Author : Bilyn Abdull Category : Romance
hararar RK ɗin yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya miƙama Yazeed hannu cike da shaƙiyanci yana faɗin, “Babban Yaya barka ƙanwa ta miƙe. ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba”.
Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK ɗin ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin RK fa bawai yasan ainahin alaƙarsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba ɗaya yake masa kenan. Daurewa yay ya ɗan sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa da, “Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ƙoƙari ai sai fatan alkairi a gareku”.
“Doctor!”.
Manaal ta faɗa a hankali cikin suɓutar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yunƙurin bata amsa Waleed yabata amsar da “Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya baki lafiya ko warke gaba ɗaya ki daina wannan ciwon ”.
Sake dai kallon RK ɗin Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a ƙirjinta da sauri-sauri kamar ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai shiru dan ita kam bata kuma san abin faɗaba bayan hakan. Ɓoyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta buɗe idanunta a kansa dan yanda yake magana can ƙasa-ƙasa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko ɗaya tayi da baki, sai jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turniƙe Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai. Rai a ɓace ya ɗan duƙo shima gareta murya can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kina son cin wani abu Miss?”.
Idanunta ta ɗan maida garesa, “Yaya su Didi na zuwa da abinci ai”. Ta faɗa a hankali dan muryan baya fita sosai. Cikin jinjina mata kansa ya ce, “Na sani, ko ɗan fruit haka baƙya so? Ko wani abu bayan abincin?”.
“Zanci apple to, amma green”.
“An gama Baby”. Ya faɗa cikin raɗa ta yanda ita kaɗai taji sai RK dake kusa da su sosai. Saurin kauda kanta tayi, sai kuma ta kalla sashen da Ammie da Daddy suke. Ganin hankalinsu na kan su Waleed yasa ta sauke ajiyar zuciya. RK ta ɗan kalla, sai taga shima yay wani kicin-kicin da fuska yanata rubutu a file ɗin ta. Tana ƙoƙarin janyewa ya ɗago nasa idanun sai caraf a nata. Wani miskilin murmushi ya sakar mata tare da sake duƙowa kusa da ita gab, cikin raɗar shima ya furta, “Apple yana cikin abinda bazaki ci ba a yanzu wife to be, dan haka kada ki ma wahalar da Yayanmu”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya sai kuma ya kalla Yazeed ya sakar masa wani ɗan iskan murmushin rainin hankali.
(Nikam mike damun waɗan nan?) Maanal ta faɗa a zuciyarta dan tama rasa yanda zata masalta al'amarin nasu. Tana fama da kanta sunzo sun sakata tsakkiya da shirmensu ya ilahil alamin. Shigowar su Shahidah ne ya taimaketa. Cike da farin ciki sukazo suka rungumeta suna hawayen daɗin ganinta. Itama farin cikin take ji a ranta matuƙa. Nanfa suka shiga nan nan da ita. Sai kawai Daddy da Ammie suka fita tare da su Waleed. Dan ba'aso suyi yawa a ɗakin sam. A hakan ma dan RK najin nauyinsu shiyyasa baiyi magana ba. Ganin Yazeed bashi da niyyar fita a ɗakin RK ya dubesa cikin danne kishinsa ya furta, “Yauwa babban yaya inama son magana da kai. Dan akwai alluran da za'a mata zuwa 6pm naga kamar babu shi anan ya ƙare, ko zaka samo mana shi a pharmacy please?”. Yayi maganar ne idanunsa a kan takardun hannunsa yana kuma ɗan tafiya, dan haka baka isa gane ainahinsa ba kai tsaye. Bin bayansa Yazeed ɗin yayi batare da yace komai ba. Maanal ta bisu da kallo ƙasa-ƙasa.
Da taimakon yayun nata biyu ta ɗan ci abincin, nurse ɗin dake kula da magungunan ta ta shigo ta bata. Babu wani jimawa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Dama haka doctors ɗin suke buƙata ta dinga barci isashe dan zuciyarta da brain ɗinta su samu nutsuwa.........✍️
_🥱Team RK & Team Yazeed ina miƙo gaisuwar ban girma😌👌._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣4️⃣
.......A ɓangaren Yazeed da RK kam suna fita Yazeed ya tsaya cak. Kallonsa RK ya juyo yanayi, sai kuma ya saki lalataccen murmushi yana dawowa da baya inda Yazeed ɗin yake. “A'a babban Yaya yaka tsaya kuma? Ya kamata muje ko”.
Murya a sarƙe Yazeed ya amsa masa da, “Rubuta sunan alluran ka bani anan. Sannan ka daina wani kirana Babban yaya dan ban san alaƙar data maidani yayanka ba”.
