AJIYA A DUHU

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   184 / 213

549K to 552K   out of 636.6K words

tana kallon Abah, ta ce, “Wlhy Aban Fadeel bamu kaɗai muka shirya hakan ba, kai hasalima ni da farko ba dani aka shirya ba Aunty ce da kakar yarinyar da matar ubanta.....”
      “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un wai Gwaggo da Sailuba?”. Oum data kasa haƙuri ta tambaya hawaye na ziraro mata tun ɗazun. Nana tace, “Tabbas su Hajiya Fateema. Kuma ga Aunty Kamila ɗin nan ta rantse batare suka shirya abinsu ba, sai daga baya aka nemoni a ciki saboda Saheeba ta auri Fadeel.”
          Idanu sosai Abah ya zubama Mamy, hakama AA da su Yaya Fawzan da Babban Yaya kallonta kawai sukeyi, Sille ya shuri Kamila da ƙarfi har sai da tayi ƙara, ya ce, “Dan ubanki bazaiyi magana ba shaiɗaniya. Annoba”.........✍️
    




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣6️⃣


______________


.........Wasu wahallun hawaye suka zubowa Mamy, da ƙyar yanzu kam ma take iya maganar. Ta jinina kai da faɗin, “Wlhy nima bani nace ayi asiri ba, dan tunda nake ban taɓa zuwa wajen malami ko boka ba. Gwaggo da Sailuba ne suka kawo maganin. Amma nice na fara zuwa musu da zancen son hana auren yarana da ƴayan Asiya, saboda nasan Gwaggo bata son Asiya dan tasha kawo min gulmarta akan alaƙarsu da Fateema. Ni kuma dama irin yanda Gwaggon kema Asiya namin daɗi, sai na yarda na haɗe kai da su musamman ma Sailuba, sai ya zama ma nice mai gayama Sailuba duk wani sirrin Asiya, takai duk wani asiri da Sailuba taima Asiya anan gidanmu ake shirya komai a bata taci ta hanyar Maanal batare da sun gane ba, shiyyasa bata gane abinda Sailuban ke mata sai wulaƙancin Baban su Maanal ɗin kawai da take fuskanta. Hatta batun bada zoɓon Gwaggo ce ta shirya komai, sai kuma aka samu matsala ita Maanal tasha zoɓon tare da Ajwaad, duk da ance a jikinta kawai zai yi tasiri abin mamaki sai yayi tasirin har a jikin Ajwaad ɗin ma. Dan lokacin da Ra'iz ya sanar mana Ajwaad yasha zoɓon tare da Maanal bamu damu ba,  mukace ya koma wajensu, ya tafi ya haɗu da Maanal zata shiga ɗakin su Ajwaad tana riƙe ciki, shine ya dawo yana gaya mana, ya tabbatar mana Ajwaad na a ɗakin shima. Hankalina ya tashi nace yaje ya kira min Ajwaad ɗin, nan ma ya koma kiransa sai yaci karo da shi ya fito neman Fateema, da wannan damar Ra'iz ya shiga wajen Maanal, ni kuma na tare Ajwaad na tambayesa mike faruwa? Yana faman riƙe ciki shima ya gaya min halin da Maanal ke ciki shine nai masa wayo nace yaje ɗakina ya ɗakko min magani na bata, ya bar Fateema tana cikin taro kada ya tada mata hankali. Yana shiga bedroom ɗina na kulleshi ta baya, ashe nabar wajen ina sauri ban cire key ɗin ba wani kuma yazo ya buɗe shi, wannan shine dalilin komawarsa ɗakinsu ya samu Ra'iz akan Maanal. Daga nan bamu san miya faru ba kawai al'amarin ya juye kan Ajwaad cewar yayma Maanal fyaɗe. Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, ga Ra'iz mun nema a gidan mun rasa tako ina. Gida kuma ya rikice akan abinda ya faru. Cikin ɓacin rai muna ɗaki inama Gwaggo da Sailuba masifa akan yaya akai haka, bayan sunce maganin Maanal ɗin kawai zaici gashi ya haɗa da Ajwaad, maimakon yaron da muka kawo fyaɗe ya koma kan Ajwaad. Suna cikin min rantse-rantse kawai juyawar da zan yi naga Ajwaad a bayanmu, kuma tabbas yaji komai da muke faɗa. Ƙoƙarin juyawa yake zai fita na damƙoshi, wannan ya bama su Gwaggo damar fita a ɗakin, kuka Ajwaad kemin akan miyasa zanyi hakan? Miyasa zan aikata, takaici ya sakani buge masa baki. Cikin ɓacin rai nace masa nayi ɗin, kuma idan ya sanarma wani ina da alaƙa ko hannu a cikin abinda ya faru ɗin wlhy sai na kashe Fateema da Maanal ɗin, shi kuma sai na tsine masa. Ko tuhumarsa akayi ya faɗi cewar Ra'iz ne ya aikata komai, shi yazo ceton Manaal ɗin ne, kuma daga ranar na haramta masa huɗɗa da Maanal na har abada. Idan kuma ya sake yarda ko zama waje ɗaya sukayi ALLAH ya isa ban yafe masa ba, ko mutuwa nayi idan ya aure Maanal nan ma ban yafe masa ba. Kai yana ma ƙara haɗa alaƙa da zuri'ar Asiya da Habibu koda ta magana ce ALLAH sai na kashe Maanal da Fateema har lahira. Ina gama yimasa wannan barazanar na fito na baroshi a ɗakin, na samu gida ya ƙara rikicewa Fateema ta faɗi, ita kuma Maanal ɗin an wuce da ita gidansu ana kuma neman Ajwaad dan maza sun shigo. Ban san ya akai ba, ban san miya faru ba kawai an tsare Ajwaad da tambaya bayan likita ya tabbatar da amma yarinyar fyaɗe yaron nan ya amsa cewar wai shine yay fyaɗen. Raina ya ɓaci, sai dai ta wani ɓangaren naji sanyi da akace za'a aura masa ita yace baya so, ta haka na fahimci kurarin danai masa akan kashe Maanal da Fateema yayi tasiri kenan. Oho ko'a hakama naci riba ai, tunda aure dai ya fasu, duk da amsar zancen fyaɗen nan da yaron nan yayi har yanzu yana min ciwo a rai, muka zo kuma muka shiga tashin hankalin ciwon daya tsinta kansa a ciki dan ni na Fateema bai wani dameni ba....”
      “Toke dama kin damu da damuwar wani ne inba taki ba Kamila”. Mabera ya faɗa yana murmushin takaici, sai kuma ya kalla ƙofa da jami'an tsaro keta faman ɓaɓatu amma sunƙi tankawa. Baki ya taɓe ya dawo da kallonsa kan Abah dake ta kallon Kamila ko ƙyaftawa babu. Ƴar dariya yayi da faɗin, “My Darma indai wannan matar ce kaɗan daga abinda zata iya kaji, dan mun yanke maku abubuwa da yawa a kanta ma saboda bamu da time sosai , dan lokacin fara aiki ya kusa cika. Bana son mu wuce 2 a jejin nan. Gashi har 12 ta wuce yanzu. Amma a gurguje zan ƙarasa muku abinda ya rage kodan kasan halin da kake ciki a yanzu kai kanka game da ƙullinta”
  Sille dake ƴar dariya ya ce, “Gara dai ka faɗa masa kam Baa! Ko dan wannan tsageran ɗan nasa da yayta ɓoye ainahin halin uwarsu da abinda ta dinga aikatawa saboda bata kariya yasan ita ɗin kara da kiyashi ce ɗaukar mara sani, ɓoye hallayarta bazai amfane shi da komai ba. Dan bana son mu rabu basu san komai akan wannan azzalumar matar ba”. Ya ƙare maganar yana shurin ƙafar Mamy har sai da ta saki marainiyar ƙara. Ko'a kwalar rigarsa.
