Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ciwo ya isheni, jin Baba yayi barci ga hadari ya taso na tabbatar kowa ya shige gidansa na lallaɓa na ɗauki sabuwar rezar dana saya a hanya da zanin wata batik ɗin atamfata da Junaid ya saya min na fita cikin sanɗa. Ta baya na kulle Baba a gidan na kama hanya ga ruwa an fara mai ƙarfin gaske daya bani damar yin ƴar doguwar tafiya zuwa bayan layinmu, zuwa lokacin azaba ta isheni sosai, dan haka na afka wani kango kusa da wata makarantar allo. Babu kowa a ciki, abinda naji yana bimin jiki yasa na durƙushe ina kuka, tun ina gane me nake ciki har hankalina ya gushe na wucin gadi, ashe ɗa har ya silmiyo ƙasa uwa ma ta biyo. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin kamar an sauke min wasu kaya masu nauyin gaske, cike da ƙarfin hali na zaro rezata na auna cibiya kamar yanda Inne ta bani labarin akeyi na yanke babu tsoron komai a raina. Dan zuciyata ta riga ta bushe Aliyu Darma kawai nake gani cikin idanuna. Sam ban damu da rashin yin kukan yaron ba, haka na naɗeshi a cikin zanin nan na tattara na fito bayan na huta shi da mahaifar dana saka a leda, na ɗaukesu na fito. Harga ALLAH a lokacin babu wani tsoro a raina, damuwata kawai na ajiye yaron na koma gida wani bai ganni ba, sai fatan mallakar Aliyu Darma a matsayin miji. Haka kuwa na ajiye yaro a bolar bayansu kaɗan da mahaifar na wuce ko waiwayensa banyi ba, badan bana sonshi ba, sai dan nasan wannan shine kawai mafitar da nake da ita da zata saka na tsira daga shiga irin halin da ƙawata fa tsinta kanta a ciki, gashi kamar wasa yau watanni kusan bakwai da rasuwarta. Ina buɗe gida na shigo Baba ya fito daga ɗakinsa yana tambayar daga ina kike. Daƙyar na iya riƙe kaina nace masa farkawa nayi sai na dinga tunanin kamar bamu rufe gida ba shine naje na rufe. Faɗan shiga ruwan yay min kawai yace na wuce na canja kayana sannan na kwanta. Na amsa masa da to na wuce. Ina shiga ɗaki abinda duk ya faru a cikin awanni ya shiga dawo min kamar wani Film. Sai a lokacin na fashe da kuma da ban san na minene ba. Kuka nayi sosai kafin na tashi na canja kayan na kwanta. Sai dai ko barcin minti ɗaya banyi ba, haka na kwana ina tunani da hawaye. Washe gari inata jiran naji ance an tsinci jariri amma shiru, tun ina a tsarge har na fara tunane-tunane, wata zuciya kuma na ayyana min ƙila ya mutu, ko ruwa ya tafi da shi, ko kare ya cinye. Kai irin waɗan nan makamantan tunanin sukaita zuwa min a zuciya. Kwana ɗaya biyu uku har sati babu labarin komai, kullum kuma sai nabi ta wajen ko zanji wani abu amma banji ba. Har aka sallami iyalle na koma makaranta. Ina ƙoƙarin kula da jikina sai dai bani da isashen lafiya, har dai fateema ta lura ta matsa min muje asibiti. Ita ta rakani, sai dai ta barni naga likita ni kaɗai, hakan yasa ban ɓoye masa komai ba ganin ƙabila ne, shiko bai min wani tuhume-tuhume ba ya sani yin gwaje-gwaje, koda na kawo masa result washe gari dan ni kaɗai na koma banda fateema sai ya tabbatar min na ƙaru ne kaɗan za'ai min ɗinki kuma zasu bani magunguna da zasu taimakawa jikina da lafiyata. Hakan kuwa akayi, komai sukai min, da yake akwai kuɗaɗen da fateema ta bani akan asibitin da su nayi komai, akai min har ɗinkin na lallaɓa na koma gida na cigaba da kula da kaina duk da naci azaba. Har lokacin su Iyalle na asibiti ba'a sallamosu ba, sai hakan ya taimakeni sosai. Dan nafi kwana biyar ma da yin ɗinkin sannan aka sallame su suka dawo gida. Shaƙuwa mai ƙarfin gaske tayi ƙarfi a tsakanina da Fateema har ina zuwa gidansu na kwana batare da iyayena sun damu ba, alaƙata da Junaid kuma ta fara sauya salo, idan yace nayi abu bazance bazanyi ba amma kuma bazanyin ba, na daina sakar masa fuska gaba ɗaya. Tun bai fara fahimta ba har ya fahimta ɗin, ya tambayeni mike faruwa nace masa ba komai kawai karatu ne, ya kai hannu jikina na janye, yace zamuje wani