AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   145 / 213

432K to 435K   out of 636.6K words

hajjajunku an lafe a jikin AA ana sauke ajiyar zuciya.....

       Na gabannin asuba kam da ya zame masa jiki kuka ta saka masa bana wasa ba, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Koda ya fita salla kafin su dawo haka ta daure ta tashi ta hau gyaran gidan, harta sakko kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa breakfast sai gashi ya shigo. Ƙin yarda tai ta kallesa, a haka ta gaishesa ita a dole tana fushi. Shi sai ma ta bashi dariya. Ya rungumeta yana murmushi da faɗin, “Haba Besty munyi faɗa ne wai?”.
      Baki ta tura gaba, idannunta na tara ƙwalla ta ce, “Eh munyi, kuma kada ka sake kulani tunda baka tausayi na. Ni wlhy sashen Oum zan koma kafin ka kasheni.”
     Sosai dariya tazoma AA wuya. Amma ya danne da ƙyar, a ransa ko ayyanawa yake (Inda ana mutuwa Besty da ba'a haifomu ba ai. Kedai kin cika raki ne kawai da tsoro. Sai kuma yanayin jikinki da sai dai nace Alhmdllh) a fili kam rungumeta yay yana lallashi, sai da tace masa ta haƙura sannan ya fara tayata sukai komai a tare, su Inte ta kira a waya suka kwashi abincin zuwa sashen Oum, dan haka take yi, a sashenta take musu breakfast gaba ɗaya, sai akai can sashen Oum, da rana kuma taje can tayi, hakama na dare. Yau da tasan zata koma aiki saita haɗama Oum harda abincin ranar ta, suma tai musu nasu ta na lunch. Tare sukai wanka suka shirya.
        Kayan farko data ɗakko zata saka AA yace bai yarda ba. Shi da kansa ya zaɓo mata wanda zata saka. Data saka ɗin kuma nan ma ya haɗe fuska wai suma ɗin dai tayi ƙyau. Gudun kar ya ja musu makara ta shiga lallashinsa, da ƙyar ya haƙura suka fito.........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣8️⃣


______________


.......Sashen Mamy suka fara nufa. Sosai zuciyar Mamy ta wani irin tsargawa. Dan wani irin ƙyau da nutsuwa ta gani a fuskokin yaran. Kodan hankalinta ba a kwance yake ba kwana biyun nan shiyyasa bata luran ba sai yau. Badan kar ace tayi ƙarya ba da tace idannunta kamar suna kallo mata yaron ciki a tare da Maanal. Kai ina abinda ma bazai yiwu ba kenan. Ciki fa, tabbas yarinyar nan akwai ƙaramin ciki a jikinta. Sai maganar wancan cikin ƙaryar ya faɗo mata a rai, a take taga wautarta a wancan lokacin, to yama akai ta zurma da wuri daga ganin yarinyar na amai, yanzu kam gashi babu wani signing na ciwo a tare da ita amma wlhy gaba ɗaya alamomin yarinyar ya mata na mai ciki.....
       Gaisuwar da suke mata ta katse mata tunaninta. Da ƙyar ta iya amsawa tana tsare AA da shima yay mata wani fresh da shi da ido. Yaron ya ƙara ƙyau da cikar kamala harda ƙiba. Kaida ka ganshi kasan hankalinsa a kwance yake, yana kuma hutawa da kwasar ganima a jikin mace dai-dai gwargwado. A lallai babbar magana. Ina hankalinta ya tafi har haka ita kuwa. Bata da amsar hakan, dan a yanzun ma dai hankalin nata baya a tare da ita har AA da Maanal ɗin suka fice abinsu. Sai Saheeba da itama jikinta ke mazarin abinda ta hango a tattare da Maanal ɗin ta maidota hankalinta ta hanyar faɗin,
       “Kai amma yarinyar nan fa wlhy kamar mai yaron ciki”.
    “Taratsatsatsa!!!!!!”. Kake jin sautin tarwatsewar abu a ƙasa. Ba komai bane face kofin shayi da Nuratu ta fito da shi a hannu daga kitchen. Dan ƙamshin turaren AA da tajiyo ne ya sata fitowa da sauri sai furicin Saheeba a kunneta babu kuma AA a falon. Muryarta na rawa ta ce, “Ciki kuma! A jikin wa?”.
      Saheeba ta ce, “A jikin wa kuwa in ba tsinanniyar yarinyar nan ba Maanal. Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara wannan yarinyar ciki ne da ita ko Mamy?”.
    Mamy bata iya ta bama Saheeba amsa ba Nuratu dake hawaye ta ce, “Kenan da gaske wancan cikin bana gaskiya bane yarinyar nan is a virgin?”.
        Saheeba tace, “Tabbas wancan lokaci mun ruɗa kammu ne kawai yanzu ne yarinyar nan ke ɗauke da ciki na gaske. Maganar budurwa ce kuwa dole shima mu bincika dan akwai ƙamshin gaskiya”.
      Saheeba ke bayanin amma zuciyar Mamy ce ke duka da ƙarfi, jikin Nuratu kuwa na rawa.....