       Cikin rashin damuwa Mabera ya cigaba da faɗin, “Bayan Ra'iz yabar gidan a wahale ya koma wajen Junaid, ransa ya ɓaci da bayanin da yay masa akan abinda ya faru yace sai ya ɗauki fansa. Nine na hanashi, na kuma sanar masa ai lokaci baiyi ba da saura dan wanan wasan ya ɓaci kuma, dan bai kamata Kamila ta faɗi ba a wannan gaɓar da sauƙi tunda al'amarin ya juye haka. Dan haka na tattara su suka koma Lagos. Sun koma da sati ɗaya Turai ma ta koma nima haka, itace ta bamu labarin dukkan cakwakiyar data ƙarasa faruwa har barinku ƙasar. Anyi haka da kusan wata guda na tafi saudia yin wani aiki, watana kusan uku na dawo, na tarar da wani tashin hankali na asalin halin da Turai ta jefa ƴaƴana a ciki, wato maida Junaid tamkar mijin aurenta. Hankalina ya tashi matuƙa, dan abune da ban taɓa kawoma raina ba. Naci mata mutunci matuƙa, na bayyanawa mijinta ainahin wacece ita, na kuma ce sai mun shiga kotu da ita tunda ta lalata min yara. Da ƙyar mijinta ya lallasheni ya bani maƙudan kuɗaɗe, ya tabbatar min idan wannan maganar ta fito shine zai faɗi a ƙasa, dan dama danginsa basa son aurensu shine ya dage. Kuɗin daya bani ne ya kashe wannan rikici, na canjama yarana anguwa dan hayar gida guda na kama musu, wannan shine sanadin rabuwarmu da Turai, su kuma suka baro Lagos suka dawo Abuja da zama, sai dai ko shekara basuyi ba mijinta ya rasu. A lokacin nima ina tsakanin Kaduna da Abujar amma ko gaisuwa ban mata ba, kai inda take ma ban taɓa nema ba. A wannan gaɓar ne kuma Ajwaad yazo Nigeria, bamu san ta yanda akai ya gano inda Ra'iz yake ba, kawai sai kirana akai wai nazo Lagos ga Ra'iz a hannun jami'an tsaro an kaishi asibiti wani ya masa dukan mutuwa, ya ragargaza masa ƙafafu ya illatashi a gabansa. Hankali tashe naje, zuwa lokacin an kaishi asibiti, hankalina ya tashi da ganin halin da yaron yake ciki, wlhy saika ɗauka haɗarin mota yayi ba duka bane, dukan ma wai na yaro kusan sa'arsa, dan Ra'iz da Ajwaad sa'anni ne ai. Junaid ya shirya ɗaukar fansa a lokacin amma nine na hanashi, muka maida hankali a kan jiyyar Ra'iz, dan bincike ma ya tabbatar min Ajwaad ya sake barin ƙasar dama yazo neman su yarinyar da akaima fyaɗen ne. Sai dai baima sameta ba, Darma yazo ya sake maida shi ƙasar da suken. A ƙarshe dai bayan gama jiyyar Ra'iz ya zama gurgu, sannan an tabbatar mana shi da mace sai dai kallo dan Ajwaad ya masa babbar illa a mazantakarsa. Wannan al'amari ya min ciwo, ya yima Junaid ma. A tsakanin kuma kuka dawo Nigeria cikin Abuja, sai dai bamu samu labari ba sai daga baya sakamakon mu duka munyi nisan kiwo, wannan shine sanadin dawowar Junaid cikin Abuja shima, muka kuma cigaba da bibiyar al'amarinku. Kwatsam kuma sai na ganku a Kaduna bikin ɗan Chalawa, sai dai ban yarda ku kun ganni ba, na taƙaice muku labari dai nine na fallasa batun yima Maanal fyaɗe da ɗanka yayi a wajen bikin nan dan kawai na ƙuntata Kamila da itama bata ganni ba. Daga nan kuma Junaid ɗan Junaid ya bayyana mata ainahin kansa. Abu na ƙarshe da nake son ka sani shine Kamila ta tanadi guba domin kasheka kaima, sai dai ban sani ba ko ta baka gubar ko bata baka ba.....”
A wani irin hankali tashe su AA da kowa ma suke kallon Mamy, Babban Yaya ya ce, “Guba?”..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣7️⃣


