Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ɗaya suke shiryawa komai girman faɗansu.
Kira Maanal ta fara jerama AA ba ƙaƙƙautawa cike da haushi, sai dai har kusan 10 mis... Bai ɗaga ba. Aiko tazo wuya sosai ta jefar da wayar saman gado ta fita a ɗakin. Sai kuma fitowar tata yay dai-dai da shigowar Ameerah. Cak Manaal ta tsaya tana kallon ta, sai kuma ta wani tuntsure da dariya tana kaiwa zaune cikin kujera. Hararrar ta Ameerah tayi itama tana zama, sai kuma ta ɗauka pillow ta jefa mata.
Cafewa Maanal tai da faɗin, “Ikon ALLAH ya da tsarguwa haka Matar Yaya”.
“Aa kakar matar yaya. Ji wani sunan tsoffi. To wlhy Aunty zaki dinga cewa. Aunty Najma Aunty Ameerah”.
“A ai ba damuwa zan faɗa, ai kallo ɗaya na tabbatar da kin zama matar yayana yau kwarai-kwarai da gaske. Inye kaga amaryar babban Yaya. Tabb irin wannan ƙyallin amarci haka, ALLAH dai ya sa ƙanina ko ƙanwa sun kwanta luff abinsu a inda ya dace”.
Ameerah dake riƙe baki ta ce, “Na shiga tara, wai dama haka kike da baki Maanal. Wlhy da nake ganinki shiru-shiru abinki miskila tsaff nazata wata salihar baiwa ce. Ashe-ashe kema ƙyalan ce ba ƙyalle ba. Koda yake Yaya AA ba wasa ba. Babban karatu yay miki na yarda”.
Maanal zata maida mata murtani Oum ta hawo, muƙuy ta haɗiye. Ameerah tai ƴar dariyar mugunta tana tashi ta amshi kayan hannun Oum. Oum dake kallonta cike da murmushi ta ce, “Daughter ai ni yau har zan tafi biko, kona tura Baby”.
Cikin jin kunya Ameerah data koma ta zauna kusa da Maanal ta ɓoye fuskarta a kafaɗarta tana murmushi. Dariya Maanal tayi, da faɗin, “Ai Oum bake kaɗai ba. Nifa nama zata ita da Babban Yaya sun wuce honeymoon ne”.
Mintsini mai zafi Ameerah tai mata. Ai ko Maanal ta ce, “Wayyo Oum zata illata miki ni”.
Dariya Ameerah da Oum suka sanya. Ameerah tace, “Masheranciya. Oum ALLAH ban san Aunty Maanal na magana haka ba fa.”
Oum ta ce, “Ameerah ai kura tayi lafiya ne kawai. Baby kuma ai gidan rikici ce daga ita har Auta. Kawai dai girma yazo ne ko Baby na”.
Hannu biyu Maanal ta saka ta rufe fuska tana murmushi. Aiko Ameerah taita dariya. A tare suka ci abinci su uku, bayan sun gama neman layin Najma a kashe. Ameerah da Maanal suka kalla juna cike da iya shege. Irin like Najma ana can ana shan bidirin nan. Sai kuma sukai murmushi. Oum dai bata san sunayi ba ma. Hankalinta na kan abincin ta. Can sai ga Babban Yaya ya shigo, kallo ɗaya Maanal tai masa tai dariya a zuciyarta cike da gulma. A fili kam sai ta shiga gaidashi cike da girmamawa. Da kulawa ya amsa mata shima yana tambayarta yaya jiki.
Ta ce, “Yaya lafiya lau fa nake. Kawai ƙamshim naman nan ne bana so ALLAH”.
“Ayya Lillyna sorry kinji, nama kam ai ba za'a sake kawoshi gidan nan ba ma okay”.
Cike da farin ciki Maanal ta ce, “Yess Yayana. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana”.
