Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Mamy ke jin tamkar zuciyarta zata fito ta baki. Nuratu zata juya ta koma ciki Saheeba ta riƙo mata hannu ta hanata. Nibras kam sai da ta ya share hawaye...
Zaman karyawa sukai, dama tea ne kawai sai ɗan abinda ba'a rasa ba. Kasancewar ciki duk a cinkushe saboda azumi da aka sha babu wanda yaci na kirki duk suka tashi. Kowa ƙara gyarawa yay suka fito domin shiga motoci. Maanal na ƙoƙarin shiga motar babban Yaya AA ya wani riƙo hannunta, juyowa tai ta kallesa dan a zatonta cikin su Najma ne. Ƙaramar harara ya sakar mata yaja hannunta kawai suka nufi tasa motar. Sai kawai Mamy catai itama Nuratu ta tafi can. Wani shegen murmushi Abah yayi, sai dai baice komai ba yay shigewarsa mota kusa da Oum dake waya bata san mike faruwa ba. Yayinda Babban Yaya da Fawzan sukabi Mamy da kallon mamaki. AA kam da sarai yaji Mamyn yi yay kamar baiji ba, sai ma buɗema Maanal yay ta shiga hannunsa na riƙe da bag ɗinta ya zagaya nasa mazauni ya zauna, ita kuma babbar rigarsa da hula na saman cinyarta ya ajiye.
Wani irin abu ya tsayama Najma na takaici, dan tunda Uncle R da Maanal suka tattauna akan Mamy a gabanta duk da basu fito fili sun ambaci sunanta ba itama ta sakama dukkan motsin mamy ido. Sai kawai itama ta fasa shiga motar Fawzan datai niyya ta koma ta AA suka shiga a kusan tare da Nuratu. Kallon juna sukai, Najma ta watsama Nuratu wani shegen harara ta ɗauke kanta.
AA kam baiyi kamar yasan bayan shi da Maanal akwai wasu a motar ba, yana gama zama bag ɗinta a saman cinyarsa ya juyo yana kallonta, sai kuma a hankali ya kai hannu ya kamo haɓarta ya juyo da fuskarta inda yake dan da ta shagala ne da kallon design ɗin jikin babbar rigarsa da yay mata ƙyau.
“Nan zaki kalla zuciyar Ajwaad. Dan rigar da mai rigar duk naki ne ke ɗaya. Aikin ya miki ƙyau ne”.
Wani kasalallen murmushi Maanal ta sakar masa mai taɓa zuciya, cike da shauƙi ta kai hannu ta ja masa hanci kaɗan, “Duk ƙyan aikin kaine zaka sakashi yay ƙyau dan kai ke saka ƙyawu yayi ƙyau zuciyar maanal. I like you in manyan kaya”.
Ya arrahaman, ji AA yay kamar zai wani shiɗe, bai ma san ya matso da fuskarta gab da tashi ba ya manna lips ɗinsa kan nata ya ɗan sumbata kaɗan. Sosai kunya ta kamata sanin basu kaɗai ne a motar ba, shiko idanunsa har sun ɗan sirka. Maanal ta ɗan maida fuskarta gefe kawai tana ɗan murmushi. Dai-dai nan babban Yaya yayima AA ɗin horn dan shine a bayansa. Ajiyar zuciya ya sauke a kasalance yay ma motar key, Nuratu da zuciyarta ke neman tarwatsewa ta kama murfin zata buɗe dan ta yanke gara ta fita a motar kawai taji ya saka luck. Dole ta koma ta zauna dan tsoronsa take ji bazata iya cewa zata fita ba kai tsaye.
