Author : Bilyn Abdull Category : Romance
ɗinsu. Dole su Abbu suka baro asibiti suma harda AA ɗan magana ta gemu-da-gemu za'ayi. Oum, Umma, Mah-mah, sai Mamy ne kawai mata a zaman. Abah ya saka Mamy ne saboda itace sanadin auren.
Bayan an buɗe yaron da addu'a Babban Yaya yayi bayani abinda suka san ya faru, dan haka aka juya ana kallon Yaya Fawzan, da ƙyar yayi Magana dan a fusace yake.
“Mamy itace ta kawo min Nibras matsayin mata bayan dawowarmu Nigeria babu daɗewa, ban kula ba dan tun zuwan Nibras da Mamanta gidan nan ni sam banga wani abin da zan so ba, ta cika sangarta da yawa. Abinda yasa na sake jin batai min ba a Paris fa Mamy ta haɗu da Mom ɗin nata, wai ƙawarta ce shekaru da dama basu kuma haɗu ba sai lokacin. Kawai muna dawowa naga alaƙarsu tayi ƙarfi harda cewa na auri ƴarta. Naso bijirewa ta sharɗanta min idan ban aureta ba bata yafe ba. Haka na amsa kawai na yarda dan a zauna lafiya. Mun riga Ajwaad dawowa Nigeria saboda yana karatu, bayan ya kammala kuma ya wuce China. Ko bikina inaga idan ban manta ba kwanansa uku kacal shi da abokinsa suka koma. Sai da muka shiga kusan wata na bakwai da aure ya dawo gaba ɗaya. Sai kuma lokacin Nibras ta ganshi duk da tasan labarinsa ta kuma ganshi a hoto. Watannin farkon nan kawai zance muyi lafiya da yarinyar nan a matsayin miji da mata. Amma tunda Ajwaad ya dawo komai ya canja, da farko ban gane take-takenta ta ba sai lokacin haihuwar Anum. Nayi mamaki kwarai da gaske kuma na girgiza, amma ban gayama kowa ba itama bance mata komai ba, ina son tabbatar wa sannan itama Mamy ta fahimci abinda nake gudu da kaina. A takaice a lokacin auren Maanal da Ajwaad na sake tabbatar da zargina akan Nibras, na kuma fahimci Ajwaad ma ya gane take-takenta sarai. Ba ƙaramin wahalar zama da yarinyar nan nasha ba a shekarun nan, ban san daɗin aure da martabarsa ba sai da na ƙara a yanzu. Tasha magani dan kar ta samu ciki saboda hankalinta nakan Ajwaad , ina sane duk na watsar da ita har kai-kawon asibitin da sukeyi yanzu akan rashin samun ciki. A wannan tafiyar tunda muka dawo yarinyar nan bata nuna tama san mun dawo ɗin ba, ashe abinda take shiryama ranta daban. Kawai a shekaranjiya Ajwaad ya kirani, tunda naji muryarsa nasan babu lafiya, koda ya buƙaci na saketa abinda na kawo a raina kawai ta samesa tace tana sonsa ƙuru-ƙuru, ashe al'amarin ma ya wuce hasashena....”
Sosai hankalin ƴan uwan Nibras ya tashi, ita kanata Mom ɗin nasu jikinta ya fara sanyi. Karo na farko Uncle Mahmud yace, “Ajwaad miya faru daren shekaran jiya?”.
AA ya jima shiru kamar bazai tanka ba. Dan zuciyarsa zafi take masa, raɗaɗi take masa baya ma son ya tuna. Da ƙyar ya iya dannewa ya zayyane musu komai daya sani tun daga dawowar sa Nigeria, da sakwanin data dinga tura masa a wannan tafiyar da sukayi ya nuna musu a waya, har shigarsa sashen a shekaran jiya kawo kiran Yaya Fawzan da yayi a waya zuwa buɗe ƙofa da Maanal tayi. Kuka kawai Momyn Nibras ta fashe da shi. Wlhy da tasan abinda Nibras ta aikata kenan da bazatayi abinda tayi ba. Ran Uncle ɗinsu sun ɓaci, haka ma yayunta. Ita kanta Mamy wani iri ta dinga ji a ranta. Dama kuma tun shekaran jiya zuciyarta ke wani irin raunana. Musamman yanda taga Maanal nayi akan yaranta, halin da yarinyar ta shiga. Ta tuna ita rayuwar data nema jefa nata ƴaƴan tun daga kan Sille data samu a waje....