Oum dake murmushi ta amsa da Amin, Ameerah ma haka, har cikin ranta kuma rayuwarsu na birgeta, dan wlhy idan baka sani ba bazaka taɓa yarda ba'a gidan aka haifi Maanal ba. Soyayya suke mata irin ta ƙanwa da yayi su duka ukun. Dan a kwana biyu kawai da tayi da Babban Yaya ta fahimci hakan, yanda Ajwaad yake zuciyar gidan haka ma Maanal take. Ita kanta kuma Maanal ɗin birgeta take yi. Kusa da Oum Babban Yaya ya zauna. Cike da kulawa ya ce, “Oum gaskiya nayi missing ɗin cin abinci tare dake”.
Murmushi Oum tayi, tare da ɗibar abincin ta kai bakinsa, babu musu kuwa ya buɗe ta zuba masa. Suna haɗa ido da Ameerah data saki baki tana kallon ikon ALLAH ya kashe mata ido ɗaya. Maanal kuwa fuska ta shagwaɓe. Ta ce, “Amma Oum idan ta gaskiya za'abi nima yaushe rabon da ki bani abinci, amma yanzu babban yaya fa, a gabana fa....”
Babban Yaya ya ce, “Yanzu nan Lilly yau nine ma na zama rival naki”.
Cikin sake shagwaɓe fuska ta ce, “Yaya kaifa ka girma.”
“Aa, a gaban Oum dai ban girma ba, ai ɗa baya girma a gaban iyaye ko Oumna”.
Oum ta ce, “Sosai kuwa, har yanzu ganinku nake ƴan yara, Baby kuwa kamar ma na cigaba da goya kayana. Kinga ƙyale babban Yaya zo na baki abinci, Ameerah kema matso”. Cike da farin ciki kuwa suka matsa kusa da Oum, ta dinga ɗiba tana sakama kowa a baki har Babban Yayan........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣0️⃣
______________
.........“Abba J. Mabera shine sunansa da na sani gaskiya, kuma duk ma wanda ya sanshi anan dai cikin Kaduna da hakan ya sanshi. Ban san asalinshi ba, dan babu abinda zan iya faɗa maka akan tushensa. Na sanshi ne a dalilin ubangidana Alhaji Bello kangiwa. (Mahaifin matata, mahaifiyar Yazeed kenan). Shine ya haɗani da shi shekaru kusan ashirin da uku da suka wuce akan na koya masa harkar kasuwanci. Na amsheshi da hannu bibbiyu kuma ina ɗorashi akan dukkan abinda ya dace. Sai dai yanayin dana fahimci rayuwarsa take sai na kasa sakin jiki da shi. Yana da son kansa gaskiya, dan yayi min ɓarna a shagona sosai a lokacin, har takai duk yanda nake kawaici na kasa sai da na tunkari Baba da al'amarinsa. Baba ya kira shi yay masa faɗa sosai a gabana. Bayan wannan faɗa sai ya gyara, ya daina ɗibar kuɗin shago har sai idan nine na bashi hakkinsa. Wannan canjawar tashi tasa baba ɗaukar auren ƙanwar matata ya bashi, wato Sabuwa kenan mahaifiyar ita wannan yarinya Nazeefa. Sannan kuma ya bashi jari mai tsoka harda muhallin zama. Sai dai ya nuna bazai zauna a Kaduna ba Kano zai zauna. Baba mutum ne mai sauƙin kai, dan da kake ganin yaransa ɗin nan babu wanda ya gado halinsa na ƙwari a cikinsu sai mutum biyu. Bai musa masa ba ya sama masa gidan haya a Kano aka kai amarya... Komawarsu Kano yasa ban ƙara jinsa ba ban ƙara jin labarinsa ba mai muhimmanci dai sai abinda ba'a rasa ba a wajen matata saboda ƙanwarta da suke tare har suka rabu da ita sabuwar bayan aurensu da shekara huɗu ta dawo nan Kaduna. Ta kai kusan shekara biyu basa tare sai kuma gashi ya dawo an sake maida aurensu, daga nan ne ya ajiyeta anan Kaduna. A dawowar tasa kuma ya dawo da kuɗi masu yawa gaskiya. Babu mai cemaka ga taka maimai sana'ar Abba Mabera ko'a yanzu, dan mutum ne ɗan buga-buga, yana kuma jikin ƴan siyasa sosai ta ƙarƙashin ƙasa.”
