AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   198 / 213

591K to 594K   out of 636.6K words

ɗin kike zagi Basariyya? Saboda ki nunama duniya ke mara tarbiyya ce. Da shekarunki da komai amma sam baki da isashen hankali. To bara kiji auren Alhaji Balala babu fashi, dan nima na gaji da zama min da kike a gida wawuya kawai. Alhaji kaje ka shirya nan da kwana uku kacal ka turo magabatanka”..
          Kuka sosai Hajiya Basariyya ta fasa da faɗin, “Wlhy dana auresa na gwammaci na gudu kuwa”. Tai cikin gida fuuu. Ƙwafa Kawu Manu yayi da faɗin, “Shike nan Alhaji in dai da sadaki a tare da kai muje masallaci yanzun nan, dole ne na nunama yarinyar nan bata isa ba kuwa. Duk da itace da damar zaɓar mijin aure bata da cikakken hankali ni zan zaɓa mata dan bazan sake bari ta koma birni ta sake fanɗarewa ba.”
     Bakin Alhaji Balala a washe ya miƙe yana faɗin, “Ai ko babu yanzu zan aika gida a ɗakko Malam, ALLAH ya saka da alkairi ya bada kadan zuminci”...........✍️

        Kambu Hajiya Basariyya an shiga gidan ɗan kande, wayaga ɗaurin goro 🤣😆.

191



.......Aure dai kam ya ɗauru tsakanin Hajiya Basariyya da Alhaji Balala. Dan ana idar da sallar la'asar ya biya sadaki aka ɗaura. Sai ga Kawu Manu ya shigo da goro da sweet, sai kuɗi dubu hamsin ƴan ɗari biyar-biyar. Wani irin kukan tashin hankali Hajiya Basariyya ta saki lokacin da Kawu ke musu bayani ita da iya. Ko kallo bata ishesa ba, sai ma miƙewa yay yana faɗa mata ta shirya gobe zuwa jibi zata tare ta bar masa gida, dan bazai iya zama da mai taurin kai da bijirarriyar zuciya irin tata ba. A gobe ma Alhaji Balala zai turo a fara kwashe kayanta zuwa can, dan haka iya ta nema wanda ta yarda dasu suje yin jere.
           Suma ne kawai Hajiya Basariyya batayi ba a ranar tsabar yanda ta dinga zuba musu bori. Da daddare ta gama shirya kayanta tsaff da shirin guduwa sai dai ta makaro, dan kar Kawu Manu ke kallonta. Tana fitowa ma taci karo da shi zaune a ƙofar gida. Turus ta tsaya tana kallon sa kamar yanda yake kallonta. Sai kuma yay murmushi mai ciwo da faɗin, “Oh guduwa kike shirin yi da aure wani a kanki? To kada ki fasa dan ALLAH ga hanya nan”. Yay maganar yana tashi ya shige gida abinsa. Ga dai ƙofa a buɗe ga kuma dama an bata amma ta kasa yin komai, sai ma rushewa da kuka tayi a wajen tare da zamewa ta zauna dirshan. Haka ta ƙara cin kukanta babu mai lallashi ta taso ta dawo cikin gidan....

