AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   170 / 213

507K to 510K   out of 636.6K words

mata, har tana jin bazata iya haƙuri ba sai taje ta samu Ameerah.
        Miƙewa tai ta sauka downstairs ɗin, dan tunda akace Ameerah keda ƙasan bata zama. Iyakarta bi ta fita. Ameerah na aikinta bluetooth a kunnenta tana jin karatun Alkur'ani Saheeba ta faɗo mata kitchen ɗin. Da farko ita tsoro ma taji, dan har sai da ta sauke ajiyar zuciya ma. Sanin babu mai shiga harkar wani tsakaninta da Saheeban yasa ta maida kanta ta cigaba da aikinta. Hakan ya ƙara saka zuciyar Saheeba zafafuwa. Dan haka cikin kaushin harshe ta ce, “K bakiga mutane bane?”.
     Banza Ameerah tai mata, duk da kuwa ta jita sarai. A fusace Saheeba ta ɗan fincikota baya ta hanyar kama mata veil. Sai kuma a fusace ta ce, “Amma ke ƴar rainin wayo ce ko? Ina magana kina wani shareni”.
        Kallonta Ameerah tayi ido cikin ido, sai kuma ta girgiza kanta cikin nutsuwa ta ce, “Ai bamma yi zaton kin san akwai mutum a kitchen ɗin ba, sannan da kika shigo ke kikace ni kuma nasan ba ƴarki bace ta fari. Zan baki shawara kodan mu kasance muna ganin mutuncin juna ki dinga sanin ta yanda zaki mu'amulanceni kamar zai fi miki sauƙi. Sunana Ameerah, sannan in zaki shigo inda nake ko ya kasance muhallina ki min sallama. Na tabbatar miki zan amsa, kuma zan darajaki har na cigaba da kiranki da sunan dana saba wato Aunty Saheeba”.
           Wani irin kallo Saheeba ke mata, sai dai ta kasa magana dan mamaki, Ameerah dai data sani mai shiru-shiru ce bakinta ya buɗe haka. Lallai ai dama barewa batai gudu ɗanta yay rarrafeba ai, jinin Hajiya Shuwa ce fa....
     Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ameerah daya zama sanadin katsewar tunanin Saheeba. Ganin yanda Ameerahn tai wani ƙayataccen murmushi da faɗin, “Amincin ALLAH ya tabbata a gareka My!. Badai har ka sauka ba?”.
      Daga can Babban Yaya ya ce, “Gani ma a gida My Soha”.
   Wani kalar waro idanu Ameerah tai da faɗin, “Are you serious Yayana?”.
         Babban Yaya dake murmushi har Ameerah na jiyo sautinsa ya ce, “Leƙo ki gani”.
       Fittt Ameerah ta fice a kitchen ɗin cike da farin ciki tabar Saheeba da ƙamshinta baki a buɗe.........✍️