★★★

      Su AA da basu san suna yi ba kuwa tuni sun isa sashen Oum. Itama dai yau kamar hasashen su Saheeban ya buɗe mata idanu akan Manaal ɗin. Dan sai duk kammanin ta suka juye mata na mai yaron ciki. Ko kuwa kwalliyar da tai ne ya canjata zuwa hakan. Duk da bawai Maanal ɗin tayi zane-zane a fuska bane. Hasalima hoda da kwalli sai lips-gloss ne kawai ta saka.
     Komai dai Oum batace akan hakan ba, sai ma gaisuwa da sukayi, dai-dai kuma nan Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo suma a tare cikin shirin fita. Manaal ta gaishesu suka gaisa da Oum da AA sannan sukai zaman yin breakfast. Yau dai Fawzan bai tsokani AA ba. Hakan yasa Oum da sauran ƴan uwansa fuskantar ransa a ɓace yake. Sun tabbatar dai bazai wuce shi da Nibras ba, dan haka cikin hikima irin ta iyayen ƙwarai Oum ta shiga yimasa nasiha, ai ko sai gashi kafin su gama su fito harda ɗan murmushinsa. Su dukansu sukan shiga damuwa a duk lokacin da suka ga babu fara'a a fuskar fawzan, ba komai yasa haka ba kuma sai sanin shi mutum ne mai sauƙi da yawan fara'a, akan jima baka ga damuwa a tare da shi ba, dan ko abu ya ɓata masa rai yakan shanye shi ta yanda da wahala a gane masa kai tsaye.
     AA da kansa ya buɗema Maanal mota ta shiga, sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da driver ya buɗe masa shima ya zauna. Yana gama zama ta kwanto jikinsa, kanta a kafaɗarsa ta lumshe idanunsa ɗan barci ne a cikinsu. Kallonta ya ɗanyi, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi ya riƙe. Ɗayan hannunsa kuma wayarsa yake dannawa yana son yay kiran RK.
     Tafiyar ƴan mintuna ta kawosu MAWAAD COMPANY. Sai Maanal taji tayi kewar wajen sosai. Yanda take kallon ko'ina yasa AA sakin ɗan murmushi. Ƙasa-ƙasa yace, “Kinyi kewarsa ne?”.
           “ALLAH sosai ma Besty”.
     Murmushi ya sake yi, sai kuma ya ɗan taɓe baki ya yunƙura ya fita dan har driver ya buɗe masa. Zagayawa yay ya buɗe ma Maanal, ya duƙo ya riƙo hannunta, ɗayan kuma ya ɗauka handbag ɗinta ya riƙe. Tuni masu shigowa suka tsaya kallon gulma, dan haka kawai suka tsargu da boss ɗin yau tare yake da amarya. Aiko sun gane ma idonsu abinda suke jiran, AA kam da baima san sunayi ba ƙoƙarin gyarama Maanal mayafinta yake yana kallon ta da murmushi, ita kuma tana masa magana a shagwaɓe dan yace mata yau a office ɗinsa zatai aiki ne, ita kuma tana cewa a'a bata yarda ba ita dai nata zata zauna sai tafi yin aiki da ƙyau. Uhhm babbar magana boss na murmushi available. Wannan shine taken gulma yau a Maawad.
     Lokacin da suke shigowa AS da shima ya iso yanzu suka haɗu a waje na biye dasu sai driver daya kwaso musu kayayyakinsu. Cike da farin ciki da girmamawa kowa kema Maanal barka da dawowa office. Itako tana amsawa kowa da kulawa da fara'a. Hakan kuma sai yayma kowa daɗi dan basuyi zaton haka ba. Jin tarihin alaƙarta da ogansu yasa suka fahimci hotonta ne a ko'ina na companyn, yanda aka ɓoye kamaninta ne yasa basu gane ba. Irinsu Zaharadeen kam kunya ce fal a cikinsu da jin shakkar haɗuwa da Maanal. Yayinda ƴammata masu ɓoyayyar manufa akan boss suke jin kishinta da shakkarta a wani gefen. Dan sun san dai lallai wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saboda muhimmancita ga boss mai girma ne ƙwarai da gaske da yanzu yake a bayyane gare su.
       Har cikin elevator hannunta na riƙe cikin nasa, amma kasancewar su AS a tare da su ya kama kansa kamar ba shi ba, itama Maanal ɗin a nutsenta take. Sai da suka fito ne ta saka masa rigimar ita dai office ɗinta zata. Dole ya haƙura ya yarda, amma sai taga ya nufi sama inda nashi yake na ƙarshe shi da AS. Zatai magana ya hanata, sai da suka iso taga AS ya buɗe office ɗin jikin na boss ɗin da ada yake kamar ma'ajiyar wasu muhimman abubuwa yasa Maanal a mamaki. Koda suka shiga sai tai tsaye tana kallon ikon ALLAH, sai kuma ta kalla AA ɗin dake kallonta yana murmushi.