__________★

         KANO

   Zaune take tana shayar da bebinta, yaro ƙyaƙyƙyawa yay ɓul-ɓul gwanin sha'awa. Sosai yake kama da babansa, haske kuwa nata ne. A zahiri yaron take kallo, amma tunaninta baya tare da shi. Sageer daya shigo kusan mintuna goma ya fahimci hakan, dan ko shigowarsa da alama bata sani ba. Numfashi ya ɗan furzar ya wuce kitchen ya ajiye kayan hannunsa ya fito. Sai da ga kai zaune har ya taɓa sannan firgigit ta dawo tunaninta. Kallonsa tayi, shima ita yake kallon, sai ta sauke kanta ƙasa kawai.
         “Har yanzu jikin ne?”.
    Kanta ta girgiza alamar a'a.
“To mike damunki?”.
Cike da son danne abinda ke ranta tace, “Babu komai fa, kawai dai na tafi tunani ne. Sannu da dawowa”.
       Amsa mata kawai yayi badan ya gamsu da abinda ta faɗa ba. Itama sai ta miƙe tana miƙa masa fodio ta nufi kitchen. Babu jimawa ta dawo da ruwa ta ajiye masa. Ta ɗan kallesa yanda yakema fodio wasa kamar yana yi da babba mai wayo. “Kawoshi kasha ruwan”.
       “No barci, ɗan samin dai ruwan wanka na watsa ruwan nan yasa garin yin sanyi”.
     Kitchen ɗin ta wuce, ta ɗauka kettle ta fita zubo ruwa a rigiya, koda tazo ta jona a wuta sai tai tsaye, sai kuma ta ɗauki wayarta, tana dannawa screen ɗin ya kawo haske hoton AA ya bayyana. Yayi matuƙar ƙyau cikin ƙananun kaya sai coat data kai masa har gwiwa fara sol mai gashi. Ya saki ƙatuwar hular rigar bayansa ta kwanta. Akwai alamun kyakkyawan hannun mace dake a kafaɗarsa alamar tana a bayansa ne, kodai zooming hoton akayi, ko kuma yanke macen akayi. Yanda AA ɗin yay wani shegen murmushi idanunsa a lumshe gashinsu sun kwanta gazar-gazar ga murmushi akan ƙyaƙyawar fuskar tashi kaɗan yaɗan turo lips gaba yay masifar yin ƙyau. Gashi ya fito tar-tar kamar kai magana ya amsa.
       Ajiyar zuciya Huznah ta sauke mai ƙarfi, sai kuma hawayen da suka taru mata a cikin ido suka zubo sharr. Hannu tasa ta sharesu... Sageer da yaji shiru ya biyo bayanta kasancewar ta juya masa baya tsaff yaga abinda take kallon. Da farko sai da zuciyarsa ta buga, wani irin kishi mai zafin gaske ya turniƙesa. Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma yay shiru ya koma da baya-baya. Kasancewar hankalinta ba'a wajen yake ba ko motsinsa bata ji ba. Koda ya koma falon ma da ƙyar ya iya nutsuwa yay controlling fushinsa. Bayan ruwan yayi ta ɗakko ta fito, da kallo ya bita har ta shiga ɗakin barcinsu. Bata wani jima ba ta fito tace masa ga ruwan can. Shima komai baice da ita ba ya miƙa mata Fodio ya wuce. Duk yanda yaso shiga wankan kasawa yayi, ya zauna bakin gado ya ciro wayarsa ya buɗe data. Karo na farko ya shiga google ya fara searching sunan AA Darma da accounts nashi na media. A X kawai ya samu, sai facebook. Na facebook ɗin ya fara shiga, sai dai babu wani abun kirki a ciki ma, dan posting ɗin abubuwan da akai basufi goma ba, duk ma agogo ne. Amma kuma yana da followers sosai. Daya shiga ainahin profile ɗin account ɗin ma sai ya fahimci kamar ba ainahin AA ɗin bane. Fitowa yay ya shiga X, anan ne yafi gaskata AA ɗin ne da kansa, sai dai nan ɗin ma babu wani posting ɗin hotonsa ko guda ɗaya balle matarsa ko wani family member na Darma kaf. Hotunan agoguna ne manyan kai na manyan masu hannu da shuni kawai. Koda ya shiga comments na posting ɗin farko yaga kusan duk manyan mutane ne ke masa comments ɗin ma. Fitowa yay zuciyarsa na tunanin a ina to ta samu wancan hoton? Sai zuciyarsa ta ayyana masa brothers ɗinsa mana. Nan take ya koma neman account ɗin su  Babban Yaya. Sai dai babban Yaya irin AA ne, shima twitter ɗin ce kawai yake da account kuma babu komai akai sai harkar business. Yaya Fawzan ne keda a Instagram da X ɗin, anan ne ya samu hotunan Babban Yaya, da AA ɗin har ma dana Abah. Mafi yawanci kuma hotunan salla ne, dana juma'a sai na ɗaurin aurarraki. Akwai wasu hotunan da dama na zuri'ar Darma, sai dai shima babu hoton mace ko ɗaya, kuma babu irin wancan hoton da yaga Huznah na kallo. Ajiye wayar kawai yayi ya shiga wankan, abubuwa da yawa zuciyarsa ke ayyana masa, ciki harda Huznah na charting da AA Darma ne ya tura mata hotunan da kansa. Sai dai zuciyarsa na ƙaryatawa ta wani gefen, dan yasan labarin wanene AA Darma da halinsa akan mata. Kai har yanda Huznah ta dinga bibiyarsa da ƙin kulata duk sai da ya binciko...