waje yana buƙatar mu kasance nace masa aa. Duk dai ta inda ya ɓullo ya kasa gane kaina gaba ɗaya. Daga ƙarshe ma na samu Babana da Iyalle nace su masa magana, idan bai shirya arena bane su dakatar da shi zuwa gidan, idan ya shirya ya turo magabatanshi kawai ayi. Nayi hakanne saboda nasan a yanzu ba auren ne gabansa ba, cimma burine kawai akan su Fateema. Gashi baya buɗe min komai kai tsaye sai dai yace nayi kaza nayi kaza kawai, a yanzu ni kuma jina nake mai ƴanci, sannan komi zai min sai dai yayi bazan iya cutar da Aliyu ba, gara-gara ma Fateemar dan ina jin kishinta sosai akan Aliyu, dannewa kawai nakeyi. Ko zuwa gidan da nake har na kwana da hidimar da nake mata inayine kawai domin Aliyu, amma shi ko kallo ban isheshiba ma. Daga gaisuwa shike nan tsakaninmu..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣3️⃣
______________
........Tunda Babana yayma Junaid managar sake turo iyayensa a tsaida rana sai ya daina zuwa gidan mu, ya turo abokinsa gidanmu wai yayi tafiya tare da babansa zuwa ƙasar waje. Ni kuma nasan ƙarya yake yi, kawai dai na lura yanzu bai cika zaman garin Kano bane amma ban san inda yake zuwa ba. Tarayyata da su Fateema yasa nasan ainahin Junaid, anan kuma na fahimci mutanen daya tura gidanmu akan batun aure na ƙarya ne ba iyayensa bane ba, hasalima babu wanda yasan labarina a gidansu, shi a matsayin baida ko budurwa yake, tafiye-tafiye da yake yi yanzu harkar kasuwanci babansa ya saka shi farawa daga Kano zuwa Lagos. Wannan magana tai matuƙar tsaya min a zuciya, kwatsam wata rana sai gashi, banyi nauyin baki ba na jero masa dukkan abinda naji a kansa, sai ya hau borin kunya da zagina, wai bincikensa naje inayi saboda ya sakani a jikin su Fateema, to wlhy nayi kaɗan, sai ya wulaƙanta ni shi ba ruwansa, kuma daga ranar ya rabani da Fateema tunda dama shine ya haɗamu. Niko nace bai isa ba yayi kaɗan alaƙa da fateema yanzu ne ma na fara, sai dai tawa da tashi ta yanke. Na gaggaya masa maganganu masu zafin gaske nima muka rabu baran-baran. Tun daga wannan lokacin ban sake ganinsa ba har muka shiga aji biyu na makaranta, inata dai neman hanyar da zan iya samun Aliyu duk da a zahiri bazaka taɓa cewa da wani abu a raina ba sam. Kwatsam sai ga batun an cirema Fateema mahaifa ya ɓullo, wato idan nace muku banyi farin ciki ba a lokacin nayi ƙarya wlhy, dan ina ganin kamar hakan wata hanyar da zanci nasarar shiga gidan Aliyu ce, sai dai ta ina? Ban sani ba. Ina tsaka da neman mafita Fateema tazo min da labari mafi daɗi da ba'a taɓa sanar min ba a duniyata, wato tana son na auri Aliyu. Ya suhanallah, a wannan rana har ruwa na zuba a ƙasa na sha, amma na dake da farko na ɗan nuna turjewa, tanata lallashina Ita kuwa. A ɗan tsakanin ne kwatsam sai ga Junaid, bayan kuma tsahon kusan shekara guda rabona da shi, har ma na fara mantawa da shi a babin rayuwata. Da farko naji tashin hankali da ganinsa, amma na dake masa nace miya kawoshi. Murmushi yay min kawai da faɗin Hummm Kamila kenan, ni kike tunanin zakici amana? To bari na gaya miki idan har kina son rayuwarki kada ki sake ki amince da buƙatar Fateema, dan nasan dama wannan shine burin ki, wannan gargaɗin kawai nazo nai miki, idan kunne yaji, jiki ya tsira, na barki lafiya. Daga haka ya juya yay tafiyarsa batare da ya bani damar cewa komai ba. Hankalina yayi ƙololuwar tashi, dan na fahimci komai Junaid zai iya aikata wa, ni kuma har abada banga kurarin da zai hanani auren Aliyu Darma ba a wannan gaɓar, hakan na nufin dole na nemawa kaina mafita da kariya kenan, sai dai ta ina ban sani ba. Haka dole na matsawa kaina da ƙwaƙwalwa ta a ɗan tsakanin, na dinga kai gwauro ina kai mari. Daga ƙarshe dai na yanke shawarar da zuciyata tafi aminta da ita. Akwai wasu ƴan daba a bayan layinmu saboda tsoronsu ko ta inda suke ba'a bi, nasan ɗaya a cikinsu a dalilin ƙawata ɗin nan data rasu, dan da