Duk uwa an santa ne da soyayyar ƴaƴanta, amma wlhy ita a shekarun baya kawo daren shekaran jiya buƙatunta kawai take kallo, bawai bata son su bane, su duka har Sille sonsa take, musamman Ajwaad tana jin yaron a ranta sosai, amma shaiɗan da kururuwarsa sun riƙe mata zuciya biyan buƙatar ta da kai wadda bata cutar da ita da komai bane ba a ranta. Anya kuwa tama Fateema da Aliyu adalci? Tama kanta adalci? Tama ƴaƴanta adalci?. Hawaye masu zafi suka cika mata idanu...
Tunanin Mamy yayi nisa a can, anan kuma iyayen Nibras da ƴan uwansa ne suka koma bada haƙuri. Brothers ɗinta harda hawayensu dan abinda ƙanwar tasu tayi ya taɓasu matuƙa, ta goge musu hadda, ta saka tsoro da shakka a zukatansu. Yanzu shike nan ta ɓata musu sunan gida za'a dinga kallonsu a masu ƙarancin tarbiyya duk da mahaifinsu yayi ƙoƙari a kansu. Kaicon wannan rayuwa, kaicon ƙawaye, kaicon gangar jikin dake ɗaura aminci da son zuciyar..........✍️
211
.......ALLAH sarki, sai ga Momyn Nibras na kuka da neman yafiyar Yaya Fawzan da AA. Suma su Abah ta basu haƙuri. Sannan ta juya wajen Oum ta neman yafiyarta. Ta ce, “Kamila ta gaya min abubuwa da dama a kanki shiyyasa na dinga miki rashin mutunci a baya. Duk da baki taɓa min komai ba ke na rashin dai-dai saima alkairi ga ɗiyata. Tabbas na yarda a yau duk wanda ALLAH ya bama kyakkyawar zuciya ya gama masa arziƙi, da ace Kamila ta nutsu ta zauna da ke da ƙyaƙyƙyawar zuciya itama da taci ribar wannan zaman naku. Amma duk da haka yanzun ma taci riba, dan badan tarbiyyarki da tsayawa akan ƴaƴan data baki saboda wani ƙudirinta ba wlhy da babu na mora a cikinsu. Da yanzu ba wannan maganar ake ba, da bata kallesu a yanzu cikin kamala da mutuntaka ba. Amma sai ALLAH ya dubi zuciyarki, ya dubi zuciyar mahaifinsu, ya jarabceta da baki su halak malak. Kinyi haƙuri da jarabawar rashin haihuwa ALLAH ya sakakanka miki da ƴaƴa masu irin zuciyarki data mijinki. Shekara da shekaru tanata shirya miki mugunta baki taɓa faɗawa ba sai itace ta kasance a cikin ramin data haƙa domin ke. Ta rasa mijin da take burin mallaka ta rabaki da shi, ta rasa dukiyar data so tarawa ta karfin tsiya-tsiya harda yunkurin kisan miji, ta rasa yayan data bada dan samun zuciyar miji. Ta aura masa wanda take so dan ta mallaki ƴaƴan cikin sauƙi. Ta rabasu da waɗanda suke so saboda suna da alaƙa da ke. Yau kuma ga wanda take so ɗin sun tabbatar mata da halaye irin nata data koyar dasu, ke kuma ga mijin a hannunki, ƴaƴan a hannunki, sun auri wanda suke tare dake ɗin batare da tursasawa ba, Fateema miya rage miki banda kita godema UBANGIJI. Tabbas kece kikaga AJIYA A HASKE maimakon AJIYA A DUHU. Yanda ALLAH ya baki duniya ina roƙonsa ya azurtaki da samun lahira mai albarka da rahama. Ki gafarceni akan kuskurena.”
Oum dake murmushi ta ce, “Na yafe miki Hajiya Shamsiyya, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Ba ma ke ba duk wanda ya taɓa min kuskure a zahiri ko baɗini wlhy na yafe masa hatta da Junaid kansa”.