     Har washe gari yana son ture abin a ransa amma zuciyarsa taƙi nutsuwa. Ƙarshe dai ya ɗauki wayar tata ya fita da ita bata sani ba. Da yake tsakanin jiya zuwa yau ya saka mata ido sosai ya fahimci password ɗin data canja yana gwada sakawa wayar ta buɗe. Haka ya shiga ya fara mata bincike daki-daki. Tun daga kan massages, bai samu komai ba ya koma WhatsApp, nan ma normal sai sisters ɗinta kawai take charting da su dan canja mata layi da yayi dama duk babu ƙawaye yanzu. Ya koma facebook, bata buɗe account tabi dokar daya kafa mata kenan, sai ya shiga Instagram. Sai ko kai tsaye ga hoton jiya tana akan shafin da hoton yake ma bata fito ba. Koda ya duba mai account ɗin sai yaga sunan Saleem Mahmud Darma. Ya shiga profile ya duba yaron tabbas da ganinsa kaga jinin Darma ɗin, koda ya shiga account ɗin sosai hotuna ne kala-kala na zuri'ar Darma. Akwai kuma na AA ɗin sosai a wajen, dan wanda ma Huznah ɗin ke kallo kwana biyu da ɗorashi, yanzu kam sosai hoton ya buɗe alamar zooming ɗinsa ita tayi, bayansa black beauty mace ce, kai tsaye ya gane Maanal ce tunda ya santa a gidan su Huznah ɗin, tana sanye da doguwar riga ta ɗora ƙatuwar jacket a kai alamar ba'a Nigeria suke ba. Kwance take a bayansa hannayenta duk biyu a kafaɗarsa ta kamo kunnensa ɗaya da baki like tana cizonsa ne. Hannunsa ɗaya ya tallafo kan nata shi kuma. Fitowa kawai Sageer yayi daga account ɗin, ya blocking ya fito gaba ɗaya yay deleting account ɗin nata na Instagram ɗin ma gaba ɗaya.
     Koda ya dawo gidan bai ce mata komai ba, amma kai tsaye ya bata wayarta. Sai da ta nuna mamaki, dan bata san ya ɗauki wayar ba sam. A ɗan daburce tace, “Dama wayata na hannunka?”.
     “Uhhhm”.
Kawai yace mata ya wuce ciki. Sai tasha jinin jikinta. Zaune ta kai jagwab fodio na bayanta, zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri. App na Instagram ta fara nema dan ta goge, saboda bai san ta buɗe sabon account ba kasancewar ya hanata. Sai me babu app ɗin ma babu dalilinsa. Hakan na nufin ya gani shi kuma ya goge. Gaba ɗaya sai taji ta sake ruɗewa, ALLAH tsoron Sageer take har ranta, duk da kuwa yana iyakar ƙoƙarin sa wajen janta a jiki ta yanda zata sake da shi. Amma ta kasa ƙarfafa kanta sam al'amarin kamar wani asiri. Ko kuwa hakkin wulƙantashi data dingayi ne lokacin yana gidansu oho. Dan babu irin zagi da cin kashin da batai masa ba ita da ƴan uwanta. Musamman ma ita ɗin daya nuna yana so. A yanzu kuma sai ALLAH ya saka mata ganin girmansa da kwarjini ƙwarai da gaske. Balle ma a tsakanin nan da wannan al'amarin ya faru tsakaninta da mahaifiyarta. Dan koda suka dawo Kano bai taɓa tayar mata da maganar ba ko tambayarta yanda akayi, ya dai sake ninka kulawar da yake bata fiye da da. Tana jin farin cikin yanda yake mata, duk da tana jin tsoronsa, gefe soyayyar AA na nan daram a zuciyarta, babu abinda ya canja..
       (In son mai karatu ya fahimci kuskuren Huznah anan. Eh zuciyarta na son AA mun yarda da haka, amma ƙyautatawar mijinta da ƙoƙarinsa na taka rawar gani shima a zuciyar tata. Sai dai bata taɓa nutsuwa miƙama UBANGIJI kukanta akan ya cire mata zuciyar wanin mijinta ba ya bata nutsuwar zama da shi ya saka mata soyayyarsa tunda ta fahimci anzo gaɓar da tafa rasa AA ɗin dole kuma ta zauna da shi Sageer. Yan uwa duk yanda muke tunanin al'amari mai ƙyau ko mara ƙyau ya tsananta a tunaninmu da zuciyar mu mu nutsu wajen maida al'amuranmu ga UBANGIJI da kai kukanmu, in sha ALLAHU zamu samu sauƙi da sassauci dan wani lokacin shaiɗan da son zukatanmu na jan zaren matsalolinmu ne kai tsaye. Idan bamu haɗa da roƙon ALLAH ba sai komai ya rikice mana mu rasa wanda muka samu, wanda yay mana nisan ya sake mana nisa. Kamar dai nan wane tunani kuke yi akan matakin da Sageer zai ɗauka a kanta yanzu?).........✍️192