Cikin gamsuwa AA ke jinjina kai. Kafin ya sauke numfashi kaɗan. Sai kuma ya ce, “Daddy akwai wani abun da nake tunani gaskiya, kuma akan mutumin nan, bance bana zargin matarsa ba, dan bazamu sakankance ba, amma koda ace itace dole akwai hannunsa a ciki.....”
“Hannunsa fa Ajwaad?”.
“Tabbas Daddy, dan naga abubuwa da yawa a cikin idanun mutumin nan. Da ganinsa kaga hatsabibin mutum. Idan har ba damuwa zan so ganawa da shi Baba dan dole muna son sanin ainahin wanene shi. Akwai wani abu dake ban mamaki, amma ban sani ba ko bayan ita surukar taka yana da wata matar?”.
“To gaskiya ban san shi da wata mata ba, ko sanda na zauna da shi yace min saurayi ne ko auren fari baiyi ba, duk da kuwa zai iya kai talatin da uku zuwa da huɗu a lokacin. Amma tabbas Sabuwa ce itace matarsa ta farko. Bakuma na jin ko sanda suka rabu yayi wani auren har suka maida auren nasu. Amma minene ke baka mamakin?”.
Kai tsaye AA ya ɗauka wayarsa ya danno hoton Sille ya miƙama Daddy. Daddy ya kalla hoton, ya ɗago ya kalli AA. Kai AA ya jinjina masa, Daddy da mamaki ya kume ya ce, “Ajwaad wannan kuma fa? Ai yana kama sosai da Mabera. A ina ka sanshi? Wanene shi?”.
“Ban sanshi ba Daddy, ganinsa kawai na taɓa yi sau uku. Gani biyu kuma duk a ƙofar gidanmu ne, ban san kuma dawa yake da alaƙa ba a gidanmu. Daga haka ban san komai a kansa ba. Amma zuciyata na sake tabbatar min nasan wannan fuskar, sai dai ganin shi wannan Mabera ɗin a yanzu ya sake raba min hankali. Shi na taɓa sani? Ko kuwa shi wannan da nake gani a Abuja na taɓa sani?”.
“Tirƙashi, eh lallai dole ka shiga mamaki. Kuma dole kam kaso sanin wanene Mabera. Ina ga kai dake da tafiya ya kamata muje muga Baban kar kuyi dare.”
“Okay Daddy, amma wani tunani ne ma yazo min yanzu akan ganin Baban, kodai mu jinkirta zuwa wani lokaci. Yanzu dai dazan samu numbers ɗin da yake aiki dasu zanso hakan”.
“Eh zaka iya samu dan nima ina da numbers nashi har biyu”.
“Bazai baka masu muhimmanci ba in har akwai saka hannunsa a wannan aiki. Dan zai yiwu ya jima yana shirya komai, muma cire hasashe dolene wannan aikin an jima ana shirya shi kafin a aiwatar. Inaga wayar Yazeed ko number ɗinsa zan amsa, sai ita matar Yazeed ɗin, da kuma number ɗin ita Sabuwa take ko mi”.
Fuskar Daddy da murmushi ya ce, “Ba damuwa Son duk za'a samu. Sai dai wayoyin nasu ne ban sani ba ko suna tare da su ko an barsu anan gida. Bari muga. Kai Waleed je kira min Auntynku Amrah”.
