Author : Bilyn Abdull Category : Romance
kunnenta a safiyar yau da tun jiya ta kama hanyar Kaduna. Takaicin data ƙumsa na kwana biyun nan ma sun wadatar. Yanda kowa ke nuna farin ciki kam ya matuƙar tsaya mata a ƙirji, tana ƙara jinjina al'amarin Ammie.
Uncle Hussain yace, “Lallai da ace yaran nan basu auri juna ba rabo zai kashe mutane da yawa a wannan gaɓar. ALLAH yay maka albarka Rafeeq. ALLAH mun gode maka”.
A take kowa ya shiga jinjina kai, dan tabbas wannan zance na Uncle Hussain haka yake. Ashe rabo ne mai zafi a tare da yaran wannan karon shiyyasa ma AA ɗin ya kusan aunawa barzahu. Ga shi nan adadin kwanakin cikin dai-dai da kwanakin tarewarsu ba ragi babu ƙari a rubuce. ALLAH sarki Oum AA ɗin da Maanal ɗin ta haɗa duka ta rungume. AA ya sa hannu ya sharema Oum hawaye yana mai girgiza mata kai....
Yiiiifffff!! Ƙarar faɗuwar Mamy ta saka kowa juyawa inda take a firgice. RK da tun ɗazun yana sane da halin da Mamyn ke ciki ya saki wani ɓoyayyan murmushi. Sai kuma ya zabura kanta yana faɗin, “Subahanalillahi Aunty Kamila”. Oum ma miƙewa tai da sauri tai inda Mamyn take. Ai kowa mamakin duniya ya isheshi da wannan faɗuwa. Sai dai babu wanda yace komai su RK ɗin suka kamata aka ɗora a saman gadon Oum. Cikin sauri RK ya fara dubata. Sai kuma ya ɗauki wata allura a kit ɗinsa ya haɗa da sauri-sauri yay mata yana faɗin, “Jininta ne ya hau sama sosai. A saka towel a ruwan sanyi ku bani da sauri jikinta ma akwai zafi mai tsanani”.
Cikin sauri kuwa aka kawo towel ɗin, Oum ta rufa mata a jiki na kusan minti biyar, RK yace a sake bashi ƙarami, aka janye wannan da har yay wani zafi. Wanda aka kawo ɗin aka saka mata a goshi sai gashi tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Baba Sardauna da abin ya girmesu sukace dama bata da lafiya ne. ALLAH sarki ɗan uwa dai ɗan uwa ne. Aunty Babba domin kare ƴar uwarta tai saurin bama Baba Sardauna amsa da Mamyn bata da lafiya, dama da ƙyar ta iya fitowa tace mata gana ganin jiri.
Ba dai dan kowa yaji ya gamsu ba akai shiru, duk da ramar da Mamyn tai a bayyane take, dan saima yanzu da take a kwance kowa ya ƙara tabbatar da hakan. Nan dai aka shiga jajanta al'amarin ana mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. AA dai yayi shiru kawai yana kallon Mamyn, zuciyarsa cike da nauyin abu biyu, farin cikin samun ƙaruwa dana halin da Mamyn ke ciki. Dan ɗazun da masifa ta koroshi daga sashen nata bayan ta gama zazzaga masa masifar da bai san laifin da yayi ba...
An sake musu addu'ar samun lafiya ita da Maanal ɗin kowa ya fice. A mamakin kowa kuma Abah bai ko taɓa Mamyn ba. Yadai jajanta kamar kowa. Da zasu fita kuma ya busu suka fice. Sai Oum, RK, AA aka bari a ɗakin, dan RK yace Mamy ɗin na bauƙatar iska....
_________★
A Kaduna kam yaran Hajiya Yaya basu san mike faruwa ba sai da asuba koma muce gari ya waye. Sun saba ita ke tashinsu sallar asuba. Amma yau sai sune suka tashi da kansu. Hankalin Amrah yaƙi kwanciya, tana idar da salla ta ce, “Aunty ko lafiya yau Mamma bata tada mu salla ba.”
Nusaiba dake kusa da ita ta ce, “Yanzu nake son yin magana Amrah, amma jeki leƙata ko itama makarar tayi jiki da jini. Balle Kinga kwana biyun nan ba wani isasshen barci take ba”.