Hannu RK ya kai ya shafo bayan ƙeyarsa yana murmushi irin na ƴan duniya shi a dole irin yaji kunyar nan. “Haba bazan iya kiranka da sunanka ba gaskiya. Ko a bayan ma kafin na fahimci kai Yayan Maanal ne yasa nake kira. Yanzu kam dana sani sam bazan iya hakan ba”.
“Ni ba yayan Maanal bane kawai mijin da zata aura ne”. Yazeed ya faɗa a gadarance. Wani irin mugun dukan zuciyar RK furucin yayi, amma sai ya dake cike da basarwa ya furta, “Irin wannan wasan ai saika saka zuciyata ta buga babban yaya, kona ɗauka baka son aura min ita ne. Please mubar zancen haka ga sunan allurar”.
Yana miƙa masa ƴar takardar da yay rubutun yabar wajen da sauri dan baya buƙatar sake jin wani furuci daga Yazeed ɗin bayan wanda yaji. Shifa wlhy san Maanal yake. Kuma baya jin zai iya barma Yazeed ɗin koma mi za'ayi. Sai dai suyi yaƙi mai rabo ya ɗauka. Babu ruwansa da ƙarfin alaƙarsu kowa ya iya allonsa kawai ya warke.
Da wani irin kallo Yazeed ya bisa kawai batare da ya sake cewa komai ba shima yabar wajen...
_________★
Ganin jikin Maanal Alhamdullah Ammie ta matsama Yazeed komawa kan saboginsa. Shima Daddy ta damesa da roƙon ya koma Kaduna kada su shiga hakkin sauran matansa. Yazeed dai ya jitane kawai. Dan ya ƙudura a ransa bafa zai tafi ya bar Maanal a hannun wannan kuren likitan ba RK. Dan haka ƙafarsa ƙafarta idan ta samu lafiya. Shi kam Daddy sai da sukai ƴar rigima sannan ya yarda zai wuce Kaduna ɗin, amma kuma dole sai tare da ita, yace nan da kwana biyu ta dawo ta sake dubata tunda dai ga Nene gasu Shahidah. Ita dai Ammie tace hakan yafi mata duk da bata so hakan ba, dan tana son kasancewa da Maanal ɗin itama amma babu yanda ta iya haka ta haƙura suka tafi bisa shawarar Nene dan itama tafi son yaje ga sauran matansa kar abin ya zama wani daban kuma. Yazeed dai ya nuna mata akwai aikin da yake anan ɗin dan gobe ma zaiyi zama da masu Companyn Mawaad ne.. Wucewar Daddy da Ammie kamar ya buɗema Yazeed da RK wani filin TAKUN SAƘA ne, dan kuwa kowa ya riƙe wuta yana baje kolin hajarsa. Yayinda ita kuma take nuna bama ta fahimci inda suka dosa ba su duka. Tun suna abin a kaikaice har ya fara bayyana kansa sosai, dan takai da Yazeed ya shigo duba Maanal tsalam zakaga RK a ɗakin ya shigo kamar wanda aka jeho. A wajen su Amal taji duk yanda akai aka kawota Abuja. Nan ta fahimci RK yaje gidansu ne sai ya kasance a dai-dai lokacin da take a halin taimako. Hakan ya kwaranye mata mamakin ganin nasa anan. Sai dai kasancewarsa likita bai bar bata mamaki ba. Dan har sukai zamansu a Jos suka gama bai taɓa nuna musu ga aikinsa ba. Kai ita tama sha yin gulmarsa da jifansa da kalmar mara aikinyi, sannan a tunaninta shi ɗin ɗan Jos ɗin ne ma ai.
Yau Nene ta ɗan tashi da ciwon kai, dan haka ta wuce gida dan ta ɗan huta. Dama itace ke kwana da ita anan, da safe zuwa goma sai ta wuce gida idan su Amaal sun zo, sukuma suke yini da ita anan har sai dare idan Nenen ta dawo sukuma sai su wuce. Daga Nene har Amal suna a gidan Shahidah ne yanzu, dan bayan wucewar su Ammie sai itama Nene ta koma can gudun karta zauna ita kaɗai anan ɗin duk da ma ƙarfin zaman nata a asibitin ne dai. Bayan wucewarta Maanal ta tashi a barci, da taimakon Nurse tai wanka, kafin ta fito an gyara ɗakin, tana ƙoƙarin zama a bakin gado take tambayar Nurse ɗin, “Nene fa?”.
Amsa ta bata da, “Doctor Rafeeq ya kaita gida ta huta kanta na ciwo”.