Amsawa Waleed yayi ya tafi kiran Amrah, babu jimawa sai gasu sun dawo. Da girmamawa ta musu sannu. Daddy yace taje ita da Waleed sashen su Yazeed su duba wayoyinsu idan sun gani su kwaso musu. Ta amsa da to suna fita. AA da Daddy suka cigaba da hiransu. Ammie da Aunty Sakina suna kitchen suna haɗa abu da zasu ba AA ya tafima Oum da Maanal, dan Ammien tasan Maanal ɗin zata so shi dan itama tana cinsa sosai idan tana da ciki, tasan kuma ba lallai a samu a Abuja ba, duk randa Maanal ɗin ta tashi buƙatarsa sai ta wahalar da su. Kusan mintuna talatin Amraah da Waleed suka dawo da wayoyin su Yaya Yazeed. Harda tab ɗin Nazeefa. Ko taɓawa Daddy baiyi ba yace su bama AA. Amsa yayi a take ya fara duba wayar Yazeed, babu wani password a jiki. Contacts ɗinsa kawai ya shiga sai kuma ya tambayi Daddy wane suna yake ganin Yazeed zai iya sakama Baban Nazeefar. Daddy ya ce, “To alaƙar tasu kafin auren yarinyar ba wata mai ƙarfi bane, amma saka Abba ko Daddy ɗin ko Mabera muga”.
Mabera ɗin AA ya fara sakawa, sai ko ga Daddy Mabera ya bayyana har 2. AA yay ɗin gajeren murmushi yana nunama Daddy, shima Daddyn murmushin yayi. Massage ya shiga yay ƴan dube-dube, ganin bai samu komai daya shafi Daddyn Nazeefa ɗin ba sai ya ajiye wayar yana faɗin, “Zan cire sim card ɗin duka biyu Daddy. Dan dolene muyi aiki a kansu, idan na gama sai a dawo masa da su”.
“Aa mizai hana ka tafi da wayar gaba ɗaya?”.
“A'a Daddy waya ai sirrin mai ita ce. Sim card ɗin it's okay. Ita dai ta matar tasa ce duka zanje dasu gaskiya. Dan anan nafi tunanin samun komai da nake buƙata”.
“Babu damuwa Ajwaad ALLAH yay maka albarka kaji, ALLAH ya ƙara ƙyautata rayuwarku kai da ƴan uwanka da matarka. Ya baku zuri'a masu albarka da jin ƙai”.
“Amin Daddy Nagode nima sosai”...
________★
“Wlhy Aunty Saheeba karki kashe kanki. Gaskiya ake gaya miki ki kwantar da hankalinki jininki ya sauka..”
Hawaye sosai suka ziraro ma Shaheeda. Muryarta can ciki dan ko fita batayi ta ce, “Humm Nuratu baki san minene kishi ba, duk yanda kike tunanin kina jinsa a ranki game da Ajwaad wlhy ba komai bane ba. Domin baki san ainahinsa ba, soyayyar da kike masa ce kawai. Amma ni fa, na ɗanɗani zama da Fadeel, nasan wanene shi ciki da wajensa, duk da aurenmu auren haɗi ne Nuratu bai rageni da komai ba. Ta kowanne fuska yana sauke haƙƙina har ma da gyara. Wlhy samun gwarzon namiji irin Fadeel sai an tona a cikin maza. Yanzu ace komai na nagartatsa zan raba da wata dole ne na dinga jin ciwo a raina”.
“Tunda kin san har haka ne Aunty sai ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya, daga nan koma wane irin yaƙi ne sai kiyi. Amma yanzu kina fama da ciwo, ciwon ma da bai san kina yi ba kinzo kin halaka kanki shike nan taci nasara, dan da Yaya Fadeel ɗin da ƴaƴan da abinda ya tara ɗin duk sun zama nata, kinyi wahalar banza kenan. Kin ganni nan nasan ban auri Yaya AA ba, ita tana ciki bazanyi sakacin dazan bar mata shi ba ita kaɗai, shiyyasa kiga ban zafafa ma kaina damuwa ba na samu na miƙe, dan babban burina na dai aure san, koma mizai biyo baya sai ya biyo, amma ita a yanzu bata gabana bata tata nake ba sam. To kema yanzu ki fara yaƙin dawo da hankalinki jikinki ki samu lafiya shine mai muhimmanci a gareki”.
