Author : Bilyn Abdull Category : Romance
yazo da labarin da mai sunan”.
Wani ƙayataccen murmushi Mamy ta saki tare da gyara zamanta na ƙasaita. “Lallai lokaci yayi ashe, lokaci yayi da za'ai fito-na-fito na haƙiƙa tsakanina da Fateema akan ƳAƳANA. Saheeba! Ki ajiye wannan batun zamuyisa daga baya, amma ki tabbatar kin bibiyeta idan har zataje asibiti duba yarinyar kuje tare. Yanzu haka Abdull ne yay kirana zasuzo da matarsa da wata yarinya wai budurwar Ajwaad ɗin”.
Wani mugun faɗuwa gaban Saheeba yayi, har sai da ta waro idanunta waje sosai sannan ta furta, “Budurwar Ajwaad Mamy? Ajwaad ke da budurwa kuma?”.
“To nima abin dai ya ban mamaki gaskiya. Amma dai mu jirasu suzo ɗin. Kisa ai abinci daga ɓangarenki dan bana son ƴar tsirkun ta fahimci komai kin santa da bin ƙwaf. Yaya yasha ruwan rubutun?”.
Da ƙyar Saheeba da gaba ɗaya take a birkice ta amsa mata da, “Eh ya sha amma da ƙyar, dan sai da taita lallaɓashi wai shi nata kawai zai sha”.
Ƙwafa Mamy tayi ranta na ƙuna, sai dai batace komai ba akan haka. Itama Saheeban saita miƙe dan zuciyarta gaba ɗaya a ƙuntace take. Da haɗa hanya ta isa sashenta, kai tsaye bedroom ta afka tana rarumar wayarta dake a saman mirror. Bata ko damu da tarin miss calls data samu ba ta shiga laluben layin mahaifiyarta. Bugu biyu kuwa aka ɗaga. Ko gaisheta batai ba ta ce, “Mama akwai matsala fa, dole ki baro Kano a yau ɗin nan gaskiya. Sannan Nuratu ta taho Kanon ne?”.
“Ke lafiya kuwa kike min maganganu a gwame? Mike faruwa ko yake shirin faruwa?”.
“Abubuwane da yawa Mama, amma yanzu ina son sanin ina Nuratu take?”.
“Nuratu tana Keffi kema kin san shiyyasa batazo bikin nan na Kano ba, zasuyi bikin birthday ɗin ƙawarta”.
“Mtsoww wlhy wannan yarinyar gantalinta ya fara isata, tana can wataran zata ji an ɗaurama Ajwaad aure tunda ita bazata nutsu ba”.
“Aure?”.
“Sosai ma kuwa Mama. Tunda ita wawuyar yarinya ce. Ita tasan wlhy badan faɗi tashin da muke ni da ke akan batuntaba da tuni Mamy ta canjata da wata. Yanzu dai ki kirata idan taga da hali ta maza ta dawo Abuja dan Ajwaad baida lafiya tun jiya ko aiki bai fita ba yau. Ga Abdull nan kuma shida ƴar iskar matarsa ɗin nan mara kunya daya kawoma mutane cikin family bisa ra'ayinsa shi kaɗai wai zasuzo da wata budurwar Ajwaad ɗin ce, kin san kuma Mamy ita kaɗai ke goyon bayan auren nan nasa dama. Ga kuma wani batun a gefe da bamu gama tabbatar da shi ba”.
A matuƙar rikice Maman nata ta ce, “Na shiga uku ni Gambo, wane kuma batu ne haka Saheeba?”.
“Humm Mama ke dai kawai sai kin dawo”.
