AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   146 / 213

435K to 438K   out of 636.6K words

ni idan na tashi bada gumamar kaya idan ta kama har ZINARI haɗawa nake a ciki🤪😂, yo miye amfaninsa ALLAH na tuba, ƙaryar banzar da wal-wal a kan wuya baya fansata ga walakirin kabari🥱. Oh oh faɗan matsoraci wai wasan sunƙuru, idan mace takai mace ta fito a bamu fili dan ALLAH, Bilyn ce fa, jinin Kanawan dabo da katsinawan dikko kunya gareku badai TSORO ba. Idan kin yarda mu fara wannan game ɗin dan GIRMAN ALLAH gobe naga raddi😏👈 .


Nawa ki ɗaukesa kamar na taba kasa ne na lashi miyau tushen faɗan yara kenan😂, koda yake muma yaran ne bamu wuce ehhhhhhhhh😉 ba, kun dai gane mutane na🤪😂.


LADIDI BISMILLAH🙄🤌 zamu iya fara wasan, ni banda matsala ko ina typing ɗin zan iya😂, yo wani abune ina gama muku posting na koma filin yaƙi💪, kafin safiya nasan koda na ciyo wuya da DUKA wajen zai huce🤣 sai a cigaba da gashi zuwa yammar washe gari a koma filin dagar, wayaga faɗan Kurame, ta AA Darma zan koma, KURMA kuma MAKAHO😆😆🤣Ladiyos bismilla👆🏻😒😣☹️😔🥶🥱🥱🥱.

Kar wanda yace Bilyn yaya akayi, shi saƙon yasan inda aka aika shi😆, waɗanda zasu ƙarɓi saƙon suma sun san nasu ne🥱. Idan kuna son kallo ku jira a maido min raddi ai kune ƴan rakkiyata faɗan🤣🤣👍.

Ina sonki masoyana, ALLAH wlhy sai da ku na Bilyn Abdull, Zafafa family na miƙo muku gaisuwa irin ta girma da mutuntawa❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰😘👏🏻

Bala'i page guda ya tafi a banza Ni balki kumuje jan labari, gulmar ta isa haka dare ya fara yi kuma.😩🏃


____________

......Anan Kaduna kam da ƙyar Ammie ta shawo kan Daddy ya yarda da batun sakawa aima Yazeed addu'a a islamiyyu. Amma da farko yace ta barshi uwar tasa ta ƙara ji a jikinta. Ammie taita masa magiya da nuna masa ba Hajiya Yaya za'a duba shi Yazeed ɗin. Dan yaron kirki ne mai hankali da sanin ya kamata. Kodan ibadarsa da ta samu rauni sa tarosa. Sannan halin da yake a cikin ba Hajiya Yayan kawai yake ƙonawa ba har da su suma. Da nasiha da lallashi dai Daddy ya amince. Dan haka Ammie ta fara fitar da kuɗinta batare data nema komai a wajen Daddyn ba taba Nene akan a dinga abinci ana sadaka. Suka kuma saka ana sauka a islamiyyun yara. Ta kuma shirya da kanta taje Kano ta amso masa ruwan addu'a a gidan Babban malamin nan....

