Author : Bilyn Abdull Category : Romance
tun ɗazun ta janye idanun ta dake cike da hawaye. Suma yaran Ammie tace, “Ku wuce muje”. Suma babu wanda yay musu. Har falo Ammie takai Hajiya Yaya, ta taimaka mata ta zauna sannan ta dubi yaran ta ce, “Ku bani ruwa mai sanyi”.
Amrah ce dake hawaye taje ta ɗauka mata. Koda ta kawo Ammie ta buɗe ruwan Hajiya Yaya ta ba, nanma bata musa ba ta amsa ta sha, dan ji take tamkar zuciyarta zata fashe mata a cikin ƙirji. Sosai tasha ruwan, dan ɗan kaɗan ta rage. Kamar dama ruwan take jira tasha kawai ta saki kuka. Yaran duk sunyo kanta a zabure zasuyi magana Ammie tai musu alamar suyi shiru. Duk komawa sukai suka zauna, sai da Hajiya Yaya tai kuka sosai sannan Ammie ta ciri tissue ta bata ta kuma sake bata ruwan tasha. Bayan wasu mintuna ta sake natsawa Ammie ta fuskanceta.
“Yaya kuka ba shine mafita ba, na barki kiyisa ne dan ki samu nauyin zuciyarki ya ragu. Kiyi haƙuri idan na shiga hurumin daba nawa ba. Amma Yazeed ba kuka ko biyema yarinyar nan ai rikici al'amarinsu ke buƙata ba. Hasalima ɗauke idanu daga garesu shine yafi alkairi, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, saboda Yazeed baya a cikin hayyacinsa gaba ɗaya. Yanzu shi yana a wani matsayine da baya banbance fari da baƙi sai wanda yarinyar nan ta nuna masa kawai. To idan muka ce ta ƙarfin tsiya zamu sakashi ya gane akwai babban matsala, dan maimakon ya gane ɗin sai ya sake rikice mana ne kawai, idanunsa su sake makancewa daga ganinmu. Dan haka dole zamuyi haƙuri da kauda kai na wani ɗan lokaci, mu shanye zafi da radaɗin da muke ji akan wannan sabon yanayin nashi tunda mun san bayin kansa bane. Ita kanta yarinyar mu barta ta rinƙa jin tamakar ta gama samun dukkan nasarar da take buƙata sai mu samu damar gayama ALLAH damuwar ya warware mana ita cikin sauƙi kuma. Amma tankawa da nuna damuwar kai tsaye a yanzu tamkar sake zaburar da ita ne ta cigaba da sabon shiri a kansa, shi kuma dama illar sihiri ɗaura wani aikin akan wani, yakan sa asha wahala sosai kafin a raba mutum da shi. Wannan shine mataki na farko da zai taimaka mana. Mataki na biyu addu'a, Yaya Addu'a Yazeed yake buƙata daga garemu baki ɗaya. Kuma taki ita ce mafi ƙololuwar daraja a gareshi, itace kuma tamkar yankan wuƙa. Kasancewar ta a hakan kuma bazai samu ba sai kin daure kin sanyaya zuciyarki, kin yafe ma Yazeed kurakuransa. Ki rage barci, ki tashi cikin dare ki gayama ALLAH damuwar ki masa kuka ki masa bagiya shi mai ji ne mai gani, kuma shine ke raba abinda duk duniya babu mai kwatantawa. Yaya da zakiji wahalhalun da na fuskanta a rayuwata data zuri'ata da kince wannan na Yazeed ba komai bane ba. Amma wlhy ban taɓa zuwa gaban wani na duƙa nace ya taimakeni da garin magani ba. UBANGIJINA na fuskanta, shi kaɗai na amince zai yaye min damuwar da ƙuncin. Na ajiye maganar barci gefe, na sadaukar da rabin nema na a sadaƙa, na maida harshena da laɓɓana a ambaton UBANGIJI ne a koda yaushe. Na rungumi ƙishirwa da yunwa a kowane yini. Na sakama zuciyata jarumta da tunatar da kaina akwai fa wanda suka fini shiga ƙuncin rayuwar, akwai wanda idan zanga halin da suke a ciki nawa ba komai bane ba. Na dinga tuna ANNABAWAN ALLAH ma an jarabcesu. SAHABBAN MANZON ALLAH sun sha gwagwarmaya da jarabawoyi kala-kala. Amma da sukai haƙuri wace irin riba ce basu samu ba. Ƙarshen dai wahala da faɗi tashin bawa shine ya samu makoma mai ƙyau ta aljanna. To su tun ma suna duniya akama mafiya yawansu albishir da aljannar, sakamakon ayyukansu na alkairi da sadaukarwar yaƙi a bayan MANZON ALLAH. Wannan abubuwan sun ƙarfafani matuƙa, na kuma saka yarana suma suka dage, dan nasan yanda tasirin addu'ar uwa take akan ɗa haka addu'ar yara nada tasiri matuƙa. Dan haka Yaya ki jure, ki gwada ki gani in sha ALLAHU zakiyi dariya nan bada jimawa ba, al'amarin Yazeed zai zama tamkar labari ne. Muma kuma ba zama zamuyi ba in sha ALLAHU. ALLAH ya baki haƙuri ya sanyaya ranki.” ta juya ga yaran suma da duk suka nutsu suna saurarenta.
