Author : Bilyn Abdull Category : Romance
da komai na bayi irin na zamani. Sai wani ƙanshi yake dan shima yaji turaren wuta. Da taimakonsa tai alwala, dan tace tana da tsarki, shima dai yana da shi ɗin, dan haka bayan ta kammala shima yayo suka fito. Anan closet ɗin ya ɗauka sallaya da hijjab da yaga an tsarasu suma a nasu ɓangaren sannan suka fito. Shi ya shimfiɗa musu sannan yazo ya gyara mata mayafin lafayar da ƙyau.
Sun gabatar da salla cikin nutsuwa, ya rufe musu da shafa'i da wutri. Sannan ya juyo ya dafa kanta yay addu'a da ya dace ango yayi, ya kuma sake cigaba da wasu addu'oin masu ratsa jiki da zuciya tsawon lokaci. Daga haka ya mata tambayoyi duk da yasan baida haufi a kanta tanan ɓangaren sam. Amma dai yayi ɗin dan yana son yasan a zuwa yanzu wane mataki take a neman ilimin. Yaji daɗi sosai jin bata zauna ba bayan rabuwarsu ma ta cigaba da neman ilimi. Dan haka ya tabbatar mata zasu cigaba da karatu a gida, zai kuma sakata wasu online class na addini suma dan ta ƙara samun sani da ɗammarar bautama UBANGIJI. Kanta a ƙasa tai masa godiya.
Hancinta ya ɗan ja kaɗan, ya ce, “Nima kike ma godiyar?”.
Murmushi tayi kaɗan, sai kuma a hankali ta ce, “Ka cancanci fiye da haka ma a gareni kai dukkan ahalinka. Tun ban san kaina ba kuke nuna min ƙauna. Ni da nawa a halin, kuna mana soyayya irin ta ƴan uwa na jini batare da kallon kun fimu da wani abun duniya ba tun ma a wancan lokaci. Abah ya zame ma iyayena Yaya, Oum ta zame musu aunty. Ku kuka zame mana yayu. Koda hararrarmu akai baƙwa ƙyalewa balle duka. Ku ɗin a garemu babban alkairi ne da baki yayi kaɗan ya furta. Bamu......”
“Shiiiiii!!!” AA ya faɗa a hankali yana ɗaura yatsarsa akan lips ɗinta. Idannunta ta ɗago a hankali ta kallesa, shima kallon nata yake cikin wani irin kasalllalen yanayi. Yanda suke kallon junan a tare tsigar jikinsu ke wani tashi, zukatansu na narkewa a ƙirazansu. AA ne ya fara janye nasa a hankali, batare da yace komai ba ya yunƙura ya miƙe. Sallayar ya ninke, ya ajiye. Saman carpet ɗin nan ya koma ya zauna a ƙasa, a nutse a kwance ɗaurin net ɗin nan da akama basket ɗin. Ya kwashe ledar da aka zuba flowers ɗin saman gaba ɗaya ya ajiye gefe. Kyakkyawar kwali ne ya bayyana, sai milk na kwali guda biyu, sai wani ɗan basket ƙarami da kayan fruits an naɗe samansu da leda suma. da aka zuba a sama gefe. Sai kwalin pizza da shawarma da sandwich suma kowanne an naɗesa daban. Sai wani kwali ɗan babba da bai san miye a ciki ba, da wata leda itama a gefe ƙarama. Juyawa yay ya ɗan kalla Maanal, ganin tana wajen zaune har yanzu ya ce, “Bestie zo kiga”.
Kallonsa ta ɗan yi, sai kuma yanda yay magana babu wasa yasa ta miƙe kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta naɗe sallayar ta ajiye inda ya ajiye waccan sannan ta nufesa. Hannunta ya kama ya zaunar da ita kusa da shi. Kwalin farko ya fara buɗewa, kaza ce da akaima gashin ƴan gayu na musamman a ciki, sai gasashen naman rago a gefenta shima masha ALLAH. Ɗayan kwalin dabai buɗe ba ya buɗe, a mamakinsa sai yaga kaya ne a ciki na barci, nata da nashi duk da a naɗe suke, maidasu yay ya rufe kawai. Ya maida hankalinsa ga abinci yace wanne take so.
