AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   213 / 213

636K to 636.6K   out of 636.6K words

sukaje sashensu sukai wanka sannan yaran suka shirya abincin da suke haɗawa tun ɗazun a ƙaton dining table dake babban falo. Zaman hira akai ƴaƴa da iyaye zagaye da su Oum har magrib, bayan an idar suka zauna akai Isha'i sannan suka dawo gida. Suma zuwa lokacin su Maanal sunyi tasu kowacce ta yi sabon wanka da kwalliya ma oga, yaran ma sun yi tsaff da su sannan aka haɗu a dining. Cike da farin ciki da ƙaunar juna sukaci abincin su. Yaran suka gyara wajen mazansu da matansu sannan aka dasa sabuwar hira. Sai kusan 11 kowa ya nema makwanci. Washe gari ɓuruntun yara ya tada kowa. Koda suka fito sai suka tarar an gyara falon anyi decorating ɗinsa tare da ƙaton Symbol an rubuta *_HAPPY WEDDING ANNIVERSARY to the world's most wonderful grandparents! Your love is our legacy, and your journey inspires us every day._* Ƙasa suka saka 67years. Gasu sunci gayu sun haɗa abincin breakfast. Mamaki sosai iyayen sukayi, ashe abinda suke shiryawa kenan tun jiya.
      Farin ciki ya kamasu, hakama Oum da Abah bakinsu yaƙi rufuwa. Haka suka sakasu yin gayu. Su ma su Babba Yaya ai dole suka koma suka sake kwalliya. Sai da RK da Nuwaira da Aliyu da Kashim yaransu ƙannen Norah. Ai fa gida ya ƙara armashi. Anci ansha Abah da Oum suka ɗaɗarama cake wuƙa. Uncle RK shine Baba shi aka fara sakama a baki, sannan su Babban Yaya da su Maanal. Aka koma kan jikoki. Sosai ƴar walimar da yaran suka shirya ta ƙayatar. Ashe basu gama ba, da yamma ba sai ga ƙawayensu da abokai sun cika gida ba. Suka sha partyn su suka rakwashe suka ƙwalle sai iyayen suka zama ƴan kallo, dama ba barinsu suke yin wani birthday ba. Dan haka yau ma komai sun yi shi cikin nutsuwa da tarbiyyar da suka samu. Sai da za'ai hotuna su Maanal suka fito compound inda yaran suke bikinsu. Haka akai hotuna sosai harma da videos zuwa magrib aka tashi kowa ransa fal da farin ciki.✍️

Alhamdullahi, Alhamdullahi, Alhamdullah!! Kamar yanda nima Bilyn Abdull anan zan tsaya raina fal da farin ciki. Kuskuren da nayi ya rabbi ka gafarta min. Wanda na faɗa dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladan ni da ku masoyana.🥰🙏

Kunyi ƙoƙarin kunyi juriyar bibiyar wannan labari daya mamaye mu yay tsayi fiye da yanda mukai zato. Amma Alhamdullah yau dai mun kai ƙarshe. Sai dai na ƙara ilimi da gane cewa lokaci na UBANGIJI ne, duk yanda ka kai ga sakashi bisa tsarin ka sai ya yarda. Sati biyu naso nayi na kammala bayan dawowarmu hutun salla. Amma sai gashi mune har a yau. To wannan itace tsarawar UBANGIJI ta gaskiya, dan dama kana naka ne yana nashi.😊❤️

Bazan gaji da godiya a gareku ba masoya, wanda suke bibiyata tun tale-tale dama masu ƙaruwa a yanzu. ALLAH ya saka muku da alkairinsa, ya tsare gabanku da bayanku, ya sanya farin ciki a rayuwarku kuma. ALLAH ya haɗamu a aljanna baki ɗaya. Ya rabbi duk wanda ya soni ina roƙonka da sunayen ka ƙyawawa masu tsarki kaima ka sosai haka shi da zuri'arsa baki ɗaya.❤️❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🙏

Duk wanda na ɓatawa a yayin rubutu littafin nan ya yafe min, nima duk wanda ya ɓata min in har ba'akan izgili da ganganci bane na yafe masa. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya.😭😭🙏

     
   Ina son ku!!🥰 ina son ku!!😘 ina son ku!!❤️. Ina taya mu murnar shiga sabuwar shekarar musulunci. Sai kuma ALLAH ya kaimu wata sabuwar shekarar munzo muku da sabon Zafafa.❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Yanda zanyi kewar Maanal da AA Darma kuma zanyi kewarku masoya.

WhatsApp number
+234 805 568 7449

Bilyn Abdull ce😘   
((C)) 2015💤🔥✨

213 / 213

Chapters