AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   185 / 213

552K to 555K   out of 636.6K words

tsaki.
     “Zanyi maganinki”.
  Mabera ya faɗa cikin zafin zuciya. Tsabar iskanci kawai Maanal tai masa gwalo. Aiko gwalon nan ya ƙona masa zuciya. Sai dai kafin yay magana a fusace Sille da azaba ta isheshi ya ce, “Kai dan uwarku kowa ya ajiye bindigarsa”.
       Da gudu kuwa yaran suka fara ajiye bindugun, to dama tun asali su ɗin rainonsa ne, suna girmama Baban nasane kawai saboda shi, amma Sillen ne asali ogansu, duk da a cikinsu akwai rainon Maberan shima kaɗan. AA daya fahimci Sillen ne lagonsu saiya saka yatsa cike da iya mugunta ya danne jijiyar wuyan Sille da ƙarfi har sai da yay ƙarar ihu. Ya ce, “Ce musu su shiga cikin ɗakunan nan....”
         “Ai ko rufe baki AA bai gama yi ba Sille ya fara musu magiya da faɗin, “Kubi umarninsa ku shige”.
       “Son kana da hankali kuwa?”.
   “Baa! Bazaka gane ba, jijiyar numfashina fa ya riƙe”. Sille ya faɗa da ƙyar. Wato AA yasan takan mugunta, sai ya sake dannawa. Sille ya sake sakin uban ihu har sai da Mabera ya runtse idanu. Ji yake zuciyarsa na tafasa kamar ya sakarma Aba kunamar bindigar hannunsa a cikin kai. Sai dai baya son rasa ɗansa. Dan shine rayuwarsa, shine komansa, ya ɓata shekarun ƙuruciyarsa kaf a rainonsa ne, sai yanzu a gaɓar da zasu ɗauki fansa ya yarda ya salwantar da rayuwarsa da kansa. Kai ina Junaid ɗan Junaid ne fa, wlhy yaron dabanne a garesa da rayuwarsa, saboda shi ya haƙura ya rasa iyayensa, bazai iya haƙurin rasashi ba akan ganganci. Haka yana ji yana gani yaran suka shige cikin ɗakunan kaf ɗinsu. Suka tada Sille tsaye akan ƙafafunsa, suma su Maanal duk suka miƙe, AA yace “Kufita waje.”
Gaba ɗaya Oum ta tattarsu sukai hanyar fita waje, da yake ƙofar a buɗe take Jami'an tsaron na hangosu, sai dai a tunaninsu su Sille na bayansu ne sai duk suka ɗana bindigu sukai shirin kota kwana.
Sai da su Maanal suka gama fita sannan su AA suka koma kan Mabera da har yanzu yake rike da Abah. Da farko yaso turjewa. Yaya Fawzan na ɗaga hannu zai daki cikin Sille da sauri Mabera ya ce, “Wai kuna mantawa ubanku na hannuna ne kuma?”.
    Abah dake murmushi ya ce, “In dai nine karku fasa yi masa duk abinda kukai niyya, na sallama rayuwata kuyi komai da yazo muku. Shi ma idan ya isa ya sallama rayuwar ɗan nasa”.
        “Amma Darma kasan abinda zan iya ko?”.
     “Sanin abinda zaka iya ɗinne ya sani basu dama”. Abah ya faɗa cikin halin ko'in kula, dan ya fahimci akan Sille babu abinda Mabera zai iya yi. Shi kansa AA ya fahimci hakan akan Maberan, shiyyasa yay masa talala da shi. Ba ƙaramin a tashin hankali Mabera yake ba, haka ya saka Aba a gaba suka nufi hanyar ƙofa bisa umarnin su Yaya Fawzan. Su AA da Babban Yaya biye da shi sun tasa Sille da idanu ke cike da ƙasa a gaba suma. Yaya Fawzan ya shiga tattare duk bindigun yaran su Mabera waje guda ya zuba a rigarsa ya ɗaure.
       Abin dariya abin tausai, yaran su Sille dake leƙe ta windows ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Waɗan da sukai kiddinapping kuwa ganin yanda wasan ya juye a wani irin farin ciki suke mara misali, tuni sun shiga fitowa daga ɗakin da aka rufesu Yaya Fawzan ya buɗe musu.........✍️