*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣2️⃣


______________


........A kofar babban falonsu kuwa Ameerah ta samu Babban Yaya, ai bama tasan ta wani daka tsalle ta maƙalesa ba. Dan wlhy da gaske tayi kewarsa kwana biyu kacal. Wani irin farin ciki mai narka zuciya ya mamaye zuciyar Babban Yaya. ALLAH kaɗai yasan yanda yake son yarinyar nan, dan akwana goma kacal datai a gidansa ta dasa wata soyayyarta mai zafi a cikin zuciyarsa. Tana riritashi da masa dukkan abinda yake so daga matarsa. Duk wani gurbi da giɓi da Saheeba ta bari yake masa ciwo da jin ƙishirwar samu a cikin rayuwar aure Ameerah na ƙoƙarin kwaranye masa su a cikin kwana kaɗan. A cikin kunnenta ya raɗa mata, “I miss you my Soha”.
       Maimakon bashi amsa sai ta ƙara ƙanƙameshi kawai. ALLAH ta manta da wata Saheeba a kitchen. Sai da Babban Yaya ya ɗagota yana ƙoƙarin sumbatarta Saheeba dake fitowa karaf a idonta zani ya harɗeta tana neman faɗi, sai dai ALLAH ya taimaka ta dafe bango da ƙyau a maimakon faɗuwar tata sai flower base ta faɗo daga inda akai ado da ita a hanyar fitowa kitchen ta faɗi, hakan ne ya fargar da Ameerah da Babban Yaya. Kallon ido cikin ido Saheeba da Babban Yaya sukama juna. Harga ALLAH baiso hakan ya faru ba, koda yake fushi da ita da son hukuntata babu tsarin cimata fuska irin haka a ransa. Dan haka yanzun ma sai ya janye idanunsa a cikin nata slowly, kafin ma yay wani yinƙuri itama Ameerah da hakan bai mata daɗi ba dan bazata so ai mata ba harta zame jikinta daga nashi. Sai dai kafin ta fita gaba ɗaya Saheeba ta wuce sama da sauri-sauri. Sai kawai baban yaya ya wani basar ya sake riƙo Ameerah ya rungume.
         “Faɗa min sau nawa kikai missing ɗina?”.
    Ganin ya basar itama Ameerah sai ta basar, cike da shagwaɓa ta ce, “Sau dubu ɗari ba adadi”.
     “Anya babu ojoro a wannan lissafin my Soha”.
        Ƴar dariya tayi da faɗin, “Da gaske fa”.
      “To ina godiya. Muje nai wanka sauri-sauri kinga ana kiran magrib”.
    Babu ja'inja ta ce, “To amma fa ina girki, ai min afuwa kaje yanzu zan ƙarasa na sameka”.
      Cikin gamsuwa ya ce, “Okay tauraruwar mijinta.” yay maganar yana ja mata hanci. Murmushi tayi tana sumbatar hannunsa. Shima sai ya murmusa kamar ba Babban Yaya ba ya nufi hanyar upstairs. Ita kuma tai kitchen...

      Koda ya haura saman kai tsaye sai ya nufi ɗakin Saheeba dan bata a falo.  Sai da yay knocking, jin babu alamar za'a amsa masa balle buɗewa ya tura ƙofar ya shiga. Zaune ya sameta a bakin gado tana kuka. Ya tsaya kawai yana kallonta tsahon minti ɗaya. Itama kallon nasa take tana hawayenta. Ganin yaƙi ƙarasowa inda take sai ta miƙe ita taje gareshi, gabansa ta tsaya ƙiƙam, muryarta na rawar kuka ta ce, “Yanzu Daddyn Naufal kana ganin na cancanci duk irin wannan wulaƙantawar daga gareka?”.
      Sosai Babban Yaya ya sake haɗe fuska, a dakensa ya ce, “Sai ki gaya min yaushe na wulaƙanta ki? Ko rungume matata ya zama laifi saboda kar ranki ya ɓaci Aunty na”.
        “Kayi haƙuri ni bance haka ba, kuma ni ba Auntyn ka bace. Amma kaji tausayina kamin adalci Ya Fadeel. Nasan nayi kuskure amma nayi alƙawarin gyarawa. Yanzu dan ALLAH ya kake so yarinyar nan ta ɗauke ni? A ranar fa da zaka dawo wajena kabar garin nan, sai yau kake dawowa, maimakon kuma kazo ka sauke haƙƙina sai ka tsaya a wajenta saboda tana amarya”.
       Sosai Babban Yaya ya taɓe baki da faɗin, “Look bana son damuwa daga shigota okay, sannan ki bama kanki dukkan amsar data dace ai, ki kuma duba lokaci yanzu nata lokacin ne, ruwanki ne ki gyara ki amfani da lokacin da zaizo nan gaba, ruwanki ne ki cigaba da shirme ki rasa gaba ɗaya. Dan ba damuwata bace na sake wata tafiyar a ranar girkin naki mtsowww!!!!”. Ya juya ya fice abinsa. Rashin iya maganar Saheeba na ƙona masa zuciya. Sam bata san yanda ake tauna magana kafin a fitar da ita ga miji da laushi ba. Kawai duk abinda yazo mata kan harshe furtawa take, shi kuma baya son raini, shiyyasa ko iya zama hira da ita baya sonyi, amma wlhy da zata san irin maganar da zata dinga masa da mutuntawa data samesa fiye da yanda take so, dan duk da auren haɗi akai musu zuwa yanzu jini ya gauraya da ruwa tunda ga ƴaƴa.......

