Author : Bilyn Abdull Category : Romance
cikin bedroom. Ya zauna tare da zaunar da ita a jikinsa yana kai yatsunsa biyu akan goshinta.
Hannun nasa ta ture tana faɗin, “Nace maka banda lafiya ne?”.
“Besty alamomin hakan na gani a tare dake. Wannan dariya ai batai kama data lafiya ba sam.”
“Uhm bazaka ganeba Besty. Najma da Ameerah ne suka ban dariya wlhy. Kaga idanunsu kuwa kwale-kwale Najma harda hawaye wai Yaya Fawzan yace ta shirya Ba ɗaga ƙafa....”
AA yaji gulma ya ce, “To shirin mi kuma kamar masu tafiya yaƙi”.
Labari kaf Maanal ta kwashe ta bashi yanda sukai da su Najma. Sai ga AA yana dariyar shima. Ya ce, “Ai Yaya Fawzan da kike ganinsa nan A ɗin kansa ne. Amma Besty wannan ai dariyar mugunta ce”.
“Ramawa nayi ai, dan baka san irin sherin da Najma ta dinga min ta waya ba ne. Ameerah ko idan Mommy (Hajiya Shuwa) tazo sakani a ruwan zafin nan biyota take dan kawai ta tsokaneni, har gwada irin yanda nake tafiya takeyi. Ai bamma yi musu komai ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu. ALLAH yasa shima Babban Yaya kada ya ƙyale Ameerah”.
Murmushi AA yay yana girgiza kansa. Sai kuma ya sumbaci lips ɗinta da yay ƙyau sosai. Tasan ma ƙarshen zancen, dan haka ta tura masa lips ɗin ta ce, “Nama san bazaka barmin ba shanye kawai”.
Kanta ya dungure da faɗin, “ALLAH kinga wajen barci na. To na bar miki yau”....
★★
Sosai aka shirya wajen lunch ɗin yay matuƙar ƙyau. Maza na dawowa sallar azhar aka fara kwasar mutane. Dan ba'a son ai African time sam. AA ya ɗauki babban Yaya da Amarya Ameerah, Maanal na kusa da shi. Dan haka Babban Yaya ya kama kansa, ya dai riƙe hannun Ameerah shima ta yanda su AA ɗin bazasu lura ba. Fawzan kuma RK ne, shima Nuwaira a kusa da shi. Nan kam babu kunya Najma na shigowa Fawzan ya rungume abarsa, sai da Nuwaira zata shigo ya saketa amma hannunta na cikin nashi. RK na son yin tsokana dole ya shanye saboda dai Najma ƴa ce, ai da kunya a raka baƙo ya ruga ko. Ameer ma wani cousin ɗinsa ne ya ɗaukesu shi da Maimoon ɗinsa. Shi kam ai sai da ya shanye lipstick dinta tas ya samu natsuwa. Cousin ɗin nasa nata dariya da faɗin, “Ɗan iska a gabanmu babu kunya”.
Ameer yace, “In kunji haushi ku ƙaro kuma ko Baby”. Yay maganar yana rungume Maimoon a jikinsa. Ita dai kunyar duniya ta isheta sai faman sinne kai take. Dan abu ne da bata saba da shi ba sai dai ta gani a film. Duk da kasancewar family ɗinsu ana karatu mai zurfi iyayensu tsaye suke akan tarbiyyarsu, dan ko namijin family ɗin Darma sai dai yayi iskanci a ɓoye amma wane mutum. Balle su mata da dukkan motsinsu akan idon iyaye da yayye da kawunnai yake.
A mota su Maanal suka bar su babban Yaya, sai lokacin ya rungume Ameerah a jikinsa. Ajiyar zuciya suka saki a tare. Murya a ƙasan maƙoshi ya gwargwaɗa mata abu a kunne. Kunya ce tai wani irin baibaiyeta. Dole ta cusa kanta a ƙirjinsa tana murmushi. Shima murmushin yake yi zuciyarsa da jikinsa na masa wani irin sanyi ƙalau. Bai saketa ba sai da akai knocking glass ɗin. A hankali ta zame jikinta da maida kanta gefe shi kuma ta gyara zamansa kamar komai bai faru ba. Uncle Najeeb ne, ya duƙo suka ɗanyi magana...