“Kuma ina muku nasiha da ku kauda kanku akan al'amarin Yayanku, komi zaku gani tsakaninsa da matarsa dan ALLAH ku daina zuwa kuna faɗawa mahaifiyarku. Ba wannan Yazeed ke buƙata ba, addu'a yake buƙata, idan ba haka ba maimakon mu tsamoshi a wannan masifar sai dai mu sake bada hanyar sakashi a cikin wani. Kunga dai abinda yaso faruwa. Da taci nasara ya mari mahaifiyarku kunga ya sake shiga wata masifar ne ai ko. Ku kwantar da hankalinku mu haɗu mu tayashi da addu'a, sadaka, komai zai wuce”.
Daga haka Ammie ta miƙe abinta. Harta kusa kaiwa ƙofa Amrah dake kuka sosai ta ce, “Ammie!”.
Tsayawa Ammie tayi, tare da juyowa tana kallon ta, sai kawai Amrah ta taso da gudu ta rungumeta tana sake fashewa da kuka da faɗin, “Mun gode Ammie, mun gode, in sha ALLAHU ke ƴar aljanna ce. Dama nace ke mai ƙaunarmu ce da zuciya ɗaya amma ba'a fahimtata.....”
Murmushi Ammie tayi, tare da ɗagota, cikin katseta ta ce, “Amrah ya isa haka kinji, mu dukanmu in sha ALLAHU ƴan aljanna ne. Kuma ba fahimtarki ne ba'ayi ba. Kowace rayuwa da nata ƙalubale ne kinji”.
Amrah zata sake magana Ammie ta hanata, sai ma share mata hawaye datai tas sannan ta maidata ta zaunar ta fice...
★Baki Hajiya Basariyya ta ƙyaɓe. Tare da faɗin, “Kai wannan kilakakkiyar mata anyi munafuka. Ita adole gata ALLAH. Yannn! yannnn! yannnn! Tana wani zabga wa'azi. Sai dai kuma a gayama wasu amma wlhy bamu ba. Ubanwa ye zai yarda wani kin tsaya a addu'a ne da azumi da mima tace. Waye wawa an gama tsaface mana miji, da samarin ƴaƴanmu sun aure ƴaƴanki”.
Haka dai ta gama surutanta sai kuma ta gyara yanayinta ta nufi cikin falon Hajiya Yayan a ɗan rikice. Har wani neman yin tuntuɓe take zata faɗi. Tadai dafe kujera tana kaiwa zaune kusa da kujerar da Hajiya Yaya ke zaune. Sudai kallonta suke kawai. Cike da makirci ta fara faɗin, “Mun shiga uku, ina wanka yanzu Jannah ke sanar min abinda ke faruwa. Kai wannan yarinya anyi ibilishiya, ita yanzu dan bata da mutunci sai ta saka Yazeed ya mareki, kai ALLAH wadan naka dai ya lalace. Amma gaskiya dai ya kamata a kira Sabuwa a gaya mata wannan ɗanyan aiki tazo tai mata faɗa dan ba halin arziƙi bane ba. Yanzu haka ƙawayen banza ne suka ɗorata a wannan hanyar mara ɓullewa. Yo mara ɓullewa mana kasa ɗa ya mari suruka ina arziƙi. Ita bata tunanin zata haifa tunda ga cikin nan a gabanta itama za'ai mata wataran. Ai ni yaran nan baku ƙyauta min ba da baku haɗu kun lakaɗama shegiya duka ba, har sauran ƴan uwanku duk basai ku kira ba damu mu haɗu mu ci ubanta ai daɗi gidan yawan kenan dama ko”.