Kanta a ƙasa tace ita ta ƙoshi. Taci abinci ɗazun. Bai takura mata ba dan yaga yau an koma salihai, tashi yay ya fita, babu jimawa ya dawo da kofuna sai ƙaramin plate. Milk ɗin ya zuba a kofi ya miƙa mata. Kanta ta girgiza sai ya ɗan harareta. “Baki so nayi koyi da MANZON ALLAH ne.?”.
A hankali ta ce, “Ina so mana”.
“To bismillah”. Ya faɗa bayan yasha madaran itama ya saka mata kofin a baki. Hannunta ta ɗaura akan nashi tasha a haka. Bai kuma barta ba sai da ta shanye tass. Shi ko ya ɗan ci sandwich ɗin dan yana sonshi sosai, ya ƙara shan madarar ya haɗe komai waje guda ya fita dasu. Babu wani jimawa ya dawo ɗakin. Ganin tana lullumshe idanu ya ce, “Barci?”. Kanta ta jinjina masa. Ya ce, “Okay buɗe kwalin nan muga.”
Kwalin ta buɗe, ganin kaya a ciki sai ta kallesa. Kai ya jinjina mata alamar ta fiddo. Itama sai ta jinjina nata kan, a bisa tsautsayi tana ɗago na saman dake matsayin nata kawai rigar ta warware kanta. Ya subahannallah, ai Maanal bama tasan ta saki rigar ba, sai kuma ta juya da sauri ta kalla inda yake. Ganin yanda tai tsuru-tsuru yasa AA kauda kansa ya fuske kamar bai gani ba kafin ma ta juyo. Aiko sai ta wani sauke ajiyar zuciya, da sauri ta cikuykuye rigar da p ɗinta daya faɗo shima ta maida a kwalin. Miƙewa yay abinsa batare da yace mata komai ba ya nufi closet ɗin ɗakin, bai wani jima ba ya dawo hannunsa da wasu kayan barcin. A saman gadon ya ajiye mata, sannan yazo inda take ya ɗauke kwalin wancan kayan da ledan nan daya buɗe yaga magunguna ne a ciki.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣2️⃣
______________
.......Haɓarta ya kamo ya sumbaci lips ɗinya. “Ga wasu kayan nan ki tashi ki canja ki kwanta ki huta goodnight”. Ya sakimmata fuska ya wuce yana ɗan murmushi. Sai da taji ya fice gaba ɗaya ya rufe mata ƙofar sannan ta wani sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske kai kace irin wadda ta kuɓuta daga hannun dodon nan. Kayan daya ajiye ɗin ta juya ta kalla a karo na farko, nan ma sai ta sake sauke ajiyar zuciya ganin su kam na mutunci ne. Amma waccan gantalalliyar riga ai ba'a magana, duk wanda ya saye ta ma ba ƙaramin ƙwallon ɗan is... Bane. Ta jima tana saƙe-saƙen ta kafin ta miƙe ta kwashi kayan ta nufi bayi. Ƙara gyara jikinta tai sosai kamar yanda Hajiya Shuwa ta ɗorata a layi, sannan ta saka riga da wandon na barci masu taushi sosai gasu basu wani kamata ba, duk da dai wandon iyakarsa gwiwar ƙafarta yafi dama-dama akan waccan rigar.. sosai ta sakama jikin wasu turarurruka masu sirrin ƙamshi da Amaal ta sanar mata sun ajiye mata su anan cikin bayin, tana ko buɗe haɗaɗɗen drawer ɗin glass dake bayin da aka cika da kayan gyaran jikin Hajiya Shuwa da turarurruka na wanka da sabulai sai ta gansu. Suma ɗin dai kala-kala ne dama Hajiya Shuwa tace mata sai tana gida kawai ko zata kwanta sannan zata sakasu, haka ma sai in tana sashenta kawai. In har zata fita koda sashen Oum ne kada ta shafa. Ita bata fahimci ma'anarsu ba, ta ɗauka kawai tsarin sakasu kenan shiyyasa ta bajesu a jikinta yanda ya kamata, tsabar rawan kai irin na amare ma kowanne saida ta ɗan taɓa kuma kala-kala ne fin goma sha. Aiko ya arrahaman, bayin kansa yasan amarya tayi shirin barci....