Momyn Nibras ta dubi Mamy da kanta ke ƙasa ta ce, “You see, Kamila kinfa ji, ki duba fa Kamila. Dan ALLAH ina roƙonki kema ki sauƙaƙama zuciyarki, ki sauƙaƙama rayuwarki tunda kin dai gane zuwa yanzu wanda ALLAH yace shine-shine. Yaranki na sonki, mijinki ya taka rawar gani a kanki, abokiyar zamanki na miki kallon ƴar uwa ba kishiya ba, dangin mijinki sun taka rawar gani a kanki. Bakici riba ko ɗaya daga abinda kika aikata ba sai faɗuwa ma da ƙasƙanta da ƙarewa da ciwuka kala-kala gasu nan. Miya rage kuma banda jiran sakamakon kabari dana makoma. Karki zama wadda bata da rabo, ki kalla ni'imar da UBANGIJI yay miki da talala na baki lokacin kaiwa zuwa yanzu ki gyara abinda ya rage a cikin rayuwar ki. Da farko naji bazan yafe miki ba saboda kin taka rawa wajen fanɗarar min da yarinya kema duk da nawa laifin, amma kece kika dinga nuna musu suyi komai ba komai a gidan nan har take jin zata iya yin komai ɗin. Amma kalaman Hajiya Fateema na yafiya sun sanyaya min jikina wlhy, yanda bata duba muguntar da kukai mata ba tace ta yafe miki nima na yafe miki. ALLAH ya ganar dake gaskiya ki saduda kafin komai ya ƙarasa ƙarewa. Alhaji Aliyu kaima dan ALLAH ka gafarcemu kai da yaranka. Ku kuma gafarci Nibras abisa ɓarnar data tafka da wadda taso tafkawa. Abu na ƙarshe dazan faɗa itama Saheeba bata da amfanin zama a tare da ku, dan sai kun kakkaɓe su gaba ɗaya a cikin zuri'arku sannan zaku zauna lafiya. Domin kuwa akwai hirarsu da naji randa na dawo da Nibras gidan nan da kuma ana gobe salla ita Nibras taji wani abu itama.”
Babu wanda bai ƙara nutsuwa yana kallon ta da mamaki ba. Hatta Mamy sai da ta ɗago tana kallonta fuska share-share da hawaye. Ta cigaba da faɗin, “Nibras taji Saheeba na sanarma ƴar uwarta bazataje idi ba dan tana son aiwatar da aikin da mahaifiyarsu ta turo musu akan Maanal. Suna son su fara salwantar da cikinta sannan su koma kan sauran suma. Dan ita kaɗai zata haihuwa a gidan nan sai Nuratu idan ta shigo kamar yanda mahaifiyarsu ta tabbatar musu ta kuma yi musu alƙawari. Na mata faɗa sosai akan miyasa bata gaya muku ba, sai tace ai tayi niyyar sai kun dawo idi ne kuma sai ta haɗu damu a wajen idin ta bimu, a lokacin da ta gama gaya min na kaɗota dan muzo mu sanar daku muka samu abinda ya faru ya faru na kidnapping ɗinku da akayi. To abinda ban sani ba a yanzu dai shine, miya faru ita ta rasa nata cikin harda cire mahaifa. Manaal ɗin bataci maganin bane ko yaya akai al'amarin ya juya haka?. Wanda naji kuwa Nuratu ce ke waya da bansan waye ba, tana tabbatarwa da alwashin sai ta sakama Kamila cutar ƙanjamau tunda a jikin ɗanta ta samu itama sai ta amshi rabonta, yanda suka rasa Hajiya Turai uwar ruƙonta a dalilin ɗan Kamila, ita kuma ta samu HIV a jikin ɗan Kamila, mahaifiyarsu ta rasa ranta a hannun ɗan Kamila, suka rasa Anum a dalilin dai ɗan Kamila itama dole ƴaƴanta su rasata. Naso yi mata magana na kwaɓi kaina gaskiya, musamman dana ga itama abinda Kamilar ta aikata na son kasheka da tai. Sai naga babu amfani ko nama faɗa babu mai saurarena. To ban sani ba ta aikata, bata aikata ba ALLAHU A'A LAM. Sai kuyi gwaji dan ku tabbatar. Ina sake neman gafarar ku ALLAH ya bamu alkairinsa”.
