Author : Bilyn Abdull Category : Romance
samu biyan tata buƙatar na auri tata ƴar bane?”.
“Amma Yazeed ƴar uwartace fa, uwa ɗaya uba ɗaya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.”
“Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma ɗin ce kawai ta kasa fahimta”.
Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana matuƙar son Maanal ta auri Yazeed kodan ƙyawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed shi kaɗai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ƴan uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta basa so sam.....
________________★
“ALLAH nazata wasa kikeyi da kikace min gaki nan tahowa Zaria fa.”
“hhhh aina fahimci hakan a muryarki. Bazaki ganeba fitowar ta dole ce. Gidanmu ne keci da wuta na gasken gaske kwana biyun nan”.
“Tofa wuta kuma Aminiya tami?”.
“Uhhm ke dai bari, tushen matsalar daga auren agolar gidanmu ne da maigidan yace zai ƙulla kusan shekara uku kenan.....”
“Kar kice na katseki wai ƴar amaryar ku? To da wa?”.
“Ita fa, dawa kike tunani idan ba ɗan sonsa Yazeed ba. Tunda fa akai maganar dama uwar tasa tace bata yarda ba. Shi kuma Daddyn Huznah bai maida kai ba yarinyar dai tana cigaba da karatu, shi kuma Yazeed yana manne da yarinya. Bayan ta kammala karatun akaso tada zancen bansan miya faru ba dai kuma aka dakata ta wuce service. Indai taƙaice miki batu ta gama service ɗin ne yanzu zancen ya sake tasowa shine aketa dam-barwa. Ita uwar ɗan tace bafa za'ai ba, kwana takwas da suka shige sukazo itada ƴar barikin ƙanwar nan tata sabuwa suka cima uwar ƴar mutunci randa muka bar nan kenan shine itakuma yarinyar ta yanke jiki ta faɗi ta kama aman jini”.
“Aman jini kuma?”.
“Uhm kin san sunce wai ai tana da ciwon zuciya”.
“Tirƙashi, eh lallai dole kice gidanku naci da wuta. Ke nan yanzu yaya ake ciki kuma?”.
“Yarinyar na asibiti a Abuja yanzu haka. Ba shine nake faɗa miki nakoma Abuja ba nima harma naga ƙanin Majdiya”.
“Oh ƙwarai anyi haka. Ko shiyyasa itama taje Abujan ita da yara duka dan gulma shine suka wuce gidan Yaseerah wai ganin ɗaki. Aiko sai da na mata tujara daga ita har mijin nata data dawo”.
Dariya sosai suka kwashe da ita suna tafawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Ai kinmin dai-dai wlhy. Kinga gobe ai ta kiyaye”.
“Karma ta kiyaye na koya mata hankali. Mu munafuncin kishiya wanne bamu sani ba kuma”.
“Wlhy kuwa. Sai dai wanda kuma aka ɓoye a zuciya. Yanzu kin san miya sani zuwa Zaria ɗin?”.
“A'a sai kin faɗa”.
“Jiya uwar gadaran gidan namu ce ta wuce gida harda kaya cike da akwatina. Dan ya hanata girki a gidan sai mu biyu mukeyi, shine jiya girkin ita shegiyar ne ita kuma taje ta samesu tai musu ɗibar karan mahaukaciya. To ban sani ba ko sakinta yayi shine ta kwashi kaya ta tafi, dan naga ɗan ma ya dawo jiya da dare su kuma matan sunata kuka. Yau kuma tunda safe mai gidan ya fice rai a ɓace matar son nasa itama dai duk ta koma sukuku. Dan haka malam nakeso ki kira mana nan ina son a ƙarama wutar fetur ne ya sake birkice musu. Sai kuma batun Huznah da yaron nan da suka haɗu a Abuja. Na fahimci kamar itace ta damu da shi, dan sai ta yini kiransa a waya bai ma amsa mata ba sai ya gadama. Ina son a riƙe masa wuta gaskiya san bana son nima ta rasashi. Nayi binciken yaron shi kansa bama ubansa ba wani shege ne. Dan Companys ne da shi na abubuwa. Ga shima uban nasa sune ƙasar. Hakama ƴan uwansa biyu kowa ƙwaron kansa ne duk da dai shi ƙanin ya fisu komai.”
“Humm wato ƙawata kina matuƙar birgeni, sam ke baki da wasa akan abu. Sha yanzu magani yanzu kikema komai shiyyasa da wahala asha gabanki”.
“Yo ai babu zama ƙawata. Lamarin rayuwar nan kana sakaci sai a tafi a barka a ƙarshe bare mu dake zagaye da shegun kishiyoyi, tako ina da hari ake kawo mana mune na tsaka. Kinga ko dole mutum ya nemo garkuwa da takobin kai nasa harin ai.”