To jama'a bari mu tsaya nan nima na ɗan huta zuwa Monday idan ALLAH ya kaimu, in sha ALLAHU mun dai kusa mu tsarge. Ko yaya Abah zai kuɓuta a hannun Mabera kuma?, yaya batun gubar da akace Aba yaci. Anum, Nana, Mamy a wane hali suke ciki. Saheeba, ɓangaren su Huznah duk yaya ake ciki? In sha ALLAHU duk zamu tsarge komai a sati mai zuwa da izinin UBANGIJI. ALLAH ji nake kamar na rufe ido littafin ya ƙare😭🤌.
     
      
     



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣8️⃣


______________



........Fitowarsu ta kasance abu biyu a lokaci guda. Farin ciki da tashin hankali. Dan anyi-anyi Mabera ya saki Abah yaƙi. Ya dage akan sai an sakar masa ɗansa sannan. Su kuma su Babban Yaya sunce bazasu saki Sille ba sai Mabera ya saki Abah. Wannan taƙaddama ita ce taja zaren sabon wasa na tsawon lokaci. Suma jami'an tsaron basa son su AA su saki Sille, saboda Sille da ubansa masu laifi ne da aka daɗe ana nema amma ba'a sansu ba saboda fuska biyunsu. Kuma suna son kuɓutar da Abah.
     A cikin wannan halin aka gama tattaro yaransu dake cikin gida, aka kuma shiga binciken jejin tako ina, su Mamy dake cikin wani hali da su Nana da wanda suka daɗe a wajen anyi garkuwa da su Ambulances na isowa aka shiga ɗibarsu aka juya. Dan tabbas suna buƙatar taimakon likitoci da gaggawa. Anyi-anyi a ɗiba su Oum sunƙi, sai da Baba yayi magana. Su baba Sardauna da su RK suna cikin matsannacin tashin hankali. Duk da dai Alhamdullah ga wasu sun kuɓuta. Amma irin wannan zakaga komai baka son ka rasa.
     Makamai sosai aka dinga tonowa a ramuka, da mashina da abinci buhuna-buhuna. Da kuɗaɗe suma a jaka ƙatuwa cikin wata mota. Jami'an tsaron sun fahimci al'amarin babbane gaskiya. Yayinda wasu a cikinsu suka fara amsa kira ta bayan fage daga wasu ɓoyayyun mutane akan komi za'ayi kada su yarda Mabera da ɗansa suyi magana. Hakan na nufin yin maganar tasu zai zama suma tasu zata fito. A yanzu ko basu shirya hakan ba ma kansu.
       Ganin komai zai iya faruwa musamman yanda su Babban Yaya suke a fusace, shi kuma IG baya son su ɗauki doka a hannunsu sai ya umarce su da su bashi Sille. Da farko sunƙi, sai da Baba Sardauna yay musu magana, wannan tarbiyyar su ce ƙin tsallake maganar na gaba da su, shi ma IG ɗin dan basu san ainahinsa bane ba, dan tabbas wannan ƙarfin nasu Mabera ba nasu bane kaɗai akwai masu dafa musu baya daga sama. In ba haka ba ta ina zasu shigo da irin waɗan nan muggan makaman har su raini yara matasa ƙanana kamar waɗan nan dake ƙarƙashin su. Al'amarin fa na aduba ne.
       Wani mugun hankaɗawa AA yay ma Sille gaban IG, sai da ya zube ƙasa aka ɗagashi saboda idanunsa basa ganin komai an cikasu da ƙasa. Amsar Sille a hannun su AA akace su shiga mota abar jejin da su Aban ma za'a taho da shi.
      “Ina wannan gamgan ne ƙafarmu ƙafarsa”. Cewar AA a fusace a kuma dake. Babban Yaya da Yaya Fawzan suka ce, “Wannan magana haka take Auta.”
    RK ma ya matso yace, “Wannan shine batu na gaskiya ranka ya daɗe. Yanda suka baka ɗanshi, shima ya baka Yaya kawai. Idan ba haka ba sai dai ai mutuwar kasko, mu duk mun sallama zamu mutu saboda shi ɗaya”.
       Ba ƙaramin ɗaukar zafi kan IG yayi ba. Dan yau yaga ainahin taurin kai da garada da yake shan ji anacewa zuri'ar Darma nada shi. Gaba ɗaya babu wani tsoro ko shakka a idanun yaran nan. A tsayensu suke zaratan mazaje, da ace yaran nan jami'an tsaro ne a ƙasar nan lallai kowa sai yaci ƙaniyarsa a hannunsu. Dan ba ƙananun jarumai za'ayi ba. Karo na farko aka fara lallashin Mabera, dan ya turje akan idan fa har ya saki Abah to an sakar masa ɗansa ne, in ko ba haka ba to fa sai dai ayi mutuwar kaskon shima ya shirya ya kuma yarda.....

