Author : Bilyn Abdull Category : Romance
Abah ta saka kowa nutsuwa a zahiri. A bayan fage kam Mamy da Saheeba a birkice suke. Dan tunda ta koma sashenta bedroom ta shige ta kulle kanta. Bala'i ne fal a cikinta, sai dai shakkar sakamakon yinsa ya hanata fitarwa. Fin minti talatin ta gama yanke shawarar zuwa yau dai ga Abah, amma kafin haka zata fara da Fadeel ne.
Babban Yaya na tsaye a compound shi da AA da Fawzan suna magana kiran Mamy ya shigo masa. Koda yaga itace bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga. Sai dai tunda ya ambaci sunanta AA da Fawzan suka maida hankalinsu kansa sosai. Koda ya sauke wayar daga kunnensa dan umarnin zuwa kawai ta bashi ta yanke baice ma ƙannen nasa komai ba sai “Ina zuwa”.
Da kallo duk suka bishi, sai kuma Fawzan ya kalla AA. “Da alama shima Babban Yaya Mamy bata son ƙara auren nan nashi”.
Murmushin basarwa AA yayi, tare da faɗin, “Kai ko Yaya taya zata so ama ƴarta kishiya”.
“Amma tana son aima ƴar wasu tunda tana son kai ka auri Nuratu. Ni nayi mamaki ma yau da bata kawo batun Nuratun ba”.
“Maybe tayi shirun ne dan na Babban Yaya ya bata mamaki, tunda koda alama shi ba taɓa nunawa yay zai ƙara ba. Lokaci guda abin ya taso”.
“Hakane kuma”.
★Babban Yaya yakai zaune yana kallon Mamy da mamakin ganin yanda ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin kasa iya shanyewa ya ce, “Mamy lafiya kuwa?”.
Bata amsa masa ba, sai ma tambaya ta jeho masa a fusace. “Fadeel wace yarinya ce zaka aura?”
Kai tsaye babu wani kwana-kwana ya ce, “Ameerah ce”.
“Ameerah! Wacece hakan?”.
Ɗan jimm yay na mamaki, sai kuma ya ce, “Wai Mamy lafiya kuwa?”.
“Tambayarka nai wacce?”.
Sai da ya furzar da iska sannan yace, “Ƙanwar Ameer nan makwaftanmu ƴar Momy Shuwa”.
“To baka isa ba! Ba kuma zai yiwu ba!”.
Murmushi ya saki a karo na farko. Cikin girgiza kai ya ce, “Mamy dan mi bazai yiwu ba? Saboda Saheeba kike tunani ko ƴan uwanki. Mamy bazan ɓoye miki ba na gaji da halin Saheeba. Na miki iya biyya akan zama da yarinyar nan mara tarbiyya, nayi haƙuri nayi kawaici, sai dai anzo gaɓar da komai zai iya faruwa. Dan zaɓi biyu ne. Kodai ta zauna da wadda zan auro, ko kuma na saita mata hanya. Amma bazan iya haƙurin ƙin ƙara aure ba. To mima ya rage iyaye har sun shiga hatta sadaki an bada. Mamy farin cikin Saheeba yafi nawa muhimmanci ne a wajenki? Nayi haƙuri na rasa Shahidah, ALLAH ne shaida kuma har gobe ina son yarinyar nan, na auri Saheeba, tsahon shekaru bana jin daɗin zama da ita, ban taɓa zuwa na miki ƙorafi ba duk wani banzan halinta na shanye ma cikina. Yanzu kuma naga wadda zata bani salama da kwanciyar hankali saboda kar ran wata banza Saheeba ya ɓaci sai na haƙura Mamy. Oum ta bani goyon baya, Abah ya bani goyon baya, miyyasa ke bazaki bani ba? Dan tana ɗiyar ƴar uwarki?. Gaskiya kimin afuwa babu abinda zai hanani auren nan sai dai idan na mutu ne kafin kwanakin”.