kamar saurayinta yake ma, dan haka cikin kasada na sameshi da batun ina son suyi min aiki. Kamar bazai amsa ba sai yace na faɗa masa aiki, ƙarya da gaskiya na haɗa na faɗi masa na kuma tabbatar masa ko nawa ne zan biya. Kun san dai ɗan daba da fusata akan wanda ya sani, cikin ɓacin rai yace karna damu basai na biya ko sisi ba, kodan ƙawata zasu min aikin. Naji daɗi sosai, amma dan na faranta musu rai na kawo dubu uku na basu a lokacin dan kaf kuɗaɗena ne na haɗa, sannan dubu uku nada daraja matuƙa gaya a lokacin. Baƙaramin farin ciki kuɗin nan kuwa suka saka shi ba, sai ma ya miƙe yana faɗin karna damu a gobe-gobe Junaid ya shigo garin Kano ko gidansu bazai je ba zasu min ram da shi, dan shima yasan shi ya taɓa masa wani rashin mutunci. Daɗi sosai naji, haka na wuce gida nai zaman jiransu. Ai ko kamar yanda ya faɗa washe gari gab da magriba akai sallama ƙofar gidanmu, koda na leƙa sai naga wani yaro yace naje baya Ɗan-taure na kira na. Ko gida ban koma ba na wuce, yana hangoni yay gaba na cigaba da binsa a baya kamar ba tafiyarmu ɗaya ba. Da yake duhun magriba yayi babu ma wanda ya maida hankali a kammu har bayan primary cikin wani kangon aji da rufinsa ya yaye. Mizan gani, Junaid ɗaure a window yaci duka yay lilis ko iya buɗe idanu bayayi da ƙyau. Abin ya min suga na shiga kwasar dariya ina tafi, ya buɗe idanunsa da ƙyar yana kallona, sai kuma yay murmushi yace Kamila dama kece kika sa akai min haka?. A gadarance nace eh, namaka hakanne dan ka tabbatar niba kanwar lasa bace. Ba kace zakayi maganina ba ka kasheni, to kafin hakan ni a yau zanyi naka a yanzu ma. Murmushi ya sake yi yana runtse idonsa da jini ke ɗiga ta sama, yace Kamila kenan, har yanzu baki gama sanin ni wanene ba, ba kuma ki gama sanin nafi ƙarfin ƙaramin kanki ba. Idan har zan iya ɗaukar fansa akan Aliyu Darma akan abinda bai taka kara ya karya da yay min ba ke mi kike tunani zanyi a kanki. Yawu na tofa masa a fuska da faɗin, babu abinda ka isa kayi, ko a wancan ƙaramin wasan naka da kake tunanin ka turani jikin Fateema kawai kake ɗaukar kanka wani shege ne kai. To daga turani jikin nata sai me ka iyayi kuma?. Nan ma yar dariya yayi, yace Kamila kenan iya abinda kika sani kuma kika gani kenan, karki yaudari kanki da ɗan guntun rainon da nai miki na shekaru huɗu kacal. Idan kuma har kina fata da son tsira da rayuwarki to lallai karki bari mutanen nan su barni da raina. Idan ba haka ba kika bari har na rayu wlhy sai na baki mamaki ƙwarai da gaske.”
“Ko'a jikina kalamansa basu wani daman ba, sai ma taɓe baki da nayi cike da rashin damuwa nace, can ta matse maka kuma wannan. Mi kuma kake ci na baka na zuba, ai dama ni ban maka alƙawarin barinka a raye ba, dan babu abinda zamu yi da annoba a cikin al'umma. Na kalla Ɗan-taure nace yayana ina son ku ɗauki wannan sakaran muje yanzu nan mu jefa shi a ruwan can na ƙasan mu, dan ko gawarsa zanji baƙin ciki idan aka sallata aka saka masa likafani. Ɗan-taure yace an gama ƙanwata, haka nake son naga mace a dake malam ba farar kura ba. Kai ku ɗaure masa baki tamau yanda ko nishi bazai iya ba muje. Dariya irin ta ainahin boss Junaid yayi, dariyar data ratsa har cikin kwakwalwar kaina ta kuma tsoratani, amma sai na dake ina kallonsa. Idonsa a kaina yace. Lallai kinyi kuskure Kamila, babban kuskure ma kuwa na cin amanata. Amma ki sani kuma ki shirya ɓadda Junaid a wannan duniyar tamkar kin KASHE MACIJI NE BAKI SARE KANSA BA. Domin akwai AJIYA A DUHUn ki a hannuna dake a karan kanki bazaki taɓa iya hasaso minene ba har sai a lokacin dake zaki koma cikin duhun. Maza jeki, jeki da iya gudun da zaki iya ki taka irin taki rawar yanda kike so, ni kuma ZAN DAWO a gaɓar da ƙafafunki da gangar jikinki har ma da zuciyarki da ƙwaƙwalwa suka gaji. Dan kinfi kowa sanin JUNAID baya barin BASHIN GABA. Koni na ɓuya ina da madadin da zai ɗauka min fansa a kanki.”