Amrah da surutun ke ƙonama zuciya ta ce, “Ai hakan baida amfani Ummi. ALLAH kawai ya shiryeta. Jarabawace watarana sai labari.”
Kasare Hajiya Basariyya tai tana kallonta, ta zata wani zai sake magana ta samu point, sai taga kowa bai tanka ba. Hajiya Yaya ma miƙewa tai abinta ta nufi bedroom. Sai suma yaran suka fara miƙewa.. ganin fa zataji kunya sai itama ta miƙe tana faɗin, “To ALLAH dai ya ƙyauta. ALLAH kuma ya kiyaye gaba iyakarta kenan”. Daga haka ta fito tana tsine musu a zuciya. Ganin nan babu nasara sai ta nufi sashen Ammie, Sakina da Waleed kawai ta samu, sukace mata Ammie na sashen Daddy. Nan ma ta fito cike da baƙin ciki, amma sai itama ta nufi sashen Daddy ɗin duk da kuwa ɗazun taje ya korota..........✍️
🤣Itafa Hajiya Basariyya tafi dacewa da haihuwar Saheeba. Kai ALLAH ya rabamu da munafunci gaskiya☹️.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣7️⃣
______________
.........Maanal na kwance barcin wuya ya ɗauketa dan oga da kansa ne ya gama wajigata. Itako sarkin raki tasha kuka har ta godema ALLAH. Sam ta kasa sabawa, gabanta har faɗuwa yake ya nuna buƙatarsa a gareta. Zata biye masa a shan minti amma da anzo fagen fama ta fara kuka da roƙo. Shi ko ya zama kurma ya zama makaho har sai ya samu yanda yake so dan bai san ɗanɗani haukaci ba bai kuma san haƙuri ba. Kwana biyun nan har ƴar rama ta fara. Ko kuma ta gudu sashen Oum sai yata zarya ko Oum ɗin ta korosu sannan. Gaba ɗaya ta ƙagara weekend ɗin nan ta ƙare, idan aka koma aiki ta samu sauƙinsa ai tunda da rana babu dama.
Oum data fahimci matsalar Maanal dan ramar da yarinyar ta fara ta fara tsaya mata a rai sai ta shiga haɗa abubuwa, ta kuma amso wasu hannun Hajiya Shuwa. Itama ta fuskanci irin wannan yanayin a hannun Abah, dan shima akwai fitina kamar AA ɗin, kai bama su kaɗai ba kusan duk mazan family ɗin Darma haka suke sai dai wani yafi wani. Gasu kuma ALLAH ya jarabcesu da son zama da mata ɗai-ɗai, shiyasa matan ke jigatuwa a hannunsu kafin su saba..
Kiran da Oum tama Maanal ɗin a waya ne ya farkar da ita, dan AA ya fita shi da Yaya Fawzan shiyyasa sai ita kaɗai. Muryarta kawai Oum ɗin taji ta fahimci mike faruwa. Dan dama tana anan sashen suna hirarsu AA yay kiranta a waya ta kawo masa wai fruits dan shi yana sashen Abah suna meeting shi da su babban Yaya. To daga kai fruits ɗin ne fa ya samu ya matseta a sashen sai da ya sauke damuwarsa sannan yay shirin fita da zasuyi da Yaya Fawzan ɗin. Ita kuma wahala ta hanata tashi dan barci ne ya ɗauketa sama-sama ma taji fitarsa. Cike da tausayi Oum ta girgiza kai, sai kuma ta ce, “Barcin yamma kike Baby?”.
Cikin sanyin murya Maanal ta ce, “Eh Oum, amma na ma tashi gani nan zuwa sashen.”
“Okay sai kinzo”.