Shiru kawai Maanal tayi, mamakin RK na sake kasheta, gaba ɗaya fa yabi ya kanainaye mata ƴan uwa kowa ya sanshi. Yanzu haka kullum Waleed da Hameed na manne da shi har sai da suka wuce aka samu lafiya. Haka idan su Didi sunzo zaizo ya zauna wai yazo gaishesu duk hararar da take masa baya ma nuna ya gani. Itako yaya zatai da wannan bawan ALLAH. Babu ma abinda ke damunta sai zaman marina da suke tsakaninsa da Yaya Yazeed, hatta gaisuwa sama-sama sukeyinta yanzu ma ta rasa mike damun kawunansu haka.... Shigowarsa ɗakin shi da Doctor Ranjet ya katse mata tunaninta, da sauri taja hulanta ta saka tana ɓata fuska. Ɗauke kai RK yay kamar bai ganta ba yama hau duba magungunanta. Shi dai Dr Ranjet matsowa yay kusa da ita yana tsokanarta, haka yake mata dan shi mutum ne mai wasa sosai. Dole ta daure ta ɗan masa murmushi dan turancinsa na sata nishaɗi, kullum gaya mata yake ita ɗin mai sa'a ce. Ruhunta nada tauri sosai, saboda da wahala kaga mai irin matsalarta ya shiga irin yanayin data shiga kuma ya tashi ya cigaba da rayuwa, dan shi kansa a randa aka kawota asibitin baimayi tunanin zata kai washe gari a raye ba. Dai-dai Dr Ranjet na ƙoƙarin mata wata allura da kullum a irin wannan lokacin ake mata RK ya ƙaraso wajen. Kujera yaja ya zauna yana mai zuba mata ido dan sai ɓata fuska take tana kallon allurar. Amma tana juyowa suka haɗa ido da shi sai ta ɗaure fuska ta fiske abinta. Kansa ya kauda kawai yana murmushi baice komai ba. Allurar akai mata, ana gamawa ta kwanta saboda jiri take sakata. Idonta a rufe har fin mintuna biyar Doctor yay mata sauran abinda ya rage har ya fice da kusan mintuna biyar sannan ta iya buɗe idanunta da suka kaɗa sosai. A kansa ta saukesu, sai kuma ta janye da sauri ganin shima ita yake kallo.
“Nifa bana son haka, azo a tasa mutum gaba ai haramunne ma wannan”.
Murmushi ya saki mai faɗi yana mai janye idanun nasa daga gareta. Sai kuma ya furzar da huci kaɗan a hankali ya furta, “To amin afuwa sarauniya. Sonki ne kawai ke neman zubar dani amma ke kina ɗaukar komai wasa”.
Shiru ta masa bata tanka ba. Shima sai ya bar zancen ya kama wani daban. “Ni kam banga Zizaah da Aneesa ba, ko basu san baki da lafiya bane?”.
Kansa ta jinjina masa alamar eh.
“A gaskiya ya kamata su sani. In sha ALLAHU anjima zan kirasu na sanar musu kuwa”.
“Ni dai ban saka ba”.
Idanu ya ɗan waro waje. “Saboda mi?”.
“Ba saboda komai ba, kawai dan mutum na ciwo sai anta talla da shi. Yanzu miyyasa ka kai Nene gida ma?”.
“Saboda taje ta huta. Ba su Didi na zuwa ba”.
Hararsa ta ɗan yi, kafin tace, “To idan kuma ina buƙatar wani abu fa kafin su suzo?”.
“Ba gani ba sai ki sakani nai miki. Ai shiyyasa nazo nan na zauna a madadin Nenen. Faɗi mi kike buƙata gimbiyar Rafeeq?”.
Baki ta buɗe zatai magana tsulum sai ga sallamar Yazeed. Kafin ma su gama amsashi ya riga ya shigo. Kallon kallo sukaima juna shi da RK ɗin sai kuma kowa ya janye cike da basarwa. Takowa yazeed ɗin ya ƙarasa yi ta ɗayan side ɗin. Saboda neman magana sai ya zauna a bakin gadon kusa da ƙafafun Maanal. A hankali ta matsar da ƙafafun nata dake cikin bargo, dan RK ya wani zubama ƙafafun nata ido kamar mai kallon television duk da a lulluɓe suke a bargon. Cikin dauriya ta gaida Yazeed. Ya amsa mata idanunsa kafe a kanta....
“Yaya jikin naki?”.
“Na samu sauƙi Yaya. Ya aiki?”.
“Alhamdullahi. Tunda kin samu sauƙi sai sallama kenan ko?”.