Acan ma dai Fawzan su RK na fita ga matse Najma. Dan shi yanayin da yake ciki kam ba'a magana. Abinka da ba'a saba samu available ba sai ansha dambe da Hajiya Nibras😂. Ita ko Najma gata a tsorace amma soyayya bata barinta yin musu. Dan haka yake samun na morewa yanda ya kamata. Sai da aka gama kimtsa komai sannan suka fito. An musu rakkiya ciki har wajen zamansu da aka tsara yanda ya kamata. Babban Yaya da Yaya Fawzan a gefe da gefe kowanne da amaryarsa, sai Ameer a tsakkiya da tashi amaryar shima. Kowannensu akwai tazara tsakanin kujerun zaman nasu dan har flowers ma aka saka. Sosai tsarin yayi yanda ya kamata. Iyaye da ƴaƴa, abokai suma nasu zaman duk a tsare. Dan ɓangaren iyaye mata daban, hakama maza daban, ƴammata daban, yara daban, samari daban. Sai aka saka masu aure a tsakkiya da matayensu irinsu AA kenan. Wajen ya ƙayatu ya kuma tara jama'a yanda ya kamata, abinka da auren mutum shida. Damma family ɗin ya kasance ɓangare biyu ne kawai. Sai dai kowa nada dangin uba dana uwa. Akwai abokai, akwai abokan aiki, akwai gayyar soɗi. To mudai ni da mutane na kowa yasan ba gayyar soɗi ba ne🙄, saura naji wani yace mana ina zamu biki, ina muka fito biki☹️😏 dan yau duk inda ka juya sai ka gammu yan discussion house da ƴan Arewabooks😌. Kai ƴan bati zamu biya acan ma fa harda su duk tare muke a wajen bikin, dan sun ce wannan karon baza'a ci amanarsu a barsu a baya da jin labari a bayan fage ba😆. Niko nace duk suzo addu'a muke musu suma ALLAH ya shiryesu ya basu halin girma su daina tarama kansu hakkin kowa kodan suma ALLAH ya tsare musu nasu kasuwancin, inba haka ba ƴan bashi su baibayesu kuɗaɗe suƙi fita🥱........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣1️⃣
______________
.......An fara gudanar da addu'a ga ma'auratan sannan aka fara abinda ya tara mutane. Biki ne irin na masu aji, babu hayaniya babu tarzoma babu juye kaji da lemuka a jaka. Komai yana tafiya a nutse kuma cike da armashi. Mawaƙa sunyi wasa yanda ya kamata. An kumaci an sha an gode ALLAH. Amare sunsha liƙi suda anguna. Dan Ameer da Yaya Fawzan sunsha rawa, babban Yaya ne dai baima miƙe ba. Amma sai da AA ya bishi har wajen zamansa ya liƙeshi da dollers (😌ato dan mu novel ne sai munyi liƙinmu, karnaji wata tace an hana liƙi a Nigeria mu Ramadhan B Hameed Taura ne shugaban ƙasarmu anan ba Tunbunu ba🤭 kuma yace muyi kayanmu yanda muke so, ko Tunbunu ya zama kuɗi sai mun liƙa shi ehe😜🤫). Ba ƙaramin wasa da kuɗi akai ba a wajen nan. Maanal da AA kamar basu san ciwon dollers ba. Yanda yake zarosu a aljihu haka take zira hannu a aljihunsa itama ta zaro ta farke. Hatta Oum da Ammie haka ta bisu har inda suke tai musu liƙi, AA ya tayata kuwa. Takaici kamar zai kashe su Hajiya Basariyya kuwa, sai dai babu damar magana sai tsaki a zuciya. Dama kuma Maanal dansu tayi hakan ƴar ƙunar baƙin waken🤣. Saƙonta kuma ya isa yanda ya kamata.