AA kam da shi yama manta da zamanta a motar a hankali yake mirza steering motar kamar baya so, dan gaba ɗaya Maanal ta gama kashe masa gaɓɓan jiki. Hannansa yakai a hankali ya kamo nata, sai ta juyo ta kallesa, shima kallon nata yay suka sakarma juna murmushi mai sanyi. Sai kowa ya janye, shi ya maida ga hanya ita kuma tana kallon waje har lokacin da murmushi a fuskarta dan ita kaɗai tasan mi take hangowa a cikin idanun ƴan maza. Najma kam cike da munafunci take musu video, dan wannan gulmar bazata gani ita kaɗai ba sai ta gumtsawa su Maimoo.. Sai kuma uban murmushin shaƙiyanci take zubawa da son ƙular da Nurry. Tako ci nasara, dan zuciyar Nurry har wani tururi take yi. Wata irin nadamar shiga motar take ji, ga zuciyarta fal bala'i amma babu damar nunawa tana tsoron shan mari a hannun AA Maanal ta samu na nata gori...
A haka suka iso massalaci. Nuratu ta fara ficewa AA na kammala parking, Najma ta bita tana ƴar dariyar ƙularwa. Maanal na yunƙurin fita AA ya riƙota. Juyowa tai tana kallonsa. Ya marairaice mata fuska kuwa da faɗin, “Idan kin fita wazai ƙarasa shiryani, bayan kin san ban saka bane saboda kema ki samu kada”.
Murmushi kawai Maanal tayi da ɗan girgiza kai, batare da tace komai ba ta ɗauka babbar rigar dake jikinta ta shiga warwarewa yana kallonta ƙuri kamar ya haɗiyeta yake ji. Amma dai ya daure dan yana son tsira da alwalarsa. Nuni ta masa da idanu ya duƙo, babu musu ya ranƙwafo sosai yanda zata ji daɗin saka masa ta saka, cike da kulawa batare data yarda sun haɗa ido ba ta gyagygyara masa duk da yana a zaune ne harda naɗo duka gefen biyu ta ajiye masa a kafaɗa duk da bawai babbar rigan nada faɗi bane. Dan anyita ne ƴar cif-cif babbar rigar zamani dai da faɗin nata duka baya wuce gwiwar hannu. Hula ta ɗauka ta shiga mata kari dan ta iya, tun suna yara tana masa karin hula, shiko sai kallonta yake, nan ma kan ya duƙo mata ta sanya masa, cike da kunya tasa yatsanta tana gyara masa ɗan gashin daya fito gefe-da-gefe kaɗan.
Batare data yarda ta kallesa ba ta ce, “An gama”.
Wani ƙaramin box ya miƙa mata, cikin raɗa muryarsa na sake komawa ƙasan maƙoshi yace, “Saura agogo da turare”.
Batace komai ba ta amsa box ɗin ta buɗe, irin na su Yaya Fawzan ne shima, hannunsa daya miƙo mata ta amsa a cikin nasa kunya na sake rufeta, tadai daure ta saka masa sannan ta ɗauka turaren dake ajiye a tsakkiyarsu ta shiga fesa masa. Sai da ta ajiye turaren ta ɗago ta wani kallesa, sai kuma ta kashe masa ido ɗaya ƙasa-ƙasa,...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣0️⃣
______________
.........“Ka cinye wannan zangon, kaine gwarzon shekara ƙyawawa na duniya my bestie”. Ta faɗa tana haɗe yatsunta babba da manuniya🤏.
“Kin fini ƙyau ai Matar AA”.
Ya faɗa cike da kasalar jiki data zuciya. Tare da kamo hannunta ya kunce agogon data saka ya saka mata wani mai shegen ƙyau dake tare da abin hannu sun sha stones farare sai ƙyalli suke, kaida da gani kasan ba normal stones bane ba. Baki ta saki kawai tana kallon hannun nata, sai kuma ta kallesa idannunta na ciko da ƙwalla. Tana motsa lips ɗinta da nufin yin magana yayma bakinsa alamar zipping. Dai-dai nan akai knocking glass ɗin motar. A hankali ya furzar da numfashi tare da cirar tissue ya miƙa mata sannan ya gyara zamansa ya sauke glass ɗin. Yaya Fawzan ne, cike da shaƙiyanci ya duƙo saitin kunnen AA yace, “Babu dai wajen canja sabuwar alwala anan a dinga tunawa ehe”.