Daga haka yay shiru ransa a matuƙar ɓace. Ai mutuwar tsaye Mamy tai tana kallonsa. To ashe gwara-gwara Fawzan ma. Tana ganin AA yafi Fawzan, to ashe Fawzan ma mai biyayya ne. Dan gaba ɗaya ma Fadeel yau ya juye mata ne kamar Abah. Wlhy saima taji ta rasa abinda zatace masa. Sai wani irin tsuma da jikinta ke mata. Zuciyarta kam zafi take mata, gashi tai nauyi a cikin ƙirjinta...
Dai-dai nan Saheeba ta shigo tana sharar hawaye. Ganin Babban Yaya zaune sai ta tsaya tana kallonsa kukan na sake kufce mata. Ƙasa takai durƙushe, tana ƙara fashewa da kuka ta ce, “Dan ALLAH na tuba Daddyn Naufal, dan ALLAH kada kamin kishiya, wlhy na rantse maka zan canja, duk abinda kake ganin inayi baka so zan daina shi. Dama bayin kaina bane Mamy da Mama ke sakani yinsu. Amma wlhy bazan sake biye musu ba....”
Da wani irin sauri Mamy ta kalla Saheeba, har taune harshe take wajen faɗin, “Saheeba! Wace banzar magana ce wannan. Nice ma zan sakaki ki masa halin rashin arziƙi?”.
Babu ko ɗar Saheeba ta ce, “Wlhy kece Mamy, ke da Mama kune ke tsara komai kuce nayi saboda na ƙwato muku shi daga hannun O......”
Ai wani irin tassss!!! Kake jin Mamy ta saukewa Saheeba mari. Zata ƙara magana ta sake ɗauketa da wani marin na biyu. Sannan ta ce, “Wawuya kawai, kin haukace ne? Kodan mijinki zai aure sai hankalinki yabar jikinki har ki kasa tauna maganar dake fitowa daga bakinki. To idan kin manta bara na tuna miki nice na haifi Fadeel har kika aura shashasha”.
Tsam Babban Yaya da mamaki ya kashe ya miƙe. Raɓasu yay ya fice abinsa zuciyarsa na matuƙar jinjina al'amarin Mamyn da Saheeba. Mizai saka Mamyn harzuƙa haka dan Saheeba tace sune suke sakata yin abu. Sannan a ina za'a ƙwatoshi kuma? To shi koma dai minene su suka sani, aure dai kam in sha ALLAHU babu fashi sai yayi. Ita kuma ya rage nata ta gyara ko ta cigaba da yin abinda tai niyya shima zai fara yin wanda yay niyya kuwa. Dan yanzu ya ɗauki ɗammarar saitata a layi. Abinda ya ɗauka a baya ko kwatarsa bazai ɗauka a yanzu ba daga garetan............✍️
😂😂Hajiya Mamy yada haka kuma. Marin surukai fa baida ƙyau gaskiya🤣.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣1️⃣
______________
.....A wannan dare dai Mamy bata iya ta tunkari Abah ba, dan Babban Yaya da Saheeba sun fusata ta. Sai washe gari da safe suna shigowa daga massallaci tai dakonsa. Dan suna fita dama ta fito a nata sashen sai ga Oum ta fita daga sashen Abah ɗin dan dama ita haka take yi. Sai kawai tai wuff ta shige ita bayan ta gama zagin Oum da tsine mata a zuciya. Anan falon Aban tai sallar asuba. Ta cigaba da zaman tsammanin dawowarsa har suka shigo.
Koda Abah ya shigo ya ganta ɗauke kansa yay tamkar bai gantan ba. Sai taji gaba ɗaya ta sake rikicewa. Amma haka ta daure tace masa ina kwana. Idan bangon ɗakin ta tanka shima ya tanka. Jikinta na ƴar tsuma ta tari gabansa, muryarta na rawa tana kallonsa da idannunta da suka kaɗe ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka saurareni ko sau ɗaya ne. Wlhy-wlhy ba abinda kake tunani bane ranar zan gaya maka gaskiyar komai, Fadeel ne......”
“Kinji nace miki ina buƙatar sanin miya faru ne?”. Abah ya katseta babu alamar hayaniya a muryarsa.