.......A nan Saudia AA ne a kitchen a gidan da su Oum suke yana dafama Maanal ƙwai da tace tana so. Yanzu kullum anan gidan suke yini sai dare su wuce masauki, jiya da Oum ta fahimci yanayin Maanal ɗin na canjawa sai tace AA ɗin ya barta anan ta kwana. Ba ƙaramin tashi hankalinsa yayi ba, ya marairaice ma Oum ya shagwaɓe murya wai ai Maanal ɗin na tayashi aikin office miye-miye. Sai da ta gama jinshi Abah dai da Babban Yaya na murmushi, Yaya Fawzan kam ya saki baki da hanci yana kallonsa kamar wani robbot. Sai da ya gama tsara Oum tsaff sannan tace, “Koma dai miye bazata bika ba Auta, shi aikin office ɗin ba'a bama masu tsohon ciki hutu. Kai baka ganin yanda gaba ɗaya yanayinta ya canja”.
      Kallon Maanal AA yayi, duk da kullum tana a manne da shi. Amma sai ya dinga binta da kallo daki-daki. Ta ƙara ƙiba sosai dan cikin ya kumburata, duk da shi cikin ba wani yayi mahaukacin girma bane abinka dana farko. Fatanta ya wani sake komawa luf-luf kamar kalar ruwan sahara. Gaba ɗaya hankalinta ba'a kansu yake ba, suna hirarsu ne su uku Ameerah na sakama Najma lalli jaa a yatsu. Idanunsa ya ɗauke, sai kuma cike da sake marairaicewa ya ce, “My Sweetheart Oumna ALLAH na miki alƙawarin zan ninka kulawar idan ma yayi kaɗan”.
          “Ikon ALLAH, yau ni Fawzana naga cingum boy, to kai malam Ajwaad ance maka kulawar da kake batan ce batai ba. Kawai ka barmin ƙanwa ta dawo gaban mamant.....”
     Cike da jin haushi AA ya ɗauki pillow ya tilla masa, mi Abah da Babban Yaya zasuyi ba dariya ba. Sai AA ya sake tunzura. Fuuuu ya tashi ya fice abinsa. Oum ma dai ta kasa daurewa dariyar ta sanya. Suma hankalin su Maanal sai ya dawo wajen. Kowa ya ɗauka fushin na AA na ɗan lokaci ne waje ya fita ya huce zai dawo sai suka ji tsitt har lokacin tafiyarsu masauki yayi. Koda Fawzan ya leƙa babu shi babu alamarsa, ya dawo yana dariya da faɗin, “Oum autanki fa da gaske fushi yayi?”.
        Oum dake murumushi ta ce, “Zai ma sakko ne, amma bazan bashi ita ba”. Cike da mugunta Fawzan ke dariya. Babban Yaya ya ce “Kadai yi a hankali dan randa yazo kanka Auta ba raga maka zai yi ba. Duk bakai ka kunnashi har yayi fushin ba ma”.
       Dariya suka sake sanyawa dan yanda AA ya fita a fusace ya kasa barin ransu. Haka dai Oum ta korasu suma. Su a tunaninsu AA yayi fushi ya tafi masauki ne. Maanal dai batace komai ba, ko'a fuska kuma bata nuna damuwarta ba. Duk da zuciyarta na cike da damuwar yanda Bestyn ta ya tafi babu ko sallama. Kama hannunta Oum tayi ta haura da ita sama, ɗakin dake kusa da wanda suke ta shiga da ita. Ɗaki ne babba, komai akwai na buƙata, hatta kayan haihuwarta na'a ɗakin. Dama daga shi sai wanda su Oum suke ciki a gidan, Naufal ke kwana anan su Oum na ɗayan ɗakin. Yanzun ma yana a gadon kwance yana barcinsa.