“Dawowa kam ta zama dole dan yanzun nan zan baro kano, yaranki ma sa biyo jirgi gobe dan ni ko ban samu jirgin ba zan biyo mota kawai”.........✍️
Humm, tofa🤔🥱🤨😌
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖4️⃣6️⃣
______________
.......Tunda Saheeba ta fita a sashen taketa faman kai-kawo. Wani irin watsal-watsal zuciyarta ke faman yimata. Tun tana jin zata iya daurewa harta kasa. Fitowa tai a sashen nata ta nufi sashen AA. Yanda ta shigo fuuu sai kuma tai laƙwas ganin doctor da RK da Oum a ɗakin. A take ta gyara yanayinta ta ƙawata fuskarta da murmushi. Sai kuma ta kalla Oum tana faɗin, “Na sake zuwa ne kar'a sakani a black list”.
Dariya Oum tayi itama, zuciyarta fes ta ce, “Kamar kin san na fara ayyana haka a raina, tun shigowar safe ban sake ganinki duba mu ba”.
“To ALLAH ya baku haƙuri na ɗan tsaya kan masu aikin nan ne kin sansu da aikin algus idan basu gadama ba. Yaya jikin naku?”.
Kallon AA Oum tayi da faɗin, “A jiki Alhamdullah”.
“To ALLAH ya ƙara afuwa”. Mamyn ta faɗa tana kallon AA itama da yay kamar bai ji shigowarta ba. Sai lokacin ya ɗan ɗago idonsa ya dubeta, da Muryar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina kwana”.
Wani irin motsawa zuciyar ta tai na takaici, amma sai ta danne ta sakar masa murmushi da amsawa da, “Lafiya Lau, yaya jikin naka?”.
A hankali ya amsa da, “Alhamdullah”.
Gaisheta RK yayi shima da girmamawa. Itama ta amsa da kulawa tana tsokanarsa wai shi da ɗan nasa ba'a san wazai riga wani aure ba. Ƴar dariya RK yay da kallon AA, sai kuma ya bata amsa da, “Karki damu Aunty muna tafe, dan gara ni na farayi kafin a fara kirana Baba na zaure”.
“Ato ya kamata dai, dan zaman ya isa haka Uncle tururu ɗansa tuzuru”.
Dariya kawai RK yake cike da jin nauyi, dan yana matuƙar girmama matar da ƙaunarta kamar yanda yasan ita da ƴar uwarsa suna ƙaunar juna. Dan in ba faɗa maka akai ba bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane. Oum ma dai dariya take kawai doctor na tayata, gogan kuwa yama lumshe idanunsa dan ruwa doctor ya sake saka masa saboda sake samun ƙarfin jikinsa. Sallama tai musu ta juya ta fita tana sanarma Oum zataje taɗan kwanta ta huta. Oum tai mata godiya...
Bayan fitarta Doctor dake kallon AA ya ce, “Ranka ya daɗe BP naka har yanzu yana a sama sosai, dole zan ƙara maka allurar nan ka samu barci”.
A daƙile AA ya ce, “Bana buƙata doctor”.
“Ai dama ba dole sai kana buƙata ba ranka ya daɗe, jikinka ne ke buƙata. Dan rashin saukar tashi matsalane gaskiya”.
Baki ya sake buɗewa a ƙufile zaiyi magana Oum ta katseshi. “Kaga doctor yimasa kaji, kai kuma idan ka sake magana sai na cire maka kunne ɗaya”. Ta ƙare maganar tana hararar AA, baki ya tura gaba kamar wani yaro, dan shi in har yana gaban Oum jinsa yake ɗan yaronsa har yanzu. Dariya RK yake yi, tare da faɗin, “Taɓaran banza”. Hararar shi AA ɗin yayi, shima sai ya rama. Haka suke kamar wasu tom and jarry, sam AA baya Uncle da RK, dan shi sunansa ma yake kira sai idan yaso yake cema Uncle ɗin. To sun tashi ne tamkar friends, babu wani tazaran haihuwa a tsakaninsu sosai. Sai dai RK ne babba, amma idan yace ya girmesa to yanzu zasu hau sama kuwa su faɗo dan shi AA ya tsani RK yace ya girmesa. A ganinsa girman da bai wuce sati Uku ba har wani girma ne. Hanyar ƙofa RK ya nufa yana dariyarsa da faɗin, “Aunty kinga nayi nan tunda ɗan naki ya samu lafiya har yana min rashin kunya ina matsayin babansa. Na tafi wajen aiki inda ake son ganina bye”.