_________★

       Anan cikin jeji anata tirƙa-tirƙa anan cikin gari hankalin mutane a tashe yake sosai musamman duk wani mai alaƙa da zuri'ar Darma. Ga dai wasu an fiddo amma rashin fitowar tasu gaba ɗaya yay matuƙar tadawa mutane hankali. Anata cigaba da tayasu da addu'a.
        Kai tsaye cikin Abuja aka wuce da su Maanal cikin asibitin KK HOSPITAL. Dan danan aka shiga basu taimakon gaggawa musamman ma Mamy, Nana, Anum da wanda akai kidnapping. Shahidah da mijinta da Amal da mijinta itama da tun ɗazun suka iso Abuja tuni sun iso asibitin. Haka suka haɗa Ameerah, Najma, Maanal duk suka rungume suna kuka. Sannan suka koma kan Oum. Su ma su Hajiya Majdiya da tawagar ƴan Kano sun iso Asibitin, dan haka kusan family ɗin Darma duk suna Abuja. Kai wanda ma basa ƙasar tuni labari ya isar musu dan wannan shine labari mafi shahara a yau ɗin tako wane bangare.....

   _______★

       A Kaduna kam kowa yayi mamakin ganin Ammie batai kuka ba, ta dai nutsu waje guda tai shiru kawai. A haka su Nene suka iso asibitin hankalinsu tashe suma da jin abinda ya faru. Daddy da Yazeed ma al'amarin ya tsaya musu a rai sosai. Abin tashin hankali dai-dai lokacin da ake sanar da kuɓutar da su Maanal Nazeerah da ake shirin farama cs sai ga haihuwa gadan-gadan. Dole aka dakata aka shiga taimaka mata, da ƙyar ta haihu ashe yaron babu rai ne. Yaro na gama fitowa kuma ta hau jijjiga. Ya suhanallah al'amarin akwai tashin hankali da tausayi musamman ga Sabuwa da abun ya zame mata goma da ashirin. Ga karaya a hannu, ga gocewar ƙashi a ƙafa. Ga halin da miji ke ciki gana ɗiya. Wani irin hawa da jininta yayi sai gata a ƙasa zube...

        Huznah an samu nasarar tsayar da jininta ita, an mata allurar barci. Sai dai doctor baice komai game da cikin na nan ko baya nan ba. Yadai ce su kwantar da hankalinsu. A wannan halin Sageer da mahaifinsa suka iso, yanda kowa baiga Huznah ɗin ba suma basu ganta ba. Haka suka zauna cikin jimami biyu suma. Na al'amarin dake faruwa a ƙasar da wanda ya shafe su na Huznah....