Rasama abin cewa AA yayi, sai kawai ya cije lips ya buɗe motar ya fito hannunsa riƙe da bag ɗinta. Itama Maanal fita tayi tacan. Kallon bag ɗin Fawzan yay cike da tsokana, sai kuma ya wani riƙe haɓa tare da faɗin, “Ni dai ka rufa min asiri karka cinye min ƙanwa ita kaɗai garan mace. Yau zan maka addu'a Abah ya baka ita mu huta dai kodan Baby”.
Karaf a kunnen Maanal data matso domin amsar bag ɗinta a hannunsa, ai da sauri tai ƙoƙarin juyawa AA daya ɗan harari Yaya Fawzan ya riƙota. Bata juyo ba, shima baiyi magana ba ya saka mata bag ɗin kawai a hannu ya saketa. Kamar ƙyaftawar ido tabar wajen. Dariya Fawzan yayi kawai.....
Anyi sallar idi bayan khuɗuba mai ratsa zuciya. An kuma sha addu'oi sosai. Koda aka idar ɗai-ɗai ahalin Darma suka dawo inda motocinsu suke. Salim ya fiddo Camara ɗinsa yace sai anyi hotuna. Babu wanda ya musa dan kowa yasan Salim mayen iya ɗaukar hoto ne. Tun ma Uncle Mahmud na masa faɗa harya haƙura ya saya masa camara ya kuma saka shi yay training class akan hakan. Tsaf ya saita camara ɗin ya ajiye shima ya dawo cikinsu akai hoton. Sunyi kamar biyar sannan suka shige motoci idan anje gida sai a cigaba. An dai yi waɗan nan ɗinne a filin idi domin tarihi...
Yanzu kam babu wanda ya shiga motar AA, dan Mamy ma bata fargaba Nurry ta afka motar Babban Yaya. Ganin haka sai Najma ta shiga ta Yaya Fawzan daketa mata gargaɗi da ido. Aiko suna shiga abinka da gilashi mai duhu AA ya wani jawo Maanal ya rungume tsam, dan ɗazun yana sassautawa ne saboda alwala. Sai kuma ya ɗagota ya manne lips ɗinsu waje guda ya shiga bata zazzafar sumbata mai tsayawa a ƙahon zuciya. Sai da yaga yana neman sakin layi jikinsa kuma na neman canja yanayi sannan ya saketa. Sam kasa haɗa ido Manaal tayi da shi har ya tada motar yabi bayan sauran. Shima bai sake cemata komai ba har suka iso gida. Anan compound aka yada zango, hotuna aka fara ɗauka kamar babu gobe. Maanal nata dojewa kar suyi daga ita sai AA, sai dai hakan bai yiwu mata ba, dan an gama ɗaukarsu ita da shi da Oum, Oum ta juya zata bar wajen saboda magana da Babban Yaya ke mata itama Maanal ta yunƙura zata gudu AA ya riƙo hannunta, kanta ta juyo kawai a hanka ta kallesa shima yana kallon nata kawai Salim ya ɗauka ƙitt. Aiko hoton yayi masifar ƙyau. Ya juyo da ita tazo dab da shi kanta a ƙasa yana kallonta nan ma Salim ya sake ɗauka. AA ya ranƙwafo sai tin kunenta zai mata magana nan ma aka ɗauka. Matuƙar ƙyau hotunan nan sunyi. Takaici kamar Mamy zata haɗiyi zuciya ta mutu. Kowa fuskarsa da farin ciki itako tata sai baƙin rai. Ko hotunan ba kowanne ta shiga ba, ta koma gefe ta zauna tana ta sauke ajiyar zuciya. Koda ta turo Nuratu su ɗauka da AA Salim na shirin ɗaukar hoton dan wulaƙanci AA ya juya baya yana amsa waya sai bayansa da Nuratun aka ɗauka. Bai kuma tsaya ba yay gaba. Nurry ta bishi da kallo idannunta na ciko wa da hawaye. Sai kuma ya juya tana kallon Mamy. Wani irin daɗi Nibras taji da hakan ta faru, duk da zuciyarta kamar ga kama da wuta akan hoton AA da Maanal. Tana can tana kishi mara amfani Fawzan na nan yana ɗaukar nasa da Najma. Ɗaukar hoton data ja hankalin Abah da Oum kansu. Dan kai tsaye suka fahimci akwai wani abu a tsakanin yaran. Wani kalar daɗi Abah yaji, sai yaji kamar ya tashi ya goya Fawzan. Oum ma jitai hawayen daɗi na ciko mata idanu, koba komai Finally shima Fawzan ɗinta zai samu mai share hawayensa. Mamy kam baƙin zuciya da sakama AA da Maanal ido datai yasa bama ta fahimci na Fawzan da Najma ɗin ba sam.