______________



........Kafin Mabera daya buɗe baki zai bashi amsa ya furta wani abu jami'an tsaro da suka gama kaiwa wuya suka bugo ƙofar gidan, suka fara shigowa. Da wani irin Sauri Mabera yay tsalle ya dire gaban Abah ya ɗora masa bindiga a kai. Haka Sille ma tuni ya damƙi wuyan Mamy ya ɗora mata bindigar, yaransu ma suka zagaye su Maanal. Cikin ƙaraji Mabera yacema jami'an tsaron, “Wlhy kuna motsawa duk sai mun kashe su. Dan haka sai ku zaɓa rayuwarsu ko fitarku waje.”
       A fusace cikin jami'an wani ya ce, “Kai ɗin banza daka isa ka bamu umarni, ka miƙa wuya kawai dan ta ƙare maka.”
      “Ta dai ƙare mana, dan sai dai ayi mutuwar kasko”. Cewar Sille yana hura hanci. Jami'an tsaron nan da suka fusata na motsawa kawai Sille ya harbi Anum dake jikin Nana. Yarinyar tai wani irin wahallen fasa ƙara, jami'an tsaron suka yunƙuro, Nana ta zabura, hakama su Oum. Sai kawai wani harbin akan Nana itama. Itama ihun ta fasa ta zube ƙasa Anum tai gefe alamar da wahala idan yarinyar nada rai. Gaba ɗaya hankalin kowa ya gama tashi a wajen. Sille ya wani share bakin bindigarsa a jikin Mamy yana faɗin, “Da kun ɗauka wasa muke, wlhy idan baku fita ba haka zan dinga musu tsinci ɗai-ɗai”.
     Hankalin IG yay matuƙar tashi, dan shugaban ƙasa ya jaddada masa kada su bari ko mutum ɗaya daga ahalin Darma yaji koda rauni, cikin bada umarni yayma yaransa magana suka fara fita da baya-baya har suka gama ficewa gaba ɗaya a gidan. Kallon Mabera Sille yayi, ya ce, “Baa! Ka shirya zamu bar gidan nan yanzun?”.
       “Son tayaya!? Ta kuma ina kana ganin sun zagaye gidan”.
     “Ta wannan ƙofar dai ba wata ba, kuma duk ku shirya kowa ya kama mutum ɗaya a cikinsu”.
     “Son!”.
  Da sauri Sille ya ɗaga masa hannu, sai kuma ya daki idon Mamy ya jefar da ita a wajen, ƙarasawa yay inda Mabera yake yana masa raɗa a kunne. Yayinda ihun Mamy ya cikama kowa kunne a wajen dan Sille fasa mata idonta ɗaya yayi, abun zattashin hankali da tausayi.
    Gaba ɗaya hankalin su Oum ya sake tashi, su Nuratu kuka sukeyi sosai, hakama su Maanal a wannan gaɓar sun kasa jurewa. A karo na farko AA da tunda aka harbi Anum ya duƙar da kai yay shiru ya ɗago ya kalli Maanal. Da salon maganarsu ta lips da suka iya tun suna yara yay mata nuni da lips ɗinsa bayan ya mata alamar share hawayenta, lips ɗin nasa ta ƙurama ido kuwa tana share hawayen nata, yana faɗar abinda yake son gaya mata ta gane. Kai ya jinjina masa tana ƙara share hawayen da suka gagara tsayawa. Shi kuma ya juya yana kallon Babban Yaya, AA ya jinjina masa kai yana miƙa masa hannunsa ɗaya, ya kama, ya juya sashen da Yaya Fawzan yake shima ya jinjina masa kai ya bashi hannu ɗayan suka riƙe juna kam. Cikin amincin ALLAH suka haɗa ƙarfin daya rage musu waje guda suka matse hannayen juna.
        A gefensu Maanal ce ta kai baki kusa da kunnen Ameerah dake gefenta ta raɗa mata wani abu. Ameerah ta jinjina kanta tana share nata hawayen. Hannuwa suka cika da ƙasa cikin dabara, cikin bushewar zuciya Maanal tace, “Kai tsinannen Sille ubanka Junaid Mabera”.