“Wannan gaskiya ne. Yanzu dai bara nasa Zaituna ta kira mana shi ta falon baya. Kin san gidan namu dai cike yake da ƴan sa ido. Damma maigidan baya gari ne jiya da yamma yay tafiya.”
“Ato ai ansha hidima dole a koma nema kuma. ALLAH ya taimaki ƴan baya suma haka dai dan wlhy rashin auren yaran nan ya fara tada min hankalina. Rigi-rigi sai samari sunzo kamar za'ayi sai ki nemesu ki rasa”.
“To ke kuwa maƙiya cike da gida za'a barsu haka ne. Ke dai kin san yaƙi da gwagwarmayar da nasha Kafin auren nan na Yaseerah ya yiwu. Yanzu saura Zaituna itama dai wani ya biyota a ƴan bikin so nake na huta gajiyar nan na fara aiki a kansa. Dan babu wasa”.
Dariya suka kwashe da ita su duka suna mai taɓawa. Hajiya Basariyya ta ce, “Haka nake fata a nawa gidan. Dan sai yaran nan sun gama aure kaf kafin yaran ɗakin gadararriyar can suyi sa. Na riga na shirya yaƙarta ta wannan fanin”.
“Wlhy ina bayanki. Shegu ai idan sunce su mugunta suka iya gidan suka taras....”
_________★
Kwanakin Maanal goma sha shida a asibiti sannan aka bata sallama. Dai-dai da cikar Hajiya Yaya kwana tara a gidansu. Daddy dai tun wannan fitar da yay daga gida a washe garin zuwan Yazeed bai koma ba. Sai daga baya suka fahimci yama bar ƙasar ne sabgar gabansa. Dan kwanansa biyu da tafiya yasa Hajiya Basariyya tabisa can. Komai Ammie batace ba akan hakan, damuwarta fushin da yake da ita da batasan laifinta ba. Gefe kuma ga yaran Hajiya Yaya sun tasota da rashin kunya da rashin mutucin a gidan. Sai idan Yazeed na gidan ne take samun sauƙin su. Dai-dai da su Hameed sun takurawa da zagi da duka. Wannan dalilin ya saka yau koda su Shahidah suka kirata akan sallamar Maanal tace Maanal ɗin ta zauna anan gidan Shahidah kawai. Nene sai ta biyo su Amaal ta dawo. Hakan yayma Maanal daɗi dan dama bata son komawa Kadunan. Sai dai ita Nene ta fahimci akwai matsalane amma batace komai ba ta shanye a ranta har sai ta koma. Dama tanata mamakin abinda ya hana Ammie sake dawowa Abujan. Kullum sai dai suyi video call safe da yamma. Takance suyi haƙuri da rashin daowarta akwai abinda take yi ne.
Badan Maanal tasoba ta yarda RK yay musu rakkiya har gidan Shahidah. Cikin farin ciki su Munaya sukazo suka rungumeta. Itama haɗasu tai ta rungume tana mai jin kewarsu dan sau ɗaya sukaje dubata asibiti aka hana zuwa dasu saboda bata son hayaniya a lokacin. Har cikin falo suna manne da ita. Kafin su fara rige-rigen zuwa ɗakko mata gift da kowa ya tanada mata.
“I love you yarana”.
Ta faɗa a hankali tana rungumesu....
“Kina da son yara kamar haka, amma kiketa ɓata mana lokaci”. RK dake gefen kujerar da take ya faɗa a hankali ta yanda itace kawai taji. Ɗago yaran kawai tai daga jikinta batare da ta kallesa ba. Shima sai ya basar saboda isowar Amal ɗauke da ƙaramin tire ta haɗo masa abin sha. Godiya yay mata hankalinsa kwance ya ɓalle ruwa ya tsiyaya a kofi ya hau sha. Ita Maanal ma sai ƙarfin halin nasa ya ɗaure mata kai. Kasa jurewa tai sai da ta ɗan zuba masa ido. Yanda take kallon nasa ne ya sashi sauke kofin daga bakinsa shima yana kallonta. Sai kuma ya wani ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa. Nata idanun ta ɗauke tana ɗan yamutse fuska da faɗin, “Kai ko kunya baka ji?”..
“Ikon ALLAH kunyar mi zanji?. Gidan yayata nake fa. Idan kuma so kike na fara jin kunyar ki bani damar sakaki a gidana na miki alƙawarin ko'ina naje aka bani ko miye bazanci ba sai naki”.