😂To Manaluwa ALLAH ya rabamu da tsautsayi da aikin danganci🥱🤫🤭🤣🤣
_______★
A dai-dai lokacin da AA ke fita a ɗakin Maanal da wancan kaya dai-dai nan Mamy ta farka a barcin da allura ta sanyata. Maman Saheeba kawai ta gani a gefenta tana latse-latsen waya. Cikin sanyin murya irin na mai tashi a barci ta kira sunanta. Maman Saheeba ta juya da sauri ta kalleta, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Lah Aunty kin tashi? Bara na kira Aunty Babba ALLAH yasa basuyi barci ba”.
Riƙo hannunta Mamy tayi a hankali tana girgiza mata kai, sai kuma ta buɗe baki da ƙyar ta ce, “Ajwaad fa?”.
Ɗan zuba mata ido Maman Saheeba tayi, sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Yana sashensa mana Aunty, yazo miki sallama kina barci ai”.
Zaramm kuwa Mamy ta tashi zaune jikinta na rawa. Sai kuma jiri ya kwasheta luuuuu ta tafi zata faɗi dole ta koma ta kwanta tana dafe kai. Muryarta na fita da ƙyar ta ce, “Shine kuka barshi Nana? Shine baku tasheni ba”.
“Aunty kenan, wa kike ganin ya isa a cikinmu ya hana Ajwaad zuwa ga matarsa ne? Sannan ke kuma taya zamu tasheki baki da lafiya....”
“Bani wayata”.
Mamyn ta faɗa da ƙyar. Miƙewa Maman Saheeba tai ta ɗauka mata wayar, haka Mamy ta amsa duk da daƙyar ma take iya kallon screen ɗin wayar saboda ciwon kai da idanunta dake gani bishi-bishi ta shiga lalubo sunansa. Dialing no ɗin tayi, cikin sa'a kuwa ta shiga, dan haka takai kunne tana jiran a ɗaga. Sai dai me harta tsinke ba'a ɗaga ɗin ba. Sake kira tayi, amma nan ma tsitt kake ji. Haka ta dinga jera masa kira a dukkan layukansa ma amma anƙi ai picking. Sosai ranta ya ɓaci, hankalinta ya tashi. Gefe ga Maman Saheeba na faɗin, “Aunty kema kin san bazai ɗauka ba shi da ke da amarya duk da dai ba sabon waje bane, amma ai bazasu barsa haka ba sai da sabon shiri...”
“Nana rakani sashen nasa”.
Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce, “Okay muje”. Ta ajiye wayar tana miƙewa. Itama Mamy ɗin ta taƙarƙara ta miƙe sai juwa kuma ta ɗebeta ta maida akan gadon. Kan ta dafe sosai, dan ya wani sara mata na bala'i. Muryarta can ciki ta ce, “Bari juwar nan ta sakeni Nana ban ruwa”....