_______★

        Tunda Doctor ta tafi tabar Hajiya Basariyya a ƙofar gidanta taji ta kasa motsa ƙafarta. Haka ta cigaba da tsaiwa ita ba gunki ba ba kuma mutum mai rai ba. Sai da taji hajijiyar dake jujjuyawa da ita na neman zubar da ita a ƙasa sannan ta daddafa ta shiga mota, kanta ta kife a steering tai shiru tsahon lokaci. Kafin ta tada motar, da farko rasa ma inda zata dosa tayi, sai da ta samu waje ta tsaya tai kiran maman Yaseerah. Harta tsinke bata ɗaga ba, dan hakan ta ɗauki hanyar Zarian.
         Tunda ta shigo maman Yaseerah ta miƙe tana kallonta, dan suna zaune ne a falo ita da yara suna cin abinci hankali kwance duk da kuwa sunji halin da ƙasar ke ciki akan zuri'ar Darma. Amma tunda ahalin kishiya ne sai abin bai wani taɓata ba ita kam balle damunta. Duk da kuwa akwai Najma da ko ba komai ƴa ce ga mijinta. Yaran kuwa duk da sun shanye a ransu suna cikin damuwa akan ƴar uwarsu. Ai jini ba ƙarya bane ba, duk da uwarsu na rabasu da ƴan uwan nasu shi tuwo dai tuwo ne ba'a sake masa suna. Najma dai jininsu ce dole suji rashin daɗi idan wani mugun abu ya sameta.
      “Lafiya kuwa na ganki haka? Badai wannan abun dake ta yawo bane ya birkitaki?”. Maman Yaseerah ce ta faɗa tana kallon Hajiya Basariyya bayan sun shiga bedroom saboda yara.
   Sai da Hajiya Basariyya ta kai zaune a bakin gado hannayenta duka biyu a saman fuskarta ta furzar da zazzafan iska a bakinta... Maman Yaseerah ta sake faɗin, “Ke ko Basariyya ki rufama kanki a siri, har miye tsakaninki da wasu zuri'ar Darma da kikabi kika birkita kanki haka. Dama Huznah ta auri jininsun ne ma sai ace. Kada ki manta Yaseerah da ƴar uwar mijinta ke ciki wlhy banji komai ba tunda ba sonta suke ba balle ke......”
       “Haba wai mi kike faɗa haka ne? Ki ƙyaleni da abinda ya dameni dan ALLAH. Kin dameni da wani maganar zuri'ar Darma zuri'ar Darma ni ban san miya faru da su ba, tawa ta isheni ma.....”
       Kallonta kawai Maman Yaseerah take yi a firgice, ganin hawaye share-share a fuskar Hajiya Basariyyan, “Basariyya kuka fa kikeyi? Wai mike faruwa ne?”.
          “Miye ma bai faru ba, na kai Huznah anyi allurar nan amma ban san yaya akayi ba ta ɓoyo waya ta kira Daddynta ta sanar masa inda muke.....”
     “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ke ko ya akai kikayi wannan gangancin haka? Yanzu ina Huznar?”.
     “Sun ɗauke ta shi da Yazeed, na tabbatar asibiti suka tafi kaita”.
     “Yazeed!? Shi Yazeed ɗin dama ya samu lafiya ne?”.
    Kasa bata amsa Hajiya Basariyya tayi, dan hankalinta baya anan gaba ɗaya. Shiru itama maman Yaseerah tai tana tunani, zuwa can ta furzar da iska tare da faɗin, “Ihmm nace ba, Hajiya Basariyya bai kamata ace nan kika tahoba ai gaskiya. Dan kinga shi Alhaji Usman zai iya tunanin dani aka haɗa wannan al'amarin, alhalin kuma ban san komai ba gaskiya. Ya kamata ki tashi kije dan nikam ban shirya rasa aurena da ƴayana ba. Nima matsalolin gabana sun isheni. Dan yanzu haka su Yaseerah na hanyar tahowa Zaria”.
     Sosai Hajiya Basariyya kema maman Yaseerah kallon mamaki, amma sai ta daure ta ce, “Yanzu ni kike kora Hajiya Jummai?”.
      “A'a nifa ba korarki nake ba Basariyya kada ki canja min magana. Amma dai kin san halin mazan nan namu ba sai na zauna miki bayani ba. Kidai je ɗin idan na samu lokaci zan shigo sai mu tattauna. Dan wlhy bana ma son Abban Yaseerah ya shigo ya sameki a gidan nan akwai babbar matsala. Sannan maganar kuɗina dan ALLAH kiyi ƙoƙarin a cikin satin nan na samesu akwai uzirin daya taso min nima gashi duka abinda ke hannun nawa na tarkata na baki”.
     Ai kaɗan ya hana zuciyar Basariyya fitowa waje. Maman Yaseerah ta miƙe ta fita a ɗakin, dole Hajiya Basariyya ta miƙe kamar wadda ƙwai ta fashewa ta bita a baya..........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣9️⃣