Kuce min ina Nibras da Saheeba manyan mata. Suna gida abinsu basu zo ba. Duk da Saheeba tayi niyyar zuwa dan ita irin mutanen nan ne dako abu na ƙona musu zuciya sun fi son sugani ƙuryanan-ƙuryanan (Inji Ayshatu ɗan Kano😆 ALLAH ya gafarta mata da iyayenmu baki ɗaya 😭🙏). Sai da Hajiya Turai ta tsawatar mata sannan ta haƙura. Mamy ma dai yau bata zo ba. Dan abubuwan sun fara kwace mata ta tabbatar zata iya tonama kanta asiri a wajen. Maman Saheeba da Nuratu ma dai yau da yake abun su aka taɓa basu zo ba, suna tare da Saheeba sunata ƙullawa da kwancenwa a gida...
Alhamdullahi biki ya ƙayatar yanda ya kamata. Ba'a gajiyar da kowa ba ba'a takura kowa ba. Anguna da amare sun zuba capacity yanda ya kamata. Kafin kace mi wannan shagali ya zama on topic na wannan rana. Tako ina shike kai kawo a yanar gizo. Ƙarfe huɗu aka tashi, mazan ne kuma suka fara fita domin yo salla. Sai da suka dawo aka fara kwasar mutane zuwa gida. Matan ma na zuwa babu zama kowa burinsa ya sauke sallar. Manaal tunda ta idar take gyangyaɗi, amma ta daure dan tace yau ko mima za'ayi bazata kwanta ba sai anyi buɗar kai da ita. Aiko taga buɗar kai dan taci wuya. Ciwon kai har jiri ke kwasarta dan masifa ta dai dage sai da akai buɗar kan nan da ita. Yanda ta sakama Najma da Ameerah kuɗi har sai da ya zama abin magana a dangin Mamy. Al'amarin kam ya girgiza Mamyn matuƙa. Har sai da ta kasa dannewa ta ɗura zagi da faɗin ai Ajwaad ɗin zaizo ya sameta ne dan tasan daga aljihunsa kuɗin ya fito, dama yan uwan nata nata hirar irin ɓarnar kuɗin da AA ɗin sukai shi da Maanal a wajen taron. ALLAH sarki, sai dai abinda Mamy bata sani ba a kuɗin da Maanal tabada na buɗar kan su Ameerah sisin AA babu. Tana da kuɗaɗen ta na kyaututtukan da ta samu a bikinta account shaƙe, a hakama taba Ammie da yawa, dan bayan bikinta sai da ta turama Ammie, ta turama Didi Shahidah da Amaal harda su Waleed. Hatta Nene da ƴaƴanta kowa sai da ta bashi, kai har su Zeezah ƙawayenta bata manta da su ba da Amrah. Wanda suka rage kuma ba wani abu take saya ba, daidai da katin waya wannan da data Babban Yaya, Yaya Fawzan, AA duk saka mata suke. Sai dai kawai taga an turo mata.
Hajiya Basariyya kanta sai da taji kamar ta zauna taita kuka. Dan jitai kamar sun rako mata duniya yau sukam, ƴar yarinya ƙarama take irin wannan ƙyautar babu ko gezau. To oho dai, sudai dangin Darma sunji daɗin halin girma da Maanal ɗin ta nuna ƙwarai da gaske. Ana gama buɗar kan su Ameerah aka shiga gidan Hajiya Shuwa akai na Maimoon. Suma sunyi rawar gani dan kowa yasan katsinawa da kara. A wajen gara da baye ba'a magana sun wuce tsara. Darma Family sun shaida hakan kuwa yau, dan gaskiya su Hajiya Shuwa suma sunyi ƙoƙari kamar yanda suma akai musu ƙoƙari akan na Maimoon.