Kai Amrah ta jinina tana miƙewa, mintuna kaɗan sai gata da gudu har maganarta bata fita sai nuna hanyar waje take. A zabure duk sauran ƴan uwan nata suka miƙe suka bita. Wani irin shock da tashin hankali suma suka shiga da ganin Hajiya Yaya a ɗaure. Ga ɗakin yay kaca-kaca alamar ansha bincike a cikinsa. Atare kuwa sukai kanta suna kiranta kowa na fashewa da kuka. Sai dai koda suka cire abinda ya ɗaure bakinta ma bata numfashi, kuka suke na tashin hankali. Siyama dake babba a cikinsu ce tai hankalin kiran layin Daddy. Yana ɗagawa ta sanya masa kuka da faɗin, “Daddy wlhy ɓarayi sun shigo mana gida jiya da dare. Sun ɗaure Mamma gashi nan ma bata numfashi”.
Matuƙar bugawa ƙirjin Daddy yayi, dama yau yake shirin su koma gida Ammie dai sai gobe idan ALLAH ya kaimu dama sukai da ita. Cikin ruɗewa Daddy yace, “Ina Yazeed, ku kirashi, nima in sha ALLAHU gani nan tahowa”.
“Daddy kasan ko mun kira Yaya ba zuwa zai yi ba. Daddy mun shiga uku idan Mamma ta rasu ya zamuyi”. Kuka ya sarƙeta. Tausayin yaransa ne sosai ya ratsa shi. Cikin kwantar da murya ya ce, “Siyama bazata rasu ba in sha ALLAHU. Ku kwantar da hankalinku bara na turo muku Doctor. In sha ALLAHU nan da awa biyu nima zan iso, idan kuma mun samu train shike nan ma, kumata addu'a kudai, kinga kace babba sai kin nutsu suma sauran zasu nutsu okay”.
Kai ta jinjina kamar tana a gaban Daddyn ta share hawaye. Gaba ɗaya Daddy ma shi ya rasa ina zai kama. Sai kawai yay kiran layin Ammie. Amma ba'a ɗaga ba. Doctor ɗinsu ya kira ya sanar masa yaje gidansa Please da gaggawa ana buƙatarsa. Yana yankewa ya kira dpo ɗin dake station ɗin kusa da anguwarsu. Da ga haka ya sake gwada kiran Ammie amma ba'a daga ba. Dole ya ajiye wayar ya tada su Waleed da suka koma barci yace su shirya. A gurguje duk sukai shiri, cikin sa'a ya kira train station ya samu ticket. Gidan su AA suka nufo yana cigaba da gwada kiran Ammie. Amma har suka iso bata ɗaga ba...
Ammie wayarta na'a silent ne, anata kuma wannan kai-kawo na Maanal sai ga na Mamy, shiyyasa sam bama tasan Daddy na kiranta ba. Sai yanzu da kowa ke fita ta ɗauka wayar dan kiran su Shahidah taci karo da miss calls din Daddy da yawa. Sai da gabanta ya faɗi, tai ƙoƙarin kiransa back. Aiko kasancewar ita ɗin shima yake son kira dama ko ringing batayi ba ya ɗaga. Cikin tashin hankali Ammie ta ce, “Daddyn Hameed lafiya dai kuwa. Tarin miss call ɗinka sun tada min hankali”.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya sanar mata ai gashi ma a gidan Darma ɗin. Yana tare da Babban Yaya yanzu haka. Dan cikin sa'a motar Daddy na shigowa Babban Yaya na fitowa daga sashensa shar da shi. Sashen Oum yake shirin wucewa ya hango Waleed na fitowa a mota shine ya nufosu. Koda Ammie ta fito ta samu har su Abah ma sun fito dan Daddy yace bazai shiga ba. Train ɗinsu na gab da wucewa.