Tsabar tashin hankali Mamy rikitiwa tayi ƙasa. Su kansu su Abah al'amarin ya girgiza su. Su Momyn Nibras na wucewa AA ya tabbatar musu da Mamy nada HIV, ya labarta musu dukkan tattaunawar da yayi da RK, dan haka a take akai kiran RK a waya dan shi yana asibiti. Haka yazo da sakamakon kuwa kowa ya gani. Mamy sai kuka take. Duk da haka Abbu yace suma su Oum sai anyi musu gwajin. Haka aka kwashesu zuwa asibiti har su Saheeba da basu san mike faruwa ba tubda bada su akai zaman ba. Kai su farin ciki ma suke da abinda ya faru a gidan ko yake faruwa. Har addu'a suke ALLAH yasa Maanal ta mutu, dan sun san dai na Nibras kuma ta ƙare tunda harda batun saki biyu. Sun kuma san yanda su Yaya Fawzan ke son junansu bazai taɓa maida Nibras ba.
Kaf zuri'ar Aliyu Darma idan ka cire Naufal dake Saudia sai da akaima gwajin HIV har su Inte masu aiki da su maigadi, su Bola kaf su Uwangale dama bata jima a gidan ba. Babu jimawa aka fidda results dan awa ɗaya tak akayi. Gida suka tattaro kaf suka dawo dan bama bari ake kowa na shiga wajen Maanal ba sai idan za'a bama yara abincinsu Oum da Ammie ke shiga kawai, sai AA time to time dake goge mata jiki.
Dole kuma akai kiran Baba Sardauna da Baba a video call dan babu abinda akeyi bada yawansu ba a family ɗin. Suna kallon kowa suna kallon komai Abbu ya fara buɗe results ɗin ɗaya bayan ɗaya. Dana masu aiki aka fara, kaf ɗinsu babu mai HIV a ciki. Kowa aka bashi result ɗinsa ya fita da farin ciki. Sai na Abah, shima normal, Oum, itama dar, Babban Yaya, shima dar, Yaya Fawzan, Alhamdullah, AA, shima dar. Maanal, Ameerah, Saheeba, Najmah babu mai ita. Nuratu, Mamy sune masu ita. Nuratu nata kuka dan bata taɓa sanin haka zata kasance ba sai a asibiti da taga za'a ɗiba jininta ta rikice. Amma AA yay mata buyagin data nutsu, taso ta gudu tun daga asibitin aka saka mata ido, dan babu yanda ta iya har akazo gida.
Mamy dake kuka tana zagin Nuratu ta shaƙure ta. Da ƙyar aka kwaci Nuratu a hannun Mamy. Aunty kanta kuka take kamar ranta zai fita. Saboda yanda makomar zuri'arsu ta ƙare. Ta kuma tabbatar tun farko tun fari komai ya faru ne daga kuskuren mahaifiyarsu. Abah da gaba ɗaya komai ya kwance masa ya fice masa a rai yace, “ALLAH ya ƙyauta, shi batun son zubarma Maanal ciki fa Saheeba yaya akai abin ya koma kanku?”.
Saheeba dake kuka ta kasa magana. Sai da Babban yaya yay mata tsawa sannan ta ce, “Wlhy ban sani ba Abah, na dai san tabbas na saka mata magani kuma taci abincin amma ban san tayaya al'amarin ya juye a kaina ba. Ban kuma taɓa tunanin reshene ya juye da mujiya ba sai yau ɗin nan?”.
A hankali Ameerah tace, “Bazaki sani ba, domin kuwa ni ce nan na maida komai a kanki”.