     A lokacin da nan su Ammie keta ƙoƙarin ganin sun maido Yazeed hayyacinsa da ƙarfin ikon ALLAH a ɓangaren mijin sabuwa shirinsa ne ya gama kammala akan Daddy, aiwatarwa kawai zai saka Yazeed ya fara masa. Dan kuwa tun randa abin can ya faru Nazeefa ta kirasu tana kuka ta faɗa musu ƙarya da gaskiya. Aiko suka ƙullaci Ammie harda alwashin yin maganinta itama. Suka kuma sake ɗammarar yin sabon shiri akan Yazeed ɗin. Washe gari Sabuwa tazo ta kawo mata komai da zatai amfani da shi. Ko kallon sashen Hajiya Yaya batai ba balle ta shiga su gaisa. Sai yara taji suna hirar zuwan Sabuwar gidan batare da sun san ma taji ba. Dan yanzu suna aiki da nasihar Ammie basa gaya mata komai daya shafi Yazeed ɗin ko sun gani...
     Aiko komai Nazeefa ta aikata, sai dai anyi rashin sa'a Sakina taga lokacin da take ajiye na sashen Ammie. Dan tsabar munafunci sashen tazo wai bama Ammie haƙurin abinda ya faru kuskure ne, miye-miye ita ba laifinta bane kaza-kaza.. Ammie bata nuna mata komai tace ta fahimta, sai ma tai mata nasiha akan hakan. Shine a zama ta saƙaka abu a cikin kujerar ta barbaɗa wani a ƙasa. Tana fita Sakina tace Ammie kada ta tashi ta jirata tana zuwa. Zuwa tai ta ɗakko kayan shara ta kwashe maganin tas, ta ciro wanda Nazeefa ta saka a cikin kujera. Sosai Ammie tai mamaki ta kuma jinjina al'amarin. Ta kuma yarda su Sabuwa da gaske suke babu wasa a shirin nasu. Ko Daddy Ammie bata gayama abinda ya farun ba kuwa, balle Hajiya Yaya. Ta dai sake dagewa da addu'a ta kuma gargaɗi su Waleed suma. Kai daga ƙarshe ma ta saka suka dawo sashen ta da kwana suka baro nasu, dan a wannan halin tako ina Nazeefa zata iya ɓullo musu. Aiko Ammie tayi farar dabara, dan kuwa a randa tasa su Hameed suka dawo sashen nata har su Amaal data zo gidan na dariya a daren suma Baban Nazeefar ya aiko abinda za'a sakama yaran. Dan ya fahimci aikin zaima Yazeed yawa sai ya haɗa da su Waleed ɗin....

    Hajiya Basariyya dai banda son ina aka tsaya ina aka kwana babu abinda ta saka a gaba. Ta kowane ɓangare kuma taƙi samun damar shiga jikin Hajiya Yayan ko Ammien balle taji. Abin na ƙona mata rai sai take ganin sun haɗe mata kai ne kawai. Gashi Daddy ma yaƙi bata fuskar yimasa batun Yazeed ɗin nan ma. Dan zuwa yanzu dai bisa dagewar Ammie ya haƙura sun koma raba kwana. Daga ita har Hajiya Yayan suna zuwa turakarsa kuma yana cin abincinsu. Basariyyar ce ma ke zumuɗin hakan, ita ko Hajiya Yaya ta kanta take, al'amarin Yazeed ya maidata shiru-shiru ga wata rama da tayi alamar abin na cimata zuciya bana wasa ba. Dan da gaske kuwa lamarin na girgiza mata zuciya, kuma Sabuwa tafi kowa bata mamaki a cikin al'amarin. Ga iyayensu sunce babu ruwansu, sanda suka ƙulla zancen yaran ai basu sani ba batun aure kawai sukazo musu da shi. Musamman ma babansu yafi ɗaukar zafi, dan har tina mata batun Maanal yayi da yanda ta katsatstsare ta dinga aibanta yarinyar da mahaifiyarta. Sai gashi yanzu Ammien ce dai tsaye a al'amarin ɗan nata da ta hana ya auri ƴarta...
     Ji Hajiya Yaya tai abubuwan sun mata yawa. Kamar tana jin nauyin Ammie kuma a ƙasan ranta. Amma dai a zahiri bata nuna ba, ba kuma ta furta ba. Sai dai duk shawarar da Ammie ke bata akana al'amarin Yazeed yi take yi. Yayinda Hajiya Basariyya ke bata mamaki.. Duk da kai-kawo gulma da Hajiya Basariyya keyi hankalinta kuma na'a kan Huznah ne, tama Daddy magana akan rashin jin Huznah ɗin ya nuna mata ta shiga hankalinta ta kama kanta, idan ba haka ba kuma zatasha mamaki. Da yake yanzu tana tsoron komawa gidan Kawu Manu sai tai shiru, sai dai abin na damunta a rai matuƙa, musamman daya kasance Maman Yaseerah ta mata bayanin komai har wayar da suka dinga yi da Huznah kwanaki ta kuma daina jinta ma gaba ɗaya......

___________★

      KANO.