Oum ta faɗa tana yanke kiran. Itama Maanal tashi tai ta shiga bayi ta gyara jikinta yanda ya kamata, koda ta fito gashinta ta busar ta shirya cikin atamfa doguwar riga tai sallar la'asar da ake kira sannan ta gyara gadon da suka yamutsa ta fita. Ta nufi sashen Oum motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Maanal bata tsaya ba tai shigewarta, dan yanzu kusan kullum Momyn Nibras ɗin sai tazo gidan. Jiya da yamma har sabuwar rigima suka tafka da Mamy.
Wani haɗaɗɗen gashin nama mai ruwa-ruwa Oum ta bama Manaal taci ta ƙoshi, sannan ta bata abubuwa na musamman data haɗasu da kanta kuma ita tasan sirrinsu dan sune take amfani da su. Har sai da Maanal taji kamar zatai amai sannan ta ƙyaleta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Su AA basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Anan suka yada zango sashen Oum sukai dinner aka ɗora da hira, hirar gaba ɗaya akan yanda bikin Fawzan zata kasance ne dan shi aka fara shirye-shirye, amma suna saka rana a haɗa dana Babban Yaya, sai dai ba'a yanke hukunci ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu su Baba Sardauna zasuje Katsina domin ganawa da dangin mahaifin su Ameerah.
Koda AA yace Maanal tazo su tafi catai ita anan zata kwana. Shiru kawai yay yana kallon ta, Oum kuma taƙi saka musu baki. Yanda AA ya tsaya yana kallonta mi Yaya Fawzan zai yi inba dariya ba. Harda ƴar waƙarsa ta neman tsokana. Aiko AA ya wuce ya tafi kawai ransa a ɓace. Babban Yaya daya bisa da kallon ƙasan ido ya ɗan murmusa a zuciyarsa. A zahiri kam fuskarsa babu alamar wasa ya kalla Maanal da itama ta kumbura baki ta kwanta a cikin kujera. A dake yace, “Lilly!”.
Amsawa tai tare da tashi zaune.
“Tashi kibi mijinki kinji, sai da safe”.
Ji Maanal tai kamar ta fashe da kuka. Amma bazata iya ma Babban Yaya musu ba. Haka ta miƙe tai musu sallama ta tafi. Babban Yaya ya bita da kallon tausayi. Dan a ransa kawai yaji cewa ga abinda takema gudun. Cike da shaƙiyanci Yaya Fawzan da baya iya shiru shi ya kai bakinsa saitin kunnen Babban Yaya ya ce, “Idan baka saita fitinannen ƙaninka ɗin nan ba watarana ma nan Lilly zata dawo gaba ɗaya dan zugeta sanyi da kaina”.
Fillo Babban Yaya ya ɗauka zai buga masa. Da gudu ya tashi ya fice yana dariya da faɗin, “Oum goodnight ”.
Oum ta ce, “ALLAH ya tashemu lafiya.”
Shima Babban Yaya miƙewa yay ya mata sallama. Oum ta amsa masa da kulawa shima, ta musu addu'a da sanya albarka.
Koda ya fito sai yaci karo da Saheeba tsaye a ƙofar sashensu tana jiransa. Tamkar bai ganta ba ya ɗauke kansa. Da sauri tasha gabansa ta durƙusa. Tare da fashewa da kuma tana roƙonsa yayi haƙuri ya yafe mata koma wane laifi ne yake ganin tayi, wlhy bazata sake ba dan ALLAH yayi haƙuri ya barta ta dawo sashenta. A daƙile ya kalleta ya watsar, sai kuma yay wucewarsa batare dako tanka mata yayi ba ya shige ciki ya maida ƙofa ya kulle...