Maimakon amsa saita sakar masa ɗan murmushin yaƙe kawai. Abinda ke hannunsa ya miƙa mata. “Ga abinda kikace kina so, shine maimakon ki sanar min kika kama faɗama su Shahidah ko? Bana gaya miki duk abinda kike buƙata yanzu ki sanar min ba. Domin nine da hakkin yimiki shi ai, kwana nawa ya rage mana zama ma'aurata”.
Kanta kawai ta jinjina masa da faɗin, “Nagode”. Yayinda RK ya saki wani ɗan iskan murmushi yana sake yin balance a kujerar. Sai kuma ya wani laɓe baki yana kauda kansa. Duk Yazeed na lure da shi, dama kuma yayi furucin domin shi ne.
“Ina Nene?”.
“Taje gida bata jin daɗi”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya. Ai tana ƙoƙari ma ga jikin girma. Su su Shahidah fa?”.
“Basu ƙaraso ba, suna hanya dai sukace”.
“Okay yayi”.
Ya faɗa yana zaro wayarsa da ake kira. Ɗagawa yay tare da kaiwa kunne, sai kuma ya miƙe saboda masifar da Mamma ke masa daga can, dan har ita Maanal ɗin taji furucinta na farko ma. Sassanyar ajiyar zuciya Maanal ta sauke ƙasa-ƙasa dai-dai Yazeed ɗin na fita. Hakan yasa RK tuntsurewa da wata dariyar wulaƙanci. Kallonta ta maida garesa cikin mamaki. Shiko ya wani ɗage mata gira cike da neman rigima ya ce, “Amma dai kina matuƙar tsoron wannan yayan naki fa. Irin wannan sauke ajiyar zuciya haka”.
Ƙin kulashi Maanal tayi, sai dai maimaita kalmar tsoron daya ambata tanama Yazeed ɗin take a zuciyarta. Shima bai sake cewa komai ba ya kawo hannu zai ɗauki abinda Yazeed ɗin ya bata tai saurin ɗaukewa tana ɓata fuska.
“Wai kai idan baka shiga rayuwar mutum ba da abinda ba'a sakaka ba baka jin daɗi ne halan?”.
“Oh haka kike fassarani ashe?”.
“Hummm”.
Kawai tai shiru. A ransa yace miskilatu kenan. Magana fal cikinta amma bata son yi. A fili kam zaiyi magana sai ga Yazeed ya dawo. Bai fasa ba ya cigaba da faɗin, “Birthday na ya kusa mi zaki bani as gift?”.
“Humm”.
Maanal ɗin ta faɗa idonta akan Yazeed daya iso gaban RK ɗin rai a ɓace. Shi kuma yayi kamar bai gansa ba. Cikin fusata ya ce, “Malam ina son magana da kai”.
Sai lokacin RK ya dubesa. Sai kuma ya nuna kansa cike da rainin wayo wai shi? A kausashe Yazeed ya ce, “Eh”.
“Okay to Bismillah ai gani. You are free zaka iya maganarka kawai”.
“Ba'a nan ba”.
Yanda yay maganar a fusace ya saka Maanal dake saurarensu kallon Yazeed ɗin a karo na farko. Sai kuma ta kalla RK dake wani shegen murmushi baida alamar motsawa balle aje ga batun tashin. A hasale Yazeed ya sake buɗe baki zaiyi magana Shahidah da Amaal sai mijin Shahidah ɗin sukai sallama. Dole ya haɗiye maganar yana mai furzar da huci, sai kuma ya juya suka fara gaisawa da mijin Shahidah. Shima RK miƙewa yay yana amsa gaisuwar su Amal, kafin ya juya ga mijin Shahidah ɗin shima suka fara gaisawa. Daga haka ya fice a ɗakin. Hankalin Manaal naga su Amal Yazeed shima ya sulale ya fita, sai da ta ɗago da nufin yin magana dashi kawai taga wayam. Waige-waige ta fara cikin mamaki, cikin tsokana Mijin Shahidah ya ce, “Oh in dai samarinki ne ai sun fice auta”.
Fuska ta ƙwaɓe kamar zatai kuka ta ce, “Kai Uncle Sadeeq”.
Dariya suka sanya mata su duka....
★★★
Sam RK bai san Yazeed na bin bayansa ba. Dan hankalinsa ma nakan wayarsa fuskarsa da murmushi saboda saƙon da yake karantawa. Jin ansha gabansa ya tsaya cak tare da ɗagowa. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Yazeed ɗin kaikace zakuna ne jirace da juna a filin daga.
“Doctor ina son maka gargaɗin farko da ƙarshe akan yarinyar nan”.
“Saboda mi?”. RK ya faɗa yana tsatstsare Yazeed da ido. Shima