Mamy dai juwa ta hanata motsin kirki, dole Maman Saheeba ta bata shawarar yin wanka ko hakan zai taimaka mata, batai musu ba tace ta haɗa mata ruwan. Aiko haka ta miƙe taje ta haɗa mata sannan ta dawo ta taimaka mata ta kamata har cikin bayin. Dama ta ajiye mata komai da zata buƙata ta fito ta barta. Wayar sahiba ta kira sukai ƴar magana ƙasa-ƙasa ta kashe. Sama-sama Mamy tai wankan nan, dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen AA ne, ta riga tama kanta alƙawarin bai isa ya kwana da Maanal ɗin ba yau, wanda yay a baya har ta samu ciki yayi na ƙarshe. Kai itafa a wannan daren take son Ajwaad ya saki Maanal saki uku duk ma wacce za'ai sai ayi, shima kuma Fawzan sai ta tabbatar masa itace ta haifi abinta shi da duk masu ɗaure masa ƙugun yin auren. Haka ta lallaɓa tai wankan sama-sama, tai kiran Maman Saheeba dake ƙofa tana jiranta. Shigowa tai ta taimaka mata suka fito, da taimakonta ta ɗan shafa mai kaɗan saboda bushewar jiki, ta bata doguwar riga ta saka, ta kuma haɗa mata tea tace tasha ko zata ɗan samu ƙarfin jikinta. Batayi musu ba kuwa ta amsa tasha dan itama ƙarfin take nema ruwa a jallo. Bayan ta gama sha magani ta bata shima ta sha, tace mata taɗan kwanta yabi jikinta sai su tafi.....
Hummmmmmm!!!!! Ashe anan ma ya kamata muyi addu'ar ALLAH ya kiyaye tsautsayi da gangancin ba wajen manalu kawai ba🥱🤣
_______★
Lokacin da kiran Mamy ke shigoma AA a waya duka wayoyinsa suna anan ɗakin Maanal kuma a silent suke. Dan yau ko a vibration bai saka su ba. Shi kuma yana can a nasa ɗakin bayan ya ajiye kayan barcin nan da ledar magunguna a zuciyarsa yana saƙa yanda zai sille RK da safe dan ya tabbatar iskancinsa ne saka kayan barcin nan da maganin ya faɗa bayi yay sabon wanka da shirin barci shima. Ya baɗe jikinsa da turarurruka masu shegen ƙamshi da saka zuciya nutsuwa daya tanada domin wannan rana kawai. Ya gyara sumar kansa da kwantaccen sajensa, sai lokacin ma ya ɗan shiga neman wayoyin sai ya tuna ya barsu ɗakin Maanal. Baiyi niyyar koma mata yanzu ba, yaso sai tayi barci dan yanda take a firgicen nan baiso hanata samun nutsuwa a barcinta kasancewar yana son bata damar sakin jikinta yanda ya kamata. Fitowa yay domin ɗaukar wayoyin sai ya dawo ya ɗan kwanta anan har sai yai barci ya koma. A dai-dai lokacin da yake tura kai cikin ɗakin bakinsa da sallama ciki-ciki ita kuma Maanal ta fito a bayin bayan ta gama leƙenta ta tabbatar bai dawo ba. Sai dai me tana gama rufe ƙofar ta juyo kawai ta ganshi tsaye a ƙofar shigowa ya wani zuba mata ido. Cak ta tsaya kamar yanda yake shima cak a tsaye. Sai kuma ta duƙar da kanta tare da runtse ido tana jin kamar ta zura da gudu ta koma wani sashe na zuciyarta na kwaɓarta da tuna mata AA ne fa Bestyn ta mijin nan nata da suka kasance tare a Chaina, a ɗaki ɗaya, gado ɗaya ba wani sabo daban ba.
Shi ko mayataccen ƙamshin turarenta ne ya wani irin dokar masa brain gaba ɗaya kasalar jiki data zuciya ta dabaibaiyesa cikin. Ga ƙyawun da kayan barcin sukai mata tamkar an zanata a cikinsu. Wani irin sulululu... Jinin jikinsa ke sulalewa a cikin jijiyiyinsa. Cikin sakanni komai na jikinsa ya canja. Wanda suke a sume domin gajiya duk suka farfaɗo. Idanunsa kam sun kasa barin kanta, sai ma takawa daya shiga yi a hankali har inda take. Yana gab da isowa ta juya da sauri da nufin komawa cikin bayin. A wani irin hankali ya kama hannunta, muryarsa na shaƙewa ya furta, “Ina zaki je?”. Yay maganar yana juyo da ita gaba ɗayanta ya tsayar a gabansa cak.