Cikin murmushi Oum ta ce, “Rafeeq kadai tasa min yaro dan kaga ba magana zai maka ba. Zuwa anjima in sha ALLAHU zan kiraka na shigo ba duba Auta ta itama”.
“To ALLAH ya kaimu muna zuba idon ganinki, idan kuma ɗan shagwaɓarki bai bari ba mun yafe zan kira a waya sai ku gaisa. Dan itama ina ƙyautata zaton zuwa anjima za'a sallameta, yau tunda safe take mitar ita a sallametan”.
Dariya kawai Oum tayi tana mai girgiza kai, tasan Maanal da ƙiriniyarta, damma taga yanzu kura tayi lafiya kamar ba Maanal ɗin ba.....
______________★
Jikin Maanal ma Alhamdullah, dan tama hana Shahidah sanarma su Ammie. Dama kuma Shahidahn ma batai niyyar sanarma Ammie ɗin ba kamar yanda mijinta ya fargar da ita cewar tunda da sauki karsu tayar musu da hankali.
Abinci Maanal ɗin keci RK ya shigo, sai da ya gaisa da su Shahidah kafin ya maida hankalinsa a kanta. Cikin tsokana ya ce, “Madam ba tayi”. Ai baima gama rufe baki ba ta miƙa masa plate ɗin. Mi mijin Shahidah zasuyi ba dariya ba. Uncle Sadeeq ya ce, “Doctor kai baka san dama neman kai take da abincin ba, an turketane tana ci dan dole”.
Fuskar RK da murmushi ya ce, “Ai naga alama Babban yaya. Irin wannan bani da sauri haka. Ni dai dan ALLAH kici abinci ki ɗan ƙara kumari”.
Hararar RK ɗin tayi, sai kuma ta tura baki gaba cike da shagwaɓa. Zama Shahidah tai kusa da ita cikin lallashi ta ce, “Kinga ƙyalesu Auta kinji, bari ma na baki da kaina”. Haka ta amsa ta cigaba da bata cike da kulawa da so. Sai RK ya samu kansa da shagala a kallonsu. Shi kaɗai yasan yanda yake jim ƙaunar yarinyar nan a ransa. Komai tayi birgesa yake. Yasan hakan daga ALLAH ne. Dan yana jin feeling akanta irin wanda zai rantse bai gaɓa ji ga sauran ƴamata ba. Kodan bai taɓa yin budurwa bane oho. Sam shi ada matsoracin mata ne, babu ruwansa da harkarsu, badan bai cika namiji bane, kawai dai karatunsa na likitanci daya ƙwallafa rai da aikin nan sun kwashe mafi yawan lokacinsa na rayuwa. Idan ka cire ibada da yake matuƙar bata hakkinta. Shifa ko irin ƴar soyayyar ƙuruciyar nan baiyi ba. Kuma a turai aka haifesa anan ya girma yay dukkanin karatittukansa. Gaba ɗaya bai wuce shekara huɗu da dawowa Nigeria gaba ɗaya ba. Amma ALLAH bai ɗora masa damuwa da mata ba. Shiyyasa shi da kansa yake sake yarda da son Maanal yake bana wasa ba. Hakama ƴan uwansa kowa murna yake da batun Maanal dan sun tabbatar da gaske son nata yake tunda shidai ba'a taba kamashi da case na mace ba.
Sosai Maanal ta matsa ita sai an sallameta ta warke. Amma Dr Ranjet ya dinga lallaɓata akan tayi haƙuri zuwa gobe. Dole badan taso ba ta haƙuran...