Fara shigowar motocin baƙi yasa hotunan sake ɗaukar armashi. Dama gidan Darma a ranar salla matattarar baƙi ce sosai. Isowar su Didi Shahidah ya saka Maanal kwasa a guje ta rungumeta. Dan bata sanar mata zasu zo ba. Tuni Barru da Haneef sun rungumeta suma Haneef harda kukansa dan yana bala'in son Maanal. Uncle Sadeeq kam sai suka bashi dariya. Dan da ƙyar suka bari Maanal tazo ta gaidashi da masa sannu da zuwa.
Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya tara mutane. Tuni an gama shirya abinci a garden kamar yanda akeyi duk shekara. Can aka ɗunguma cin abinci. Manaal dake manne da Didi duk sanda ta ɗago sai sun haɗa ido da AA. Dan cin abincin sashin maza daban na mata daban. Anci ansha an godema UBANGIJI. Baƙi suka cigaba da zuwa, Maanal ta gaisa da Ammie ta video call, ta kuma kira Daddy shima tai masa barka da salla. Da Nene da duka kawunan su ƴaƴan Nene. Sai Didi Maanal itama da suka jima suna hira dan ɗakin Oum suka shige ita da Didi sukai hirarsu ta yaushe gamo. Sai ga kiran su Aneesa suma. Nan ma sun sha hira sosai. Bata sake ganin AA ba tunda suka shigo. Sai bayan sallar la'asar da su Didi suka tafi tai kira Mah-mah ta kano (Nasan kun gane Maman su Oum kuma tasu RK😀) harda Abbah suka gaisa da su Yaya da aunty Rufaidah da amaryar RK Nuwaira. Shima RK ɗin ya amsa suka gaisa cikin girmama juna. Hakan yayama Mah-mah daɗi ta dinga sakama Maanal albarka ita da Abbah. Maanal ta dinga amsawa a kunyace. Daga nan Baba Sardauna ta kira, shima suka gaida harda Ummah, su Uncle Mahmud, Hassan, Hussain duk suna nan tare da matansu suma duk suka amsa suka gaisa. Sosai abinda tai ɗin yay musu daɗi, dan su Saheeba basu taɓa ɗaga waya sun kira wani a cikinsu ba, sai dai in Kanon sukaje ko su sunzo Abujan. Itako Maanal a wajen Najma duk ta amshi numbers ɗinsu. Daga nan Baba ta kira. Wato mahaifin Abah shima ta gaisheshi shi da Mamma matarsa, nan ma ta gaisa da su Uncle Najeeb da matansu. Kowa sai saka mata albarka yake. Tana yankewa ta kira Gwaggo Khadijah, mahaifiyar su Nuwaira kenan, baiwar ALLAHr nan kamar ta zuƙo Maanal ta wayar ta goyata dan farin cikin wannan girmamawa datai mata. Itama ƴayanta na gidan suka gaisa. Hajiya Majdiya ce ƙarshe. Ita kam ai tamkar uwa take, nan fa ta fara mata hira tana sanar mata ta shirya salla da kwana uku zatazo Abuja da kayan gyara dan sai ta gyarata tsaf kafin tarewa. Kunya duk ta ishi Maanal. Suna yin sallama ta fara neman layin AA, ganin har biyar ta wuce a tunaninta ma baya gidan. A mamakinta sai taji karar wayar a cikin ɗakin, da sauri ta juya bayanta sai ganinsa tai tsaye a bakin ƙofa ya wani harɗe hannaye a ƙirji ya jingina da bango ya zuba mata idanu. Sosai ta waro nata idanun waje dan sai kamar taji tsoro, harga ALLAH bata san ya shigo ɗakin ba balle sanin tun yaushe yake a wajen.