       “Office ɗin waye?”.
   “Matar AA Darma mana. Kina tunanin zan barki ki cigaba da zama can ni ina nan? Sannan kema president ce kuma (Chairwoman) a wannan companyn, kina kuma da damar cigaba da kasancewarki a artist dan bazamuyi sakacin rasa gwarzuwarmu ba a wannan fanin. Barka da zuwa sabon office Bestyna”.
       Rasa ma abin cewa Maanal tayi, sai taji kawai ƙwalla ya cika mata idanu. A hankali ta shige jikin AA ta rungumesa tsama ta wani kalar sakar masa kuka. Shima slowly ya lumshe idanunsa tare da rungumeta yana ɗan murmushi. Saɗaf-saɗaf AS ya lallaɓa ya koma tare da ja musu ƙofar gulma da dariya fal cikinsa.
     AA cak ya ɗauka Maanal har zuwa office chair ɗinta dake sabuwa fil dan komai na office ɗin sabone irin na office ɗinsa, wancan kuma office ɗin Yaqub aka maida ciki a madadinta. Zama yay a kujerar ya sakata a cinyarsa. Sai da ya ɗiba tissue dake a saman desk ɗin ya share mata hawayen sannan cike da lallashi da soyayya ya ce, “Babyn Oum kwana biyun nan shagwaɓa kike jin yimin da yawa. Komai kuka kina son zama rigimammiya. Minene abin kuka anan, companyn ki ne fa, ko office ɗina kikace na fito na baki ba da gudu zan fito ina faɗin, “An gama Madam ba”.
    Dariya yanda yay ya bata, sai ta saki murmushi da ɗan ja masa hanci ta ce, “Daka zama mijin tace”..
     Murmushi yayi mai ƙyatarwa, tare da sumbatar lips ɗinta ya ce, “Aini mijin kafin tace ne ma. Idan kuma da abinda yafi ma hakan to gaskiya duk ni ne Besty”.
         Dariya sosai yanzun kam Maanal keyi, shima yana tayata da murmushi. Zata fara masa godiya ya rufe mata baki da nashi. Bata hanashi ba, sai da ta tabbatar ta nuna godiyar tata a haka sannan. Ya rungumeta shima yana sanya mata albarka. Jin yanayinsa na ɗaukar sabon salo cike da wayo ya zame jikinsa ya bar office ɗin zuwa nashi shima. Ita ko ya barta da farin ciki tana faman zagaye office ɗin da kallo komai. Daga ƙarshe tai kiran Ammie a waya tana sanar mata. Ita kanta Ammie sai da taji ƙwalla ya taru mata a ido, dan a rayuwa takan ji matsannacin farin ciki idan taji Maanal a farin ciki. Kodan yarinyar ta wahalu a shekarun baya ne fiye da sauran oho. Bayan ta katse kiran su Didi ta kira suma ta gumtsa musu. Suma suka tayata farin ciki sosai....
       Aikin dake a companyn sosai yasa babu zama, kowa aiki yake tuƙuru a tsakanin nan. Ita kanta Maanal yau gaba ɗaya bata huta ba. Sun shiga meeting har sau kusan huɗu kafin break. Sun fito na ƙarshe ne lokacin salla yayi, AA yaja ra'ayinta suka je office ɗinsa sukai alwala. Sannan suka fito zuwa yin salla. Ana idarwa suka dawo, a hanya ne suka haɗu da CFO. Sai tai saurin ɗauke kai kamar bata gansu ba. Murmushi Maanal tayi a ranta tace (ƙyaji da shi dai) a fili kam yitai kamar bata ganta ba. Dan taga dama wani ɗacin rai da take a wajen meeting. Shi kam AA baima ɗauka abinda CFO ɗin keyi a komai ba. Dan yanda ta iya takunta yasa bai wani fahimci take-takenta ba har yanzu. A office ɗinsa sukai zaman cin abincin data shiryo musu sukazo da shi. Suna nishaɗinsu da soyayyarsu. Bayan sun kammala Maanal ɗin ya haɗe komai waje guda ta koma nata office ɗin. Bata wani jima da zama ba suka sake fita yin meeting, sai dai yanzu babu AA yana ganawa da baƙi, AS ne ya zauna a madadinsa. Meeting ɗin ya jasu lokaci mai tsayi kafin su fito. Dan lokacin ma la'asar tayi........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖9️⃣9️⃣