To aifa da kama-kama su Amaal suka kai Maanal sashenta dan juwa take gani matuƙa. Hankalin AA ya tashi sai da ya kira RK ya dubata. Oum ma nata faɗa, dan dama gaba ɗaya hankalinta ya rabu biyu wani akan buɗar kan wani akan Maanal dan tasan wannan rashin kwanciyar zata iya zame mata damuwa. Ita kanta Ammie data san yanayin duk inda Maanal ɗin tayi idonta na kanta. Daga baya kuma ta ɓace mata. RK yace su kwantar da hankalinsu da tayi barci zata tashi normal, rashin yin barcin ne ya kawo mata juwar. Dan haka yace AA ya taimaka mata tai salla tai wanka dan inta kwanta da wuya ta tashi a kusa maybe sai asuba. Haka ɗin kuwa akayi, bayan fitowarsu da kansa yay mata wankan, tai sallar daga zaune ya bata fresh milk ɗin tata ta fama tasha sosai. Shi kansa bai ƙara leƙa wajen ba tunda ya dawo daga sallar isha'i. Kajin da yay niyyar fita siyoma su babban Yaya sai order yayi, da'aka kawo ya fita ya amsa ya danƙama RK, dan yace babu shi a ƴan rakkiya. Na su Oum da suma ya saya musu yaje yakai musu ita da Ammie, itama Mamy ya aika mata ya wuce sashensa. Aiki yay zaman yi a kan gadon kusa da Maanal dake barci mai nauyi sosai. Lokaci-lokaci yana kallonta, musamman idan taja numfashi. Dan ƙwaƙwƙwaran motsi dai batayi. Dariyar data dingayi ɗazun ta mugunta ta shiga faɗo masa a rai sai yayta murmushi. Wayarsa ya ɗauka ya rubuta saƙo ya turama Yaya Fawzan yana cizar lips...
_______★
A ɓangaren anguna su Babban Yaya kamar yanda aka saba su Baba Sardauna sun zaunar dasu sun musu nasiha mai girma da nuna musu bambanci auren farko dana yanzu. Da a baya hakkin matan nasu ɗaɗɗaya ne a kansu. A yanzu kam su biyu ne. Nuna rashin adalci ko rinjaye a ɓangare ɗaya babban damuwace a rayuwarsu ta duniya da lahira. Dole ne su zama jarumai wajen tsayawa akan ƙafafunsu matsayin mazan ƙwarai a tsakanin matan nasu. Su zama masu adalci, kuma masu haƙuri da juriya dan ajiye mace fiye da ɗaya bana rago bane. Maza da yawa sukan ɗauka jarumtar ajiye mace fiye da ɗaya a shimfiɗane kawai, sai dai ba haka bane ba, wannan ma idan da hali a kallesa a matsayin matakin ƙarshe shine yafi dacewa a zamantakewar jarumtar. Idan ba haka ba kana nan kana hura hanci kai soja a gado ka tara mata huɗu, uku, ko biyu, amma kanata ginama kanka ƙofar shiga jahannama sakamakon kasa banbance hakkin daya kamata ka sauke da ruɗin duniya. Shi aure ibada ne, komai dake cikinsa kuma shine tubalin gina ibadar. Gwarzon namiji nutsuwa yake ya gina ganuwar adalci a cikin iyalansa da kewayansu, ba yazama shashasha mai tauye wata ya ƙuntatama wata ba. Karka wulakanta matarka ta farko dan ka ƙara aure, kar kuma ka wulaƙanta wadda ka aure daga baya saboda wai uwargida. Kalmar uwargida da amarya kalmace ta al'ada. Addini yana kallonsu ne da sunan matanka ne kawai. Kuma kowacce tana da hakkin a kanka da in ka gagara saukewa tofa ka shirya amsar sakamako a inda ba'a neman yafiya, ba kuma akarɓar tuba dan lokaci ya gama ƙurewa.
Daga ƙarshe sukai musu addu'a sosai mai kuma ratsa jiki da ɓargo kafin suka sallamesu. Suna fitowa Babban Yaya ya gudu. Dariya su Uncle Najeeb suka sanya. Dama shi da Uncle Sulaiman Yayan RK ne masu rakkiyar tasa. Yaya Fawzan kawai akama rakkiya, babu kowa a sashen kuwa ta ɓangaren Najma dai, Ammie da kanta ta tattarosu, wasu suka koma sashen Maanal wasu suka zo nan sashen Oum. Itama Nibras ɗin kasancewar duk ƴan gari ne wanda ke tare da ita sun ware. Sai mutum biyu a tare da ita da Mommynta tace su zauna su kwana. Dan ana gama buɗar kai sai Nibras ɗin ta tsinta kanta a wani irin tashin hankali tanata kuka. Zuwa yanzu dai ta tabbatar da bata samu AA ɗin ba, shima Fawzan ɗin ya ƙaro mata wata. Gashi baya ɓoye farin cikin da yake ciki ko kaɗan.