Kuka mai tsuma zuciya da ruhi Saheeba ta saki. Wlhy ta gaji da zaman sashen Mamy bazata iya ba. Dan duk daɗin wani waje naka wajen daban ne. Ga Mamy da saka aikin tsiya. Haka zatai zaune saboda ƙafarta ba gama ƙwari tai ba taita sakata Safa da marwa tsakanin upstairs da downstairs. Wai sai tace bata gamsuwa da aikin su Haule ita tai mata da kanta, Nuratu kuwa lafkewa take ita adole bata da lafiya. Gaba ɗaya ta maidata wata ƴar aikinta ma. Ga kewar mijinta da buƙatarsa ya riga ya saba mata da fitinarsa. Ga kewar ƴaƴanta dako kallonta basayi gaba ɗaya sun koma sashen Oum ko tunawa da zamanta a gidan basayi. Ga jiya mamanta tace mata ta sanya ido akan Babban Yaya dan tasan mike faruwa tsakaninsa da ƴar Hajiya Shuwa. Wannan magana ma tafi komai ɗaga mata hankali. Dan a duniyar nan babu abinda ta tsana irin kishiya. Kai itafa ko ƙawarta akama kishiya ta daina ƙawance da ƙawar kenan. Shiyyasa ta shirya zuwa ta bashi haƙuri dan gara ta dawo kusa da mijinta in ma nesa da shi da take ne ya sashi fara kallon wasu matan. Tun ɗazun take dakon fitowarsa daga sashen Oum. Dan ita Nuratu yau taje gida amso musu wasu kayayyaki da mamansu ta aiko da su..
Ta jima a wajen tana kuka. Kafin ta tashi ta koma sashe Mamy. Ta buɗe ɗakin da take zaune ta shiga, waya ta ɗauka tai kiran Mamanta tana mata kuka ta zayyane mata komai daya faru. Ran Maman ya sake ɓaci, amma ta kwantar mata da hankali akan ta ƙyalesa indai sukai amfani da wannan kayan data turo duk wani girman kansa zai saukane. Wannan ya sake Saheeba jin sanyi a ranta, har tai shirin barci ta kwanta....
_______★
A ɓangaren Maanal kuwa koda ta shigo sashen nasu ta samu AA ya haye sama abinsa, har yama kashe wutar ko'ina sai amfani tai da fitilar wayarta. Tana shigowa bedroom ɗin yana fitowa daga bathroom, bathrobe ce a jikinsa alamar wanka yayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan harga ALLAH yaji haushi. Itama sai ta ɗauke nata tare da ɗan murguɗa baki ta wuce closet tana ƙunƙuni. (Haka kawai sai na zauna ka kashe ni. Sam babu tausayi a al'amarin ka. Yo in haka auren yake banga abin cewa akwai daɗi ba. Tsabar jaraba sam bana son naga mun kasance mu biyu kawai a waje tunda nasan ƙarshen zancen. ALLAH in zan dawo sashen nan gabana gabana har faɗuwa yake yi. Abu dare da safiya, yammaci da rana idan kana gida ma ba hutu.....) Haka dai taketa masifarta a rai idonta har yana cika da ƙwalla. Wai a hakan ma maganin nan na sit bath da Hajiya Shuwa ta bata yana matuƙar taimaka mata ne. Koda ta fito har ya gama nashi shirin yana zaune a cikin sofa ya ɗakko laptop yana kunnawa. Gefe ɗaya takardu ne sai kwalin fresh milk da kofi. Ɗauke kanta tai tayi shirinta. Tana gamawa tai shafa'i da wutri ta haye gado ya kwanta. Idanu AA ya ɗan ɗaga ya kalleta, sai kuma ya cije lips ya cigaba da aikinsa.
Tun fa yana aikin da marmari har yaji ina bashi yiwuwa. Tattare komai yay ya ajiye, ya tashi ya kashe fitilar ɗakin ma gaba ɗaya dan dama mara haske sosai ce ke a kunne. Maanal datai barci cike da farin cikin fushin nasa dan tasan ko dai yaya ne ta samu sauƙi kawai ta farka a rikice jin ya nutsata cikin jikinsa. Muryarta na rawa ta buɗe baki zatai magana, ai bai bari a ta gama fita ba ya rufe shi ruff da nashi. Bore taso fara masa ya nuna mata ƙarfin ba ɗaya bane, wayon ma kuma ba ɗaya ba, dan sai da yasan duk hanyar da ya bi wajen lankwasar mata da jiki ta fara amsar saƙonsa. Sai da tafiya taje gaɓar tayar mata da hankali ta sanya masa kuka. Baiko saurareta ba sai da ya samu yanda yake so. Daga ƙarshe ya koma lallashinta da mata wayon daya saba. Sai ga