______________

🥱🥱 Nace ba, na fara saida GUMAMA ta yara data manya mai so yayi magana kafin ta ƙare. Dan na sakata a farashi mai RAHUSA da ARHA, karku damu tana ƙamshi yanda ya kamata😆🤌.



Hhhhh Haba hajjaju ya da fara maida murtanin faɗa bayan WASAN bama a farashi ba. Banning number Bilyn Abdull tamkar an kashe MACIJI ne ba'a sare kansa ba wlhy😂. Dan ko mutuwa Bilyn Abdull tai in sha ALLAHU ina ji a raina zan cigaba da zama a zukatan masoyana zasuna min addu'ar kwanciya lafiya a kabari. Karki kuskura kice zakiyi wannan wasan, dan wlhy mamaki zan baki keda ƴan jagaliyar taki. Ke reporting kika sa akayi a WhatsApp ni kuma dare zan raba ina reporting naki ga babban sarki. Kinga maimakon Banning a WhatsApp ke a media ɗin gaba ɗaya ma UBANGIJINA zai yi banning ɗinki, (Wayaga ruwa zai ƙarema ɗan kada, dama kuma da ruwan muka dogara😜😆🤭).

Wannan Bilkisun da kike ganinta ba ƙyalan bace ƙyalle ce, kawai kafin mu sara ne mu sai mun dubi bakin gatari ALLAH wlhy. Ina ƙara baki shawara karki ce zaki saka Game dani akwai damuwa, ubana har ya rasu albarka yake zuba min, uwata kullum sai tace ALLAH yay miki albarka Bilkisu dan dattijuwar ƙwarai ta kullum goshinta na bisa ƙasa tanama UBANGIJI Sujuda. Mijina kam ai duk motsinsa sai ya ce Bilyn Abdull ALLAH yasa ki gama da duniya lafiya, yo an gaya miki a banza nake ɗaɗara shi a littafin🤪, gata yake bani iya gata, tsaro iya tsaro, naci shinkafa na kora da ruwan fanfo ga windows ɗin gidana iska tako ina ko ba'a bamu wutar nepa ba bana damuwa. Idan zai fita yanda nake masa addu'a haka yake min shima kaga shalelen Bilyn sa ALLAH yasa muna jone har a aljanna🤏🥰.