Koda Daddy ya gaya mata ta shiryo su wuce hankalinta sake tashi yayi. Abah ne yace ta kwantar da hankalinta ga abinda ke faruwa ne. Aifa Ammie da saurinta ta juya ciki tana sanar masa Hajiya Basariyya na nan tare da su ai. Daddy yace ya korata. Shi kuma ya fara ƙoƙarin saya mata ticket ɗin da farko ya manta ne ma gaba ɗaya tana nan itama. Babu abinda Ammie ta ɗauka sai wayarta da handbag, acewarta Amaal ta taho mata da sauran kayan. Kowa nata jajanta al'amarin. AA nason tashi babu dama, haka ya haƙura yabi Ammie da addu'a, amma yasa a ransa in sha ALLAHU ko yau bai bi bayansu Kaduna ba zuwa gobe zaije.
Sai da su Ammie suka wuce sassan su Oum suka dawo ciki ana ƙara jajantawa. Sai lokacin kuma Babban Yaya kejin Lilly da Mamy babu lafiya. Sai ga Yaya Fawzan shima kamar an saita. Farin ciki matuƙa suka nuna da jin labarin cikin jikin Lilly, suka jajanta na Mamy dake kwance tana jin kowa amma tai lambo. Shi dai RK yasan ba barci take ba, amma yay shiru kawai....
Cike da tsokana Yaya Fawzan dake kallon AA bayan ya gama duba result ɗin gwajin Maanal da RK ya bashi dan neman magana. Kasancewar yana zaune ne a bed side drawer kusa da AA ƙasa-ƙasa ya ce, “Uhm-uhm wato yaron nan kai bala'i ne, afa ranar daka tafka tsiyarka a ranar komai ya kankama...”
Baki buɗe AA ya kalla Yaya Fawzan, sai kuma ya kalli inda Babban Yaya ke tsaye jikin mirror yana danna waya. Ganin hankalinsa ba'a kansu yake ba ya dawo da kallonsa kan Yaya Fawzan dake dariya shi da RK. Caraf RK yace, “Kai ko babban sauro ne fa, kaima kasan sau ɗaya yake shan jini a kwanta. Bugun ƴan ball ake gaya maka Son”.
Ai dariya suka sake kwashewa da shi, har Babban Yaya na ɗagowa ya kallesu. Ya ce, “Kuna lafiya kuwa?”.
AA daya watsa musu harara ya ce, “Inafa sukaga lafiya Yaya. Ai sai kun haɗa da addu'a”.
“Tare dakai za'a haɗa ai mana addu'ar ai. Ka gama tafka tsiya a ɗaki ka fito kana mana wani sanyi-sanyi kai na ALLAH”.
RK ne mai maganar yana hararar AA. Kai AA ya girgiza kawai. Babban Yaya yayi murmushi da faɗin, “Ku biyun nan dai kun saka min Auta a gaba. Bayan kuma da naku tambarin a goshi.”
Yaya Fawzan ya ce, “To ai mu Yaya bamuyi musu ba. Shi ko fa, yayta wani ciccin magani yana dakewa. Kai yau ba gashi fuskarka murmushi yaƙi barinta ba alamar godiyar UBANGIJI ”.
Da gudu Babban Yaya ya waro idanunsa akan Yaya Fawzan. “Oh iya shegen naku ya bar kan Auta ya dawo kaina kuma kenan?”. Yay maganar yana wurgoma Fawzan gwangwanin turare. Mi RK da Fawzan zasuyi in ba dariya ba. Shi kansa AA ƙasa yay da kai yana murmushi, dariyar kuwa ya danneta da ƙyar. Dan harga ALLAH shima fa tunda Babban Yaya ya shigo gulmarsa yake a zuciya. Fuskarsa a sake, ga wani ƙyallin angwanci da cikar kamala a tare da shi. Ƙamshinsa kam gaba ɗaya ya gauraye da wanda ba nashi ba...........✍️
Ehem-ehem 🤣🤣😂🏃🏃🏃
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣2️⃣0️⃣
______________
.........“Oh jama'a, yaran nan jiyya kukeyi ko shargallenku?”.
Oum data leƙo ta faɗa tana kallonsu. Muƙuy AA ya haɗiye murmushinsa yana nuna RK da Fawzan. “Oum kin san in dai waɗan nan biyun na a waje to sai addu'a. Sun addabemu ki korasu waje dan ALLAH”.