__________★

         Sai da Rabilu yaci yay nak da abinci ya sha lemon kwali sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya fuskanci Sen... Bukar da ƙyau. Sen... Bukar yay gajeren tsaki. Dan tun ɗazun ya ƙosa Rabilun ya kammala. Cike da takaici ya ce, “Kai idan ka kama abinci baka ji baka gani kamar wani jinin yunwa?”.
      “Ranka ya daɗe miye maraba? Ai jinin yunwar ne. Rabona da abinci lafiyayyen irin wannan tunda nabar gidan nan. Kai dai ALLAH ya rabamu da faɗuwar baƙar tasa kawai ranka ya daɗe. Yanzu dai gani nayi darrr mikake so? Kasan ni ko wuta kace na faɗa ALLAH kafin ka rufe baki na gama ma cinyewa a cikinta”.
      Wata dariyar ƙeta Sen... Yayi, ya ce, “Ja'iri, lallai kaji wuju-wuju Rabilu. Shiyyasa gaka nan ko'a ido duk ka zama wani kwashe wuya kamar mariƙin lema. To manta dai komai ya wuce. Yanzu sabon aiki ne ya tashi, amma kuma tsoho ne daya kwanta za'a tayar.”
    “To to ranka ya daɗe yanda kace ai haka za'ayi, na gabashi ne? Ko kudanci? Ko arewaci?”.
        “Batun yarinyar nan ce da ɗan gidan Darma ya aura, ina son kayana su dawo hannuna koda tsiya koda tsiya-tsiya. Dan haka kawo shawara”.
    Sosai Rabilu ke jinjina kai kamar tsohon ƙadangare, sai zuwa can ya ce, “Turƙashi, ranka ya daɗe wannan fa tamkar tado da yaƙin duniya na uku ne lokacin yinsa bai kai ba. Ka sani na sani wannan yaron ba ƙyale bane ƙyalle ne. Shifa baya tsoron TAHO MU GAMA! a mutu ko'a rayu akan mutuncinsa zai iya sallamawa rayuwar. Balle wannan yarinyar naji gagarumin tarihinsa da ita. Tsohuwar zuma ce, sannan renonsa ce ta ainihi. Dan tare uwar goyonsu ta goyasu, ta kuma yi musu tawai. Ba wannan bane ma matsalar, saboda yanda suke son juna bayan an musu sharrin rabuwa tazo sunyi shekarun da basa tare da juna da ciwon ZUKATA, amma suna sake haɗuwa sai kaji lufff ko ciwon ƙirji wani bai sake kukan yanayi ba a tsakaninsu. Kasan kuwa wannan ƙauna takai ƙauna. Danni in ma ba'a film ba wlhy ban taɓa ganin irin wannan soyayyar a zahiri ba. Bawai fa ba'ayi bane ba. Anayin ma irin wadda tafi tasu zafi, amma sai kaga da anyi aure labarin ya canja salo, duk da dai suma har yanzu ba'a tsallake koda goma ta marmari ba balle mu tantance....”
        “To kaima kaji ka bama kanka da kanka amsa, a wannan zamanin har wata soyayya ce tsakanin maza da mata in ba ta ina son kuɗinka kana son jikina ba. Malam kuɗi itama ta gani shiyyasa ta riƙe amana, shi kuma shegen kayan marmari ya gani shiyyasa. Dan haka wuta zamu bata iya wuta da kuɗaɗe na tabbatar da gudu zata saki wancan layin ta dawo namu....”