“Duk da maganganunsa sun min dukan guduma a saman kai sai na taɓe baki, cikin halin ko'in kula nace kai ka sani kuma wannan. Sai ka bari har sai ka rayu kafin kai tunanin bibiyar bashin gabar. Yayana na gaji da jin muryarsa a cikin kunena Please ku ɗaukesa muje dare nayi. A gabana suka daure masa baki suka saka a buhu suka ɗaukeshi, ni kaɗai mace a cikinsu amma ko ɗar banji ba na bisu har bakin ruwan. Haka suka jefa shi a cikin ruwan nan ina kallo, banji ko tausayinsa ba na juyo na tafi gida suma suka koma wajen zamansu. Da farko abin ya dameni dan a ranar harda mafarki na, amma zuwa kwana biyu da Fateema ta sake zuwa min da batun Darma sai na manta da wani al'amarin Junaid gaba ɗaya, ga dawowar mahaifiyata da ƴan uwana a lokacin, sai daɗin yay min yawa matuƙa. Haka aka sha bikina da Aliyu Darma duk da na fahimci ba sona yake ba sam. Oho karya sonin ai ni wanda nake masa ya wadatar. Tabbas ban wani samu tarbar arziƙi daga Aliyu ba a gidansa, hasalima randa aka kaini ko ganin idonsa banyi ba, bamma fahimci a gida ɗaya muka kwana ba sai da safe. Al'amarin ya cizar min zuciya amma na dake na kuma daure. Nayi zaton abin zai tsaya a iya kwanakin farko-farko ne sai naga fa da gaske yake bana gabansa, matarsa ce ta tirsasashi aurena sai na kasa danne zuciyata, shiko ya tabbatar min akan matarsa fa zai iya komai, kodai na nutsu ko kuma na kama hanyar gidanmu. Dan wlhy bazai taɓa rayuwa a inuwa ɗaya da maƙiyin Fateema ba in har ya sanshi. Bayan ya gama gasa min magana yace naje gida. Tofa babbar magana. Hankalina ya sake tashi, kofa wata ban cika ba, hasalima ko kwanciyar aure bai taɓa yi da ni ba.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣4️⃣
______________
........Bayan an maido ni sai na canja takuna akan Fateema da shi kansa. Na boye komai a zuciya har Aliyu ya yarda dani, ya kai gareni kuma a shimfiɗa. Atsorace nake da sakamakon jina ba cikakkiyar mace ba da nasan zaiyi, amma sai naji baice komai ba, naga dai canji a tare da shi na wannan yinin harma sati guda, amma cikanki baice dani ba, tun ina a tsorace da hakan harna saki jikina, cikin ikon ALLAH ma sai ga ciki, farin cikin samunsa kuma nake tunanin ya goge komai a ran Aliyu game da ni mara ƙyau, nima kuma sai na sake nemawa kaina fada ta hanyar bata ya'yan da duk na haifa ɗin. Na kuma kauda mata ido a kansu kamar ban damu da su ba....”
Zuwa yanzu jami'an tsaron sun zagaye gidan tako ina, harma suna bada sanarwar su Mabera su miƙa wuya kawai. Amma da yake zuciyar a bushe take sai Sille ya bama yaransu umarnin harba bindugunsu sama duka a lokaci guda. Hakan kuwa sukayi, yanda sukai ɗin kuma ya isar ma jami'an tsaron saƙon waɗan nan a shirye suke. Dama saboda tabbatar da hakan yasa Sillen saka su yin harbin. Matuƙar tashi hankalin su Baba Sardauna da su RK yayi, dan harda su aka shigo jejin, duk da jami'an tsaron basu so hakan ba, amma sukace bazasu iya zama ba, dan RK ma harda likitoci ya shirya da Ambulance har biyar saboda shirin kota kwana. Sai dai Ambulance ɗin da sauran jami'an da suka biyo mota basu kai da isowa ba...
A karo na farko Abah ya jefama Mabera tambaya idonsa akan Sille dake ta zuƙar sigari kamar ALLAH ya aikoshi, kai da ka kallesa kasan hankalin maza a tashe yake.
“Da gaske shi ɗin wanda ta haifa ta yadda ne?”.
Murmushi Mabera yay da faɗin, “Tabbas shine, domin kuwa abinda bata sani ba nasan