Babu wanda bai kalla Ameerah ba da sauri..........✍️212
........Babu ko ɗar Ameerah ta cigaba da faɗin, “Tun washe garin gama bikinmu naji wayar da Hajiya Turai tayi da wanda ban sani ba, sai daga baya na fahimci Sille ne. Daga nan na sanya muku ido da kowane motsinku. Daren salla kamar yanda Momyn Nibras taji abinda kuke faɗa nima naji, dan haka na kira Inte na roƙeta zatai min wani abu amana. Tace min zatayi. Na sake jaddada mata tace wlhy zatayi in dai ba abinda zai cutar da wani a gidan bane ba. Ban ɓoye mata ba nace duk abinda Saheeba zatayi ta saka mata ido idan mun tafi massallaci. Tace min to. Muna a massallaci ta kirani ta sanar min taga tana zuba magani a abincin da Maanal tace a dafa mata. Nace duka ta ɓata? Tace eh. Nace to su sake mata wani. Tace min to. Bayan mun dawo massallaci nacema Inte ta zubama Saheeba wanda ta zubama maganin a gabanta. Haka kuwa akayi, na tabbatar kuma Saheeba taci abincin ne dan hankalinta nakan ganin Maanal taci batare data fahimci ma irin wanda Maanal ɗin tace a dafa mata bane itama. ALLAH kuma ya ƙaddara akanta al'amarin zai koma ba Maanal ɗin zai sama kamar yanda suka shirya ba. Amma wlhy ni ban san munin maganin ya kai har yanda yay mata illa ba”
Sosai Babban Yaya yayi murmushi, babu wani kauce-kauce ya ce, “ALLAH yay miki albarka Ameerah. Ke kuma azzaluma kinga sakamakonki right.” yay maganar yana kallon Saheeba dake kuka kamar ranta zai fita. Cikin ɗacin murya ya cigaba da faɗin, “Kuka baki fara ba ai, sai yanzu ne zakiyi shi daga ke har wannan azzalumar ƙanwar taki, kunga dai yanda uwar taku ta ƙare kanta fal haƙƙin mutane, ya rage naku kuma ku dawo hankalinku ko kuyi irin mutuwarta koma wadda ta fita. Dan basai mutum ya wulaƙanta a duniya bane ake gane ya shiga uku, tafiyarsa lahira da hakkin mutane shine babban shiga uku. Kunyi abinda kuke so, UBANGIJI kuma ya nuna muku yanda ya tsara. Nayi nadamar haɗa zuri'a dake, kai Alhmdllh da Anum ma taru, inama Naufal ɗin ya bita na tabbatar banda sauran alaƙa dake jaka jahila kawai..”
Riƙe Hannunsa Yaya Fawzan yayi cike da lallashi, dan muryarsa ta farayin sama alamar fusata, kuma tabbas idan yakai maƙura sai Saheeba ta ɗanɗana irin abinda Nibras ta ɗan ɗana a hannun AA.
Aunty dake share hawaye tace, “Saheeba kun cucemu ku da Kamila, dama wannan abun ne Nana ke son faɗama su Fadeel? Fadeel halan baku duba video ɗin dana baku ba”.
Kai tsaye Babban Yaya yace, “Aunty bama buƙatar dubawa, bama buƙatar jin komai daga gare ta. Kiyi haƙuri, amma wlhy na tsani azzaluman cikinku. Ita tana son salwantar da jininmu, mahaifiyarmu na son kashe mana mahaifi. Ɗanta na son kashe mu. Saurayinta na son kashe mana Oum. Wannan wace irin rayuwa ce dan ALLAH, wai minene a duniyar nan da har idanu da zukata ke rufewa wajen aikata zalunci. Yanzu da kenan so sukai su kashe abinda ke cikin Maanal, su lalata mata mahaifa kamar yanda akama Oum? Wane irin zalunci ne wannan da bushewar zuciya dan ALLAH. Mata, mata da suka san ciwon yan uwansu mata, cikin ne fa a jikinta, shekaru ta ɗauka tana haukan neman sake samunsa amma har ake shirya sharri a lalata ma wata nata daya kasance na farko haba-haba idan naso zuri'arku na zalunci kaina ai..” kawai ya tashi ya ɗauke Saheeba da maruka, itama Nuratu ta samu rabonta. Aunty suka ruƙunƙume suna kuka da Mamy, sai da Oum ta tashi ta kama hannun Babban Yaya dake huci.
Da ƙyar aka samu falon ya lafa. Baba Sardauna dake ta video call yay gyaran murya, duk hankalinsu suka maida a kansa. Cikin son danne ɓacin ransa ya ce, “Tone-tonen ya isa haka. Sannan batun cigaba da zama da su a gidan nan gaskiya bazai yiwu ba kamar yanda Fateema da Maanal suka roƙa. Dan nakai wata gaɓa da a yanzu ko canjawa sukai suka koma aikata alkairi zuciyata bazata nutsu ba zanta kallonsu ne da zargin zasu sake cutar min da zuri'ata ta wata hanyar kuma. Kamila bazamu taɓa wulaƙantaki ko tozarta ki ba saboda darajar waɗan nan yaran uku da kika haifa mana, duk da da hannunki kika ɗauka kika bama Fateema tuwo dai sunansa tuwo ba'a canja masa suna. Kece