Oum dake satar kallon Babban Yaya ganin yanda fuskarsa ke ta annuri ga murmushi yaƙi barinta ta ce, “Ai za'a kai ga hakan Auta. Kunsa marasa lafiya gaba dan iya shege sai dariya kuke?”.
RK yace, “Aunty ai barci suke. Kuma dariyarmu nutsuwa ma zata basu su duka kedai jeki cigaba da hidimar bikinki Maman anguna”.
Kai Oum ta girgiza kawai da faɗin, “ALLAH to ya shiryeku” ta juya ta fita. Kusa da Babban Yaya RK ya koma ya tsaya. Da sauri Babban Yaya yace, “Kana cewa tak zan ajiye kawun gefe nima nayi ta auta yau. Tunda na fahimci kai da Fawzan kun zama ƴan iska yanzu”.
Ai yanzu kam AA sai da ya dara. ALLAH sarki babban Yaya yana tsoron yan iskan biyu su tasashi gaba. RK da Fawzan kam dariya ba'a magana. RK ya ce, “Haba Son yada tsarguwa haka? Nifa tambaya kawai zanyi amma kana neman fassarani da wani abu kuma”.
Babban Yaya ya hararesa da faɗin, “Bar tambayarka na yafe. Shiyyasa auta ya raina ku wlhy, manyan banza ne anan kawai. Kudai tuna ga Lilly nan kwance zata iya farkawa ta jiku. Ga kuma Mamy”.
Cike da mugunta RK yace, “Ai Mamy barci take bil haƙƙi, Lilly kam tashinta ba yanzu ba.”
A hankali hawaye suka silalo ta gefen fuskar Mamy, kasancewar tacan take kwance ta juya musu baya ba gani suke ba. Tsinuwa take jerama RK a zuciyarta tari-tari. Dan yau tsanar da take ji tana masa tafi ta kullum shi da kowa ma dake a Darma Family. Wani irin sukar zuciyarta da ƙonata dukkan hirar da sukeyi take mata. Zuwa yanzu ji take tazo gaɓar da bazata iya haƙuri ba, dan in har tai hakan lallai Fateema na shirin cinta wasa ne. Kuma wannan cikin tayi alwashin ko zata tafi tsirara sai ta zubar dashi wlhy. Manaal bazata taɓa haihuwarsa ba...
Ehem-ehem. Ashe watan samun matsalar AA da Mamy ya tsaya kuwa🤭, dan wannan cikin duk wanda yay gigin taɓashi to bara dai nai shiru, ɗan soyayya ne fa, komu ai sai inda ƙarfinmu ya ƙare ko ya kukace mutane na?😆😜
_______★
Anan Mamy na a birkice da batun ciki can ma ɓangaren Nibras da Saheeba da su Nuratu da uwarsu cike zukatansu suke da baƙin ciki bayyananne kai kace sun haɗa miji ne da Maanal ɗin su duka, dan kishinta suke ji na gaske a zukatansu bayan kishiyoyin nasu. Karan farko Nibras taji wani abu mai kama da tashin hankali a ƙasan zuciyarta game da haihuwa. A sati huɗu kacal cikin na biyar Maanal nada cikin masoyinta AA, itama Najma fa nanda wata sati biyar ɗin za'a iya cewa tana da cikin mijinta kuma. Hakama Ameerah zata iya samu. Ga Saheeba ance ciki ne da ita itama. To itafa?. Zuciyarta tai wani kalar motsawa. Ai babu shiri ta ɗauka waya ta kira mamanta ta labarta mata komai. Itama dai Maman tata hankalinta ne ya tashi, dan sak irin tunanin Nibras ɗin ne yazo mata. A sanyaye Mom dinta ta ce, “Nibras kodai kinsha wani abun hana ɗaukar ciki ne a farkon aurenku? Shekara biyar ana shirin kulle ta shida ba wasa ba. Kin fa samu Saheeba da tsohon ciki a gidan nan, ta haihu kina nan, ta raina ta yaye ta sake samun wani ta haifa ta raina ta yaye, badan ma jinkiri data samu ba da yanzu maybe tayi wani wannan cikin da akace ta samu zai zama na huɗu ne. Ga kuma wadda aka auro jiya-jiya itama harta samu. Suma wannan da suka shigo karki raba ɗayan biyu nan da sabon wata su fara nasu amaye-amayen tunda ɗaukar cikin yanzu ba wuyane da shi ba. Shi ke nan kin zama ƴar kallo mu da dukiyar Darma sai hasashe daga nesa muna ji muna gani wasu naci. Lallai muna cikin babbar jarabawa, dan ba haukan kishi ya kamata na tayaki ba Nibras rashin samun cikin ki ya kamata ya dameni ma a wannan gaɓar. Nibras kinsha wani abu ne? Ki gaya min dan ALLAH nasan ina zan kama ina zan samo mafita”.