To Ladidi banda kankamba😲 ke wacece da kike tunanin zaki nuna min yatsa ban karya shi ba🤣 ina da waɗan nan ƙafofin murhun uku na haye kansu na zauna matsayin tukunya na dafa duk kalar ruwan dana gadama TSAYAWAR ALLAH kenan. To gaskiya ina baki shawara, kawai dai ki daurewa zuciyarki abar kaza cikin gashinta, dan in akace figeta za'ayi wallahi jikinta zai koma ne kamar na BALBELA. Shegen tsuntsu kenan ƙyau iya ƙyau a waje ciki kam ba'a cewa komai. WAJENJI FARI CIKINKI BAƘI KENAN😂.



Nifa a duniya cakwakiya na birgeni kwarai-kwarai da gaske kun ganni nan, ALLAH birgeni take😆, idan akai wasa ana gama AJIYA A DUHU zan saki sabon Update na zazzafan littafi mai suna Ladidi a harhaɗa🤣, alƙalami ɗan albarka, kun san yafi takobi kaifi, balle na Bilyn Abdull har ƴan a leƙa katanga zanowa yake, gashi baya yafiya dalla-dalla yake cika aikinsa🤫.

Bari dai nayi shiru, tsiyar Mamy ma ta ishi al'ummata, ita kuma Sille ya isheta😂, wayaga AJIYA A DUHU.

Kai idan akace ƴar baka za'ai na rantse akku zan koma muku ALLAH dai ya ƙyauta ba shekarar zazzaga bace ta kama😆, dan wata tabarmar idan aka zazzageta babu mai sake ɗora ɗuwawunsa akai saboda ƙazantar da aka zubar a bisanta.

Kudai kuyita salati ƴan uwa karna zare a maimakon labarin na koma muku tatsuniyar gizo-gizo. Dan labarin ƙoƙi dai baya wuce na gizon Update iya Update 😎.


🤔To Kuma su Haƙilah a dai kiyaye dan mun jima da sanin suna kuma mun san numbers, yanzu komai mai sauƙi ne a buga maka sallama a ƙofar gida daga ƴar jagaliyar media ki jawa kanki ai miki tonon leƙa katanga a gaban Rijalu da matan anguwa, ya barki a gida da tunanin ya killaceki ƙarƙashin igiya uku a kira shi ace kina ofishin ƴan doka. Banu taci ƴan a ara a yafa kenan, bamu san tushe ba amma muna rawar takaɗiɗi akan nera biyar-biyar😂. Tab ɗin wayaga goge hadda, kajawa kanka daga karanta HIKAYIYIN su Bilyn Abdull a tuɓale ƴar igiyar auren😮‍💨 dama lamarin rijalu yanzu ana basu wuta a sama suna bama Nisa'u a cikin gida, yana ƙaraki gaba wlhy galleliya zai santalo, idan dama kuma kina da abokiyar burmi a cikin gidan shike nan ya samu filin shakatawa, yo kunga laifinsa ne, koni na auri mace ta zama ƴar ARE-ARE (Gayyar SHANU) a media walle na kamata zanen yarbawa zan mata a uwawu😌 kafin na saita miki hanya zuwa gidan tsoho.🥳

To kama kanki wannan kokawar ta GIWAYE ce, ke kunama daga neman suna ko na gwajin harbi karki jama kanki ƙafa ta takeki batare da ansan da ke a cikin ƘURAR YAƘIN ba. Idan kunne yaji jiki ya tsira. 👉🙆👈

Dan

145 / 213

Chapters