Kallo ta jefa masa mai kama da harara sai kuma ta girgiza kai kawai ta miƙe. Harta gama hayewa upstairs idonsa a kanta, sai da takai step ɗin ƙarshe itama ta ɗan juyo dan tana jin kaifafan idanunsa na yawo a kanta. Da sauri ya ɗauke kansa ya basar. Ita kuma taja ƙaramin tsaki ta ida hayewa. Daga haka bata sake sanin sanda yabar gidan ba. Dan wanka ta samu tayi a ɗakin Shahidah tai kwanciyarta sai barci. Dama sunce zata dinga samun isashen barci yanzu hakan ne zai dawo da kuzarinta data rasa...
Bayan sallar la'asar Nene dasu Amaal suka wuce. Sai suka koma daga ita sai Shahidah da mijinta da yaranta biyu a gidan kawai. Sai kuma masu aikinta guda biyu. Jitai kuma duk babu daɗi, dan tana matuƙar son ta gansu su duka a waje ɗaya hakan na sakata a farin ciki. Sai dai yaya ta iya aure ya rarrabasu. Hira suke da Shahidah, koma ace Shahidah ke hiran dan Maanal dai daga guntun murmushi sai eh ko a'a ne nata. Muneff ne ya shigo da ɗan gudunsa, autan Shahidah, dan daga shi dai har yanzu bata sake ba ko tana hutawane ko ta tsaya oho mata.
“Muneff ban hanaka wannan guje-gujen ba wai nikam?”.
Shahidah ta faɗa cikin taka masa birki. Yaron bai damu ba ya ce, “Mamy Uncle Yazeed ne yazo”.
“Uncle Yazeed na kd?”.
“Eh Mamy. Yana waje ma”.
Kallon Maanal Shahidah tayi. Itama Maanal ɗin ita take kallo. “Kije ki shigo da shi”.
“Ni Didi ƙafata ke ciwo”.
Kai kawai Shahidah ta girgiza tana miƙewa. Hijjab ɗinta da takan ajiye a falo saboda baƙi irin haka ta ɗauka ta saka sannan ta fita. Babu wani jimawa sai gata ta dawo Yazeed biye da ita. Yana shigowa idonsa akan Maanal ya fara sauka. Itako ta ƙurama television ido kamar bata san da shigowar tasa ba.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣7️⃣
.......Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta ɗan kallesa ta ce, “Yaya Yazeed ina yini”.
Sai da yaja kusan minti ɗaya kafin ya amsa da, “Lafiya lau. Yaya jikin naki?”.
“Alhamdullahi”.
“Masha ALLAH”. Ya faɗa yana maida kallonsa ga Shahidah. “Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai da naje asibitin yanzu akace kuna gida”.
“Kayi haƙuri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu.”
“ALLAH ya ƙara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen?”.
“Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba ɗaya”.
“Kai da sauri haka?. Ita Nene ko ɗan hutawa bazatayi ba”.
“Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake kwana a garin nan ba”.
Murmushi kawai yay da faɗin, “Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam”. Ya ƙare maganar idonsa akan Maanal.
“Ni Ammie tace ai na zauna anan”.
“Anan kuma? To saboda mi?”.
Shahidah ce ta bashi amsa da, “Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta ɗan ƙara murmurewa ne dan suma likitocin sunyi gargaɗi sosai akan ta huta a waje mai ƙarancin jama'a da hayaniya. Amma tana ƙara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed”.
Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce, “Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi”.
“ALLAH ya taimaka ya bada nasara”. Shahidah ta faɗa cike da girmamawa. Dan suna matuƙar giramam yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya taɓa musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can ƙasa ya ce, “Baki jin komai dai zuwa yanzu?”.
Kanta ta jinjina masa alamar eh.
“Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko?”.
Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce, “Ni ALLAH babu ruwana.”
Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya ɗan murmusa tare da duƙo da kansa kaɗan murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Adana shagwaɓar nan ba yanzu ba”.
Kanta ta duƙar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yunƙura zata tashi. Cikin bada umarni ya ce, “Koma ki zauna”. Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna ɗin tana ɓata fuska....
_______________★
“Da alama wannan karon mijinki yana son nai matuƙar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya ƙarama”.
Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da duƙar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce, “Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da wannan zaman ƙuncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ƙarƙashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan alƙawuran da girmana agaban ƴaƴana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba'a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace faɗa a gabana Baba”. Ta fashe da kuka.
“Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan ɗauka jeki kwanta”.
Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana miƙewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai da ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, “Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa zakaje ka tasata gaba ka haɗasu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye masa hakki akan ƴar da ka haifa.”
“Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali da gaskiya ko”.
“Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta ƙisa, ka ƙisa duniya ta soshi. Usman na maka matuƙar biyyar da kosu ƴaƴan da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a cigaba da ƙasƙantar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine shugaba a gidan, yin kutse a al'amarin kamar ƙasƙantar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba”.
Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. “Hakane kuma Adama nagode da tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman ɗin baya ƙasar, amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo”.
“To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin sai kuje, ALLAH