______________



.........Anyi hannun karɓa hannun bayarwa tsakanin Mabera da jami'an tsaron akan Abah da Sille. Duk da dai bai yarda ya bada Abah ba sai da ya shiga mota shi da ɗansa. Kafin ya shigan ya kalla jami'an tsaron da su Baba Sardauna fuska da murmushi ya ce, “Ku kwantar da hankalinku bazan taɓa kashe Aliyu ba duk da shi a baya yayi iƙirarin kashe ni akan laifin da ban aikata ba. Ba buƙatar haka dan shi kam babu abinda ya rage masa sai jiran mutuwar tasa in har ya tabbata matarsa Kamila ta bashi gubar data saya da kuɗinta domin sa. Na yafe masa a yanzu, sai dai ku sani zan dawo ɗaukar fansar ƴayana akan ɗansa Ajwaad....” ya hankaɗa Abah ya wani irin ja motar da masifar gudu. Da gudu wasu a cikin jami'an sukayo kan Abah, wasu kuma suka shiga motoci akabi bayan su Mabera.....
     Matuƙar tashin hankali su Baba Sardauna sunji akan batun wannan guba. Hakama su AA da suka zo da gudu suka kama Abah. Suna tada shi tsaye akan ƙafafunsa Abbu ya da zancen guba yafi tsayama a rai ya matso ya buɗe idanun Abah, ya kuma ɗaga ƙasan harshensa ya duba. A rikice ya ce, “Mutumin nan fa da gaske yake akwai guba a jikin Aliyu harta fara nuna kanta. Oya ba ɓata lokaci maza muje”.
     Lallai tashin hankali ba'a saka maka rana, ahalin Darma sun shaida wannan salla. Ana murna an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kafin wani dogon lokaci an wuce da su Aba gaba ɗaya cikin jirgi mai saukar angulu. Sauran jama'an da aka bari a jejin kuma suna tattare komai da aka samu. Ga yan jarida har sun ƙaraso sunata ɗaukar komai. Dole kafin isowar jirgin aka tsaida motoci a kan titin asibitin KK domin samawa jirgin wajen sauka. Su Maanal da dukkan ahalin Darma sun fito suma wajen asibitin sunata kuka harma da mutane masu majiyyata. Dan labarin akwai guba a jikin tsohon ambassador Aliyu Darma harta fara yawo. Yanda al'amura suka gudana da batun gubar nan ya tsayama Abah a zuciya, dama ga waɗanda ya jima yana tarama zuciyarsa akan Mamy tsahon lokaci. Zancen lalata mahaifar Oum da kashe masa yaro da Mabera yayi duk sai suka taru suka tsaya masa a ƙahon zuciya. Dan da nan jininsa yay wata irin hayewa ta tashin hankali. Lokacin da ake fiddoshi a jirgin ai komai ya rikice. Da gudu ma'aikatan asibitin suka fita da gadon ɗaukar mara lafiya, yanda ƙirjin Abah ke wani irin ɗagawa da sauka tamkar numfashin nasa zai bar gangar jikinsa dole ne hankalin duk wani mai imani ya tashi. ALLAH sarki Oum sai a lokacin ta yanke jiki ta faɗi. Dama tunda aka baro jejin da su bata furta ko a ba na magana. A take hankalin kowa ya ƙara tashi, itama aka kwasheta zuwa ciki.
      ALLAH sarki

185 / 213

Chapters