Ganin yanda ta daburce sai yay murmushi, cike da basarwa ya iso yana faɗin, “sarkin tsiro”.
Cikin tura baki ta ce, “ALLAH ka bani tsoro fa. Babu ƙyau irin haka kaɗan ya rage na fasa ihu ALLAH”.
Kusa da ita ya zauna ya jawota jikinsa ya rungume. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Sorry bazan sake ba.” kanta ta jinjina masa. Ya ɗagota yana kallonta cikin ido gira a ɗage. “Kina missing ɗina ne?”.
“Bance ba”.
Ta faɗa tana kauda kai gefe.
“Uhyimm! To miyasa ake kirana? Bayan ba'a taɓa ba!”.
“Ni bakai zan kira ba, kuskure aka samu”.
Kwanciya yay ya ɗaura kansa a cinyarta, hannayensa harɗe a ƙirjinsa yana kallon fuskarta cike da shauƙi ya ce, “Ba ƙyau ƙarya fa, gashi nan idanunki sun nuna kina kewar ɗan saurayinki”.
Murmushi tayi tana kauda kanta gefe. Yasa hannu ya dawo da fuskar ya hanata hakan. Dole ta haƙura ta tsaya. Bai saki fuskarta ba sai ma murza babban yatsarsa daya cigaba da yi a hankali kamar mai share mata hawaye, yana kallonta da wani irin sanyin yanayi ya cigaba da magana a hankali. “Ina can ina barci sai mafarkinki nake yi, da ƙyar na daure na fara zuwa sallar la'asar amma nazo ban ganki ba. Da ƙyar Oum da taga na damu taji tausayina tace min kina nan”.
Samun kanta tai da ɗaura nata hannun itama akan lallausar sumarsa data sha gyara, yanda ta tura yatsunta cikin sumar yasa AA lunshe idanunsa a hankali yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya buɗe idanunsa slowly ya ce, “Thanks You”.
“For what?”.
Ta faɗa a hankali.
“Everything Babie”.
Ya bata amsa cike da raɗa yana lumshe idanun da buɗewa a lokaci guda. “Kin kira dukkan ahalina kin gaishesu, ke ta dabance a rayuwata Manaal”.
“Oh ahalinka ne kai kaɗai?”.
“No sorry ahalinmu”.
Murmushi tayi, sai kuma tace “Nima ai Ammie da Daddy da Nene sunce ka kirasu ka gaishesu tun ɗazun”.
Murmushi kawai yayi, cikin son kauda zancen ya ce, “Ina son mu ɗan fita yawon salla fa”.
Ɗan jimmm tai sai kuma ta ce, “Yaushe?”.
“Yanzu idan anyi magrib. Sonai tun la'asar ma, amma ba damuwa zuwa bayan magrib ɗin ma yayi”.
“Amma kai zaka gayama Oum?”.
“Babu damuwa. Sarkin kunya.”
Yay magana yana ɗan jan lips ɗinta masu taushi da santsi..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣1️⃣
______________
........A falo kam a kusan dai-dai lokacin ne Ameeran Hajiya Shuwa ke shigowa gidan. Riƙe take da hannun ƴar gidan yayanta Ameer sai ƙaramin basket mai ƙyau ɗauke da ƙyawawan bowl a cikinsa. Mutanene sosai a gidan, dan haka kanta a ƙasa take gaida duk wanda ta gamu da shi harta isa sashen Oum. Anan ɗin ma dai da mutanen, haka ta daure ta shiga ciki bakinta da addu'a. Dai-dai tana saka kai ciki shi