Anan Kano kuwa abu biyu ne ke shirin faruwa a ɓangare biyu. Bangaren Huznah mahaifin Sageer yace ya barta taje ganin gida dan a tunaninsu Hajiya Basariyya ta risina yanzu zata kama kanta akan al'amarin auren yaran. Yazeed dai zuciyarsa bata so hakan ba. Amma bazai iya jayayya da iyayensa ba ya amince. Amma ya roƙa alfarmar a bari har sai babbar salla dake tunkaro mu. Zuwa lokacin itama ta ƙara jin sauƙi sosai duk da dai Alhmdllh zuwa yanzu ma taji sauƙin. Shi kuma yana samun damar baje hajarsa yanda ya kamata a jikinta, sai dai taci kukanta a ɓoye da jera masa ALLAH ya isa babu damar yi a gabansa dan wani tsoronsa take ji bana wasa ba. A hakan ma sai yaga ta takura kanta da yawa ne yake ɗan sassauta mata. Ko in yaga laulayin ya takura mata, dan wani lokacin takayi lafiya na kwanaki sai kuma jikin ya rikice..
     Ga kewar yan uwanta dana mahaifiyarta, dan Alhmdllh a cima babu abinda ta rasa a gidan Sageer. Duk da kasancewarsa talaka yana iyakar ƙoƙarin sa na bata abinda take ci a gidansu. Kuma duk abinda zai sakata a farin ciki yana iyakar ƙoƙarin sa yay mata gwargwadon ikonsa....

     _______★

    Ɓangare na biyu kuwa su Baba Sardauna da Baba, Abbah, Uncle Mahmud, Hassan, Hussain, Najeeb da wasu aminansu Baba Sardauna uku a yau suka shiga garin Katsina domin ganawa da dangin mahaifan su Ameerah. Kwarjinin Darma a idanun al'umma da yawa daban ne. Ko sunan wannan family kaji alkairansu nasa kaji kimarsu da girmansu a zuciya. Duk irin alwashi da cika bakin da dangin mijin Hajiya Shuwa suka dingayi akan sai sun nuna mata su ɗin sune a bikin Ameerah sai gashi sunyi kurum. Dan kuwa wata gaban ai tafi gaban a taka...
     Jikunnansu na rawa suka ma su Baba Sardauna tarba ta mutuntawa, ta girma, ta kuma martabawa. Dan kuwa cikin ikon ALLAH a cikin ƙannen baban su Ameeran akwai mai aiki a ƙarkashin asibitin Abbah. Wato KK HOSPITAL dake garin Kano. Babu wani ja'inja ko kai kawo sukace sun bama Babban Yaya Ameerah, kuma sun yarda a haɗe biki dana Fawzan nan da kwanaki goma kenan.
     Matuƙar jin daɗi su Baba Sardauna sunyi da wannan karramawa. A take Uncle Najeeb ya ajiye sadaki daga aljihunsa. Uncle Hussain ya ajiye kuɗin gaisuwa dana mungani muna so dama duk wani tarkacen tsarabe-tsarabe na aure. Akai huɗɗar arziƙi aka kuma rabu cikin mutunta juna da karramawa. Suma sukace suna nan tafe Kano nemawa Ameer auren Maimoon.
         Shi halin girma duk mai shi to mai halin girman ne. Sai kawai Baba Sardauna yace in dai haka ne wace wahala kuma. Ai kawai ayi komai anan a gama sun hutar dasu a haɗe ranar ɗaurin aure. Babbar magana. Dangin mahaifin su Ameerah fa mamaki ya sake kamasu da waɗan nan bayin ALLAH. A take sukai kiran Hajiya Shuwa suka sanar mata. Ai sai ta sanya kukan farin ciki, babu wani jeka ka dawo tasa Ameer ya tura ma kawunansa kuɗaɗe. Suma dai a take anan akai hannun karɓa kuma hannun bayarwa. Dan suma dai sun ajiye kuɗin gaisuwar Ameer da sadaki da dukkan abinda ya kamata na aure. Kafin aka sake sabuwar addu'a suka musu rakkiya airport dan dama ta jirgi suka zo. Dan haka komai da komai cikin awanni biyar aka yishi aka kammala tamkar a cikin Kano akayi...