        “Eh to ban musa maka ba ranka ya daɗe, amma dai da zaka fahimceni ka kuma ji shawarata da ita ɗin an barta, mudai sake komawa matsayar ta inda aka hau tanan ake sauka. Wato can wajan ubanta, dan kasan su har yanzu fa zaman jiranka suke yi ka dawo azo a baka ita. A bincike mai ƙarfi kuma da nayi har yanzu basu san tayi aure ba, tama auri ɗan gidan Darma, dan kakar nan tata ta tsaneshi, da ace sun sani ai da yanzu wani batun ake ba wannan ba”.
        “Banƙi ta taka ba Rabilu, amma kasan akwai ƴan kuɗaɗena dama a jikinsu, kuma dama dole zan bibiyi kayana, sile bazan iya yafewa ba a ciki kaima ka sani”.
       “Tabbas hakane Alhaji, nima ban baka goyon bayan yafewa ba. Kuma zan tayaka yaƙin ƙwatosu. Shiyyasa nace mu sake komawa ta can wasan zaifi daɗi. Zamu jefa tsuntsu biyu da dutse guda kenan. Mu haɗa rikicin bala'i tsakanin su da ɗan gidan Darma ɗin, mu kuma ce kuɗinmu ko yarinya, dan na tabbatar a yanzu babu ko sisi a bishashar arziƙin nan da kai musu. Kasan mutumin ƙauye idan yaga banza (ALLAH dai ya saka mana mu mutanen ƙauye🙄😏). Ya iya kwanciyar magirbi, sai dai kuma akwai tsoron ɗan sanda, wuta zamu basu iya wuta muce kuɗi ko ƴa, ko ofishin ƴan doka”.
       “Kai banza ne, ka manta ubanta ɗan dokar ne da kansa”.
     “Eh kuma fa haka ne, to ranka ya daɗe shirinmu zamuje da shi. Barikin sojoji zamuje ka samu gidiba-gidiba majiya ƙarfi kamar guda goma zuwa ashirin, kawai mu ɗebesu atai kauyen nan a tattarosu”.
       “Eh kaima ka kazo da magana anan Rabilu. Indai wannan wasan ya faɗa fiye dana farko, a maimakon mota da kaci wancan karon wannan karon harda kuɗi”.
      “To ranka ya daɗe ina godiya, amma motar ma fa ta waccan karon har yanzu ba'a bani ba. Kasan daka turani wajen Oler daga cewa sai an min sabon fenti har yanzu sai binsa nake baya ma saurarena.”
      Dariya Sen ya kece da ita. Sai kuma ya bubbuga kafaɗar Rabilu yana faɗin, “Kwantar da hankalinka wannan karon hannu da hannu ni zan baka. Sai ma ka zaɓa ka darje sannan. Kai ina ga ma harda ƙyautar gida zaka samu. Dan ni kaɗai nasan irin romon lagwadar demokradiyyar dana hango, kaga yarinya tako ina ta cika tai ciff-ciff rainon madara da lemon kwali, wato shegen yaron nan da alama akwai lafiya, dan yarinyar nan ƙyawun daya ƙara badai shinkafa ba wlhy sai dai madarar kwalli”.
        “ALLAH ranka ya daɗe?”.
   “Hummm ai Rabilu ba'a magana wlhy, dama fa mace ce iya mace a wajen nan. Kasan baƙaƙen matan nan da muke rainawa kullum idonmu a nunar ranar nan, ƴan bleaching ma sunfi yawa, dan shi farin usil farin so ne fa ƙauna dan fenti ne daga ALLAH, amma baƙaƙen matan nan ƴaƴan malam Shehu wlhy talaucin ne kawai amma kadara ce mai girman gaske. Yo hauka ake na ƙara auren fara”.
       Dariya sosai Rabilu ya kece da ita............✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣4️⃣3️⃣