     A wani mugun fusace Sille da a duniya babu abinda ya tsana irin ka zagar masa uba ya juyo. Kawai suka ambula masa ƙasa akan fuska harma da idanun wasu a yaransu musamman na kusa da su. A bazata sai cikin idanunsa daya zazzaro dan fusatar zagin da sukai masa. Wani irin ihu Sille ya saki dan abin yazo masa a bazata, hakama yaransa da ƙasar ta shigarma idanu duk sun saki bindigu a ƙasa. Bindigar hannunsa ta shima faɗi. Yay taga-taga zai faɗi hakan dai-dai da miƙewar su AA tsaye kawai suka saka ƙafafu suka taɗesa ƙasa suka take, yanda kuka san ragon layya ko sa mai gardama haka akai masa...
    (🤣🤣kuyi haƙuri wlhy dai gurin nan dariya ya bani 😆😂🤌).
        A gigice Mabera dake ɗan nesa da su bindigarsa akan Abah yayo baya saboda ihun Sille, hakama su Oum da su Nuratu duk miƙewa sukai suna kallon su Maanal da su AA ɗin, dan tuni Ameerah ta jefa ma su AA bindigar Sille data faɗi. Mabera na isowa Babban Yaya na ɗora bindigar akan kunnen Sille. Yaransu suma suka ɗana kunamin bindigunsu akan su Maanal. A kausashe AA yace ma Mabera, “Kuna motsawa zamu tarwatsa kansa wlhy. ALADEN banza. Kai ka isa kace zaka sake barin nan da mu ne. Wawa matsoraci, ai da ka isa ɗan iska da bakai mana wannan allurar ba kaga a maimakon Ragunan layyar mu idan bamu maidaka RAGON LAYYAR ba tun a gidanmu.”
        “Amma kun san zan iya kashe ubanku ko? Yarana zasu iya kashe kaf iyalanku”.
     Mabera ya faɗa a fusace yana sake danna bindigar hannunsa akan Abah.
     Cikin bushewar zuciya Ameerah ta ce, “Mun sallama rayukanmu indai a kansu ne.”
     Manaal tace, “Tabbas Ameerah idan sun isa su kashe mu ɗin?”.
        Najma ta ce, “Wannan haka yake ku kashemu mi kuke jira ne karnuka”.
      A fusace shima Yaya Fawzan ya amsa masa da, “Ai sai dai ayi MAJA kuwa, dan muma za mu kashe wannan TSINANNEN da kai kanka!!”.
        Babban Yaya ya wani ja kunamar bindigar cike da ƙwarewa ya sake ɗanata dan ya iya harbi sarai, kai su dukansu ma babu wanda bai kowa ba a zamansu turai. Cikin ihu da hargagi na firgita, Mabera ya ce, “Stoppp!!!”. Yana ɗagama yaransu dake shirin harbi hannu
      “Oh kace kai ɗan iska ne”.
  Cewar AA dake kallon yaran Maberan da ke zagaye da su da bindigu suna ja da baya. Sai da ya gama ƙirgesu tas da ido sannan ya maida idonsa akan Mabera. “Idan kana son rayuwar wannan JAKIN ɗan naka waɗan nan ƴan iskan su ajiye bindugunsu. Kaima kuma ka saki mana Abah”.
     “Anƙi ayi hakan.....”
  “Please Baa! Su ajiye su ajiya idona wlhy bana ganin komai. Ka sakar musu ubansu su sakeni Baa!”.
        “Baka da hankali Son, kasan wanene Darma kuwa? Ko kana tunanin ƴaƴansa ba jininsa ne ke yawo a jikinsu ba duk da waccan tsinanniyar ce ta haifesu”. Yay maganar yana kallon Mamy da azabar ciwon ido ta sakata nutsuwa waje guda. Ya cigaba da faɗin, “Bakaga shegiyar yarinyar nan data ambula maka ƙasa a ido rainonta kawai sukayi ba amma idanunta a bushe suke like soyayyar gyaɗar ƙauye”.
        Baki Maanal ta murguɗa masa, taja

184 / 213

Chapters