Author : Bilyn Abdull Category : Romance
daukar hankalinsa yay ba, amma yasan yana yin magana zata birkice masa, dan haka yay shiru ya cigaba da cin abinsa yana diba yana bata kuma. A mamakinsu sai gashi su ci sosai abinsu. Sun kammala kenan tana gyara wajen kiran waya ya shigo masa, AS ne ya sanar masa ma'aikata fa sun taru domin masa murnar aure.
Amsa ya basa da cewar suna zuwa. Daga haka ya yanke kiran.
"Oya let's go mutane na jiranmu".
Da mamaki Maanal ta bishi da kallo dan ya nufi inda rigar suit dinsa take, "Wai mi?". Ta fada cikin sigar tambaya.
Batare daya kalleta ba yace, "Zasu tayamu
murnar aure ne".
Kasa sake cemasa komai tayi, ta karasa tattare komai kawai ta maida a basket din sannan ta mike, veil dinta ta gyagygyara tare da daukar wayarta a inda ya ajiye sannan ta nufi kofa inda yake tsaye yana jiranta.......Chapter: 14
.HUZNAH
Sosai gabban jikinta ke mata ciwo, duk yanda take tunanin iya daurewa hakan ya gagara.
Kuka kam taci harta godema UBANGIJI. Zagi babu kalar wanda Sageer bai sha ba a wajenta.
Gashi bata sake jin motsinsa ba a gidan sai bayan magrib. Tana zaune wujiga-wujiga har yanzu bata gyara jikinta balle sauke nauyin sallolon dake a kanta ya shigo dakin. Kallo daya yay mata ya dauke kansa, batare da damuwa da hararar da take binsa da shi ba ya wuce bathroom din dakin. Ruwa mai dumi ya tanada sannan ya fito, batare da Huznah data cusa kanta a kafafunta tana sabon kuka na takaicin ganinsa ta ankara ba taji kawai an ciccibeta.Mutsu-mutsu ta farayi na son sauka, amma da yake karfi ba daya ba ko gezau ya shige bayin da ita. Tana kai masa duka da komai da fisge-fisge ya taimaka mata. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa mata jiki ta samu yar nutsuwar da yake bukatar ganinta a ciki sannan ya fito a binsa muryarsa babu alamar wasa ya bata umarnin yin wanka tare da gargadinta mintuna biyar ya bata tazo tai sallolin data tarama kanta. Idan kuma ba hakaba zata sha mamaki.
Haka kawai taji wata masifaffiyar shakkarsa, babu bata lokaci ta gabatar da duk abinda ya sanyata ta fito tana dingisa kafa daure da towel.
Duk da ta bashi dariya da tausayi duk sai ya danne, fuskarsa babu fara'a ya mika mata riga da hijjab, komai batace ba ta dauka ta sanya ta fara gabatar da salla. Sai da yaga har tayi raka'a biyun farko sannan ya fita domin zuwa massallaci shima.......
Karfe biyar Abah ya kirata yace ta fito su wuce. Lokacin tashi yayi, amma akwai aikin da take yi, sai dai bazata iya cema Aban haka ba, sai kawai ta tattara aikin da abinda duk zata bukata ta tafi da su bayan ta kashe wutar office din ta fice. Kai tsaye inda AS ya nuna mata zata dinga ajiye key dan masu shara da safe su gani ta ajiye. Batare da tabi takan AA ba ta fice abinta ta samu su Abah. Cike da girmamawa ta gaisheshi sannan ta shiga driver ya maida kofar da dama shine ya bude mata ya rufe. Fuskar Abah da murmushi ya danka mata tsarabar da yayo mata, dan shi fa har yanzu kallonta yake tamkar su Naufal a gabansa. Cike da jin dadi tai godiya ranta fal farin ciki...
Sam AA bai san da tafiyar Maanal ba. Aiki ya masa yawa harya shiga over time din nasa na tsiya. Kiran magrib ya sashi kallon kawataccen agogon dake a office din. Dan tsai yay cikin tunanin Maanal data fado masa a rai. Sai kuma ya dauka waya yay kiran AS dan yasan tunda bai shigo masa sallama ba shima yana nan bai wuce ba. llai kuwa hakanne. Yana dauka daga can AA din ya furta, "Zo mana". Ya yanke kiran.
Babu jimawa sosai AS ya shigo, sai da ya masa sannu da aiki kafin yace, "Gani sir".
Batare da AA ya dago daga abinda yake ba
ya ce, "Besty fa?".
Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce, "Sir Besty kuma?"
Karan farko AA ya dago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya dan murza. Cike da basar da subutar bakin nasa ya furta, "Maanal".
"Oh l'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi".
Jimmm AA din yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima mikewa da yay ya nufi bedroom yay alwala.
Koda ya fito tattara dukkan abinda zai bukata yay a cikin briefcase dinsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya hada da nashi shima, a tare suka sauka kasa. Sai da suka fara salla a massallaci su yan tsiraru dan akwai irinsa yan over time sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan.....
Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi daki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai ishai sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama.
Gaba daya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matukar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da karfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce...
Bayan wucewar Oum zaman shurun
ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar daukar novel dinta da glasses ta yafa karamin veil a kanta batare data daura dan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta dauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin koina dake kwanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA ya taba kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can din ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata niimtacciyar iska mai kanshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumudin karasawa gaban ruwan. Sai dai me tana daga kafa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta bukatar jin bakaken maganganun da Mamyn ke fada akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana fadin, "Amma Mamy yanzu bakya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kerna fa gashi fada kike kullum akan Abah. dan na tabbata da ace baku hada miji da Oum ba amintarku har abada bazata taba rawa balle har kukai ga wannan matakin.