“Kayi haƙuri dan girman ALLAH. Zan maka bayani koda bakace kana buƙatar ji ba ko hakan zai sa ka sassauta min. Wlhy a duniyar nan fushinka shine mafi ƙololuwar tashin hankalina fiye da komai kaima ka sani”.
“Ni a suwa da fushina zai zama ƙololuwar tashin hankalinki Kamila. Idan ma shi ɗinne kwantar da hankalinki baki da matsala dani. Duk abinda kike tunanin dai-dai ne ƙofa a buɗe take kiyi abinki.” ya ƙare maganar da raɓata zai wuce. Da sauri ta riƙo hannunsa tana fashewa da kuka. Fisgewa yay ƙoƙarin yi ta riƙesa da hannu biyu duka da iya ƙarfinta kuma.
“Amma kin san zan iya marinki ko?”.
“Gara ka marenin, wlhy gara ka mareni da wannan fushin dai da kake yi dani. Ka tausaya min dan ALLAH ka duba min, wlhy ji nake kamar zuciyata zata tarwatse.” kuka mai ƙarfi ya sarƙeta. Shiru kawai Abah yay yana kallonta. Kamar wanda ya fahimceta sai kawai jitai ya zare hannunsa yay gaba. Sai da yaje zai shiga bedroom a kausashe ya ce, “Ki gayama ƴan uwanki akan wannan bikin wlhy-wlhy duk wanda ya nema ɗaga hankalin iyalina nima sai na ɗaga nashi. Ba kuma lallai dole bane sai ƴaƴana sun zauna da ƴaƴansu. Hanawa su ɗauki wani mataki akan yaran adalcina ne, amma a wannan gaɓar duk wadda tace zata kawo musu shirme zan basu damarsu ta ɗaukar matakin da duk sukai niyya dan ina son farin cikinsu. Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu. Idan kunne yaji jiki ya tsira”.
Yay shigewarsa. (Dan ko kece kika ce zaki ɗaga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu) Wannan kalma tai matuƙar dukan zuciyar Mamy da girgiza mata duniyarta. Ta kuma fahimci eh lallai da gasken gaske Abah yake yi. Itako ta shiga uku, shin mike faruwa ne? Anya kuwa? Anya ganin da Abah yay musu sun fito a sashen Ajwaad ne kawai matsalar kuwa? Kai da mamaki gaskiya, akwai lauje cikin naɗi. Dole akwai wani abinda ke a ƙasa. Batun Ajwaad da Maanal ya faɗo mata a rai. To kodai binciken da take tunanin zasu iya yi suka yin ne?. To amma ta ina? Inma zasu bincika ai Doctor ne kwai, jiya jiyan nan kuma Hajiya Turai ke sanar mata a binciken da tai Dr Tofa ma baya Nigeria kusan shekara biyar kenan. To kodai munafukar matar can ce tai mata wani ƙullin?. Zuciyarta tafi tsayawa a hakan, sai dai hujjar ta mata rauni da yawa. Amma ko akan batun auren nan ta tabbata akwai saka hannun Fateema. Kenan dai Fateema ta cita wasa. Ajwaad ya auri ƴar ƙawarta, Fawzan ƴar ƙanwarta, ga Fadeel ma zai auri ƴar ƙawarta. Shike nan yaƙinta na shekaru ya tashi a banza. Tunda ga Saheeba nata auren na rawa, Nibras ma bata sakata a sahun mata ko wanda take amfana. Auren Nuratu na tangal-tangal. Tana a ruwa fa kenan har yana shirin zuwa mata wuya idan bata tashi tsaye ba. Ga wancan batun duk da tana ƙoƙarin hidden ɗinsa yana nan daram a ranta, yana kuma cimata zuciya.....