     Cike da lallashi Oum ke kallon Maanal, dan tasan raba Besty da Besty ba abune mai sauƙi ba. “Babyna kada ki sanya wata damuwa a ranki kinji, zaman na kwana kaɗan ne kawai zaki koma wajen mijinki. Fatan mu dai ALLAH ya saukeki lafiya. Ki ajiye waya a kusa da ke da kinji wani canji tare dake ki kirani, nima kuma zan dinga leƙoki akai-akai kinji ko?”.
       Kanta ta jinjina ma Oum tana haɗiye hawayenta. Sarai Oum ta karance, amma sai ta basar, a ranta kam fal mamaki ne na irin wannan soyayya da ƙaunar juna da ALLAH ya haɗa tsakanin Ajwaad da Maanal. Koda yake itama gata nan da Abah, koda rayuwa ta gangara musu da shekaru ji suke kamar yanzu suka fara son juna. Tabbas soyayya gaskiya ce, kowa kuma da irin yanda zuciyarsa ke ɗaukarta. Oum ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Tashi kije ki kimtsa ki kwanta, komai da kike buƙata na ajiye miki a wadrob, kinyi shafa'i da wutri ko?”.
    Kanta ta jinjina ma Oum. Oum tai mata addu'a da sallama ta wuce. Sai lokacin ta saki hawayen da take riƙewa. Sai kuma ta ɗauki wayarta ta shiga WhatsApp, voice call tai masa har sau uku bai ɗaga ba. Ta koma video call, nan ma shiru, tai massage nan ma shiru. Sai ta sake rushewa da kuka. Kamar wata almara sai ga AA ya buɗe ƙofar toilet ya fito, ita Maanal ma razana tayi. Ta zabura zatai ihu a tunaninta aljani ne ke neman buɗe mata ido yay saurin ɗaura yatsarsa a kan baki yana mata alamar tai shiru. Dole ta saka hannunta ta rufe bakinta. Shi kuma ya rage hasken fitilar ɗakin ya ƙaraso inda take tsaye kawai ya rungumeta. A tare suka saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske, sai kuma a hankali ya saukar da kansa a dokin wuyanta ya shiga kissing nata step-by-step. A haka yay sama zuwa fuskarta ya cafke lips ɗinta. Babu musu ta bashi haɗin kai suna sauke ajiyar zuciya, kai kace shekara sukai basuga juna ba. Hannayensu ɗai-ɗai akan cikinta, kai da kaga yanda suka dafeshi kasan wannan abinda ke a ciki akwai ɗumbin soyayyarsa a zuciyar iyayen nasa. Sai da ya tabbatar yayi irin lallashin daya dace kafin ya janye lips ɗin sa ya sake rungumeta, sai kuma ya kamata suka zauna a ƙasan tattausan carpet dake a gaban gadon yana shafa bayanta, ita ko ta kwanta lamo a ƙirjinsa.
        “Besty baka tsoron Oum ta dawo ta ganka?”.
     “Komai zan iya ɗauka a kanki Maanal”.
    “Dama fushin ƙarya kayi kenan?”.
  “Na gaskiya ne mana, harna koma masauki kawai naji bazan iya daurewa ba kawai na dawo.”
        Ƙaramin murmushi ta saki, sai kuma ya ɗaga kai tana kallonsa, shima kallonta yake yi cike da kulawa da soyayya mai karfin gaske. Fin mintuna biyu sunama kansu kallo mai rugurguza garkuwar jiki kafin ta motsa lips ɗinta cike da raɗa, “Ka zama aljani ko? To ta ina ka biyo?”.
       Sai da ya kashe mata ido ɗaya sannan yay mata nuni da window.
    “Are you serious?”.
“Akan besty da unborn ɗina zan iya komai, idan nace komai ina nufin komai fa ina har bazan saɓama UBANGIJI da sakawa da hanin MANZON

198 / 213

Chapters