Duk da dai daga bangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki hakuri da fada miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai kurewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran yan uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi hakuri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a kaddararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....
"
"Hakane ubana".
Mamy ta fada cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa.
Sai kuma ya dan kalleta da idanunsa da suka kade sosai. "Kiyi hakuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar dan uwansa.....
"
"Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na fada maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...
"Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba".
Mamy ta fada cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa.
Sai kuma ya dan kalleta da idanunsa da suka kade sosai. "Kiyi hakuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar dan uwansa.....
"
"Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na fada maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...
"Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba"."Okay haka kace? Toni zan tunkareta na
amsa tunda ba uwata bace ba ai".
"Mamy Please...."
Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta labe a dan lungun da akai adon wajen. Dan bata bukatar Mamyn ta ganta.
Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matukar tausayin AA na ratsa mata bargon jiki. Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damar tana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matukar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin karar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya din tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin karfin zuciyarta.
AA da ganin Maanal din ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taba son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga hadiye nannauyan abinda ke tsaye a makoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta.
Kayan hannunta ya dan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da kankanceta ya furta, "Daga ina?".
"Sama".
Ta bashi amsa.
Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake budewa a kanta. "Bakin nan dai bazai daina ma mutane bakar magana ba ashe?".
Samun kanta tai da dan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai labe bakin kadan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita.
Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kadan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita.
Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu daya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba daya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan kamshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gabbai. Shima din wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta, "Bestie, please give me a hug mana".
Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta dago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na kyallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne.
Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da bacin rai.
To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Wannan ai cin amanar Abah ne Gaskiya
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣
______________
........Samun kanta tai da sakar masa sassanyan murmushi, tare da buɗe hannayenta a hankali alamar bashi damar daya buƙata.
Idan yace zuciyarsa bata nema tarwatsewa ba a wannan gaɓar yayi ƙarya, amma wannan ba lokacin tunani ko nazari bane. Duk da ya mata tsaho sosai cike da jin illahirin jinin jikinsa na narkewa ya wani irin shigewa jikin nata ya rungumeta tsam har sai da ta ɗan rumtse idannunta. Sosai tausayinsa ya shiga marmashe mata illahirin zuciya, dan kasancewar kanta kwance a ƙirjinsa tana iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, ga hucin numfashinsa na sauka a kunnenta da zafi-zafi. Sun kai tsahon mintuna biyar a haka, ita harma ta fara jin ƙafafunta sun mata nauyi. Sai taji shima kamar ya mata nauyin. Muryarta na wani irin komawa sanyi ƙalau ta ce, “You're sleepy?”.
Maimakon bata amsa sai ya girgiza mata kai kawai. Sai kuma ya miƙe tsaye sosai ya ɗagota itama daga ƙirjin nashi ta tsaya da ƙafafunta. Fuskarta ya kafe da sassanyan kallo, ita sai ma ya bata kunya. A hankali ta risinar da idanunta ta koma kallon yatsun ƙafarsa dake fes-fes cikin tattaunsan baƙin takalmin daya sanya. Hannu yasa ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta cikin hannunsa. Maimakon ta kallesan kamar yanda yake buƙata sai ta lumshe idanun nata. Murmushi ya saki kaɗan, cike da son tsokanarta ya ɗan ranƙwafo ya dai-daita fuskar tasu numfashinsu na sauka a fuskokin juna. Cike da shauƙin yanayin nasu ya furta, “Besty!”.
Kasa amsawa tayi, dan gaba ɗaya jinta take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shima fahimtar bazata amsa ɗin ba sai ya sake sakin murmushi irin mai maƙalewa a gefen bakin nan. Cikin maida muryar tasa ƙasa-ƙasa sosai tamkar mai raɗa ya ce, “An bani Hug saura kis....”
Ai baima kai ga ƙarasawa ba ta waro idanunta gaba ɗaya warrr a kansa. Sai dai kasancewarsu gab da juna ya sata maidawa kuma da sauri ta lumshe tare da janye jikinta baya tabar wajen da sauri. Dariya sosai ta bashi, amma sai baiyi ba ya saki ɗan murmushi yana miƙewa tsaye da ƙyau ya zuba duka hannayensa a cikin aljihun farin jeans ɗin wandonsa ya bita da kallo. Sai da ta zauna batare da ko waiwayensa tayi ba ta buɗe novel ɗinta ta sanya eyeglasses a idonta sannan ya shiga takawa a hankali zuwa inda taken..
★ Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing ɗinta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taɓa tunanin a rikicen take ba dan ta maze ƙwarai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing ɗinta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faɗar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da ƙyau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television ɗin kallo.
Cike da tsokana ya furta, “Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA”.
Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauƙin ƙaunar Autan nata tace, “ALLAH to ya tabbatar Autan Oum ɗinsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.”
Murmushi AA yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta, “Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.”
Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce, “Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu”.
“I'm so happy, Oum! gamu nan”. Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) ɗinsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book ɗin Maanal tare da ɗaukar kwalin popcorn ɗin nata da goran ruwan ya ce, “Oya let's go Oum na kira”.
Komai bata kawo a ranta ba ta miƙe kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaɗa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya ɗan ƙawata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaɗi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suɓuce mata da ƙyar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaɗan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Daƙyar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faɗin, “let's go tunda gasu can.” bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riƙewa. Suna zuwa ƙofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haɗa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu.
AA kam daya shige shi kaɗai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da ƙyau, sai kuma ya ɗan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA ɗin yayi,