________★
Anan ɓangaren Oum kam shirye-shiryen biki suke hankali kwance. AA ya riga yay order ɗin kayan lefen Fawzan tuni, yanzu kuma gana babban Yaya. Duk da zai iya yin hakan shima saboda kawai yaje ya ɗan huta da tashi amaryar sai suka tsiri tafiya Dubai wai haɗo lefe shi da RK da Maanal da Nuwaira. Sarai Oum ta fahimcesu, dan haka batace komai ba face binsu da addu'a. Shima Abah koda suka faɗa masa addu'ar yayi. Dan daga shi har Oum ɗin ƴan ba ruwa na ne.
Haka kuwa suka shirya suka tafi, suka bar su Oum kuma anan Nigeria suna shirin fara gyara amare ita da Hajiya Shuwa. Sai dai ita Najma ma can wajen Ammie zata zauna nata gyaran. (Kun san dai itama Ammie tsohuwar mai gyaran jiki ce) Dan haka Hajiya Shuwa data haɗa duk abinda ake buƙata aka aikama Ammien, itama kuma daga can Ammien ta aiko musu da tata basirar da za'ama Ameerah da Maimoon da itama ta dawo nan Abujan amma a sashen Oum zata zauna dan ba'ayi abin kunya suruka Hajiya Shuwa tayi gyara ba..
Babban Yaya da Yaya Fawzan kuma sai suka maida hankali a gyaran sassan nasu. Amaren zasu zauna a downstairs kafin a gama musu nasu ginin. Amma duk da haka sai da aka gyara duka sashen biyu. Hakan yasa Nibras komawa sashen Oum da zama. Saheeba dama har yanzu tana a sashen Mamy. Duk da dai sunata zuba rikici ita da Mamyn, dan kota sakata abu yanzu batayi. Mamanta da itama ta tadama Mamy hankali tace Saheeba ta taho gida amma Saheeban tace babu inda zataje, dan Babban Yaya ya rantse mata indai ta fita a gidan ta fita kenan na har abada.
Hajiya Turai ce da ƙyar ta sasanta Mamy da Maman Saheeban. Ta kuma nuna musu illar bari kan nasu ya rabu. Acewarta a yanzu ne ma ya kamata kansu ya haɗu suyi yaƙi na gaske dan abaya wasan yara sukayi. Fargarwar tata ta shigesu, dan haka suka sasanta ɗin itama Saheeban mamanta ta ƙwaɓeta. Ita kuma ta bazama gidan bokaye da malamai neman sa'a...
_______★
Rayuwa a Dubai ta sati ɗaya kacal rayuwa ce mai tsayawa a zuciya da ɓargon jiki tsakanin Maanal da AA. Hakama Nuwaira da RK ba'a barsu a baya ba. Ƙara'in amarci akai sosai mai kuma ƙayatarwa. Sunyi wani fresh abinsu musamman Maanal data fara shiga wani yanayi na biyema fitinar AA. Shi kanshi har mamaki abin ya fara bashi. Tana shan wahalar amma tana nane da shi yanzu ba kamar da ba. Takai wani lokacin ma ita da kanta take takaloshi koda zatai masa rakin daga baya. Ranar dai suna hira shi da RK Maanal da Nuwaira kuwa sun fita kasuwa dan yau su AA ɗin sunce sun gaji sukam, sai AA ke ɗan yima RK tambaya akan hakan. Murmushi RK yayi dan shikam tun a Nigeria ya fahimci Maanal nada shigar ciki. Amma rashin tabbas ya sashi yin shiru tunda mata nada abubuwan ban mamaki a tattare da su.