     ________★

      Lokacin da duk su Maanal ke dawowa aiki da wannan farin cikin suka iske Oum a ciki, su Mamy dai basu san anayi ba. Sai da su Oum da ƴayanta da RK da Matarsa dake gidan suka gama farin cikinsu da murna RK da Fawzan harda ma Babban Yaya liƙin kuɗi dan neman tsokana. Abin ya bama Oum da Maanal dariya sosai, AA kam sai murmushi yake, shi kaɗai yasan a irin kalar farin cikin da yake a ciki yau. Yayinda yake sake girmama al'amarin UBANGIJI. Wani gefe na zuciyarsa na addu'a da fatan ALLAH yasa Mamy kada ta ɗaga hankalinta akan wannan al'amari dan itace kawai damuwarsa ba wata Saheebar banza da wofi ba.
        Sai bayan sallar isha'i a karo na farko tun bayan bikin AA da Maanal Abah yay kiranyen meeting a sashensa. Tsoro fal zuciyar Mamy kamar tace bazata je ba ita dai, sai dai bazata iya ba, dan koba komai tana matuƙar jin kishirwar rashin ganin Abah na tsawon kwanaki. ALLAH ya jarabceta da son bawan ALLAHr nan kwarai da gaske. Zata iya yin komai akan Abah. Jiki a sanyaye ta kimtsa ta amsa kiran ita da Saheeba. Nuratu nason zuwa Mamyn ta hanata. Sanda suke shigowa kowa ya gama hallara. Abah ne kawai da Oum basu fito ba suna bedroom ɗin Abahn.
       Ganin harda RK da Nuwaira abin ya tsayama Mamy a rai. Amma dai batace komai ba ta zauna. Nuwaira bata taɓa damuwa da zuwa gaida Mamy ba a gidan, dan tunda RK ya bata wasu labarai akan Mamy taji ta tsani matar sosai. Haka family ɗin Darma suke akwai kishin nasu. Akan ɗan uwansu komai zasu iya maka suna son juna. Yanzu ma darajar su Babban Yaya dake a wajen taci Nuwaira ta gaisheta. RK ma dai ya gaisheta dan shi akwai iya taku, yanda Mamy ta iya fuska biyu shima baka isa sanin shike ƙullama Mamyn tsiyataku ta ƙarƙashin ƙasa ba. Suma su Maanal su Yaya Fawzan duk sun mata Barka da fitowa. Tadai danne duk tana amsawa fuska a sauƙaƙe. A haka Abah da Oum suka sakko daga sama suna dariya. Daka gansu kasan baibaye suke da kwanciyar hankali da farin ciki, ga tarin ƙaunar junansu da bata ɓoyuwa a cikin idanunsu kida a gaban ƴayansu ne. Abu mai nauyi ya tsayama Mamy a maƙoshi, haka dai ta danne sa da ƙyar Hari Abah ya zauna Oum kuma ta zauna a kusa da ita tana gaisheta fuskarta da fara'a. Dannewa tai ta amsa, Saheeba ma da tunda ta shigo babu wanda ya kulata ta gaida Oum da Abah........✍️