______________



............“Ni ALLAH bana son kitso. Baga salla na zuwa ba saura ƴan kwanaki ka bari zanyi”.
      “Haba Besty! Wai kina son komawa ƙazama ne, mata ai da kitso aka sansu, amma tsakani da ALLAH ke babu abinda ake kai ruwa rana dake a kansa sai kitso. Kanki wata kusan biyu ke nan babu kitso. Kullum sai dai mu taje a ɗaure diba har ya fara raguwa.”
    Hawaye sosai ke ziraro mata, dan a duniya babu abinda Manaal ta tsana irin kitson nan, da ace fa an yarje mata suyi aski da itace zata zama shugabarsu. (Hhhhh wayaga su Bilyn Abdull 🤣🤣adai rufe rufau kawai na Maanal ne ya fito filin subahana). Zuru AA yay yana kallonta, ƙasan ransa ko dariya ke cinsa sosai. Kusan fa sati biyu kenan yana wannan faman da ita amma ƙiri da muzu da yay magana sai ta hau ciwon ƙarya. Shi kuma harga ALLAH yana mugun son ganin ta da kitso. ALLAH dai ya taimake shi idan Baby girl za'a haifa masa kada a haifo mai gudun kitso....
      “Besty”.
Ta kirashi cike da shagwaɓa tana girgiza masa hannu. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Uhhyim Besty ”.
     “Dan ALLAH ka haƙura zaka bari sai sallar. Kaga kwana tara fa ya rage duka-duka. Kuma kace zamuje Giro da KD, basai kawai nayi kitson ba”.
         “Uhm-uhm Besty, karfa lokaci yayi kice zaki saka min rigima”.
    “ALLAH bazanyi ba”.
“Kin tabbatar?”.
Da sauri ta ɗaga masa kai. Ya ce, “Shike nan, gashi nayi recording zan ajiye, zan kuma turama Oum da Yaya Fawzan ma su ajiye dan sune shaidun mu. Tashi ki haɗa min shayin bara naje balcony na motsa jiki kwana biyu jikina na ciwo ban motsa shi yanda ya kamata ba”.
         Fuskarta cike da murmushi ta ce, “Ina ƙaunarka Besty”.
      “Nima haka Bestyn Besty, a yanzu kune duniyata mai girman gaske ke da unborn ɗina”. Yay magana yana kamo ƙugunta ya matso da ita gabansa ya sumbaci cikinta. Sai kuma ya ɗaura kunnensa a kan cikin, murya ƙasa-ƙasa ya furta, “Ko waye kwance a wannan wajen mai albarka ALLAH ka albarkace sa, ya rabbi ka kare min shi ko ita da mahaifiyarsa, ALLAH ka bamu tsahon rayuwa, ka kashemu tare ni da matata dan in ɗaya ya tafi yabar ɗaya bazamu iya jurewa ba ya rabbi. Ya ALLAH kasa itace matata har a aljanna”.
         Murmushi mai faɗi Maanal ta saki, tare da rungume kanshi a saman cikin nata sosai, sai kuma tai ƴar ƙara tana sassautawa saboda zafin da taji. Da sauri ya ɗago ya kalleta tare da faɗin, “Meya faru?”.
     Murmushi ta masa tare da jan hancinsa ta ce, “Zafi naji kaɗan dana danna ƙaton kan nan naka”.
     “La'ilah yanzu Besty mijin naki ne mai ƙaton kai. Jama'a kuzo mu tayata istigafari dan ALLAH”.
     Dariya sosai Maanal keyi, ta dungure masa kai. “ALLAH ka iya sharri wani lokacin, wanda bai sanka ba sai yay ta yabonka ana kiranka shiru-shiru basu san hali bane ba”.
        Murmushi yayi shima har haƙoransa na bayyana, ya ce, “Oho dai, kema naga ai hakan kike ko. Gwara ma ni ai”.
    “Wace gwarar kullum fuska a haɗe, magana kamar ana maka dole. Ai wlhy sai na koya maka surutu”.
    “Yo miyay saura kuma ALLAH na tuba Besty, tsabar maganar da kike sakani a gida da office kullum yawo nake da kwalin paracetamol a gida da office da mota”.
         “Kai Besty kaji tsoron rabbu”.
   “Kema beaty kiji tsoron rabbu”.
“Shike nan bara dai naje na dawo zakayi bayani, badai yau lahadi ba ko nan da falon ƙasa bazaka sauka ba yau sai kaga asalin koyan surutu mai saka ciwon kai”.
       Hannu ya kai zai cafkota ta zille ta fita da ɗan gudu. “Ki tausaya min ki daina gudun nan dan ALLAH ɗan tayima bai gama zama mutum ba”.
     Sarai ta jisa, dan ya ɗan ɗaga murya, sai dai bata amsa masa ba, ta dai ɗora hannunta a saman

170 / 213

Chapters