Cikin nuna rashin tabbas RK ya ce, “Ciki zai iya saka mace hakan, dan wani lokacin idan suna da ƙaramin ciki sukan buƙacemu a kusa da su fiye da ko yaushe. Dan a farkon aure gaskiya mune zaka samu muna zalamarsu amma su ba sa jin daɗin yanayin gaba ɗaya wahala tafi yawa. Shiyyasa sukafi son a tsaya iya romancing kawai. Wata macen zata iya maka haihuwa uku sannan ta fara sanin muhimmancin yanayin. Wata ɗaya, wata biyu wata ma har biyar. Idan kuma ba'a haihu da wuri ba zakaga an ɗauki shekaru, bawai basa so bane gaba ɗaya, a'a badai kamar mu ba, doke zaka ga dai sai sunja shekarun nan sannan komai me daidaita musu. Sai dai idan suna shan ƙwayoyin saka ƙarfin sha'awa ne ko wannan kayan nasu na mata”
Cikin gamsuwa AA yake jinjina kansa. A ƙasan zuciyarsa kuwa wani irin farin ciki yake ji da fatan ALLAH ya tabbatar da hasashen RK ɗin na batun cikin ne bawai shan maganin Maanal keyi ba duk da dai bai taɓa gani ba. RK da duk ke lure da shi ya ce, “To amma fa kaima sai ka ɗan sassauta a irin wannan yanayin. Dan in har hasashenmu ya zama gaskiya cikin ne ALLAH zaka iya ɓaro shi. Ka aikata hakan kuma ba yafe maka zamuyi ba”.
Harararsa AA yayi, sai kuma ya ɗauke kai gefe da faɗin, “Shiyyasa bazan taɓa Kawu da kai ba dan kawun banza ne anan”.
Dariya RK ya shiga yi. Dole AA ɗin ya tayashi da murmushi.
★ Satinsu ɗaya suka dawo Nigeria, a kallo ɗaya kuma Oum ta tabbatar da hasashenta akan Maanal. Dan komai na jikinta ya ƙara canjawa a sati ɗayan nan. Sai wani mahaukacin ƙyau takeyi da haske. Sai murmushi ya kasa barin fuskar Oum, duk motsinta addu'a take na ALLAH ya tabbatar da hakan. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta bata gumtsawa Abah ba........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣2️⃣
______________
....Washe garin da suka dawo wasu cikin ƴan Kano suka iso Abuja. Dan za'a kai lefen Najma Zaria. Koda Maanal ta nuna zataje AA yace bai yarda ba. Dan tunda RK ya masa kanta farga yake wani kaffa-kaffa da al'amarin Maanal ɗin duk da ba tabbas. Koyaya yaga zatai wani aikin da zai jijjiga mata jiki yanzu zai amshe gara shi yayi. Tunma yana yi a su kaɗai harya kasa daurewa bai iya kawaicin hakan ko a gaban Oum. Ita ko Oum babu ruwanta, irin wannan abubuwan kawaicema yaran nata take tayi kamar bata gani ba. Dan farin ciki hakan ke bata akan kulawar da suke bama matan nasu.
Kamar wasa rigima ta kacame akan zuwa Zaria. Dan AA ya dage kuma ya ɓata rai a yanda Maanal ɗin bata taɓa gani ba. Ita kuma ta rigime akan sai taje sai masifa take masa kamar dama jiranshi take yi. Kuma tana masifar tana kuka. Takaici ya sashi yinƙurin baro mata sashen gaba ɗaya. Amma sai ta biyoshi yana gab da fita ta riƙeshi wai wlhy bazai fita ba.
Tsayawa yay yana kallonta, fuskarsa babu alamar wasa ya ce, “Sakeni”.
“Anƙi ɗin”.
Ya faɗa a fusace. Sai ma ya rasa mi kuma zai yi. Dan kallon ma abin yake a matsayin rainashi ta farayi ne ko mi bai san yazai fassara ba. A wani kuma gefe na zuciyarsa yana ƙara yarda lallai mata zuma ne ga zaƙi ga harbi. Duk yanda kake da su idan suka kuma maka wani takaicin sai kaga kamar basu taɓa ma saninka ba. Wannan yanayin dakan gitta lokaci zuwa lokaci shine iyaye kullum ke tisa mana kalmar haƙuri a kansa, sai anyi haƙuri da mata sai anyi haƙuri da mata. Idan ka fusata ka zafafa su kuma matan su kalleka a matsayin namiji ba ɗan goyo ba. Jiba fa ƴar ficiciyar yarinyar nan daya raina da hannunsa ce yau take neman birkita masa lissafi gaba ɗaya. Ƙiri da muzu yace baza'ai abu ba tace sai tayi. Yayi yunƙurin bar mata gidan yaje ya