*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣0️⃣0️⃣


______________


.....Sai a lokacin Nibras ta shigo, duk tayi wani wujiga-wujiga itama ta rame. Itama dai ta gaida kowa sannan ta nema waje ta zauna. Aba ya fara da gyaran murya dan haka kowa ya sake nutsuwa ya bashi hankalinsa. Yay musu sallama da addu'a, kafin ya fara da faɗin,
      “Na tara ku anan ne domin dalilai guda biyu. Na farko nasiha a garemu baki ɗaya. Musamman akan zamantakewar gidan nan da nake ganin tana neman canja salo daga bigiren da muka ginosa na shekaru zuwa yanzu. Hakan baya min daɗi. Muɗin ahali ɗaya ne, da su da aka haifa a gidan, da ku da suka auro a wajena a yanzu duk matsayinku ɗaya ne, domin duk ƴaƴa kuke a wajenmu. Ita rayuwar aure ibada ce, daga ɓangaren mace har na namiji duk wanda ya samu raunin sauke hakkin ɗan uwansa akan ganganci UBANGIJI bazai barshi ba. Sannan kuma masu haihuwa ne, wataran zaku aurar da naku ƴaƴan ko mazan su auro muku. Dan haka ina nasiha a gareku da komai ma a ajiyeshi hakanan ya isa. Mu haɗu mu zauna lafiya da junanmu kamar yanda muka saba. Karna sake jin ko ganin wani yazo daga waje ya tada min tarzoma a gida akan abinda bai shafesa ba. Idan ba hakaba kuma zan ɗauki mataki.”
       A nutse suka shiga bashi haƙuri, tare da neman afuwa. Aba ya cigaba da faɗin, “Abu na biyu hidimar biki dake tunkaro mu. Kowa dai yasan an ɗaurama Fawzan aure a cikin hidimar bikin nan na Ajwaad, bata tare bane saboda exam da take yi kuma Alhamdullah ta kammala. Dan haka zamu fara shirye-shiryen tarewarta nan da kwana goma. Sai dai ba ita kaɗai bace, dan wani alkairin ya sake shigo mana. Shima Fadeel zai ƙara auren......”
     Wani irin kallon Abah Mamy da Saheeba sukai. Cikin rawar murya Saheeba ta ce, “Abah! Fadeel kuma?”.
    Wani banzan kallo Babban Yaya ya jefa mata na ki shiga hankalinki. Abah kuwa sai yay murmushi. A nutsensa ya ce, “Tabbas Fadeel Saheeba, domin ALLAH ya bamu dama mu maza muyi mace daga ɗaya har zuwa huɗu. Sai dai ba hakan na nufin ku da muka fara ajiyewa zamu wulaƙanta ku ba, ko kuma mun ƙara ne dan mu wulaƙantaku. Sam ba haka bane ba, shi ƙarin aure da son mace fiye da ɗaya a jininmu mu maza yake”.
    Ƙasa-ƙasa Maanal ta kalla AA, sai akai sa'a shima kallonta yake. Ganin yanda idanunta suka cika da ƙwalla sai ya shiga girgiza mata kai, tare da yi mata alamar shi dai banda shi. Ba AA da Maanal kawai ba Nuwaira nacan ta tsare RK da ido itama fuska kicin-kicin. Shima dai lallashi yake da ido dan Abah na neman ɓallo ruwa da wannan jawabi gaskiya. Duk abinda suke Abah na lure da su, dan hankalinsa nakan kowa. Sai abimma ya bashi dariya. Amma dai ya danne baiyi ba. Cigaba yay da faɗin, “Amma hakan ba yana nufin kowane namiji nada wannan ra'ayin ba. Wani ƙaddara ce take sakawa ya ƙara, wani auren dole ma ake masa da tsiya-tsiya....” kallonsa Oum tai dan tasan da ita yake kuma yanzu, aiko shima kallon nata yake, ya saki wani guntun murmushi ya ɗauke kansa. Mamy kam wani irin dukanta kalaman Abah ɗin sukayi, suka kuma shiga yimata kai-kawo a zuciyarta da tai nauyi sakamakon ambata zancen auren Fadeel. Oho Abah ya cigaba da maganarsa. “Wasu kuma sakacin matan dake gidan ne ke sakasu son su ƙara ɗin, wani kuma shi dama ra'ayinsa kenan. Kai wani jin daɗin ƙyautatawar da ake masa ma zata iya sakashi ya ƙaro dan farin cikinsa ya ƙaru. To koma dai miye sai mu zama masu tsarkake zukatanmu a komai na rayuwa. Ku dukanku shaida ne kun taso kunga iyayenku su biyu ne, kuma babu wanda zaice ga wata rana tazo suna sa'insa a tsakaninsu, ko cin mutuncin juna, ko wani abu makamancin hakan. Ina son kuyi koyi da su, domin mu haɗu mu gudu tare mu tsira tare. Hakan zai sakamu a farin ciki baki ɗaya, dan gaskiya bana son halin banza. Nayi tunanin a saka musu gini suma, sai dai guri ya ƙure mana gaskiya, dan haka kuyi haƙuri zaku fara zama a tare waje guda zuwa bayan babbar salla za'a sanya aikin nasu suma tunda muna da filin yin hakan. Akwai auren Maimoon itama da Ameer, dan haka sai mu fara shirye-shiryen dukkan abinda ya dace. Ina sake gargaɗin kowa da bana son kowane irin tashin hankali a gidan nan, mu mutunta kammu ayi taro lafiya a tashi kamar yanda aka saba. Idan ba haka ba, duk ta inda wani abu ya ɓullo to lallai Zan hukunta ko wanene da hukunci mai tsauri. ALLAH yay muku albarka. Ya bamu zaman lafiya baki ɗaya. Kuje abinku. Amma Saheeba da Nibras su zauna zanyi magana da su. Kaima Rafeeq zauna”....

  _________★
      
       Nasihar

146 / 213

Chapters