Shiru Nibras tayi kalaman mahaifiyarta na mata luguden daka a zuciya da ƙwaƙwalwa. Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa daga can. “Nibras! Magana nake dake fa kika min shiru! Ki faɗa min kinsha wani abun hana ɗaukar ciki ne dan ubanki?!!!”.
Tsabar yanda tsawar ta ratsata sai da ta zabura jikinta na ɗan rawa. Sai kuma hawaye sharrr suka shiga ziraro mata kamar an buɗe fanfo. Tasan halin mahaifiyarsu sarai, da abinda zata iya, ta musu raino na gata musamman ma ita da take mace, amma idan tana son abu bakai mata ba ka banu, sarai zata iya ɗaukarta takai asibiti a bincikata. Dan haka gara ta faɗa mata gaskiya kawai. Murya na rawa ta ce, “Wlhy Mom allura ce kawai nayi kuma lokacin ma da sukace zata daina aiki tuni yayi, kuma wlhy daga nan ban sake zuwa nayi ba, ban kuma sake shan komai ba shekara kusan huɗu kenan”.
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Amma ban taɓa sanin ke wawuya ce ba mai dusa a cikin kai irin yau. Ashe ni wahalar banza ma nake. Nibras dama ke muguwar yarinya ce ban sani ba. Wlhy dana san abinda zakiyi kenan da ni na auri Aliyu Darma ɗin ma kawai bayan mutuwar ubanku, kuma wlhy babu abinda zai hana na haihu masa a shekarun nan nawa. Ai shike nan sai ki fara shirin dawowa gida mu cigaba da goga jigida dan amarya dai kam ta gama samun gida. Dama gata ƴar uwarsa, ke da kanki yanzu kike faɗin irin murnar da sukeyi akan cikin facalarku, shiyyasa dama gaki nan ko kwarjini baki da shi a gidan, to kin kasa sama musu abinda suke so mara hankali wawuya kawai......”
Ƙitt ta yanke kiran. Wani irin fashewa da kuka Nibras tayi dan kamar uwarta ta mata wata allura ne mai ƙarfin gaske a yanzu.....
★★
A ɓangaren su Saheeba kam, ko leƙowa duba Mamy basuyi ba kuma sunji sarai ance ta faɗi, balle Maanal ta samu itama, suna can suna ƙulla hanyar salwantar da cikin Maanal ɗin kamar yanda Mamy tai alwashi. Maman Saheeba ta rantse ta ƙara rantsewa Saheeba ce kawai zata haihu a gidan sai Nuratu idan ta shigo itama. Amma har Najma da Ameerah da Nibras basu isa ba, dukiyar Aliyu Darma ta ƴayanta ce kawai a gidan. Har Mamy data haifi ƴaƴan zero zata tashi. Balle Oum datai wahalar banza.
Saheeba dai da akema ƙarin ruwa hawaye kawai take yi, hakama Nuratu kuka take rurus jikin Hajiya Turai data zo da likitar data duba Saheeba. Dan da wani mugun zazzaɓi ta tashi tanata sambatu dole Nuratu ta kira Nana ta sanar mata. Shine Babban Yaya na fita suka shigo bayan hanyar bedroom ɗin Ameerah tasha harara. Hajiya Shuwa kanta yau tasha zagi gwargwadon iko bama Oum kaɗai da Babban Yayan kansa ba.
Suna gama ƙulle-ƙullensu Hajiya Turai data fito tai kiran Sille