Sosai Saheeba taji ta gamsu da shawarar ƙanwar tata. Dan haka a wannan yinin ta dinga ƙarfafa kanta sosai. Tana kuma ƙoƙarin amfani da dukkan shawarwarin da itama Nurse ɗin dake zaryar zuwa dubatan ke bata. Sai dai ta kasa daurewa sai da ta tambayi Babban Yaya. Nuratu da itama ba sauka ƙasan take ba ta ce, “Nima ba ganinsa nake ba, amma time to time nakan ji motsinsa ya shiga ɗakinsa ko ya fita. Sai dai da alama shima ya tare a ƙasan ne dan ba sosai nake jinsa ba. Bara dai yanzu idan na gama cin abinci zan sauka na duba miki harma su Naufal. Wai yaran nan ko leƙo sashen nan basayi fa”.
“Humm Nuratu ke nan. Baki san wacece matar can ba. Koda yake koba komai tafi Mamy ta wani ɓangaren wlhy, dan yanzu kinga komai zataima yaran da kanta, amma Mamy sai dai ta saka ƴan iskan can su Haule suyi musu”..
Nuratu ta ce, “Hummm”..
To nima bari nace, “Hummm ɗin duk da ban san ma'anar na Nuratu ba😂.
_________★
Anan ɓangaren Oum kuwa su Maanal suna tare da Oum suna hirarsu, a haka Yaya Fawzan yazo ya samesu. Sai hirar ta ƙara armashi, koda suka tambayi Najma sai cayay musu tana barci kanta na ciwo. Ƙasa-ƙasa Maanal da Ameerah suka kalla juna cike da gulma. Har la'asar suna sashen, anan ma sukai salla, Babban Yaya da Fawzan suka wuce massalaci. Zuwa lokacin kuma damuwar Maanal ta fara bayyana akan rashin jin AA. Oum dake lure da ita sai ta fara janta da tsokana, sai dai Maanal ɗin murmushin ƙarfin hali kawai take yi. Zuwa can Oum tayi baƙi, wasu maƙwaftansu ne dake anan cikin layin sun shigo yimata ALLAH ya sanya alkairi. Oum na sauka downstairs idon Manaal ya sauka akan wayar Oum ɗin, wani tunani ne yazo mata, ta ɗauka wayar kawai tai kiran AA. Shi ko daga can yay zaton Oum ce, ya ɗaga cike da gajiya yana faɗin, “Oumna”.
“Humm ashe nawa kiran ne baka son ɗagawa, ALLAH ya baka haƙuri”. Ta faɗa kawai tana yanke kiran, hawaye masu zafi na cika mata ido. Zuciyarta kam tuni ta kumbura, wani irin fushi take ji matuƙa. Ameerah bata san mike faruwa ba, tana ɗan nesa da ita ta juya mata baya tana ƙoƙarin saka turaren wuta a bunner..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣1️⃣
______________
..........Wani irin rumtse idanu AA yayi tun fara maganar Maanal, koda ta tsinke kuma bai iya ya buɗe ba sai ma lips daya cije. Sun baro gidan su Ammie, amma suna cikin Kaduna har yanzu basu gama fita ba. Driver na aikinsa cike da ƙwarewa shi kuma yana zaune a baya ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna waya kiran ya shigo masa. Ikon ALLAH kuma Maanal ɗin yake ƙoƙarin kira a lokacin na Oum ɗin ya shigo. Ashe gimbiyar ce da kanta. Ya jima shiru bai ma san miya kamata yayi ba. Zuwa can kuma a hankali ya buɗe lumsassun idanunsa yana sakin guntun murmushi. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita da nutsuwa ya ɗauka wayar dake daga gefensa ya kira layin Oum, har ta tsinke ba'a ɗaga ba, ya sake kira nan ma haka. Ya fahimci wayar na'a hannunta har yanzu. Layinta ya koma kira, amma har sau uku ba'a ɗaga ba. Sai kawai ya ajiye ya maida kansa ya kwantar a jikin kujerar ya sake lumshe idanunsa. Ƙasan ransa yana mamakin kansa, a