______________★
Kusan ƙarfe uku na yamma Abdul da amaryarsa Yaseerah sai Huznah suka iso katafaren family house ɗin na Ambassador Aliyu Darma. Dan a gidan su Yaseerah Huznah ta kwana. Daga Mawaad Company can ta wuce ranta a ɓace tana hawayen abinda AA ya mata. Shine Yaseerah taita lallashinta da tabbatar mata a yau zasuzo Darma's house. Hakan kuwa akai, tun a daren take lallaɓa Abdull akan suje har ya amice. Sai kuma gasu sun iso yanzu.
Sun sami tarba daga Mamy, ƙyaƙyƙyawar mace ƴar ƙwalisa data gama tafiya da zuciyar Huznah. Kai tun kafin ma Mamyn Darma's house ya gama tafiya da Huznah. Ta gama sallamawa da jinjina kuɗi irin na gidan su AA ɗin. Ta kuma yarda kuɗin ma hawa-hawane. Tasan mahaifinta nada kuɗi, tunda suka tashi suke jin ana sakashi a jerin masu kuɗin jihar Kaduna, kai bama Kaduna kawai ba a dattawan arewa masu kuɗi za'a iya sako mahaifinsu. Sai dai kuma Baba ma fa da babansa. Ta shaida hakan a yau kuma ta aminta.
Yanda take ta faman sinne kai da kaffa-kaffa da komai sai ya baka mamaki, ko gaishe da Mamy sai da ta duƙa har ƙasa. Sai Mamyn ce dake binta da kallo ta kamata ta tadata ta zaunar a kujera. Still dai Huznah ta kasa kallonta. Ita ma dai Yaseerah bata da wata sakewa, dan dangin mijin nata ƙalilan ke sonta, duk da dai ita Mamyn na sonta. Kawai dai dan Abdull ɗin ya dage sai ita ne yasa suka ƙyalesa. Hakan yasa su biyun duk suka nutsu, sai Mamy da Abdull ne ke hira. A haka Saheeba ta shigo suka gaisa tare da saka masu aikinta jere abincin da Mamyn tace tayo a sashenta na tarbar baƙin. Saheeba dai ta danne sun gaisa da su Yaseerah, sai dai hankalinta nakan duk motsin Huznah ne. Bisa umarnin Mamy sukaje d/table, anan ɗin ma dai Huznah bata sake ba ita adole mai kunya. Ita dai Mamy sai kallonta take tana murmushi. Dan haka kawai kuma sai taji son yarinyar a ranta saboda kunyarta da nutsuwa gefe ga ta ƙyaƙyƙyawa. Dan duk ƙyawun Nuratu da da take kallo dai-dai da AA sai taga ai Huznah ta takata ta shanye. Dama dai a ƴan kwanakin nan wasu abubuwa na Nuratu sunsa ta fara shakkar haɗa aurenta da AA ɗin, amma bata fito ta faɗama kowa ba. To tana ganin yarinyar nan itace zata zama raba gardama. Dan kodai ya aurenta ita kaɗai kota sakashi ya haɗa da Nuratun su biyu a masa auren gata auren huce takaice auren da tasan zai baƙanta ran Oum fiye da auren su Fawzan.
Bayan sun kammala cin abincin ta umarcesu da suzo su duba AA. Abdull ne ya tambayeta “Baida lafiya ne Uncle AA ɗin Grandma?” (dan haka yake kiranta kasancewarta ƙanwar kakarsa uwa ɗaya uba ɗaya). Amsa ta bashi da “Eh son, yau ko aiki ma bai fita ba yana kwance”.