Maimakon bashi amsa sai ta ɗago idanunta da suka tara ƙwalla ciki ta kallesa. Kauda nasa yayi, sai dai ina zuciyarsa tabbatar masa take bazata bashi haɗin kai ba. Hakama gangar jikinsa gaba ɗaya. Kuma harga ALLAH bai niyyar taɓata a yau ba dan shi kansa a gajiye yake barci kawai yake son yi. Amma a yanzu daya kasance a cikin yanayin ƙaulani bashi da tabbacin hakan sai abinda ALLAH yay kawai. Jawota yay jikinsa ya rungume ko zai ɗan samu sassauci, amma ina komai ma sake yin tashin gauron zabi yayi cikin ƴan sakkani, farashin ya sauya daga ainahin farashinsa. Tuni yama manta da wani batun ɗaukar wayoyi da komawa can ɗakin. Cirota yay da ƙyar a jikin nasa ya kaita bakin gado ya zaunar, sai kuma yay mata nunin ta kwanta.
Kamar mai shirin yin kuka ta ce, “Bana jin barci”.
Murmushin gefen baki ya ɗan saki, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan. Sake matsowa yay kusa da ita sosai, ya matsota ya saka a cikin jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya, hannunsa na shafa gadon bayanta ya furta, “Yau gadin gida zamuyi ke nan?”.
Ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a kai ka kwanta kayi barci”.
“Ke kuma fa?”.
Shiru tayi taƙi yin magana.
AA da dariya ke cinsa sosai yana dannewa dan wannan asanyayen data koma abin dole ya baka dariya, “Anya wannan amaryan rowanta baiyi yawa ba?”.
Baki ta ɗan tura kaɗan, sai kuma ta ɗan ɗaga ido ta kallesa, shima kallon nata yayi, amma tai ƙoƙarin janye nata dan bazata iya kallon juyayyun idanunsa ba. Ƙin bata damar cire idanun nata yayi, ya sarƙesu da nata dake cike da rauni da fargaba. Rau-rau suka cika da hawaye, maimakon ya tausaya mata ya barta sai ma ya sake narke nashi dake cike da salon shauƙi da buƙata. “Miyasa bazaki iya cigaba da kallon idona ba Besty? Babu abin da zai same ki a cikin su sai natsuwa.”
Cikin raɗa, da muryarta mai rawa ta ce, “Ina jin tsoro”.
“Why? Zaki ji tsoro Maanal, Ajwaad ne fa, Bestyn ki. Ni ba ƙarfe bane mai dukan farin ciki ko ruguzashi. Ni ruwa ne, mai goge tsoro, in shayar da kwanciyar hankali musamman a duniyarki”.
A hankali hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta samu damar lumshe idanun tare da kife fuskarta a ƙirjinsa. “Kalamanka nasa zuciyata tana bugawa da sauri, kamar tana son faɗin wani muhimmin abu a kanka, amma bana jin kalmanta sam.”
Murmushi ya saki mai taushi, tare da motsawa ya ɗagata cak ya maida saman gadon ya shimfiɗar, kanta na a saman damtsen hannunsa, sai ya ɗan rufu a kanta hannunsa kwance a saman ƙirjinta ya kai yatsun yana wasa da gashin kanta mai laushi da santsi........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣3️⃣
______________
........Gefen fuskarta ya sumbata kaɗan, cike da raɗa ya furta, “Kar kiji komai, zan saurari bugun zuciyarki har sai ta tsaya cikin nutsuwa. Zan jira fitar sautin kalmanta har su bayyana a cikin kunnuwana. Kin manta na faɗa miki zan iya jira na har abada ba a matsayin mijin da ke da HAƘƘI ba, domin ke nake kallo a matsayin ke ba surar jiki ko manufar sauke buƙata ba”.
Numfashi ta sauke mai ɗan nauyi, sai kuma ta buɗe idanunta kaɗan tana kallonsa yanzu, cikin ido. Idonta yana ɗauke