Yanzu ma tana jin hayaniyar ƴar rakkiyar Fawzan ɗin jikinta ya kama rawa. Bayi ta afka ta jingina da kofa ta fashe da kuka...
To shi dai ango baima san tana yi ba, sun isoko amarya Najma ne a ɗaki zaune a bakin gado kanta rufe a cikin lafaya.. Kasancewar su daga kawunnai sai yayye aiko tuni kowa ya kame girmansa akai mata nutsatstsiyar nasiha, ita dai tanata hawaye kanta a cikin mayafi bata ganinsu. Sai dai tana jin ƙamshin turaren Yaya Fawzan matuƙa a hancinta dan yana zaune ne a kusa da ita. Basu wani jimaba sukai musu sallama suka fice. Yaya Fawzan bai ma motsa ba balle su saka ran rakkiya. Dai-dai sun gama ficewar saƙon AA ya shigo masa a waya. Fasa maganar da yay niyyar yima Najma yayi ya ɗauka wayar yana dubawa.
_(Ka bimin ƙanwa a hankali dan ALLAH Yaya Fawzan, karkace zaka rama abinda naima taka ƙanwar tsautsayi ne. Idan ba hakaba sai dai a rabamu a DSS office gaskiya da safe. A huta gajiya angon Najma)_
Murmushi Yaya Fawzan ya saki mai nauyi, sai kuma ya cije lips yana girgiza kai. Wato tunda Autan nasu fa ya shiga daga ciki bakinsa ya buɗe. Har mamaki yake idan yaji Ajwaad na zaro magana sai yaga kamar bashi ba. Ƴar gyaran murya yay yana ajiye wayar, cike da raɗa ya ce, “Amarsu baza'a buɗen fuskarba?”........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣2️⃣
______________
.......Shiru Najma tai taƙi motsawa, sai yay murmushi, tare da kama lafayar ya yaye gaba ɗaya. Ganin hawaye share-share a fuskarta ya ce, “Oh oh kukan dai har yanzu bai isa ba ƙanwar Yaya Fawzan”. Sai ya jawota jikinsa kawai ya rungume. Kamar jira take sai ta sake sakar masa kukan. Shiru yay yana shafa bayanta a hankali, a cikin kunenta ya ce, “Kodai nima na tayaki muyi kukan kamar ƙyafi saurin gamawa da wuri”.
Ƙwace jikinsata ta shiga ƙoƙarin yi tana ɗan kai masa dukan wasa a ƙirji kaɗan-kaɗan, ya sanya dariya yana ƙoƙarin riƙe hannun, kafin ya kaita kwance ya rufu a kanta yana bin fuskar tata da wani narkakken kallo. Baki ta tura masa. Ya ɗan ja lips ɗin kaɗan da faɗin, “Na tayaki kukan muyi saurin gamawa?”.
Kanta ta girgiza masa.
Ya ce, “To kema daina in gani”.
Hawayen ta shiga sharewa da lafayar, sai da ta goge su tas ya ce, “Inyeee kaga amaryar Fawzan, kinfa daina kukan da gaske dama lallashina ake jira kenan”.
Murmushi ya suɓucema Najma. Ta kauda fuskarta gefe tanayi. Shima murmushin yake mai ƙayatarwa, kafin ya maido fuskar tata suna kallon juna. Lips ɗinta ya ɗan sumbata tare da faɗin, “Karna ƙara ganin hawayen nan kinji ko. ALLAH yay miki albarka. Ya bamu zaman lafiya, ALLAH yasa yau mu samo Baby mai kama dake ƴar mutan Zaria”.
Hannu tasa ta rufe fuskar ta da faɗin,