintuna biyu suna kallon junan, su sauran da basu san mike faruwa ba sunyi gaba abinsu dan komawa sashen baƙi su samu su kwanta suma su huta, gobe kuma in sha ALLAHU Kano tai ɗiba.
Da wani irin hankali AA ya shiga jawo RK baya sannu-sannu harya dawo gabansa gab, cak ya tsayar da shi akan ƙafafunsa suna kallon juna cikin ido. Sai kuma kawai AA ya wani kalar jawo RK ya rungume. A tare suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi, RK yay murmushi yana ɗagowa bayan ya ɗan bubbuga bayan sa. Magana AA ya buɗe baki zai yi, amma RK ya hana hakan ta hanyar yimasa zipping a baki yace, “Shiiii karkace komai, oya good night my son. Dan ALLAH karka ɓaro min aiki da safe kaga dai na gaji nima mamanka zan ɗauka mubar gidan nan ta ɗan min tausa”. Daga haka ya barsa anan tsaye. AA ya bisa da kallo harya ɓacema ganinsa, a hankali ya furta, “I love you Uncle. Kai ɗin na daban ne a gareni ƙololuwa”. Sai kuma ya ɗan murmusa tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda sannan ya murɗa ƙofar ya koma ciki, key ya sake murzawa daga cikin ya kulle........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣1️⃣
______________
.........A inda suka barta anan ya sameta. Ya ɗan bi falon da kallo kafin ya cigaba da takawa a hankali inda take. Komai baice ba ya kama lafayan ya yaye, kaɗan ta ɗago ta kallesa ta maida idanun ta rissinar, ya ɗan zubama hannayenta data matse cikin juna ido, sai ya saki guntun murmushi. Duƙowa yay ya kama hannun nata ya miƙar da ita tsaye, ita dai taƙi yarda ta kallesa. Da wata irin murya mai laushi da komawa can cikin maƙoshi ya ce, “Bestie ki kalleni mana”.
Kanta ta girgiza masa alamar a'a. Cikin sake sauke muryar ƙasa sosai ya ce, “Why?”.
Da ƙyar ta iya motsa lips ɗinta, batare da sautin muryarta ya fita ba ta ce, “Ba komai”.
Kaɗan ya wani ɗan laɓe baki da jinjina kansa still yana kallonta. Sai kuma ya furta, “Okay, to ko zaki koma sashen Oum ne?”.
Ai baima gama rufe baki ba ta wani ɗago tana kallonsa. Da ƙyar ya iya gimtse dariyar data taho masa, dan tsoro sosai ya karanto a cikin idanunta. Duk ta koma sanyi-sanyi kamar ba ita ba, “Zaki je kenan?”. Ya faɗa yana riƙo haɓarta dan ƙoƙarin duƙar da kan take. A mamakinsa sai ta girgiza masa kai, idannunta a lumshe. Kafin yay magana ta cigaba da faɗin, “Akwai baƙi sashen Oum. Su Didi Amaal dai sun ce zasu zo su kwana nan suna sashen Oum”.
Nan ma dai sai da abun yaso bashi dariya. A zuciyarsa yace (Childish) a fili kam sai yace, “Okay! Ni kuma fa ina zan kwana?”.
Idannunta ta buɗe ta nuna masa stairs. Kallon wajen yay shima a ransa yace (Da sauki ma tunda za'a bani wajen kwana baza'a korani ba). A fili kam yace, “To ina godiya, yanzu dai kafin dawowar nasu muje ki tayani yin salla, kafin sannan suma sun shigo sai na rakoki ki dawo”.
Kallonsa ta ɗanyi, ganin yana son maidata wata ƙaramar yarinya. Wai ya manta ne takai 20+, tana da ilimin addini dana zamani, tama karance-karance. Tunda aka tsira bikin nan komai buɗe mata shi ake da sunan nasiha. Musamman Hajiya Shuwa sai abinda ta manta ne kawai bata faɗa mata ba a rayuwar aure...
“Miye kuma na tunanin?”.
AA ya faɗa cikin kunnenta. Ajiyar zuciya ta saki a hankali. Batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannunta. Sai ta ƙi motsawa. Dawowa yay ya tsaya a gabanta, “Goyo kika so?”. Kai ta girgiza. “Ɗauka?”. Shiru tai dan saƙe-saƙen ta yanda zata zille masa kawai take a cikin zuciya. Shi ko sai ya ce, “Uhhmyimm”. Babbar rigarsa yasa hannu ya zare tare da hular damar duk sun gallebesa, ya dawo ta gabanta kawai, cak ya ɗagata daga ƙasa riƙe a hannunsa. Sai tai saurin kallonsa dan abun yazo mata a bazata. Ido ɗaya ya kashe mata, babu shiri ta kife fuskarta a ƙirjinsa tare da saka hannunta a kafaɗarsa ta dafe. Murmushi yayi kawai ya fara takawa a nutse kai kace ba mutum ya ɗauka ba. Haka ya dinga taka steps ɗin cike da ƙasaita har upstairs. Kai tsaye ɗakin dake matsayin nata ya kaita, duk da shi a ransa ya gama sakawa babu batun raba ɗaki, adai yi a gama kawai zai canja tsarin komai na gidansa. Sosai ɗakin yayi ƙyau, ga wani irin ƙamshin mai saka kasala na tashi a kowacce kusurwa. Wani irin shegen mayataccen royal bed ne aka saka, gashi an bisa da wata irin rumfa mai shegen ƙyau da idan ana sanyi ka shige ciki sai ka manta anayi. Shi kansa ɗakin yay masa ƙyau sosai. Saman gadon yaje ya ajiyeta, batare da yace komai ba ya juya ya fita. Ba'a wani rufa mintuna bakwai cikakku ba sai gashi ya dawo. Basket ɗin nan ne da kuɗin sayen baki a hannunsa. Ajiyesu yay a gabanta saman lallausan carpet ɗin gaban gadon mai kamar gashin mage gashi milk color sai ɗaukar ido yake. Idan ka taka kuwa ƙafarka nitsewa take a ciki.
Kusa da ita ya zauna, ya kamo hannayenta cikin nashi ya rumtse. “Barka da zuwa duniyata a karo na biyu Besty. Gidanki na miki marhababika da shigowarki bayan tsohon shekaru daya ɗauka yana jiranki, da kuma baki zo ɗin ba zai cigaba da jiranki na har abada dan bazai taɓa amsar kowacce mace ba sai ke kaɗai da aka gina domin ke. Yanda UBANGIJI ya nuna mana wannan rana, ina roƙonsa ya sa mu gammu a aljanna tare kamar haka. Maanal kece Ajwaad, idan babu ke shima babu shi har abada......”
Hawayen da take yi ne suka sauka akan hannunsa, ya ɗan zuba ma ruwan hawayen ido sai kuma yay ɗan murmushi tare da matsota jikinsa ya rungume. Bayanta ya shiga shafawa alamar lallashi. Kafin ya ɗagota ya share mata hawayen tas da faɗin, “Tom kuka ya ƙare haka, muje muyi alwala domin godiya ga ALLAH. Dare na ƙara yi kizo ki kwanta ki huta gajiyar biki okay”.
Kanta kawai ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya. Shine ya miƙar da ita, ya kama hannunta, closet ɗin ɗakin babba shima suka fara shiga kafin toilet. Komai an tsara mata na kayanta abin dole ya birgeka, su Amaal sunyi ƙoƙari. Bayin ma ƙaton gaske ne, sannan ya haɗu