Gaba ɗaya ji Huznah tayi hankalinta ya tashi, dan har fuskarta ta nuna hakan ɓaro-ɓaro, amma dai ta daure batai magana ba. Mamy dai na lure da ita. Hakama Saheeba dake jin kamar ta shaƙo Huznah ɗin. Sai faman tsine mata take a zuciya. Sashen Oum suka fara zuwa, Oum ta tarbesu da kulawa kamar yanda ta saba ma ƴan uwan Mamyn, dan haka cikin girmamawa Abdull ya gaisheta, hakama Yaseerah da Huznah data kusa zubewa a tsaye da mamaki tana satar kallon Oum. Tabbas bata manceta ba, itace ta gani a gidan Shahidah tare da namiji mai kama da AA ɗinta. Rashin sanin alaƙarsu da su Maanal ɗin kuma yasa har yanzu bata sanarma mahaifiyarta ba, gefe kuma ta ɗan shiga ruɗani, shin tsakanin Mamy ɗin da matar wacece mahaifiyar AA ɗin? A dai kamanni yafi tsananin kama da Oum, shin yaya take ne?. Da ƙyar ta iya dannewa dai suka baro sashen bayan Oum ta cika su da abin arziƙi, sai dai fa da alama ita Oum bata gane Huznah ba. Koda yake a gidan Shahidah da suka haɗu ita bawani ta maida hankali a kanta bane lokacin.
Daga nan sashen AA suka nufa kamar yanda Mamy ta sanarma Oum cewar zata kaisu su dubashi. Wani irin lumshe idanu Huznah tai lokacin da suka shigo main falo ɗin sashen da wani irin ƙamshi mai daɗi ke tashi. Suna isowa falo na biyu taji zuciyarta na wani kalar tsaitsinkewa saboda haɗuwarsa. Falo kamar bana tuzuru mara mata ba. Anan Abdul ya dogare, fuskarsa da murmushi ya ce, “Grandma bari mu dakata anan a masa magana idan zai iya sakkowa mu gaisa. In ba hakaba bara na haura ni kaɗai sai na dubashi kin san Uncle baya son wargi bakamar Uncle Fawzan ba”.
Murmushi Mamy tayi, dan itama dai tasan maganar Abdull ɗin gaskiya ne. Dan in har ta hau da su Yaseerah sai yaji haushi. Su Saheeba ma dake matsayin matan yayyansa kuma ƴan uwansa na ƙut sosai yake tujara idan suka shiga masa koda falon sama ne balle. Yanzu haka ko ɗazun tana jin yanama Fadeel mitan shi matansu su daina shigo masa har bedroom.
Mamy ce ta haura saman da kanta. Dai-dai AA daya farka daga barcin da Doctor ya sakashi dole ya fito wanka. Knocking ƙofar da akai ne ya sashi yamutsa fuska cikin yanayin mara lafiya, muryar shi ƙasa-ƙasa da kamar baya son buɗe baki ya furta, “Ina zuwa”. Daga haka ya ajiye towel ɗin hannunsa da yake goge sumarsa da ruwa ya jiƙa saboda ciwon da kansa ke masa har yanzu kaɗan-kaɗan ya sakarma kansa ruwan. Boxer ya saka tare da cire bathrobe ɗin ya saka jallabiya sannan ya nufi ƙofar dan duk zatonsa Oum ce. A hankali ya buɗe ƙofar, cikin ɗan shagwaɓa ya furta, “Oum sai yanzu, ni nayi fush.......”
Kasa ƙarasawa yay saboda yin tozali da Mamy ba Oum ba. Ta koyi kicin-kicin da fuska tana masa wani irin kallo, kansa ya duƙar ƙasa yana mai haɗiye busashen yawu ya furta, “Am sorry, nazata Oum ce”.
“Humm” kawai ta furta batare data kula zancensa ba ta juya tana faɗin, “Kasameni a ƙasa baƙi zasu gaisheka”.
Kallo ya bita da shi, harta fara taka stairs case ɗin. Kaɗan ya lumshe idanunsa ya buɗe, sai kuma ya ɗan furzar da iska ya koma cikin ɗakin..........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖4️⃣7️⃣
______________
........Fin mintuna goma bayan sakkowar Mamy sannan ya sakko. Duk da sanye yake da slippers